Showing 195001 words to 198000 words out of 325075 words
murgu?a tana bu?e ?ofar ta fito. Cikin ?un?uni tace, "Kaima dai nakusa fara kiranka Silly boy ?in nan daka ishi mutan da shi". Ta ?are maganar tana ?arasawa inda yake tsaye yana gyara p-cap ?in da a yanzu itadai ta gansa da ita. Dan da suka fito kansa babu hula. Kallonsa tai ta ?auke kanta, a ranta kuwa tana yaba yanda p-cap ke masa ?yau idan ya sanya. Musamman a yanzu da komai na jikinsa ya kasance ba?i, hularce kawai fara.
"Malama kallon da kikemin ya isheni". Taji maganarsa a bazata. Sai dai yayi gaba kamar bashine ya fa?a ba. Murya ta?an ?aga ka?an yanda zai jita tace, "Kai da wane idon kasan ina kallonka?".
Tsayawa yay tare da juyowa gaba ?ayansa. Ita kuma ta riga da tazo gab da shi sai tai ?o?arin yin baya ganin zasuyi karo. Tako tafi gaba ?ayanta zatasha ?asa. Da sauri ya bita ya tallafo ?ugunta ta dawo jikinsa. A yanda ?irjinta ke bugawa ya tabbatar masa taji tsoron fa?uwar sosai. Samun kansa yay dajin dariya na taho masa. Ya ?anyi kamar zai saketa, tai wani uban tsalle ta mamu?esa zata saki ihu yay azamar danne bakin da ?ayan hannunsa yana kallon yanda tsirarun mutane dake shiga da fita cikin wajen suna kallonsu. Wasu na dariya wasu na gulma.
Idanunsa ya rumtse da sauri yana fa?in, "Shikenan kin tara mana mutane hankalinki ya kwant..." Ai baima kai ?arsheba ta fincike jikinta tana turesa. Sai kuma tai saurin komawa bayansa ta ?uya ganin da gaske kallon nasu akeyi. Gaba ?aya kunya ta dabaibayeta kamar ta nutse ?asa takeji.
"ALLAH ne ya rama min". Ya juya da wani salo yana yin manar a cikin kunnenta kamar bashi ya fa?a ?in ba. Da sauri tabi bayansa tana tura baki gaba. Sai dai da alama bakin tsuwar ya mutu kam.
Kamar yanda ?a'idar shiga wajen take sai da akai bincikesu sannan suka shiga, sai dai yanzu kam a jere suke tafiya gwanin sha'awa. Batare da ya kalleta ba yace, "Mizaki saya?".
"Duka shagon". Ta bashi amsa itama batare data kallesa ba.
Shima da yake ya iya ba?ar maganar sai cewa yay, "Okay sai muje a saidama Shekau ?in da kikace Kano muzo musai shagon da ku?in".
Babu shiri taja birki harda ri?e ?ugu. Shima tsayawar yay ya tura duka hannayensa cikin aljihun yana kallonta fuska a ciskule. "Ai wlhy sai dai a saida garinku, dan kano tafi ?arfin shekau".
"Trouble maker".
Ya fa?a yanayin gaba. Bayansa tabi tana ?un?uni, sai dai bajin abinda take fa?an akeba. A haka suka shiga wajen kayan ?walam da ma?ulashe. Irin kalolin biscuits da kayan ?wa?ayin dataga ya tara a gida yaketa ?iba yanzun ma, hakan yasa ta dinga binsa da kallo kawai tana gulmarsa a cikin zuciya, (wai ma?wa?aici ne??).
Sai da ya kusan cika keken sannan ya kalleta. "Kifa ?eba naki, dan ba ?ara cimin nawa zakiyi ba yarinya". Idan ba ita datasan shine yayi maganarba babu yanda za'ai ace shi yayita. Dan ya ?auke kansa ya cigaba da harkar gabansa.
