Showing 216001 words to 219000 words out of 325075 words
bayanin nawa bayi kukaiba??, nace karku sare, kar kuma ku saka rai, amma shine harda masu rusar kuka??, da masu kirana suna kuka??, kai jama'a gaskiya jiya kun sani dariya kun kuma sakani hawaye saboda tausayin kammu, saboda tunawa da muma mutuwar nan tana tafe a garemu duk daren da?ewa, sannan wasu a cikinmu ma an zare mana mutane masu muhimmanci a rayuwarmu a yau babusu tare damu????. ALLAH ka gafarta mana baki ?aya. Wannan itace makarantar JIKI MAGAYI bisa gaskiyar zancen Nu'aymah_*??????.
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????
Mamu gee??
MIN ?ALB!!????
Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????
Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????
Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????
?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.[6/21, 12:29 PM] +234 901 860 0202: *_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.
No. 57
________________
*Sunana Nafisa k Abdullahi am a singer, actress.. wakokina are based on siyasa da kuma na sarakuna *
https://youtu.be/1VyZ6f1GTWg
*(YouTube link)????*
*This is my YouTube channel IN SHAA ALLH! I will be bringing to you my latest films, And musical videos*
*NafisaKabdullahi* *Sabuwar ficacciyar jaruma ce data shahara wajen fina finai da kuma wakoki na siyasa, Masarautu da sauran su*
*Ina masoya makaranta littafan zafafa? Ku fito ga dama ta samu, Munason a nuna mana k'auna ta hanyar subscribing a sabuwar channel dinnan ta Nafisa mai suna a sama. ????A kalla a kuma danna kararrawa domin sauraron shirye shiryen ta a duk sanda ta dora..*
*Danna kararrawa domin kasancewa da ita da zarar ta dora sabbin shirye shrye.*
*DAN ALLAH! Ayi subscribing, Akuma dinga viewing, Inda hali ma ayi comment da sharing zuwa ga wanda basu sani ba...*
*Akwai Facebook page dinta mai suna: https://www.facebook.com/preetyfeenat.abdullahi*
*Domin karin bayani sai a tuntub'i Nafisa kai tsaye ta number ta: *
*08071172003*
*kada ku mance ko minene daya danganci wakokin al'adun hausa, Da ire-iren fina-finan mu na hausa, Nafisa zata dinga kawo muku shi a wannan sabuwar channel din nata, Saboda haka MASOYA a temaka aje ayi mata subscribing a kuma dinga kallan abubuwan data dora.*.
__________
No. 57
...........?arfe goma dai-dai na safiyar wannan rana agogon ?asar Nu'aymah ta farka a gaban Dr Yoohan da sauran likitocin da sukai mata aiki. Sai baba malam da Umm. Dan ana bu?atar tabbatar da ingancin lafiyar ?wa?walwar ta da kuma tabbatar da idan bata manta komai ba.
Gaba ?ayansu idanunsu cak akan yatsun ?afarta dake motsawa. Har zuwa hannayenta biyu da suma ke motsin. A hankali gashin idanunta suma ke motsawa, sai numfashin ta dake sauya salon fita daga na barci zuwa na wadda take a farke.
Da farko bata ia ganin komai, ta cigaba da motsa idanun a sannu-sannu har ta fara ganinsu dishi-dishi. Idanun ta maida ta rufe tana matse fuska, babu dai wanda ya motsa a cikinsu harta sake bu?ewar a hankali. Akan Dr Sophia ta fara saukesu, tayi kusan sakan goma tana kallonta kafin ta janye zuwa ga na kusa da ita. Shima dai tai masa kallo mai tsaho ta sake maidawa kan ?ayan likitan. Idanun ta lumshe ta sake bu?ewa akan Dr Yoohan. Yanda take kallonsa haka shima yake kallonta cike da fargaba. Tafi tsayin mintu uku tana masa kallon ?urullah da duk ya basu tsoro, dan tamkar tana hasashen wanene?. ?auke kanta tai a gareshi ta maida kan Baba malam dake a kusa da shi, sai kuma ta kalli Umm. Haka ta ringa raba kallo a tsakaninsu na tsahon mintuna.
