Showing 321001 words to 324000 words out of 325075 words
ya basu mamaki anan ma sai akai musu tarba ta mutunci da kulawa. Hakan yasa suka sakeji a ransu lallai hausawa nada ?ya?y?yawar zuciya a duk inda suke. Sannan musulmai ba mutanen banza bane kamar yanda a kullum papa ke musu hu?uba a gida da church. Sai gashi tundai suna ?ari-?ari har suka saki jikinsu. Bayan Jay ya dawo suka zauna aka ?ara tattaunawa. Mama debora da su Momy Destiny sunsha kuka. Su kansu su Joy sunji ciwo da kunyar halayen iyayen nasu matu?a. Sunata kuka da bama Yoohan ha?uri. Shi dai murmushi kawai yake musu. Nu'aymah ma ha?uri sukaita bata akan abinda sukai mata. Tace babu komai ita ta yafe musu. Gebrail kam ko yarda su ha?a ido Aymah baya yarda suyi sam saboda kunya. Ita har dariyama abin ke bata.
____________
Ranar data kasance za'a shiga kotu da su papa ?an jarida a abuja har bama magana. Kowa burinsa ayi komai akan idonsa. Kuma burin kowa ya nuna komai live. wannan kuwa duk a cikin shirin su Jay ne. Sun gayyato ?an jaridune ta kowanne ?angare dansu katange dukma wata kitumurmura da za'a iya ?ullawa game da shari'ar.
Kotu ta cika ma?il itama da al'umma, musamman wa?anda aka samu ?a?ansu a gidan papa. Duk da ma wasu iyayen nasu sun gagara ganesu, sukuma basusan daga inda aka ?akkosu ba dan tun suna ?anana ne. Shari'a ce da bata bu?atar lauya sam, saboda komai na papa a bayyane yake. Zamane kawai da za'ai maganar ?arajin abinda ya shuka a yanke hukunci kuma.
Yoohan dai da farko baiso su Gebrail su bisu ba. Amma sai Uncle Jay yace ya barsu suje ?in dan wannan itace ka?ai damar da zasu samu ganawa da iyayen nasu. Badan yasoba kuwa suka shirya suka tafi kotun, cikin amincin ALLAH kuwa sun sami gaba-gaba saboda sun tafi da wuri.
Sai da kotu ta gama cika tab da al'umma, al?ali ya shigo sannan aka shigo da papa da su Mike. Papa saboda harbin da yasha a kafafu sai a wheelchair, sauran kuwa babu ko ?warzanen duka a jikinsu amma a ido zaka gansu a wani irin bala'in galabaice. Su Jay ka?ai sukasan irin horon da sukema rayuwarsu cikin hikima. Bayan buga gudumar al?ali kotu tayi tsitt na wasu mintuna, dan da anata ?an kananun magana saboda shigo da su papa da akayi.
Al?ali ya sakeyin gyaran murya sannan ya fara magana, "Wannan shari'a ce da kowa zai iya fahimtar bata bu?atar wani kaiwa da komawa balle zaman lauyoyi a tsakani. Dan komai a bayyane yake wa duniya akan masu laifin. Amma duk da haka dolene mu karanto musu laifinsu su amsa kafin mu yanke hukunci". Bai jira amsar kowaba dan ba ita yake jiraba daman. ya bama jami'an tsaro damarsu. Dawood ne ya mi?e ?auke da file ?in dukkan bayanan laifukan Papa ya kai ga al?ali. Batare da al?ali ya amsaba ya bashi damar karanto komai.
Tsayuwa Dawood ya gyara yana fuskantar su papa. Ya fara bayani dalla-dalla. a duk ga?ar da yazo ?arshe al?ali zai ma su papa tambaya akan shin hakane sun aikata?. sukan ?an nuna tirjiya kafin papan ya tabbatar da sun aikata ?in. A haka aka dinga bin duk laifukansu daki-daki tare da shedun da suka gani da ido wajen tabbatarwa. Hakanne yaja shari'ar tai tsaho sosai aka jima ba'a tashiba.
