Showing 300001 words to 303000 words out of 325075 words

Chapter 101 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29142

"Wannan shine halin ?an adam ?in da ake fa?a Dude, munada son kanmu, duk kuma mutum mai son kasa zakaga shine kullum a cikin wahalar nema da fa?uwa. Dan bazai ta?a doguwar nasara ba. Daya samu take kufece masa. Amma saboda bushewar zuciya gobe ma sai ya koma sake neman sa'a. Kowane addini akwai na banza akwai na gari. Irin wa?an nan mutanen suke ja ana zagin addinin islama bayan shi kuma addinine mai koyar da ?yawawan ?abi'u. Ko shekara banyi da shiga musilinci ba, amma wlhy Yoohan na fahimci babu wani addini dake gogayya da shi akan koyar da ?ya?y?yawar rayuwa. Komai musilinci ya ha?a. Amma ka duba su da keda ilimin sani a tsahon shekaru sunfi za?ar su sa?ama ALLAH bisa son zukatansu".
Sosai zukatansu Yoohan suka ?ara rauni da wannan al'amari. Imani da tsoron ALLAH ya sake shigarsu a zuciya da ?argo. Suma kansu dai a wannan dare sunyi barci ne kawai badan jin da?i ba.

*_WASHE GARI_*

Washe gari aka bama su baba malam damar shiga su duba Abban Abdallah. A lallai duniya abin tsoro. Bawa daina cikama rayuwa baki kai ba komai bane. Duk damar da kaga ka samu a rayuwa da ga rahamar ALLAH ne. Amma wlhy idan yaso ko ?yaftawar ido baka isa gittawa ba. A jiya iyanzu shine zaune tare da ?an uwa da iyalansa. Amma yau gashi babu ko ?yan gani a fuska saboda tsabar jigata da rayuwarsa tayi. Ita kanta Addah jikin nata babu da?i.
Duk wanda ya shiga duba Abban Abdallah sai kaga ya fito da kuka. Hakan yasa dama Yoohan bai bar Nu'aymah a wajenba. Suna zuwa ma ya jata wai tazo suje wajen awo. Bata fahimci wayo yake mataba ta bishi. Sai ya kaita office yasa aka kawo mata abinci. Duk da tace masa ta ?oshi, dan basu fitoba sai da Umm ta bata abinci ya dage sai taci. Dole taci ka?an dan ya barta. Sauran kuma ta bashi dan ta fahimci shima yana bu?atar a tsaresa yaci abincin.

