Showing 213001 words to 216000 words out of 325075 words

Chapter 72 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29188

tattare da shi, sai ma sake ?aimi da yayi akan harkar karatunsa fiye da farko. kuma shine dalilin saka masa rashin barci yake ?aukar tsahon kwanaki, a dabarar bokan nata wannan galabaitar da zaiyi zai sakashi shan wani abu ya fita hayyacinsa. Ita kuma sai tai amfani da damar wajen kusanta kanta da shi har ta dinga biyama kanta bu?ata.

Sai dai kuma shi UBANGIJI alhakimu ne. dan hakan data aikata sai yazam kiyayewa ga Yoohan bai ta?a aikata zina ba. saboda tayi a sirin ne a dai-dai ga?ar da girmansa ya kai zai iya sha'awar kasancewa da macen. Dalilin rashin barci kuma bai sakashi shan giya ko kayan maye ?inba, abinda ma bata saniba ba aikinta bane ke hana Yoohan rashin barci. Wani kuma ?ullinne daban, ga wanda batai zatoba da ita kanta bata fahimtaba. Duk da kuwa tun yana yaro tasa akai masa wannan asirin.

To masu karatu sai muyi fatan samun lafiyar Aymah dan muga yaya wannan wasan zai kaya tsakanin madam Chioma, uwa ga Yoohana da kuma Madam Nu'aymah mata ga Yoohana. Ga Papa ga baba malam, ga kuma Yoohan ga Abdallah dan tabbas idan mun tuna abinda ya faru ranar shopping hakan na nufin akwai zazzafan wasa a ?asa. Tsakanin Ayma da papa ma akwai game, hakama tsakanin Yoohan da family ?in Aymah akwai game. Sai kuma Nasir da Abdallah. Tabb gyama-gyamanfa na da yawa. Kuma da alama samun lafiyar Nu'aymah ne kakar buga wasannin sai muje zuwa muga yanda za'a kafta wasannin??????????.

________¡ï¡ï¡ï¡ï________

Washe gari kamar ha?in baki su baba malam da papa a tare suka taho ?asar Austria a jirgi ?aya kuma. Suma basu fahimci hakaba sai da suka sauka kowanne yaga ?an uwansa. Kallon kallo akaima juna tsakanin Papa da baba malam, Umm da madam Chioma. Sai dai baba malam ne ya fara kauda shirun da mi?ama papa hannu. Itama Umm sai tai ?an murmushi tana kallon madam Chioma da ke jinjina ?yawu da kamalar mahaifiyar Nu'aymah. A ranata tace, 'Ashe anan yarinyar nan ta ?akko ?yau kamar ?ar aljanu'.
Itako Umm mamakinta yanda babu wani kamannin Yoohan da madam Chioma kamar yanda tai tunanin gani.
Sun gaisa kowa yana ?o?arin danne abinda ke cikin ransa. Richard da Solomon dama sukazo ?aukarsu, dan shi Yoohan sarai yasan a jirgi ?aya zasu taho amma ya?i sanarma kowannensu.
Tun a wajen su Rich suka sakejin labari mai da?i daya sake saka musu nutswa a zukata. Sai dai na papa da madam Chioma iya kan fuska ne kawai. Sai da aka fara kaisu masauki da Yoohan ya tanada musu, Rich yace su huta nanda awa uku zaizo suje asibitin dan ko sunje yanzu baza'a bari suga Aymah ba tunda ba'akai ga fiddota daga wancan ?akin ba har yanzun. Duk da kodama sun fiddotan da wahala subar wani shiga inda take sai dai likitocin kawai.
Su baba malam basu damuba. Dan mutanene masu tawakalli da kawaici. A ganinsu kuma tunda har suka iso ?asar ai magana ta ?are kuma.