?ara jin bayanan sai ya ?ara komawa mutane tamkar sabo a cikin kunne, wasu harda hawaye sukeyi, wasu ko kawai gani suke babu hukuncin da su papa suka dace dashi sai mutuwa. Da ?yar Al?ali ya samu kotun nan ta lafa da ga hayaniyar data ?auka akan cecekucen jama'a. Ya ?auki ruwan dake a gabansa ya sha cike dajin gajiya da damewar tunani wajen yanke wannan hukunci.
Bayan kotu ta sake lafawa al?ali ya fara magana kamar haka, "Ya kamata kuyi hakuri ku bamu ha?in kai, nasan duk wani hukunci da zamu yanke anan bai zama lallai ya gamsar da wa?anda wannan mutane suka cutarba. Amma zamuyi iya bakin ?o?arin mu dan ganin mun yima kowa adalci. Sun tafka kura kurai da kowanne idan zamu ?auka yanada nashi hukuncin ne, to amma kisan kai da suka shigo sun shanye duk wani laifuka nasu. ALLAH ka?ai yasan iya rayukan da suka salwantar, dan kosu a yanzu ba iya lissafawa zasuyi ba. Dan haka wannan kotu mai adalci, ta yankema wa?anan mutane hukuncin kisa ta hanyar rataya". Yana gama fa?a ya doka gudumarsa.
A take kotun ta ?auki ihun kace nace ?in mutane. Har bakajin zancen wani. Sai dai duk wannan surutai babu mai goyen bayan su papa. Wasuma duk da an ambaci kashesun za'ayi su hukuncin sai bai musu ba. a ganinsu ayi gunduwa-gunduwa da su kamar shine yafi dacewama kowa ya huta. Kamar yanda kotu ke a harmutse haka jama'ar gari ke a harmutse dan ?an jaridu nata kai rahoto live. A take duniya gaba ?aya ta ?auka. Inda wasu ?ungiyoyi kamar Masu kare ha??in ?an adam suka fito suka nuna bore da wannan hukunci. Har suna i?irarin ?aukaka ?ara. Sai dai to bamusan zuwa wane kotu suke da burin ?arar ta kaiba, tunda mudai anan Nigeria a babbar kotun ?asa gaba ?aya aka yanke hukuncin.
Duk yanda Yoohan yaso su mama debora su gana da Papa al'amarin ya gagara dan da ?yarma aka fiddasu daga cikin kotun.
______________¡ï¡ï
Bayan kwanaki biyu da faruwar wannan al'amari da safe su Jay na tsaka da yin breakfast ya samu waya daga al?ali cewar sufa sun gama yanke hukuncin su papa. Dan sun fuskanci al'amarin neman canja salo yakeyi na ?ir?irar rikici da hukumar kare ha??in ?an adam ke neman haddasa musu. A yanzu haka maganar da ake ga gawarwakin su papa nan, a gaban ?an jarida akai komi yanzu kuma zasu bada damar a saki labarin.
Al-amarin ya girgiza zuciyar Jay matu?a, to amma shima hakan yafi masa sau?i tunda dai shine hukuncin da aka yanke musu a gaban kowa. Koda sukai sallama da shugaban al?alai bai iya yima su Yoohan bayanin abinda ya faruba sai Miemaa kawai. Ita kanta duk da tasan su papa masu laifi ne sai da tausayin mama debora ya ?ara kamata da su Victoria. To amma wannan shine dai-dai kuma abinda ya dace..
Kafin shabiyun rana labari ya gama zagaye ?asar dama duniya akan zartar da hukuncin da aka yankema su papa. Wasu kam sun ?auki ?umi akan hakan, dan duk da mummunan halin su papa suna samun magoya baya musamman masu irin halayyarsu da ayyukansu. To andai yita ta ?are. labarin su papa kuma ya zama tarihi, sai kuma na baya garesu, dan yanda mutane. kirki basa ?arewa hakama mutanen banza kullum sake yawaita suke.
Mama debora dai tasha kuka a ?oye, dan ?a da mahaifi sai ALLAH, musamman daya kasance mazan ?a?anta har uku. To amma tunda ta rasa mahaifin Yoohan da yafi sonta da ?yautata mata tai ha?uri, dan ta rasa wa?anan azzaluman minene zaisa ta takura kanta kuma. Su Joy ma dai saida suka koka sosai. danma an hana Abraham da Victoria kallo sam.