Zuwa ranar dai dukan ahalin gidan sunsan halin da ake ciki, ?a?an Addah dake aure da ?annen Abdallah ma duk sunzo. Ansha sabon kuka dai kam yau ma. Daga ?arshe baba malam dake ta ?o?arin danne tasa damuwar yay musu nasiha da nuna musu muhimmancin ?addara. Ya tabbatar musu da cewar hakan jarabawane. Dan bazai yuwu dama a rayuwa a rayuwa babu jarabawa ba. Ya hana kowa kakkausan lafazi akan su Addah, dan kuwa shi a take ranar ya tabbatarma da kowa cewar ya yafe musu. Sai su cigaba da musu addu'ar ALLAH ya basu lafiya kawai.
Baba malam ya ?ara kima a idanun iyalan Addah da Abban Abdallah. Musamman ma Abdallah da har ran yakejin tsanar mahaifinsa da Addah. Sunso su gur?ata masa tunani ALLAH ya hana hakan. Dan bayan Addah ta ?ale a cikinsu Abbansa sake zaunar da shi yay ya ?ora masa sabon karatu akan maido da Nu'aymah rayuwarsa koda ta ?arfin tuwo ne. Wannan shine dalilin da yasa dinga bibiyar rayuwarta. Ko a randa ya bisu shopping mail ?in nan da nufin kidnapping Nu'aymah ya je. Sai akai rashin sa'a Yoohan ya gansa tun lokacin da suke fa?ansu da Aymah harta fa?a a jikinsa. Dai-dai lokacin da yake cemata ta tara musu mutane idonsa ya sauka akan Abdallah ?in. Har suka shiga mail ?in kuma yana sane da shi. Sannan yana akan sani yabar Aymah a wajen ita ka?ai dan yaga mi Abdallah zaiyi?.
Lokacin da Nu'aymah taji ?amshinsa da gittawar mutum Abdallah ne, yana gab da isa gareta Yoohan ya jasa baya da ?arfi ya toshe masa baki suka koma ta bayansu. Cikin fushi Abdallah ya haka?e Yoohan ?in yana fa?in. "Kai shasha minene haka?".
Murmushi Yoohan yayi sannan ya ha?e fuska. Cikin ?an?ance ido ya nuna Abdallah da fa?in, "Idan ka bari gangancinka ya ?ora zuciyarka bisa dokin shiga gona ta. Na rantse da ALLAH Abdallah sai na dawwamar da rayuwarka a dana sani. Na fika hatsabibanci fiye da yanda kake tsammani. Dan haka ka kama kanka kafin na ajiye mutuncin ahalinka da nake gani gefe na ?ata rayuwarka. Karka zata bansan wanene kai ba da ubanka. Ka kiyayeni kona fallasaku duniya ta sanku da aiyyukanku akan ahalinku".
Yana gama fa?a yabar wajen, shine yaje yaja Aymah suka wuce wajan biyan ku?i.
Tabbas kalaman Yoohan sun girgiza Abdallah. Hakan yasa ya janye daga bibiyar Nu'aymah. Dan dama can shi mutum ne da a rayuwa bai son yawan matsawa kansa, sannan baison fitina sam. Wannan halayyar tasa tasa lokacin yana yaro ake ganinsa matsoraci a cikin yara ?an uwansa. Dan da gaske tabbas yanada tsoron fa?a a rayuwarsa. Dai-dai da film ?in fa?a Abdallah baya zaman kallonsa sam saboda baya ra'ayin fitina, daya zama saurayune ma dai ya fara canjawa. har zuciyar tasa tai tauri saboda zuciyar gidansu ta gado.
?in fa?ama Abbansa zancen yayi. Amma yayi ?udirin janye jikinsa daga bibiyar Nu'aymah. Daga bakin Abbansa yaji samuwar Uwaliya, dan a randa aka kawota a ranar Abbansa ya tattauna da ita tun a office kafinma a kaita gidansa. Uwaliya akwai son ku?i. jin ma?udan ?u?in da Abban Abdallah ya tabbatar mata zata samu akan kaso masa auren Nu'aymah da kawo musu dukkan bayanai a kanta yasa ta amince zatayi. A ranar ya bata rabin ku?in, sauran kuwa sai aiki ya kammala.
Tasha murna a ranar, ta kuma tabbatar da lallai ta shigo Abuja da ?afar dama. Yo ko Yoohan ?in sukace ta bibiya akan wa?anan kudin ai ta halakashi kuwa.
Wannan shine dalilin da yasa ta fara musu aiki. Sai dai abinda bata saniba suna amfani da wayar Rabi da muryartane idan suka kirata.
Lokacin da aka wuce da Nu'aymah Austria da gaske Abdallah yaje dubatane saboda son da yake mata. Sai dai baiso Yoohan da su baba malam su gansa. Shine yaso su fara ha?uwa da Abbansa. koda suka ha?un Abban ya dinga masa fa?an da har zancen Nu'aymah ya shigo ciki saboda Addah da tazo taga Abdallah ta zata cutar da Aymah zasuyi. Anna ne Yoohan yaji da Hajjo sukaji, abinda kuma basu saniba shine baba malam ma ya gansu, ya kuma jisu. amma sai bai ta?a nunawa ko da Umm ba balle su..........?
[7/6, 6:56 AM] +234 901 860 0202: *_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.


