Showing 51001 words to 54000 words out of 325075 words

Chapter 18 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29109

yau zasuje taron wani wa'azi a jihar katsina. Bayan ta ajiye masa duk abinda tasan zai bu?ata ta fita zuwa ?akin Muhammad danta taimaka masa yayi shirin makaranta shima.

*_08:15am_*

Kusan takwas da kwata su baba malam suka hallara a falonsa shi da sauran ?an uwansa domin karyawa. Sun sake gaisawa cikin girmamawa kamar yanda suka sabama kansu. Kafin su zauna su fara karyawa abin cike da birgewa.
Sunyi nisa da cin abincinsu sukaji sallama. A tare suka amsa idonsu akan ?ofar. ?arasawa ciki falon Abbas da yay sallamar yayi. Ya dur?usa har ?asa ya gaidasu. kafin cikin damuwa yace, "Abba ?an sandane ke sallama".
"?an sanda kuma Abbas? Lafiya dai ko?". Baba malam dake kallon Abbas babu ko ?yaftawa ya fa?a.
"Abba ban saniba wlhy, amma sun nuna wai an turosu su tafi da Nu'aymah ne".
Ran Abban Adawiya a ?ace yace, "Wace irin Nu'aymah kuma? Miya ha?ata da ?an sanda banda shashanci irin naka Abbas?". "Wlhy Abba haka sukace, dan hotonta ma suka nuna". Mi?ewa sukai su duka hu?un, sai dai su uku suka fara fita, kafin baba malam yabi bayansu..............?

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________


Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????

Mamu gee??
MIN ?ALB!!????

Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????

Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????

Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????

?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.
[3________________________
*ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE*

*_KAJI shahararrun kuma mandiyoyin ?an ?walisar kawo kayan kitchen masu tafiya dai-dai da zamani. Idan nace nadaban ina nufin su?in nadabanne wajen kaya ?an gaske dake ?awata kitchen ?in amarya harma dana uwargida ?ar ?walisa. Ka siya ka tabbatar ka saya ?in ko a gaban tsaranka sai ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. sunan kayansu sa kishiya cin bashi??, dan tana ?yalla ido taga kitchen ?inki tsarin amerikawa tuni zata fara ?wafa da tunanin zuwa gidan delu dillaliliya mai saida kwanika. Sai dai kuma kama da wane akace bata wane, dan haka ku maza ku garzaya ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. domin samun naku kuma. Suna kawo kaya daga ?asashen ?etare akan farashi mai sau?i da rahusa. Suna order ?in products kamarsu, dukan kayan kitchen na zamani, bedsheets, shoes dade sauransu, products ?insu pre-order ne dake zuwa akan lokaci batare da mai kaya ya ?osa da jira ba ko samun matsala. Zaku iya samunsu a Number waya kamar haka ko Location nasu. Phone number: 08102393622. Location Gombe. Amma Zasu iya turawa kowani gari dake a lungu da sa?o na ?asarnan. Sayen nagari maida ku?i gida. Ku garzaya kar ayi babu ku. Da ?yar nasha yafi da ?yar aka kamani inji masu iya magana??????????._*

_______________________________

14

.................A tare suka fito harabar gidan, inda suka iske matan gidan da sauran samarin da basu kai ga ficewa sabgoginsu ba duk sun fito suma.
Suna ?arasawa ga ?an sandan Nu'aymah da Amal taje ta kira itama sai gata ta fito tana ?an ?ingisa ?afa. Sanye take da siket da riga na atanfa, sai ?aramin hijjab da Umm ta sabar mata da sakawa a cikin gidan saboda samarin gidan tunda ba muharramanta bane ba.
Tunda su Baba malam suka fito jikin wasu a cikin police ?in yayi sanyi ganin dai da gaske an turosune gida mai daraja kamar wannan dan suyi abinda basu da tabbacin faruwarsa tunda ba'a gabansu akaiba. To amma yaya zasuyi, d.p.o ne da kansa ya sakasu zuwa su kama Nu'aymah, ga kuma ku?a?e da sukaci har kashi biyu daga Papa da kuma guards ?in Yoohan na toshiyar baki. (Ya rabbi ka tsaremu cin rashawa da bada ita. Amin??????).