Yoohan kansa sai da yay hawaye, koba komai yasan su ?in jininsa ne. Nu'aymah ce kawai ta iya fahimtar shima kukan yayi, dan haka tana ganin ya fita itama ta bisa a sace ta ?ofar kitchen. Acan baya ta hangosa tsaye ya jingina da bango yay shiru idanu a lumshe. ?arasawa tai garesa ta kamo hannunsa cikin nata. Kusan a tare duk suka sauke ajiyar zuciya. Batare da yace da ita komaiba ya jawota jikinsa ya rungume. Luf kuwa tayi kusan mintuna uku sannan ya ?agota yana murmushi. Kafin yay magana tace, "Silly boy! Kuka kakema wa?anda suka kashe mana su Abbabmu saboda son zuciya".
A karon farko ya saki murmushi da shafa fuskarta. Murya a raunane yace, "Silly girl! Kin samin ido da yawa fa".
Dariya tayi ka?an ta kwantar da hankali, sannan ta ?an marairaice fuska cike da kulawa tace, "Sai ha?uri Yah Maleek, haka rayuwa take, wani farkonsa yaji da?i ?arshen yasha wahala. Wani yasha wahala a ?arshe yaji da?i koba a duniyaba. Kaji labarin gwagwarmayar da Uncle Jay yasha shima shi da Miemaa. Amma bagasu komai ya wuce a garesuba tamkarma bai faru ba. Muma idan mukai ha?uri sai kaga komai ya zama tarihi insha ALLAH ".
Cike da jin da?i ya sake rungumeta da sumbatar la??anta. Ya lumshe idanunsa ya sake bu?ewa a kanta. "Thanks you Zeeynab. Kin gama bama rayuwata dukkan abinda take bu?ata, ALLAH yay miki albarka ya albarkaci Deen, ALLAH yasa ya zama mai gadon baba malam. ALLAH ya gafartama iyayenmu ya ?ara mana ha?uri da abinda ?addara ta dan?a mana a tafin hannunmu".
"Amin ya rabbi yah maleek".
Sake rungumota yay jikinsa yana dariya ?asa-?asa da fadin, "Sunan nan fa yayi da?i Sweet girl".
"Sosai ma, Mami da Abba sun iya za?en suna. Kaga yanzu ka zama mai suna biyu, danni kam daga yau Abdul-maleek zanke fa?a".
"Silly girl! ki rage jan fa?a yanzu akwai Deen a gabanki". Ya fa?a yana jan hancinta.
A tare suka sanya dariya, suna maijin farin ciki mai yawa a ransu.
A daren ranar kuma sai ga sa?on rasuwar Addah ya samesu. Duk da abinda ta tafkama rayuwarsu Nu'aymah sai da taji duk ta rikice. Tasha kuka kuma a daren ranar. Washe gari kuwa tunda safe suka ?auki hanyar kano a mota harda su Jay, cikin sa'a kuwa suka samu jana'izar Addah, dan sai goma aka kaita masaukinta na gaskiya. Sai kuma aje a girba abinda aka shuka.
Duk da abinda Addah taima Umm rasuwarta tayi masifar girgizata, dan saida takai an saka mata ?arin ruwan daya sakata dogon barci saboda ru?anin data shiga. Jikin kowa ya ?ara sanyi kuma a agidan harma da sauran ?an uwa.
Da yamma su Yoohan suka koma Abuja aka bar Nu'aymah anan kano, sai bayan anyi addu'a Yoohan yace zaizo ya ?auketa dan zasuje Oman wajen dangin mahaifiyarsa da ?addara ta maida can.