No. 75

.............Su Jay dai sun wuce abuja, amma duk da su Addah na a asibiti suna a ?ar?ashin kulawar hukuma ne. Bayan wucewar su Jay shi ma Omar da Yoohan suka wuce da yamma. Ya bar Nu'aymah anan kano saboda Umm bata da lafiya. Har yanzu ta kasa fida daga ru?anin data shiga. Ga jininta ya?i sauka yanda ya kamata. Ita kanta hajjo jininta ya hau sosai. Sai dai ita Alhmdllh bai kai na Umm da komai yazo mata a yanda bata zata ba. Bama Umm ka?ai ba hatta da ?an uwan Umm dana Addar wannan al'amari yay masifar rikita tunaninsu da basu tsoro. Anatama Addah ALLAH wadarai da wannan hali nata. Su Hajarah kam sunyi kuka har sun rasa hawayen zubarwa. Musamman Kubrah da dama ba da?in zaman gidan mijin take jiba. Fitinar yau daban ta gobe daban.
Yanda gidan dai yay wani iri daga shigowa zaga fahimci akwai matsala. Baba malam salla kawai ke fiddashi. Da an idar yake dawowa gida. Komansa ya tsaya cak. Dan duk da daurewar da yakeyi a bala'in gigice ya ke da al'amarin. Bai ta?a ?awowa a ransa cikin ?an uwansa za'a samu mai wannan tunaninba akan dukiya dau?ar duniya. Yayi kuka bana wasaba a ?oye, har ji yake gaba ?aya ?asar ta fita masa a arai.