Le?e Aymah ta ciza, a ranta take raya 'zakaga mugunta kuwa yau ?an balarabe' komawa baya tayi itama ta jawo nata keken. Ta shiga lodar chocolates da kayan ciye-ciye iri-iri. Wanima ko saninsa batayiba balle tasan zaiyi da?i ko bazaiyiba. Saida ta cika kwandon nan dam da kayan ?wa?ayi kawai har tana turawa da ?yar tsabar mugunta. Tana a layin ?arshe zata ?auki wani roban chewing gum taji ?amshin turaren da ya sakata waige-waige da sauri. Cikin kwandon ta jefa chewing gum ?in tai saurin fitowa a lungun tana le?e. Babu ko mai alamarsa, sai dai tabbas wannan ?amshin shi ka?ai ta sani da shi. Duk da zuciyarta na ayyana mata wanine bashi ba ta kasa aminta. Sai ?ara kutsa kai take kowanne layi dan dubashi. Wani irin mugun bugawa ?irjinta yayi jin an ri?o mata hannu. Ta waigo da sauri sai taga Yoohan ne.
"Miye kike nema haka?".
Yay maganar babu wasa a fuskarsa. Sannan muryarsa a kausashe kamar wanda yake cikin fushin da ?acin rai. Kanta ta girgiza masa tana ?o?arin maida ?wallar da suka cika mata ido. Bai sake cemata komaiba yaja hannun nata suka bar wajen. Duk da taga bai maidata wajen kayanta data bariba, ba tai magana ba. A mamakinta saita hangi kayan can wajen bada ku?i ana loda musu a ledoji. Suna isowa matar fuskarta fa?a?e da murmushi tace, "Doctor ATM". Zarowa yay a wallet ya mi?a mata batare da yace komaiba. Ta amsa idanunta akan Nu'aymah dake sake waige-waigen ko zata gansa anan.
"Amaryar Doctor Good evening ". Maganar matar ta maidota hankalinta. A ta?aice ta amsa mata duk da ta fahimci akwai sanayya tsakaninta da Yoohan ?in. Ta ?an dubesa lokacin da ma'aikatan wajen ke kwashe ledojin zasu kai masu mota. Har yanzun fuskarsa babu sau?i. Gashi ya wani ri?e mata hannu gam kamar za'a saceta. ATM ?in ya amsa yaja hannunta suka fita.
A can wajen motar da sukazo taga anata loda kaya harma da wanda bataga sanda aka sayaba ita dai. Batayi magana ba dan bataga fuskaba. Saima bu?e mata murfin yayi yay mata alamar ta shiga. Tana shiga ya maida ?ofar ya rufe mata. Ta mazauninsa ya zagaya, taga ya bu?e lokar motar ya ciri ku?i ya maida ya rufe. Batasan waya bamawa ba, sai dai bai jimaba ya dawo suka fice a wajen.
A lokacin anata kiraye-kirayen sallar magriba. Gudu yake yanzu sosai, kai tsaye anguwar su Abban Abdallah ya nufa. Da?i ya kama Aymah sai dai ta ha?iye abinta a ciki har suka isa. Anata hada-hadar shiga sallar magriba a massallacin ?ofar gidan. Horn ?aya kuwa yayi maigadi dake ?o?arin fitowa zaije salla yay murmushi yana komawa ya bu?e musu. Shiga Yoohan yay da motar har ciki yay fakin Aymah nata mamakin ?arfin halinsa.
"Kije ciki zanje nai salla". Yay maganar yana bu?e motar ya fita. Ai tuni ma ta rigashi fitar. Sai hangota yay ta tsilla da gudu hanyar shiga cikin gidan. Da kallo kawai ya bita harta bu?e ?ofar falon ta shige.
Ya ?an lumshe idanunsa ya bu?e yana nufar hanyar fita gate ?in da hanzari jin za'a tada salla.