Gaba ?aya jikinsu duk yayi sanyi har likitancin, dan da alama ta manta komai. A bazata sukaji ta fara magana da ?yar,
"Yah Yoohan da gaske su Abbana ne?".
Maganar da ?yar take fita. Amma duk sunjita duk da a hankali ne. Rikicewa sukai da farin ciki. Yoohan yay azamar zuwa gabanta ya ri?e hannunta data dafe kai da shi saboda yun?urin tashi zaune da taso yi.
"Please relax koma ki kwanta".
Cikin rawar murya hawaye na zirara mata a idanu tace, "Kaina namin ciwo kamar zai rabe biyu".
"Okay, kiyi shiru ki daina magana".
Ya sake fa?a yana maidata ya kwantar. Kunyar su baba malam da yakeji ne ya hanashi rungumeta dan farin cikin yanda komai yazo yanda sukai fata. Ya ja baya ka?an dan bama su Umm damar ganinta da ?yau. Idanunta a lumshe kuwa ta mi?oma su Baba malam hannu alamar suje gareta.
Kallon Yoohan baba malam yay. Ya jinjina masa kai yana murmushi da sake matsawa baya yanda wajen zai ishesu. Ya kuma jawo musu kujeru su zauna.
Tabbas Yoohan da su baba malam suna cikin ?unbin farin ciki, hatta da Richard ma farin cikin da yaga ?an uwansa a ciki shima sai yake tayasa. Duk da dai a yanzu shima jin wani girma da mutuncin baba malam ya keyi a ransa. Mutumin yana da wani kwarjini na musamman da iya mu'amula wa mutane.
Hatta da Solomon duk da munafunci nacin ransa sai da ya nuna farin cikinsa. Kafin ya zagaye can baya yay kiran papa ya sanar masa halin da ake ciki. Aiko dai ba ?aramin ba?in ciki papa ya shigaba. saboda karma Yoohan yay kiransa ya sanar masa farkawar Aymah sai ya sakashi a black list. Sai dai abinda ma bai saniba Yoohan sam bai nemesa ba a lokacin. Dan sunata shigi da fici akan Aymah daketa complain ?in ciwon kai. Ko idanunta data ?an bu?e da farko yanzu bata iya bu?esu. Tsoron kar matsalar ta shafi idanunta ya sakasu sake mata allurar barci na awa hu?u. Sunason suga ko barcin bai gama wadatar kanta bane jijiyoyin basu gama dai-daita ba.
Da wannan damar suma su baba malam sukai amfani wajen komawa masaukinsu suka du?ufa addu'a a gareta a cikin tsaftataccen ruwan zam-zam da dama sunzo da abunsu.
A wanni hu?uu na cika Aymah ta sake farkawa. Cikin amincin UBANGIJI kuma an dace dan kuwa yanzu tana bu?e idanun, ciwon kan ma tace can ?asa yake mata. Kowa yayi farin ciki da hakan. Yoohan ya bata ruwan zam-zam da su baba malam sukai mata addu'a aciki ta sha. shine abu na farko data fara sha. Ya kuma ?iga mata a cikin ido kamar yanda baba malam ?in ya sanar masa.
Babu mai shiga inda take sai shi, saboda ba'a son mata hayaniya. Duk da tanata damunsa da ?ara son ganin su baba malam yana lalla?ata.
A daren wannan ranar su Hajjo suka iso. Hajjo, Abban Adawiya, Abban Abdallah, Abba Musbahu. Sai Addah data takura akan sai tazo taga jikin Aymah ?in. Duk da kuwa ance baza'azo da matan gidan da yara ko ?aya ba. Su yi ha?uri har Aymah ta dawo tunda ance jikin Alhmdllh. Amma Addah ta nace, da kantama ta biyama kanta ?u?in jirgi. Dan ita dai a ganinta bai kamata a yanda suke da Umm ba ace batazo ta duba NU'AYMAH ba. Sha?uwar tasu hajjo ta kalla tace a barta taje tunda tace zata biyama kanta. dan bazai yuwu a biya mataba sauran matan suga anyi son kai.
