Showing 81001 words to 84000 words out of 325075 words
ri?e da shi Yoohan bai motsaba, duk da kuwa Rich na masa bayani ne akan wata harkar business ?insu da sukeyi tare.
Katafaren church ne mai girman gaske, wanda akaima gini na ?awa da ?aukar hankali, dan a gaba ?aya gaban church ?in da idanuna ke iya gani anyisane da zalkar glass. Yayinda akasa ?aton tambarin Cross da akayisa da golden ?in abu. Tun a farkon shigowar titin zaka faracin karo da muryar papa dake lecture. Gaba ?aya titin wajen sun kashesa babu maibi saboda motocin da duk akai parking masu tarin yawa. Securitys ?in church ?in da sauri suka shiga bama motsocin su Yoohan ?in hanya cike da tsantsar girmamawa. Sai da sukai parking a waje na musamman da aka tanada domin motocin nasu dama sannan aka shiga bu?e musu suna fitowa.
Yoohan ne ?arshen fita, dan sai da ya gama jan ajinsa kafin ya ziro sandarsa ta gayu sannan ya fito gaba ?ayansa. Gebrail da tun a hanya yaga alert yay saurin ?arasowa ya rungumesa yana godiya. Baice dashi komaiba sai shafa masa baya da yay ka?an.
Yanda securitys ke basu kariya da tsantsar kulawa sai ka ?auka dajin sambisa zasu shiga????, suna zagaye dasu har ta ?ofar da take ta musamman domin iyalan papan kawai da shi. Tanan suka shiga cikin church ?in dake a cike ma?il da mabiya kamar zai fashe.
Duk suka zuba musu idanu suna mi?ewar girmamawa a garesu cike da sha'awa da ?auna. Sai da suk suka ?aga musu hannu banda Yoohan da ko kallon basu ishesa ba sannan suka ?arasa wajen zamansu na musamman dake a gaba duk suka zauna.
Papa dake a gaban wani glass mai ?yau da aka ?awata da golden ga abin magana kusan hu?u a jiki yay murmushi yana ma iyalan nasa barka da zuwa, kafin ya cigaba da zubo bayani cikin kwakwazo da kara?in da aka san fastoci da shi, ko ha?iyar yawu bayayi??.
A hankali sai hayaniyar ta fara takurama Yoohan, duk da kuwa tunda ya zauna yana jingine ne da kujera idanunsa a lumshe kamar mai barci. Siririn tsaki yaja yana yamutsa fuska. Ya shafa kunnensa na dama dake manne da Bluetooth yana cizar lip. Sai kuma ya bu?e ido da motsawa zai mi?e Rich yay saurin ri?e masa hannu. Ransa a ?ace ya kallesa, sai dai baice komaiba.
"Please ka daure" Rich ya fa?a cike da marairaicewa dan kar Yoohan ?in ya bijire. Siririn tsaki ya kuma ja ka?an ya maida kansa ya sake kwantarwa ya rufe idanu.
Kusan awa guda Yoohan nata sake daurewa duk da kansa ya fara masa wani azababben ciwo. Kiran daya sake shigowa a wayarsa ne a karo na babu a dadi ya sakashi yamutsa fuska, duk kiran da ake masa bai amsa ko guda ?aya ba, amma yanzu sai yaji bu?atar amsawar. Mi?ewa yay zai fice Rich yay saurin sake ri?osa. Nuni yay masa da Bluetooth ?in kunnensa batare da yayi maganaba. Hakanne ya saka Rich sakinsa yana gya?a kai.
Sama-sama ya amsa mutumin dake gaishesa, kafin yay shiru yana sauraren bayaninsa da magiyar da yake masa akan bu?atar mutanen da kimarsu ta wuce ace Yoohan ?in ya?i bu?atarsu.