*_BAYAN SATI GUDA_*
Bayan sati ?aya da rasuwar Addah da mutuwar su papa Yoohan yazo da kansa ya ?auki Nu'aymah da Deen suka koma Abuja, zuwa yanzu kuma Alhmdllh Umm ta ?an dake saboda kulawa da baba malam keta bata dan ganin ta samu kwanciyar hankali. Hakama Hajarah daketa fama da tsohon ciki sai Umm ta ro?u mijinta ya barta ta dawo nan gida harta haihu dan itama rasuwar mahaifiyar tata ta ta?ata sosai. Bai musaba ya barta ta dawo, tana nan zaune wajen Umn yanzu haka. Zaman natanema ya ?an ragema Umm ra?a?i. Hajjo kuma koda yaushe takan yawaita shigowa ta sake kwantarma da Umm hankali itama, hakama Ananah da bata komaba.
*_OMAN_*
SU Nu'aymah sun isa Oman lafiya, inda suka sami tarba ga dangin Mami (Anum) dan tunkan zuwansu labarin komai yazo musu. Abin mamaki sai su Yoohan suka sami Dr Shikurah acan Oman, ashe kanwarta datake fa?a ?anta na kama da Yoohan itace ke auren yayan Anum da suke uba ?aya. Sun ha?une acan Oman da taje karatu, a yanzu haka yaransu kusan shidda. Mahboob mai tsananin kamanni da Yoohan shine yaronsu na farko. Idan ka gansu shi da Yoohan saika ?auka tagwayene saboda tsabar kamanni da sukeyi da juna, abin mamaki har tafi har maganarsu iri ?ayane. Sosai abin ya birge Yoohan. Har yaji a ransa inama ya amince tun sanda Dr Shikurah ke masa kamanni da Mahboob ?in ya amince ta kawosa yagansa. To amma ya ?auka hakan kawai matsayin abinda ALLAH bai hukunta ba.
Da yake anzo dasu mama debora suma sai hakan yasaka dangin Anum ?ara jin da?i, dan koba komai sun ?ara yarda IBRAHEEM mutumin kirkine shi. Ansha kuka da tunawa da rasuwarsu da yanda rasuwar tazo. tare da jifan su papa da kalmomin ALLAH wadarai danma ana ?an tagawa darajar mahaifiyarsa dake a wajen.
Deen da Nu'aymah kam lallai sunga soyayya ?ar gaske, dan gatan da Yoohan bai samu ga dangin uwaba a yanzu kowa ?o?arin ganin ya nunama Deen yakeyi. Sunga gata kam sun kuma sha da?i Alhmdllh. Satinsu uku cif suka dawo Nigeria badan ?an Oman sunso hakaba.
Suna dawowa kuma aka shiga hidimar bikin Naser & Yusrah, Abdallah aka maida masa Adawiya suje su cigaba da ha?uri da juna. Amal da malam ?arami. Ahmad da Nanah yayar ?anwar Umm. Ansha biki an ra?ashe an ?walle Alhmdllh, yayinda Abban Abdallah ke kwance yana fama da kansa shima. Dan shikam bikinma bazaice yasan anyiba. To dama haka rayuwar take ai.
Bayan an gama biki an mi?a amare ?akunansu komai ya zama Alhmdllh Yoohan ya tattara matarsa da ?an ?ansu da yay ?ul-?ul gwanin sha'awa syuka koma ?asar U.S saboda karatun Aymah, shi kuma zai koma aikinsa na hidima wa al'umma.
Basubar ?asarba sai da ya nemawa su mama debora gida anan kusa da su Uncle Jay aka saya musu, dan mama debora ta rantse bazata sake zama gidan can da papa ya gina ba. Hakan yasa aka saidashi suka dawo nan. Gebrail da Joy an nema musu makaranta a ghana. Mama debora zata cigaba da zama dasu Victoria dasu mama Destiny da suma suka dawo nan tare da mazajensu. Dan zaman can kauyen kam bazai yuwu yanzu a garesuba.
_____¡ï
Tunda su Nu'aymah suka dawo fa sai ta ?aura ?ammarar dagewa akan karatunta, haka shima Yoohan ya sake dagewa akan neman iliminsa na addini. Ga renon ?an ?ansu daketa ?ara girma masha ALLAH.
Soyayyarsu da sha?uwa kuwa sai abinda yay gaba. Yayinda Hajiya Nu'aymah aketa ?ara canjawa ana hankali da rage fitsara kamar ba itaba. Ga jikinta sai bu?ewa yake tana ?ibarta masha ALLAH.