Sun gaisa dasu Abba cikin girmamawa, kafin su sanar musu daga station ?in da aka turosu da kuma abinda zasuyi. Kusan a tare su Abbah duk suka juya suna kallon Nu'aymah. Baba malam ne kawai kansa a ?asa yana ?an murmushi. Batare da yace komaiba ya nufi inda jama'ar gidan ke tsaitsaye suma suna kallonsu hankali a tashe.
Hannun Nu'aymah ya kama batare da yacema kowa uffanba. Itama kuma babu musu ta bisa har wajen ?an sandan. Ya mi?ama macen hannun Nu'aymah yana fa?in, "Itace wannan?".
Kallon hoton dake a waya babban nasu yayi, kafin ya kalli Nu'aymah. "Eh itace ALLAH ya gafarta malam". Ya fa?a cike da girmamawa ga baba malam. Murmushi baba malam yay musu yana nuna masu Nu'aymah dake kallonsa kamar wata sokuwa. "Gata nan, zaku iya tafiya da ita". Da sauri Abban su Abdallah ya yun?uro zaiyi magana baba malam ya ?aga masa hannu fuska a ?aure. Cak ya tsaya hankalinsa a ?ololuwar tashe. Hakama su Abban Adawiya hankalin nasu a tashe yake da hukuncin da baba malam ya shirin yankewa. A ganinsu ai basai anje station ba, zasu iya tsayawa su tattauna anan, musamman ma shi Abban Adawiya da yana cikin Orphanage randa abin ya faru. Kuma an sanar masa komai akai.
Godiya ?an sanda sukai tare da juyawa da Nu'aymah zasu tafi. Tirjewa tai tana kallon Baba malam daya ?auke kansa gaba ?aya daga garesu tamkar baisan mi akeyiba. Hannunta ta fara ?o?arin fisgewa idanunta na cika da ?walla. "Abba wlhy bansan mina musu ba". Tai maganar muryarta na rawa.
Juyawa baba malam yayi zai bar wajen batare daya kula maganar Nu'aymah ba. Sai da yay taku biyu uku sannan ya tsaya tare da juyawa ya kalli ?an sanda da Nu'aymah data fisge zata dawo. Cikin tsananin kaushin murya yace, "Idan bazata biku da arzi?iba ku ?auketa!!".
Tsayawa Nu'aymah tayi cak tana kallon baba malam ?in. Sai kuma ta kalli inda su Umm suke. Sake dawo da idonta tayi kan ?an sandan da suma ita suke kallo. kunyar baba malam ce kawai ta hanasu fara cin ?aniyarta tun anan. Tsaf ta ha?iye kukanta. Ta juya cikin ?ingishi ta nufi ?an sandan. Basuce mata komaiba suka tasa ?eyarta gaba suka fita waje inda motarsu take.
A gaban ?an anguwa daketa kai kawo aka sakata a motar ?an sanda. Gaba ?aya hawayen da Nu'aymah ta fara ?azun sun ?ame ?af. Ta cusa kanta tsakanin cinyoyinta tai shiru. Sai faman cije baki kawai take saboda zugi da ?afarta ke mata. Har suka isa police station ?in bata ?agoba. Sai da ?ar sandar ma ta ta?ata sannan ta san sun iso. ?ago kanta tai a hankali ta kalli station ?in, sai kuma ta juya ga ?ar sandar dake mata kallon tausayi. Dan ita yanda taga mutanen na han?oro akan yarinyar ta zata ma wata tsohuwar macece, ashe yarinyace ?arama. Itace ta taimaka mata ta fito, ta kama hannunta ganin kamarma ta kasa tsaiwa. A haka suka shiga cikin station ?in da taimakon ?ar sandar.