Suma sunji da?in ganin yanda jikin Aymahn yayi ?yau sosai. Dan da taimakon Yoohan suka samu suka shiga wajenta. Alhmdllh kuma duk ta ganesu. Harma hajjo ta tsokaneta aka cuna mata baki. Dariya duk sukayi, Yoohan ya girgiza kai yana wani ?an munafukin murmushi, a ransa yana fa?in, 'Ta dawo duniya yanzu zata addabi kowa. Barema ni data gama rainawa'.
Kamarko Aymah tasan mi yake rayawa. Dan tana can tana masa kallon ?asan ido ganin yanda ya rame mata a idanu. Sai dai batai tunanin komai a ranta ba ta maida hankalinta gasu hajjo.
Bayan wucewar su hajjo Richard ya kawo abincin da zataci lokacin shan maganinta yayi da barcinta. Dan a yau ne zata fara cin abu mai nauyi bayan kullum da ake bata iya mai ruwa-ruwa kawai dan ba'a son ta tauna abu saboda jijiyiyin kanta dake tare dana ha?ori.
Cikin jin da?i Yoohan ya amsa yana fa?in, "Thanks you Rich". ?an hararsa Richard yayi da fa?in, "Dama akwai godiya ne tsakanina da kai Mr X". Murmushi kawai Yoohan yayi amma baice komaiba. Shima Richard ?in sai ya murmusa yana binsa da kallo. Sam baya iya dogon fushi da Yoohan. ?auna yake masa ta gaskiya kuma ta ha?i?a har cikin ?argonsa. Yanajinsa a jinin jikinsa tamkar ?an uwansa da suka fito ciki ?aya. Kuma shi harga ALLAH bai ta?a jin zafinsa akan auran Nu'aymah da yayiba duk da kuwa ta kasance Bahaushiya kuma musulma. Sai dai salla da Yoohan ya farayi yanzu yana matu?ar damun ransa. ya rasa wane kalar tunani zaiyi akan wannan matsalar, wazai tunkara su tattauna domin ha?a hannu wajen dawo da Yoohan cikin hankalinsa?. Da yayi yun?urin sanarma wani sai yaji rauni da fargaba ta kamashi. dan haka ya barma ransa ko sauran abokansu su Joseph ya kasa fa?amawa....
Yoohan dai tuni ya fice a office ?in abunsa ya bar Rich da fa?awa dogon tunani. A waje yaga Solomon tsaye. Ya ?an kafesa da kallon mamaki dan ganin yanda Solomon ?in yay fakare kamar wanda ya tsorata da ganinsa. Bai dai ce da shi komaiba yay wucewarsa.
Nannauyan numfashi Solo ya sauke yana rumtse idanunsa da wayarsa dake cikin hannu. Yau shikam ya shiga uku, yana fatan Yoohan baiji wayarnan da yakeyi da papa ba. Gaba ?aya sai wani tsoro na tashin hankali ya kuma baibayesa. Barin asibitin yayi jikinsa na tsuma. dama zuwansa kenan shi da Richard.
Yoohan da haka kawai yanayin Solomon yaso ?arsa masa zargi a zuciya ya ?arasa ?akin da Aymah take yana wasiwasi. Kwance take akan gadon jiyyarta idanunta a lumshe. Har yanzu bawai jikin nata yayi ?arfi baneba. Dan ko magana ma da ?a'ida takeyinta. Kai duk ma sauran abubuwa komai zatayi da ?a'idarsa saboda ?walwarta ana bu?atar ta samu isashen hutun da komai zai gama dai-daita. Dan yanzu dai su Yoohan sun tabbatar da komai Alhmdllh, sai dai zata ringa yawaita ciwon kai kafin wani tsahon lokaci da suma basusan adadiba. Sannan idanunta sun raunana zatake amfani da glass shima kafin zuwa wani lokaci. Bawai bata gani bane, tana ganin komai Alhmdllh, sai dai ba a yanda ya kamataba. Dan idan abu yayi mata nisa tana ganinsa bibbiyu ko dishi-dishi. Sannan sun tabbatar da zata rage yawan hayaniya yanzun.