Da uban ihu Nu'aymah ta shiga tana ?walama su Amal kira. Aiko kamar jira suma sai gasu da gudun sun fitowa suna ihun murnar ganinta. Momy na salla take jiyo ihun nasu. Sai da sukayi mai isarsu sannan suka sarara. ?akin Amal ?in suka nufa inda Yusrah da Adawiya data?i fitowa suke hutunsu da basusan dalilinsa ba balle ranar komawa kano.
Duk da idon Aymah ya ga Adawiya dake kwance a kan gado tana danna waya sai tai tamkar bata ganta ba ta cigaba da biyema su Yusrah dake mata sherin wai ta canja saboda da?in aure ko sun sami baby ne?. Sha?iyanci sukaitama juna suna she?a dariyar dake sake ?ullar da Adawiya. Dan suma su Amal ?in ta ishesu. Kullum haka take yini a gidan cikin ?acin rai, bata shiga sabgarsu basa shiga tata. Momy tayi fa?an harta gaji ta zuba musu idanu.
Sallar suma sukayi, kafin su idar Adawiya tabar ?akin ta koma falo. Bayan sun idar cikin dabara Aymah take tambayarsu Amal yaushe Yusrah zata tare tunda taga Yah Ab bai koma ba. Da mamaki sosai Amal tace, "Yah Ab ?in da ya koma Saudia tun randa aka ?aura miki aure. Kuma Yusrah ai tace bazata tare a gidansa ba saboda fitinar Adawiya".
Bayanin Amal ya matu?ar ?aure kan Aymah, dan ita dai tabbas-tabbas tanaji a ranta da Yah Ab sukai gamo a inda suka baro. Sai dai batasan dalilinsa na ?oye mata kansa ba. Danne wannan tunanin tayi a zuciyarta ta fuskanci Yusrah datai kamar bataji mi suke magana a kai ba.
"Yusrah! Miyasa ba?ya son zama da Yah Ab wai dan ALLAH?".
Murmushi Yusrah tayi tana ?o?arin mi?ewa daga wajen gaba ?aya, Aymah tai saurin maidata ta zauna. "ALLAH babu inda zakije sai kin amsamin tambaya ta".
"Humm Aymah kenan, ba amsa tambayarki bace mai wahala, hujjar amsata. Ni bancema kowa bana son Yah Ab ba ai. Kawai dai zaman aurene banason yi da shi. Fatan da nakeson muyi ni da ku kawai shine ya maida Adawiya ?akinta. Indan ba hakaba kuwa tsugunne bata ?areba a family ?inmu wlhy. Adawiya na son Yah Ab sosai duk da nasan tabbas Nu'aymah kin fita sonsa. Amma ke yanzun wannan babin ya shafe a gareki dan dama ?addarace tazo muku da wannan yanayin".
"Amma Yusrah......"
"No Aymah karki sake cewa komai dan ALLAH. Mu ajiye wannan maganar haka kawai. Ku tashima muje dan ga kamar momy can ta fito".
Badan Nu'aymah taso ba tai shiru.
A falo kam zaman Adawiya babu jimawa Abba da Yoohan suka shigo falon Omar biye da su. ?ago kanta tayi da nufin yima Abba sannu idanunta ya sauka akan Yoohan da shi koma kallon inda take baiyi ba. Ganin har zasu wuce batai magana ba Abbah yace, "Adawiya baki iya gaisuwa ba ne? Ko bakiga mijin ?ar uwarkiba Nu'aymah?".
Da gaske gaban Adawiya sai da ya fa?i. Bakinta na rawa ta gaida Yoohan. Sau ?aya ya amsa tare da mata kallo ?aya ya ?auke kansa. Binsa da kallo kuwa ta cigaba da yi harya shige falon Abbah.
A fili tace, 'Dama Aymah ba ?abila akace ta aura ba? Naga kuma balarabe?'. Bata da mai bata wannan amsar dan haka tai shiru tana sa?e-sa?enta a cikin zuciya har Momy ta fito tana tambayarta ihun mi takeji ?azun. Tana cikin sanar ma Momyn ne su Aymah suka fito. Zuwa Nu'aymah tai ta rungume Momy cike da murna.