Papa dai kam bai zauna ba. Yana tabbatar da Rich sunbar hotel ?in ta hanyar Solomon ya shirya shima ya fito zuwa inda sukai zasu ha?u da Dr Mateo, Sai da ya isa wajen shan coffee ?in da kusan mintuna goma sannan Dr Mateo ya iso.
Gaisuwar arzi?i Papa bai bari sunyi ba ya rufesa da jarabar miyasa yasan bazai iya aikinba ya amsa zai masa har kuma yama biyasa ma?udan ku?a?e?.
Dr Mateo dake kallon papa a yatsine yace, "Na kula ?walwarka bata aiki da ?yau Mr Goshpower. Wannan ?asar tamufa ba irin africa ?inku bane da kuka ?auki ran mutum ba abakin komaiba. Sannan mutanenmu ba wawaye bane irinku da suke abu da ka babu wata ?a'ida. Duk da aikine mai ha?arin gaske amma na gwada son ganin na aiwatar dan in faranta maka. Sai dai matsalar da aka samu bani ka?ai nayi aikinba. Kuma duk Doctors ?in da mukayi aikinnan tare suna bala'i-bala'in ganin mutuncin yaronka Yoohan, dan yanada mutunci da karfi a wannan asibiti saboda yayi mana manyan ayyuka da ko gwamnatin ?asarnan bazata manta da shi ba balle asibitin kansa. So Please kayi wani tunani akan kisan yarinyar ta wani hanyan amma ba wannan ba. Dan koni kaina yanda na fahimci Dr Yoohan nason yarinyar bazan iya kasheta ba dan ina girmama soyayya sosai".
A rikice papa yace, "Ban gane bazaka iya kasheta ba. Kana nufin kaci ku?ina a banza kenan?".
"A wofi ma kuwa Mr goshpower, dan na gwada maka aikin daka bani nasarace kawai ba'ayi ba, saboda yarinyar ?ar baiwa ce. Sannan ka yarda da shawarata kar kayi wani gangancin koda na saka wanine ya kasheta a cikin asibitin nan, asirinka zai tonu. Dan koshi ?an naka bazai barka ka kuma zu?ar iska ba a duniya inhar ya fahimta. Ni kaina dasun fahimci nine naso ?ata musu aiki har Dr Yoohan ya tsorata ya suma da baka ganni anan gabanka ba. Abu na karshe dazan sanar maka kuma shine zagaye take da securitys ta ko ina saboda girmamawa ga Dr Yoohan akan hidimarsa. Dan tunda kowa ya fahimci matarsace kaf Doctors ?inmu sun sake ninka kulawarsu fiye data farko a gareta. na barka lafiya". Ya kare maganar da wani ka?a masa yatsunsa da kashe ido yana wani shegen murmushi.
Tamkar wani soko haka Papa yabi Dr Mateo da kallo harya tare taxi ya shige. Jiyay kansa ya masa wani irin shegen nauyi, ya ?auki butar da aka zubo musu coffe a ciki ya tsiyaya a karamin kofi. Duk da turirin da yakeyi bai damuba haka ya kafa kansa ya hau kwankwa?a yana ?ona masa baki da ma?ogwaro. Wato lallai ya fahimci baturen likitan nan ?an iska ya maidashi kawai. Duk yasan da wannan dokar amma ya amsar masa ku?i ya kuma amsa masa zaiyi aikin?. ?aga kofin yayi kamar zai rotsa da ?asa sai kuma ya fasa ya ajiye ya mi?e a fusace ya baro shagon shan coffe ?in yana kumbura kamar wani kububuwa????.

Nannauyan numfashi Richard dake kujerar bayan su papa ya sauke, tsabar ka?uwa da tattaunawar papa da Dr Mateo ta sakashi cire p-cap ?in kansa ya hau fifita da ita. Mi?ewa yay da ga shagon coffe ?in shima ya fice zuciyarsa na bala'in masa kai kawo.