?amshinsa da taji ya yawaita a ?akinne ya sakata bu?e idanunta a hankali. A kansa ta zubasu, sai dai batai masa kallon sakan uku ba ta janye. ?oyayyar ajiyar zuciya ya sauke. ya matsa gaban gadon sosai ya zauna, kama hannunta yay cikin nashi. Cikin magana ?asa-?asa da ko kana a ?akin bajinsu zakai ba yace,
"How are you feeling?".
Hannunta da ke a cikin nasa ta?an motsa, idanunta a lumshe, cikin magana a hankali fiyema da tasa tace, "Alhamdulillah".
"Masha ALLAH". ya fa?a da harshensa karyayye.
Batare da yace mata komaiba ya kamata zai tayar. Bu?e idanun tayi sosai. A rashin sanin ita yake kallo suka fa?a a cikin nashi. Saurin kauda kanta tayi tana motsa baki ka?an. Duk da ba magana taiba yasan tsiwarce ta motso, sai dai yanzu kam babu bakin yi yanda ya kamata. Filo ya saka mata ta jingina yanda zataji da?i. Ya zauna a kusa da ?afafunta dake a mi?e. Gaba ?aya jitai ta gama takurewa a wajen. Ga ?amshinsa yayi bala'in adabawa numfashinta. Shi dai da baisan tanayi ba, ya san dai tunda ta kasance jinin masoyinsa baba malam bazai ta?a gajiyawa wajen jinyarta ba tamkar yanda yasan iyayenta zasu kula da ita. takeaway ?in ya bu?e yana fuskantarta. Duk da ya fahimci kallonsa takeyi sai bai nuna ya ganiba. Batare da ya kalleta ba yace, "Yau zaki fara cin abinci mai nauyi. Insha ALLAH yanda jikinki keyin ?yau zamu samu sallama da wuri. Amma sai kin daure kin ringa cin abinci ko yaya ne. Dan yanzu zakiji ?an?anon sa sam baya miki wani da?i. Sai a hankali ne ?an?anon harshenki zai warware".
Fuska kawai ta?an yamutsa. Dan harga ALLAH kam abincin ma ganinsa kawai da takeyi yanzu amai yake neman sakata, sai dai kuma itama tana bu?atar ganin an sallameta ta bar asibitin nan da duk take jinta a takure.
Bai damu da rashin yin maganar tata ba. Ya ?iba abincin a spoon ya nufi bakinta da shi. Har zata kauda kanta yay saurin fa?in, "No, Please!". Daurewa tai ta bu?e bakin idanunta a rumtse. Ya zuba mata tausayinta na ?ara ratsasa. taja kusan minti biyu tana juya abincin a baki sannan ta ha?iyeshi da ?yar. Sake ?iba yayi ya bata. Nanma dai sai da ta ?ata lokaci. Da ?yar ya samu ta?anci, sai dai sunja lokaci mai tsaho ana ?a?a nakayi, dan harda hawayenta sha?e-sha?e a fuska. Da ga ?arshe dai ganin ta ?anci ya ha?ura ya barta. Tissue yasa ya goge mata bakinta da hawayen datayi. Yana ?o?arin tashi ta ri?o hannunsa. Kallonta yay kawai sai dai baice komaiba.