Momy dake dariya tace, "Ja'ira, an girma ba'asan an girma ba".
Dariya ta sakeyi su Amal na taya ta. Adawiya dai tai mu?uy kamar bata falon abin duniya ya gama isarta a rai game da ganin mijin Nu'aymah..
Tura Amal momy tayi ta kira Uwaliya mai aikin da aka kawoma Nu'aymah daga kano. Ashe dama ita suka biyo ?auka batare da Yoohan ya sanar mata ba. Ba wata tsohuwa bace ba. Zata iya kai kimanin shekaru talatin da bakwai dai. Sun gaisa da Nu'aymah momy tai musu bayanin juna. Har cikin zuciya Aymah taji son zama da Uwaliya kuwa. Dan haka cikin jin da?i ta mi?e domin zuwa falon Abbah ta gaidashi shima.
Basu bar gidanba sai goma saura. Sun tafi da Uwaliya. Su Amal ma sun mata al?awarin zuwa next week dan dama Abbah ne ya hanasu wai karsuje su tada mata hankali. Amma yanzu daya ganta babu wata damuwa yace zai barsu suje ?in amma sai weekend insha ALLAH.
Papa kawai suka samu a harabar gidan zaune. Sai su Solomon da suma ke tasu hirar acan gehe. Ita dai tana gaida papan ciki suka wuce da Uwaliya. Shi kuma ya nufi inda papan yake zaune.
Basu sami kowa a falon ba. Gidan ma shiru alamar duk sun kwanta. Ta fahimci ?abi'arsu ce barcin wuri, musamman ma yaran saboda makaranta. Da kuma su ?in kansu daya kasance duk suna fita aiki da safe. Uwaliya nata kalle-kalle ita dai har suka ?arasa sashensu. Sarai Aymah taga Momy acan ?ofar sashenta zaune. Amma sai tai kamar bata ganta ba suka shige abinsu.
A falo suka yada zango. Kusan zaman mintuna ashirin sai gashi ya shigo tare da su Solomon da suka kwaso kayan. Anan tsakkiyar falon duk suka zube komai suka fita suna musu sai da safe.
Batare da Yoohan ya zauna ba ya dubi Aymah yana fa?in, "Ki kaita ?akin kusa da sashen nan anan zata zauna". Kamar Aymah zatai magana sai kuma tai shiru ganin ya juya abinsa ya nufi hanyar ?akinsa. Ta fahimci har yanzu ransa a ?ace yake dai, kamarma an sake tunzurashi ne yanzu da suka shigo. Tashi tai ta raka Uwaliya ?in, ?akine babba da katifa a ciki da kwabbot na kaya da toilet ?insa kamar kowane ?aki. Hakan yasa hankali Aymah kwanciya. Itama Uwaliya sai faman washe ha?ora takeyi ganin ita da aka kawo tai aiki amma irin wannan aljannar duniya haka.
_________¡ï¡ï¡ï¡ï_________
Washe gari da yamma tana ?akinta bisa gado ta baje littatafan ta na islamiyya tana dubawa ya shigo. Batare data ?ago ba ta amsa masa sallamar da yayi. Sai da ya zauna a bakin gadon tare da ?aukar littafin gabanta na SAHIH AL-BUKHARI da take dubawa sannan ta ?ago.
Idanu ta ?an zaro tana kallon abinda ya ke ci. Ta tsuke fuska iya gaskiyarta tana fa?in, "Tab wannan ai chocolate ?ina ce, naga kaine kace kowa yaci abinda ya sayo ai ?azun da safe ko?".
"Oh ashe babu da?i hajjaju, ni da kika tasamin biscuits a gaba kika cinye banyi maganaba, sai ni danna sha wannan chocolate ?in da ko wani da?i babu".