******

A ?angaren su Baba malam kuwa awanni uku na cika sai ga Solomon ya dawo ?aukarsu. Ya iske papa baya nan dan haka ya tafi da su su uku tunda yasan inda papan ya tafi. Sun isa asibitin dai-dai da fitowar Yoohan daga wani aiki da sukai shi da wasu likitoci. Dan dama akwai yarjejiniya tsakaninsa da asibitin akan zasu taimakesa aima Nu'aymah aiki, shima kuma zai taimakesu wajen duba musu nasu patients ?in da sukasan yanada basira a kai. Ya kuma amince zaiyi, dan haka bayan an kamalama Aymah shima ya maida hankali wajen cika musu nasu al?awarin duk da kuwa duk abinda yakeyi hankalinsa na a kanta.
Cike da murmushi ya tarbi su baba malam. Kamar yanda suma suke nasu ?ayataccen murmushi. Madam Chioma kam kallonsa take kamar ta hadiyesa. Ta bu?e masa hannayenta alamar yazo gareta. Daga shi sai ita ma baya iyawa balle yanzu akwai baba malam a wajen. Kafa?arsa ya ma?e mata tare da cigaba da takowa zuwa gaban baba malam. Shi ya fara gaidawa da girmamawa. Baba malam ya ri?o hannunsa yana murmushi sukai musabaha. Daga haka ya gaida Umm itama data amsa masa cike da kunyar surukuta. Shima dai ya kasa dubanta da ?yau dan tana masa tsananin kwarjini ainun.
Juyawa yay ga Madam Chioma data cika tayi fam da takaici da kishi. Bai damu da yanayin nata ba ya kamo hannunta ya sumbata yana murmushi. Danne zuciyarta tai da ?yar ta nuna masa kulawa da tambayarsa yaya daughter ?inta. Cike da kulawa a gareta da nuna jin da?i ya sanarmata suna fatan nasara ga farfadowar dota ?in tata.
Daga haka yay musu jagora zuwa zuwa ?akin da aka maida Nu'ayma mintuna talatin da suka shu?e. Basu shiga har inda takeba. Dan hakan dokar take ba'ason motsin komai a inda take. Hatta da takalmansu duk sai da suka cire suka saka na roba duk da kuwa ba ainahin ?akin zasu shiga ba. Ta cikin glass ?in daya raba tsakanin inda suke da dakin da Ayma ke a ciki suka lekata. Dolene mai imani ya ganta yaji tsananin tausayinta, dan bata da maraba da gawa a kwance, na'urorine kawai ke aiki a jikinta ta ko ina. Sun mata addu'oin samun lafiya a zukatansu suka baro wajen Umm na share hawaye. Baba malam ma dai dauriyace kawai da jarumta.
Office ?in da Yoohan yake suka koma, anan yay musu bayani sosai akan nasarorin da aka samu a wajen aikin da wanda suke fatan samu idan ta farka. Sunji da?i sosai, sunata kuma godema ALLAH. Madam Chioma dai murmushi kawai take wanda yafi kuka ciwo. A haka papa yazo ya samesu shima.
Shima dai sai da aka rakasa yaga Nu'ayma dan ya dage cike da nuna damuwa da alhini kamar har cikin zuciyarsa ne.
Lokacin da zasu koma masauki tare suka tafi da Yoohan dan zaije yay hutun awanni biyar kafin ya sake dawowa asibitin.

¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï

?arfe takwas da rabi na dare agogon ?asar su Yoohan suke saka ran farfa?owar Nu'aymah. Amma sai bai sanarma su baba malam ba dan basu san mizai biyo baya ba. Yafi son sai sunga komai yanda suke fata kafin yay musu albishir. Daga shi sai Rich nema sukazo asibitin, Solomon ma sun barshi a masauki. Yauma sai da yay salla raka'a biyu da addu'ar neman nasara kafin su shiga ?akin da Nu'aymahn take. Duk da ransa cike yake da tsoro haka yaketa ?arfafa kansa suna ?o?arin janye duk wata na'ura dake tare da jikin ta.. Sai da suka cire komai aka barta da na'urar numfashi kawai kafin Yoohan ?in da kansa yay mata wata allura. Daga haka suka koma gefe suka zubama sarautar UBANGIJI idanu kuma.
Mintuna sha biyar da suke jira ta cika Aymah bata motsa ba. Suka sake ?ara biyar suma suka shu?e shiru. Sha biyar suka ?ara nanma babu labari. Dukansu babu wanda tsoro da fargaba bata riskesa ba, musamman Yoohan da ru?aninsa ke neman fitowa fili. Dr Sophia ta bada shawaran ko zasu sake mata allurarne dan dama ta fahimci jininta nada matu?ar ?arfi. Duk sunyi na'am da hakan tunda sunsan ba illa bane. A ?a'ida ma za'a iya yimata sau uku. Daga hakane idan bata farfa?o ba sun tabbatar mutum ya mutu kenan.
A yanzun kam Yoohan bashi yay alluranba dan bazaima iyaba. Koda suke maganarsu zaune kawai yake yana kallonsu bai saka bakinsa ba. Hakama har akai allurar bai motsa daga inda yake ba. Yanzu dai mintuna talatin suka bata na jira.
Cikin amincin UBANGIJI minti ashirin da bakwai na cika tai wata irin mahaukaciyar zabura. Sai jikinta ya kama rawa har gadon kansa na jijjiga. Gaba ?ayansu suka rufu a kanta kowa na nuna farin cikinsa. dan kuwa dai ta wuce mataki na biyu kenan. Wanda kuma yafi kowanne ha?ari dama a aikin. Matakin ?arshe shine abubuwan dake a ?wa?walwar ta zasu dawo ko zatayi loosing ?insu. Kasancewar ta yarinya ?arama basu cika damuwa da wannan ba dan a ganinsu tanada sauran isashen lokacin da zata koya duk abinda ta rasa. Sai dai ga Yoohan sam baya fatan haka. Burinsa komanta ya kasance tare da ita musamman karatunta na addini koda kuwa zata manta da sauran abubuwan ciki harda shi kansa.
Dukkanin taimakon daya dace shi suke bata cike da ?warewar aiki. A awa guda suka dai-daita komai Alhmdllh. Allurar barci aka sake mata da bama Nurse ?in da zasu goge mata jiki dama. Amma sai Yoohan ?inma yace su barshi. da kansa ya gogemata jikin ya canja mata kaya sannan aka maidata ?akin da zatai jiyya.
Farin cikine sosai tattare da Yoohan. Dan yanaga komai ya dai-daita tana sauke numfashin barci da ajiyar zuciya a kai akai sai ya fito ya koma masauki dan ya sanarma su baba malam wannan dadda?an labari.

Aiko basu ka?aiba hatta da su hajjo ?an Nigeria dake can cike da fargaba da alhini duk sun kaure da farin ciki da murna tamkar ance Aymah ta mi?e a kan ?afafunta. Hajjo ta kuma sakawa akai abinci mai yawa akai sadaka da shi. suka kuma shirya ita da kaf ?an gidan sukaje asibiti sukai ziyarar marasa lafiya da bama masu bu?atar taimakon tallafi.
Suma anan daga su baba malam har Yoohan sunta nafilfiline suna nunama UBANGIJI godiyarsu akan wannan ni'ima da yay musu. Washe gari kuma suka tashi da azumi a bakinsu na sake jaddada godiyarsu ga ALLAH. Sun kuma je sun duba ta suma hankalinsu ya sake kwanciya da samun nutsuwa fiye da farko.
Shi kansa Yoohan yau yini yay yana barci cike da kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya tare da dadda?an mafarki.
Su papa dai ba?in ciki fal ransu. Dan a ranarma sukace zasu koma tunda ta farfa?o. Daga Yoohan harsu baba malam basu kawo komai a ransu ba game da hakan. Sai ma godiya da sukai musu tare da rakkiya har airport. Shima Yoohan ?in a ganinsa zaifi samun sakewa da su baba malam ?in a yanzu fiye da su papa na tare da su.