"Amma Yaya ka......." hannu baba malam yay saurin ?agama Abban su Adawiya dake son masa bayanin ainahin abinda ya faru. Ya kallesa fuskarsa babu wasa, "Banason jin komai akan hakan Mustapha. Kaje ka shirya mu wuce banason yazam mu ake jira".
Kai kawai Abban su Adawiya ya ka?a masa. Kafin ya kalli su Abba Musbahu ya bar wajan jiki a sanyaye. Da sauri su Abban Abdallah suka nufi mota da nufin bin bayan su Nu'aymah, sai kawai a bazata suka tsinkayi muryar Baba malam na fa?in, "Na haramtawa kowa bin bayanta a cikin gidan nan, idan kuma wani ya aikata koda ban saniba zai fuskanci fushina".
Cak suka tsaya daga yun?urin shiga motar, kowannensu goshinsa na tara zufa. Babu wanda ya iya sake cewa komai har Baba malam ya shiga sashensu ya fito cikin shirin fita. Ta gabansu ya wuce zuwa sashen Hajjo data sha maganin mura tun ?azun ta kwanta. Duk wainar da ake toyawa bata saniba dan barci takeyi. Baifi mintuna biyarba sai gashi ya fito. Yanzunma bai kalli sashen da kowa yake ba ya nufi inda motar da zasu tafi take, sauran motocin uku da ?alibansu zasu shiga da ?an agaji kuma duk suna a harabar massallaci.
Suna kallo motar ta fice batare da ko mutum ?aya ya iya cemasa a dawo lafiya ba, shima kuma bai nuna ya damu da hakan ko jiran cewar tasu ba.

Umm ce ta fara sulalewa ta koma ciki, kafin sauran suma su fara zare jiki ?ai-?ai suna shigewa sashensu. Addah dai bayan Umm tabi tana share hawayen da ke sakko mata batare data farga da fitowarsu a cikin idanunta ba.

_____________
*_ABUJA_*

Tunda labarin kama Nu'aymah ya isa kunne Papa farin ciki ya mamayesa shi da Madam Chioma, breakfast da suke shirin zamanyi ma su kasawa sukayi, sai kai kawo sukeyi zuciyoyinsu fes kamar an basu rabin duniya.
Dolene yasa a koyama yarinyar hausawan nan hankali, dan shi a rayuwarsa idan da abinda yafi tsana a rayuwarsa to ?an yankinta ne. Ya tsani yarenta fiye da mutuwarsa, a cewarsa babu abinda suka iya sai haihuwa, ?a?an nasu kuma babu tarbiyya sam, daga ?an bangar siyasa sai masu bara. Sam mutanen da yankinsu basu masaba, inda ace zai iya zama shugaba, sai ya shafe yankin ko tarihinsu baza'a sake aji ba. (hummm Papa, a ringa sara dai ana duban bakin gatari).
Abinda papa ya keta faman rayawa a ransa kenan yana murmushi. Waya ya sake ?agawa yay magana da d.p.o ?in akan yanzunan a bama guards ?in Nu'aymah su taho masa da ita Abuja. Shi kuma d.p.o ya turo da accaunt Number ?insa yanzu zaiji alert.
Cike da farin ciki d.p.o ya amsama papa. Babu ko tunanin komai a ransa ya aika da accaunt details nashi, ya kumayi zaman shirya takardar ?arya akan laifin da bashi Nu'aymah ta aikataba.

(Humm! Ya ALLAH ka shiryemu ka shiryi shuwagabannin mu da jami'anmu. Ka tsame bara gurbin cikinmu, idan masu shiryuwane ka shiryesu. Idan bazasu shiryuba UBANGIJI kafimu sanin miya dace dasu, mun barka dasu??????).