Ture buks ?in tai gefe ta mi?a hannu zata warce a hannunsa. "Tunda babu da?i bani abuta".
Hannun ya ri?e yana wani kafeta da narkakkun idanunsa. Yayinda yake ?an motsa bakinsa a hankali yana cinye wadda ya gutsira. ?ara matsowa tai tasa ?ayan hannun zata warce again, dai-dai zai kai bakinsa.
Fisgota yay gaba ?ayanta ta fa?a jikinsa. Yay baya shima suka fa?a saman gadon. Zabura tai tana fa?in, "Malam kana shigarmin hanci da yawa wl......"
Bai bari ta ?arasa ba ya juyata ta koma ?asa shi ya koma sama. Sai dai rabin jikinsa ne a kanta, a hakanma bai sakar mata nauyinsa ba dan a ganinsa bazata iya ?auka ba. Amma tsabar ragwantaka na Aymah sai ta wage baki zata masa ihu. Hannu yay saurin ?orawa akan bakin nata yana ?an waro idanunsa waje. "Idan kikai ihun nan na ratse sai na ha?iye bakin kinnan yanzun nan".
Hannu tasa ta ture nasa hannun tana fa?in, "Tunda kai maye ne basai ka ha?iye ba mugani".
"Kema zaki koma mayyar ai"
Yay maganar yana saka idanunsa cikin nata yanda ta kasa magana ta kuma kasa janye nata idanun saboda tsabar yanda ya sar?eta da nashi.
Cikin wata irin kasalalliyar murya yace, "In sammiki chocolate ?in?".
Duk yanda taso bu?e baki tayi magana ta kasa. Dan yanda yay maganar gab da fuskarta, ga idanunsa cikin nata sai taji kamar ya mata wani ?aurine da igiyoyi.
Chocolate ?in ya kai bakinsa ya sake gutsira ka?an, har yanzu idanunsa na a cikin nata bai janye ba. Ya sake matsar da bakinsa gab da nata. A hankali cikin maganar ra?a yace, "Bu?e bakin".
Kamar wadda ake juyawa da remote Aymah ta motsa la??anta ka?an idanunta dake cikin nasa na cikowa da ?walla. Bata ankara ba taji la??ansa akan nata, a tare suka lumshe idanu, sai dai ita wasu hawaye da batasan na minene ba suka shiga silalo mata saman kumatu da gudu. Yayin shi kuwa Yoohan yake juye mata narkakkiyar chocolate ?in daya narkar da yawunsa......
(Kai zafafa fans wannan bada cakuleti na Yoohan yafi ?arfina, bara na?an fita na barsu su sarara??. Amma zan le?a muku ta kafar mukkuli??).
Gaba ?aya Nu'aymah ta kasa fahimtar kanta balle abinda Yoohan yake mata. Shi kansa da yake aikatawar yayi masifar shafa'a da wadda yake tare. Sai da labari ya nema canja salone ?wa?walwarsa ta fara aikin masu hankali. Da ?yar ya iya janyewa daga jikinta ya koma gefenta ya kwanta rufda ciki. itama saurin juyawa tayi ta koma can gefe taja bargo ta ?udundune jikinta na wata irin karkarwa.
Sunja tsahon mintuna goma a hakan kafin Yoohan ya bu?e idanunsa dake a rufe da ?yar. Ya cija lip ?insa na sama tare da sake lumshe idanu ya sake kuma bu?ewa akan Aymah dake a cikin bargo har yanzun. Tsaf yanayin ya shiga dawo masa a cikin kai. Duk da cikinsa daya ?ulle hakan bai hanashi tashi zauneba da sauri jin ajiyar zuciyar da Nu'aymah ke saukewa. Ya matsa inda take tare da jan bargon data kudundune a ciki har kanta.
Cikin muryar da bata ta?a saninsa da itaba yashiga kiran "Zeeynab! Zeeynab!".
"Hasbunallah" tai saurin ambata akan la??anta jin zuciyarta na neman