Aiko hakance ta kasance. Dan suna dawowa daga rakkiyarsu Umm ta koma ?aki, shiko shi da baba malam wani wajen hutawa suka zauna a cikin hotel ?in suka shiga hira mai da?i tamkar ?a da uba. Dan idan ka gansu bazaka ta?a ?aukar ba shine ya haifesaba. Yoohan yana bala'in sakin jiki da baba malam fiyema da papa da ke amsa sunan mahaifi a garesa.
A haka Rich daya tashi a barci yazo ya samesu shima. Da farko ya zaunane kawai dan yanajin zafin baba malam da kuma son fahimtar ta wace hanya suka dilmiyar masa da ?an uwa ya fara salla. Sai dai hirar batai nisaba Rich ya farajin nutsuwa da baba malam ?in. Harma yake jin hirar na masa da?i da basa wani irin farin ciki.
Baba Malam kam tsaf ya fahimci Rich najin zafinsu tun isowarsu ?asar. Sai dai baisan akan wane daliliba. Amma kasancewarsa mutum mai zurfin ilimi da hikima sai ya dinga mu'amulantar Richard ?in cike da kulawa. Har i zuwa yanzun da suke zaune a tare.
Yoohan duk yana lura da yanda Rich ya fara sakin jiki da baba malam sa?anin farkon zamansa a wajen. Murmushi kawai yakeyi a cikin ransa, yana mai ro?on UBANGIJI ALLAH yasa abokin nasa nada rabon shiriya shima kamar yanda ALLAH ya cidashi ya tsamosa da ga DUHU zuwa HASKE.
Sunja lokaci mai tsayi suna hirar kafin su koma ?akunansu. Shi dai Yoohan shiri yay ya tafi asibitin dan akwai abinda zaiyi. Kuma lokacin gogema Nu'aymah jikima yayi

____________¡ï

Alhmdllh, yau kwanaki biyar kenan da yima Nu'aymah aiki. Sai dai zamuce har yanzun ba sanin inda kanta yake tai ba. Dan kullum a cikin barci take. A bisa ilimin likitanci ake bata taci ake bata ta sha ta allurai da sauransu.
A komai Yoohan ne ke tsaye a kanta. Dan duk abinda ya dace shine kema matarsa da a kallo ?aya zaka fahimci ?unbin tausayinta da tsantsar kulawar da yake bata akan fuskarsa. A yau ne ake shirin barinta ta dawo hayyacinta gaba ?aya. Dan haka tun sha biyu na daren jiya babu wata allura da aka ?ara mata. Duk wata na'ura dake tare da jikinta kuma an janyeta.............?

*_Hummm. Ashe haka kuke da tsoron mutuwa dama? Tofa inhar a ranku kunajin jaruman littafi bai kamata su mutuba sai ku daina ?alubalantar marubuta nasaka rayuwar littafii daya wuce kima. Idan kuma har kun shirya kar?ar littafi dai-dai da zahirin rayuwa dolene ku shirya amsar ?addarar cikinsa itama dai-dai da zahirin rayuwa. Mutuwa dolece akan kowanne bawa. Dan haka jiya na tunatar da ku muhimmancinta dan shima littafin bazai zama kullum farinciki ba. inhar mutuwar jarumar littafi zata iya ?aga hankalinku irin haka harda masu iya bu?e baki su zageni bayan sunama karantawa ne basu biyaba??, to lallai ku ji tsoron zuwan mala'ikan mutuwa mai ?aukar rai a zahiri ranar da babu tsumi babu dabara, sannan kuji tsoron cin ha??in abinda koda ?aukarsa kuke ba komaiba. Muguji son ziciya dan ?arshe ?acin zuciya take zamarwa mai ita. Kai da karantawa kake kaji zafi a ranka dan an rubuta sa?anin abinda bashi kaso ganiba harka furta ALLAH ya isa. Mu kuma da muka ?ata awanni muna rubutawa kika fitarmana, ke kuma kika gani kika karanta da ya?inin kin samu bati, bayan mun ha?aku da Girman ALLAH mi kake tunani koda bamuce da ku komai ba?. Kunbi kun ru?ar da kanku koma fahimtar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login