Haka rayuwa ta ciga da gunguramawa wa?anan bayin ALLAH, yau asha zuma gobe asha ma?aci. Da sun sami hutu sukan shirya suje Nigeria, hakama ?an Nigeria ?in lokaci-lokaci Yoohan kan ?akko wasu a cikinsu suzo su musu hutu.
Daga Deen dai Nu'aymah shiru, da alama kuma dai sune asuka tsarama kansu hakan, dan a yanzu haka ga Deen da shekara ta hu?u, Nu'aymah kuwa na shirin kammala karatunta. Yaro ya girma yay wayau, ga miskilanci ga zuciya ko kuturu haka ya gansa ya bari.
burin Yoohan dama nu'aymah ta kammala karatunta ya tarkatasu ya maida Nigeria, cikin amincin UBANGIJI kuwa sai gashi ta kammala lafiya cike da nasarorin rayuwa. Wannan karon kuwa Umm da baba malam ma sunzo U.S, taso azo da hajjo baba malam yaki dan tsufa sosai ya ?ara kamata, ga ciwon ?afa dake damunta. Kowa ya taya Aymah murna da nasarar data samu daga ita har mijinta, bayan kammala komai suka tattaro zuwa ?asarsu ta haihuwa, inda Yoohan ya saya musu gida suma duk da su Jay sunso Yoohan ?in yay zamansa anan gidansu, amma ya ?i, dan gaskiya yanajin kunyarsu ainun.
?an uwa da abokan arziki sun tayasu murnar gida. Dan ?an kano ma duk saida sukazo, harda su Aunty Kubrah da zuwa yanzu tayi ha?uri a gidan aurenta duk da ba da?in zaman takejiba dai.
A wannan dawowane kuma kowa ya fahimci Nu'aymah laulayin ciki takeyi. Anko tayasu murna da addu'ar ALLAH ya raba lafiya.
Dawowarsu baifi da wata guda ba ALLAH yayma abban Abdallah rasuwa shima. Ansha alhini ansha kuka, daga baya kowa ya rakasa da addu'a.
*_A KWANA A TASHI_*
Lallai kam akwana atashi babu wahala wajen UBANGIJI, dan yanzu shekarun Auren Nu'aymah da Yoohan goma kenan. Zuwa yanzu ALLAH ya azurtasu da ?a?a uku, Deen, Ibrahim, sai auta Anum. Jay ne ya hana a ?oye sunan yaran, yace a bari ake kiransu da sunansu hakan zaisashi farin ciki. Dan haka aka barsu kuwa da sunayensu ana kiransu da shi.
Abubuwa da dama kam sun faru a wa?annan shekaru, masu da?i da akasin hakan sai dai kawai muce Alhmdllhi ala kulli halin.
*_"Sweet girl! Sweet girl!!"_*
Nu'aymah da ke a can backyard tana shanya kayan su Anum data wanke tana mita ta jiyo Yoohan na ?wala mata kiran mafarauta. Kanta ta dafe dan ta tabbatar su Anum ne suka hanashi barci. Dawowarsa kenan babu jimawa daga asibiti a gajiye matu?a. Sabodama kar yaran su gansa su hanashi hutawa a wajen gate yay fakin, ya shigo gidan a sa?a?e saima yay sa'a su suna a can garden suna wasa Nu'aymah ta korasu itama ta huta. Shiyyasa itakam batama cika son weekend tai musu a gidanba. Tafi bu?atar su wuce gidan Uncle jay ko gidan Aunty Little ko wajen su maman Destiny.
Jin ya cigaba da ?wala mata kiran yasa ta ajiye abin matse kayan dake a hannunta ta nufi ciki da sauri. Ilai kuwa samun duk yaran tayi a bedroom ?insa ?ane-?ane bisa gado kusa da shi kowa na ihun sai ya tashi an kaisa gidan Abie (Jay). Kai Nu'aymah ta dafe sannan ta ?aure fuska ta daka musu tsawa. Tsitt kuwa sukayi kowa na kwa?e fuska.
Sai a lokacin Yoohan ya janye filon daya cusa