________________
*_LAGOS_*

Fitowarsa kenan daga ?akin theatre a matu?ar gajiye. yanda yake tafiya kawai zai baka wannan amsar. Tare yake da likitoci uku da suka tayasa aikin, sai Nurses suma guda uku. Dai-dai sun ?araso ?ofar wani office nurse ?in dake a gefen damarsa ta mi?a masa tasar hannunta ya jefa hand gloves ?in daya cire daga hannunsa ya jefa a ciki, hannu ya ?aga musu kawai alamar su dakata anan ya tura ?ofar ya shige.
Basu damu ba, dan kowa yasan Dr Yoohan haka yake, mutum ne mai ?o?ari akan aikinsa da himma, ga tausayi sosai musamman ga marasa ?arfi. Bashi da yawan magana, sannan baida fara'a. Wanda bai fahimcesa ba zaita ?auka kamar kullum shi cikin ?uncin rayuwa yake, kokuma girman kaine bisa ga ?aukakar da ALLAH ya basa. Idan kuma ka fahimcesa zaka gane cewa haka halayyarsa take, shi kawai aikinne a gabansa ba shiririta da shashanci ba. Akance likitoci mafiya yawansu sunada son mata, sai dai ga Dr Yoohan sam ba haka baneba. Duk yanda matan ke binsa da soyayya shi bama su ishesa kalloba, shi fa a rayuwarsa damuwarsa kawai shine aikinsa, sai ko family ?insa da taimakon marasa ?arfi. Idan ya shiga cikin musulmi bazaka ta?a cewa shi ba musulmin bane, musamman daya ajiye ?asunba da yanda yake gudanar da al'amuransa sak halayyar musulman ?warai. Sai dai fa idan kaci karoda sar?ar Cross a wuyansa da akoda yaushe baya fashin sakawa ne zaka gane daga ina ya fito. ALLAH ya ?aukakashi a duniya a dalilin ?wa?walwar aikin likitanci daya azurtashi da ita, likitane shi da kota wane fanni zai iya gunar da aikinsa akan mara lafiya, sai dai abinda ba'a rasaba kam, dan UBANGIJI shine mai komai da kowa.