A mamakinsa sai yaga ta ?auki cokalin daya bata abincin ta ?ibo ta nufo bakinsa. ba ?aramin harbawa zuciyar Yoohan yayiba. Duk da ba abincine daya cika damuwa da shi ba haka ya bu?e bakin kawai yana kallonta. Zuba masa tayi kuwa batare da ta yarda sun ha?a ido ba. Ta ?ara ?ebowa tana magana a hankali. "Ka rame da yawa. da alama kaima baka da lafiyar kuma bakacin abinci. Amma gashi ni kazo ka tsareni sai da naci. To kaima tsareka zanyi sai kaci".
Yanda tai maganarne a sakalce ya sakashi yin murmushi. ya fahinci kuma da iya gaskiyarta take fa?in abinda ke a ranta. Hannu ya kai saman fuskarta a hankali yana fa?in, "Thanks you". Kallo ?aya tai masa ta janye idanunta batare datace komaiba. Sai dai taji da?in thanks you ?in daya ce mata. Hannu tasa akan hannunsa dake saman fuskarsa ta janye, dan yanda yake mata a kumatu jitake tsigar jikinta na tashi. Murmushi ya kumayi yana cigaba da amsar abincin. itako ta?i yarda su ha?a idanu sam, sai danna masa abinci takeyi.
A wannan yanayin Dr LiLiya shigo ya samesu. Da tsokana yake cewa, "Irin wannan soyayya haka bazasu bari a warke ba?".
Sosai Aymah ta waro idanu akan baturen likitan. Sai dai kuma batai magana ba. Ta ?an harari Yoohan dake murmushi. Sai kuma ta ajiye spoon ?in ta kwanta abunta da juya musu baya. ?aramar dariya Yoohan yayi har ha?oransa na bayyana sosai. ?asa-?asa ya cema Dr Liam "Kaga ka jamin an bar bani".
Dr Liam dariyar shima yayi yana ha?e hannaye waje guda alamar Sorry.
Ita dai Aymah bata sake kulasuba. Da za'a bata magani ma ?in yarda tayi ta kalli kowa a cikinsu. Tana sha kuwa ko mintuna goma cikakku batayi ba barci mai nauyi yay awon gaba da ita. Sassanyar ajiyar zuciya Yoohan ya sauke. Ya kama hannunta data bashi abinci ya sumbata yana wani lumshe idanu. Daga haka suka fito suka bar mata ?akin shi da Dr Liam
____________¡ï¡ï
Yau kwanakin su Hajjo biyu da zuwa. gobe idan ALLAH ya kaimu kuma zasu koma harda su baba malam ma. Sunzo sun duba Aymah da jikinta keta ?ara warwarewa Alhmdllh. Sai dai batason cin abinci sai Yoohan yata lallashi da dabara. A hakanma bata yarda taci ita ka?ai. sai dai idan ya ?eba spoon ?aya ya bata itama sai ta ?iba ta bashi. Ita a ganinta wayo takeyi dansu cinye tare ya rage mata aiki. shiko hakan ba ?aramin shau?i yake sakashi a ciki ba, da jinsa on top. Ta kai ko ruwan addu'arta ya bata tasha itama shima sai ta rage ta bashi ya sha. Dan harga ALLAH ramar da taga yayi kuma na damunta a cikin rai. Ta tabbatar koda rashin lafiya yayi to harda damuwar halin da take a ciki. Dan ta fahimci shi mutum ne mai tausayi sosai dama.
Dr Yoohan da Dr Liam Sai Richard sun fito daga Ward ?in dake gefen wanda Aymah take sai wayarsa tai ring. dakatawa yay domin ya amsa su kuma suka wuce. Papa ne, sun gaisa da maganar data shafesu ya maida wayar cikin aljihun farar rigarsa ta likitanci daya ?ora ya cigaba da tafiyarsa dansu Rich sun wuce.
Kamar da wasa sai yaji ana hausa ta lungun daya gitta. Duk da bajin hausar yake ba mu'amula da hausawa da yakeyi a yanzu tana ?ara sakashi fahimtar yaran hausa ka?an-ka?an. musamman zama da Nu'aymah