___________¡ï¡ï

Su Yoohan na isa Abuja suka iske sabon tashin hankali. Dan sun iske gidansu zagaye da jami'an tsaro. Da ?yar ma aka barsu suka shiga saboda sanin Yoohan ?ansa ne. Cikin tashin hankali Yoohan ya ?arasa falon inda ya tarar da ?annensa duka da mama debora a hagitse. Suna ganinsa kuwa duk suka taso kansa a guje suna rusar kuka. Su duka rungumeshi sukayi har mama debora da Gebrail dake gudunsa a da.
Kallonsu kawai Yoohan keyi cike da tsoro, maganama ya kasa yi. Sai da Umar yay dauriyar cewa, "Granny wai mike faruwa hakane? Ku sanar mana Please. Gida zagaye da ?an sanda. Gaku kuma cikin tashin hankali. Ina su papa suke ne?".
Cikin matsanancin kuka joy tace, "Sun gudu Brother Richard".
"Sun gudu kamarya? Ban ganeba nikam Joy?".
Sakin Yoohan duk sukayi, mama debora ta kama hannunsa ta zaunar a kusa da ita. Shima Umar ?in ya zauna. Sauran yaranma duk zama sukayi bisa umarnin mama debora. Tana sharar hawaye ta fara musu bayani.
"John munata kiran wayarka tun jiya ai amma mun kasa samunka. daren shekaran jiya kusan ?arfe goma na dare wani mutum ya shigo gidan nan a ki?ime jikinsa jina-jina saboda harbi da akai masa. Lokacin duk munyi barci, kururuwarsa ta sakamu tashi batare da mun shirya ba duk muka fita compound. Tun a yanda mahaifinku ya ambaci sunansa a ki?ime na fahimci ya sanshi. Dan gaba ?aya ya ru?e shi da Chioma da guards ?insu. Shine ya sakamu komawa ciki akan dole batare da munji mike tafe da wannan mutumi dake a cikin jini ba. Muna falo tsaitsaye mun kasa komawa ciki mu kwanta sai ga shi sun shigo. Duk ?akunansu suka shiga batare da sunce mana komaiba. Sai kuma suka sake fitowa a rikice. Mahaifinku ya rungumeni yana fa?in, karna damu na masu addu'a kawai, ga ATM card ?insa nan duk abinda muke bu?ata Gebrail zai dinga ciro mana ku?i. Daga haka suka fice zuwa garden. Ban ta?a sanin akwai wata hanyar fita gidannan ta garden ba sai a ranar. Dan sai bayan wucewarsu da kusan mintuna talatin ?an sanda suka shigo anguwarnan sunata harbe-harbe. wasu suka shigo nan gidan suna nemansu harda guards ?inkun nan. Sai lokacin mukasan guduwa sukayi harsu Solomon. Amma an kama guards uku a cikinsu. Su kuma ba'asan inda sukeba har yanzun".
Wata irin masifaffiyar zufa ce ke ketoma Yoohan ta ko ina, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un yaketa faman maimaitawa. Shi kansa Umar zancen yay masifar rikita tunaninsa. Batare da Yoohan yace komaiba ya kama hannun Umar suka haye sama. Duk binsu sukai da kallon mamakin mizaiyi?. Bai saki hannun Umar ba sai da suka shiga sashensa can cikin ?akin motsa jikinsa. Inda tanan yana iya hango duka ?an sandan dake a compound ?in gidan da anguwar ma.
Cikin matsanancin fushi ya yarfar da hannun Umar sannan ya tsatstsare sa da jajayen idanunsa. Muryarsa da tsananin kaushi da fushi yace, "Umar mi kuke ?oye min kai da Matata akan iyayena?. kar kaimin ?arya, dan ba ita nake bu?ataba a yanzu na ro?e ka".
Yanda ya ?are maganar muryarsa na rawa kamar zaiyi kuka da ha?e hannayensa waje guda kuma sai zuciyar Umar ta ?ara raunana. Hannayen ya ri?e duka a cikin nasa ya sauke. "Yoohan anzo ga?ar da basai ka ro?eniba zan sanar maka. Sai dai inason ka fahimceni Please. Nima bani da wani za?in daya wuce hakan".
Komai Yoohan bai ceba, saima cire rigarsa da yayi ya hau wani machine ?in motsa jiki ya fara da sauri-sauri. Huci Omar ya sauke tare da fara bama Yoohan labari. Tun daga abinda ya fara ji akan kashe Nu'aymah da papa ya bama Dr Mateo kwangila har zuwa ?oyayyun har?alloli daya fahimci papa nayi a ?oye. Kamar safarar miyagun ?wayoyi da cocaine. Safarar makamai, satar yara yana tarasu a wani gida acan ?auyensu........
Ihunsu Mama debora daya cika gidanne ya saka Yoohan dan Umar fita da gudu zuwa ?asa.
Cike da firgici da tsoro Yoohan da Umar ke kallon Little bee da tawagar jami'an hukumarsu. Ta ha?e fuska matu?a, babuma alamar tasansu. A fusace Yoohan yace, "Lafiya kuwa?".
Uffan Little bee batace masa ba. Sai ma i'd card ?inta kawai ta nuna masa. Sannan ta ?ora da fa?in, "Muna bu?atar shiga ?akin Mr Goshpower domin yin bincike".
Magana Yoohan zai sakeyi Umar ya girgiza masa kai alamar karya ce komai. Hannayensa duka biyu ya tura cikin aljihun wandansa ya koma jikin bango ya jingina saboda jiwa dake neman yaddashi a ?asa.