Office ne daya amsa sunansa office. Bakajin komai sai sassanyan ?amshin turarensa dana ac. Wanda ke zaune a rikunin kujeru uku dake can gefen office ?in yana aiki ya mi?e yana masa barka da fitowa cike da kukawa.
Kansa ya ?aga masa fuska a yamutse na alamar gajiya. kafin ya ?arasa ga kujerar zamansa yaja wani file dake a jiye ya fara singing.
Tasowa Richard yay da sauri garesa yana murmushi, ya ajiye files ?in hannunsa gaban Dr Yoohan ?in yana fa?in, "Doctor akwai mutane biyu da zaka ganifa yanzun kafin ka tafi hutun awa uku da rabi, idan lokaci ya cika zaka sake shiga theatre room, na mutane biyu da suka rage suma". Da sauri Yoohan ya ?ago yana kallon Richard fuska a marairaice kamar zai fasa kuka. Richard yay saurin ha?iye dariyar dake neman kufce masa dan yasan shima da gaske Yoohan ?in ya kai iyakar gajiya, amma sai ya fiske yace, "Da gaske nake Yoohan, gama files nasu na kammala dubawa".
"Rich.. Please, wlhy na gaji, sai dai kai ka dubasu" ya fa?a yana sauke numfashi da mi?ewa ya nufi wata ?ofa.
Murmushi Richard yayi yana binsa da kallo harya shige. Ya ?an girgiza kansa da kwasar files ?in ya fice daga office ?in zuwa nashi shima.
ALLAH ne ya ha?ashi da Yoohan tun a secondary school, a farkon ha?uwarsu sam basa shiri, dan abokan fa?an junane a aji. Ba komai yasa rashin jituwa tsakaninsu ba sai kasancewar su duka sunada matu?ar ?o?ari, kafin Yoohan yazo school ?in shike ?aukar na ?aya a ajinsu, amma Yoohan na zuwa ya amshe wannan matsayin. Kafin zuwan Yoohan ?in kuma kowa sonsa da girmamasa yake a ajin, hasalima shine Monitor, ?ammatan ajin ji suke tamkar su ha?iyesa kuma. Amma Yoohan na zuwa nanma komai ya canja, kan ?an ajin ya rabu biyu, wasu na ?angaren Yoohan wasu Richard. Dan haka aka zama abokan dabin juna, duk da sam Yoohan baya kula duk haukarsu. Rashin kulawar Yoohan ?in tasa a koda yaushe shi da tawagarsa suke ?auka Yoohan matsoracine, dan babu wanda ya ta?a ganin fa?ansa. Sai fa wataran da suka kaishi bango yayma Rich dukan mutuwa, da ?yar aka kar?esa a hannunsa dan Yoohan akwai zuciyar tsiya. Tun daga wannan duka da Yoohan ya masa suka koma abokan juna, tun sauran ?alibai na ?alubalantar abotar tasu har suka fahimci ta gaskiyace suma sukabi. Shi da Yoohan duk burinsu ?aya ne akan karatu, dan haka ha?ewarsu waje guda ta ?ara musu himma da ?wazo. Koda suka kammala secondary kuma cikin amincin ALLAH iyayensu suka amince musu tafiya karatu tare. A gaba ?aya rayuwarsu tare ta gudana, sai daga bayane Yoohan daya cigaba da wasu kwasakwasai (Courses) ne suka ?an rabu, danshi ya amshi aikin da aka bashine a ?asar London bayan zamowarsu cikakkun likitoci, sa?anin Yoohan daya ?i amincewa.
Daga baya Yoohan ya kuma samun ?aukaka fiye da tashi, danshi ya ?ara fa?a?a wasu karance-karancen daya bashi damar iya duba marasa lafiya ta kowane fanni, aikinsa ya zam zai iya yinsa a kowacce ?asa kuma.
Bayan shekara ?aya da fara wannan gwagwarmayar Yoohan ya fahimci bazai iya shi ka?aiba sai da taimakon Richard, dan haka yaje ya dabaibayesa da da?in baki har saida ya amince suka sake curewa waje guda suke gudanar da aikin a tare. Yanzu haka shekararsu ta biyu kenan da fara aiki, suna ?aya daga cikin manyan matasan likitoci da duniya ke alfahari dasu bama ?asarsu ko yankin Africa kawai ba.
A yanzu haka dai shi Richard ana shirin aurensa ma da wata baturiya, shiko Yoohan ya?i motsawa sam, a cewarsa shi bama zaiyi aure yanzuba sai nan da wasu shekarun daya tsara.

?akine madaidaici dake ?auke da kayan ?aki complete, shima sai ?amshi yakeyi kamar ba'a cikin asibiti ba. Kansa tsaye toilet ya nufa yana faman lullumshe idanu dan barci yake matu?ar ji. Tunda ya iso Lagos a daren jiya bai hutaba, dan ya iske patients da yawa da sukai booking ?in ganinsa. Tun a jiyan yay dauriyar zaman duba files ?insu, wa?anda yasan akwai mafita ya rubuta musu Doctors ?in da zasuje su gani ya turama Rich. Wa?anda kuma yasan sai shine zai duba ya sanar da Richard ya sanar musu time ?in da zasu gansa ta hanyar text messeges.
A safiyar yau tun ?arfe hu?u na asuba ya baro gida, tunda yazo kuma aiki yake bai hutaba. Bayan ya gama duba adadin daya ?ayyade ya shiga theatre akan matsaloli daban-daban kuma, yanzunma ba ya gama baneba, yanada loacin hutawa ne na awa uku da rabi kafin ya koma ?akin theatre ya ?arasama mutane biyu dake a ?asa kamar yanda Rich ya fa?a. Bayan ya kammala dasu zai ?ara hutun awanni uku jirginsa ya ?aga zuwa ?asar Kenya inda wasu patients ?in ke jiransa canma.
Bayan wasu mintuna ya fito daga toilet


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login