Da Gebrail sukai amfani ta hanyar ?ora masa bindiga akai. Tuni fitsari ya ji?e gaban wandonsa kuwa. Babuko kwana-kwana wajen kaisu har sashen papa. Tun a falo suka fara bincikensu. Yoohan baiyi niyar binsu ba, amma sai Omar ya kama hannunsa suka shiga. Basu sami komai a falon ba sai cctv dake a ?oye. dan haka suka wuce cikin bedroom. Akan idon su Yoohan akaima ?akin dalla-dalla. Ta hanyar tsabar ?warewar aiki su little suka gano ?oyayyar drawer ?in nan ta sirri dake a jikin bango. Sai dai kuma gar?ame take da security, gashi kuma basu sani ba. An gwada password kala-kala baiyiba. Daga ?arshe suka yanke shawarar yin amfani da na'urar fasa ?arfe ko wane irine. Ta wannan hanyar aka fasa wajen. Sosai Yoohan ya firgita da ganin kalolin bindigu, da harsasai kala-kala. Sai tarin hodar ibilis da ?wayoyin shaye-shaye masu matu?ar ha?ari.
Kasa daurewa Yoohan yayi, sai da ya furzar da wani zazzafan hucin da sai da kowa ya juyo ya kallesa. An ?ara bibbincika ?akin sosai kafin su kwashe duka kayan da suka samu ?in sannan suka sakko ?asa inda su mama debora keta faman kuka. Ganin makaman kuma ya sake rikitasu fiye da farko.
Koda suka fito sai suka shiga bincike gaba ?aya lungu da sa?o na gidan, su dai su Yoohan suna binsu ne kawai da idanu. Sai da suka tabbatar da basu sake samun komaiba sannan suka tattara wa?anda suka samu ?in zuwa mota. Sun bu?aci tafiya da wasu a cikinsu zuwa asalin ?auyen su Yoohan ?in, zakuma su cigaba da ri?esu har sai papa da madam Chioma sun bayayana kansu.
A take falon ya sake ru?ewa da kukan su mama debora. Ganin yanda suke neman fita hayyacinsu Yoohan ya ce zai bisu kawai shi da Gebrail. Kuka harda kururuwa Gebrail ya fashe da shi. Abun zat-tausayi zad-dariya. Haka su Mama debora naji na gani aka wuce da Gebrail daketa kwasar kuka da Yoohan.
Yoohan bai sake fahimtar al'amarin mahaifin nasu babba bane sai da suka iso airport, anan ma wasu jami'an suka tarar da alama jiran isowarsu sukeyi. Babu wani tsayawa ya akai ya za'ai aka shiga da su jirgi. Gebrail na nane da Yoohan cikin tashin hankali. Koda suka isa canma sun iske wasu jami'an tare da helicopters biyu. Nanma babu ?ata lokaci suka shiga zuwa can ?auyensu. A canma sun iske garin a ru?e sosai, dan uban batakashi akeyi tsakanin jami'an tsaro da yaran su papa. Gaba ?aya ?auyen a harmutse yake, dole aka bar su Yoohan a helicopter ?in su little kawai suka firfita suma da nasu bindugun. Sai a yanzu ne fuskar Yoohan ta nuna tsantsar ru?ani. Gaba ?aya komansa ya sare akan wannan al'amari. Lallai da alama mahaifin nasu ya jima cikin wannan mummunar harkar batare da su sun sani ba. Haba no wander yake ganin mahaukatan ku?i basa gajiya da shiga accaunt ?in papa. Sannan sam bayajin fargaba ko ciwon fitar da ku?i wajen musu hidima ta bajinta.
Kallo dai iya kallo su Yoohan sun yisa. Daga ?arshe su Little bee suka sami nasarar cafke gaba ?aya yaran papa da su Uncle Godwin da aka ritsa a garin tun jiya. wasu sun sami raunika, wasu ko ma an kashesu. A cikin su little ma wasu sun sami raunuka.
Daga haka aka fasa ?aton gidan da su papa ke ajiye yaran da suka sato ciki. 'Hazbunallah'. Yarane mata da kananu, sai wasu ba?a?en ?artan bayi da kallonsu kawai ya ishi mutum amai, wasu da tsohon ciki, wasu cikin ?ananu ne, wasu kuma suna a tsaka tsaki. Sai jariran da aka haifa da har an gama cinikinsu ga masu bu?atarsu.
Tsabar tashin hankali little sai da tayi kuka ita da sauran ?an uwanta jami'ai mata. A take Dawood yay kiran Jay ya tabbatar masa al'amarinfa babbane gaskiya. Ga ?an jarida sunyi caa suna neman bayanai. Kamar yanda I.G na ?an sanda ya kasance a wajen dole Jay ma ya taho ?auyen da tawagarsa su Hafeez. Hakama gwamnan jihar dole ya shigo ?auyen, dan kuwa kowa yasan da taimakon su papa ya hau mulki. Dan papa nada matu?ar ?arfi cikin jahar tasu musamman daya kasance yana ri?e da mu?amin shugaba (Pastor).
Dole aka kawo manya-manyan motocin guda uku aka kwashe kaf mutanen dake gidan zuwa can babban birnin jihar. Su Dawood kuma suka shiga yima gidan filla-filla da bincike ta ko ina. daga haka suka sake kwasar jiki zuwa ainahin family house ?in su Yoohan ?in da suke zama idan sunzo garin. Ananma an samu abubuwa da dama, harda ?akin sirri dake dan?are da Computers da suke gudanar da ayyukansu na yima mutane kutse, da zuba uwar sata a asusun


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login