Ajiyar zuciya Yoohan ?in ya sauke a karon farko, batare da ya amsaba ya yanke kiran kawai. Wayarsa ya ciro yay ?an typing ya tura abinda shi ka?ai ya sani. Mintuna uku ba'a rufaba saiga reply an naido masa. Bu?ewa yay ya gani, batare da yayi maganaba ya maida wayar aljihu yana ?an dube-dube kamar mai neman wani abu. Sai kuma ya sake zaro wayar ya sake yin wani abun.
Yanzu kam ya kai tsahon mintuna biyar yana jiran reply ?in kafin a turo masa. Shiru yay yana ?an kallon wayar kamar mai nazari, kafin ya gya?a kansa da nufar inda motocinsu suke da wasu a cikin guards ?insa tsaye a wajen.
Batare da yayi maganaba ya mi?ama drivernsa hannu da masa nunin ya bashi key. Kamar driver zaiyi magana sai kuma ya ha?iyeta da sauri ganin kallon da Yoohan ?in ya zuba masa. Saurin bashi key ?in yayi, shi kuma ya bu?e motar da kansa ya shiga mazaunin driver yay mata key tare da yin reverse ya bar wajen securitys nata risina masa cike da girmamawa.............?
To ?an dabe ina zuwa kuma?????.
_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????
Mamu gee??
MIN ?ALB!!????
Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????
Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????
Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????
?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.
[4/6, 6:47 PM] +234 901 860 0202: *_INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN:_*
*_HERBALS APHRODISIAC NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_*
*_TO KU SAURARA KUJI, DOMIN NESA TAZO KUSA.._*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!!_*
*_MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA CIKI DA WAJE_*
*_MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI! LUWAI! TAMKAR TA JARIRAI_*
*_AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._*
*_KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_*.
*_AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_*
*_KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_*
*_MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_*
_INSTAGRAM LINK DIN MU:_
www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac
_WHATSAPP LINK DIN MU:_
https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz
_NAMBAR TARHON MU_
08169380189
*_KARKA BARI A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA 'DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYANMU A KO'INA A FADIN NAJERIYA._*
__________________________________
No. 22
...............Hankali tashe guards ?insa ke kallon juna, kowa nama ?an uwansa tambaya da idanu dan bakunansu sun musu nauyi har Yoohan yabar sashen church ?inma gaba ?aya.
Jigum-jigum sukai da fatan ALLAH yasa ya dawo da wuri kafin madam Chioma ko papa wani ya fito daga cikin church ?in.
Sai dai kuma addu'ar tasu bataci ba, dan bayan kamar mintuna ashirin da barin Yoohan wajen Rich da ya ga bai dawoba ya mi?e ya biyo bayansa bisa umarnin Madam Chioma. Yanda yaga Guards ?in sunyi diri-diri da idanu lokacin da yake tambayarsu ina Yoohan ya sakashi daka musu tsawa. Sake rikicewar sukayi, kowa na inda-indar bada amsa. A haka Madam Chioma itama data biyo bayan Rich ?in ta samesu. Sake ru?ewa sukayi, dan sunsan idanma azaba ce tafi papa akan Yoohan, ga Rich shima ?an babu sau?ine.
Da ?yar driver ya iya dauriyar fa?a musu yanda akayi, jikinsa har rawa yakeyi. Yanda Madam Chioma ta rikice sai ka rantse yaronta ?an shekara biyu ko uku ne ya ?ata. A take ta birkice lissafin Guards ?in Yoohan da securitys ?in church ?inma kansu. Ta kuma tabbatar musu nanda awa biyar idan Yoohan bai dawo ba saisun gane kuransu.
Ana a cikin wannan dambarwar ne aka tashi daga church ?in. Mutane suka fara tururuwar fitowa suna nufar inda ake rabon abinci. gudun kar ai abin kunya Rich ya shiga lalla?a madam Chioma akan ta kwantar da hankalinta maybe Yoohan gida ya nufa, tunda duk sunsan a yanayin da yake baya bu?atar kowanne kalar hayaniya. Zata iya yuwuwa ya ?osa ne da zaman shiyyasa. Da wannan ya samu yaci ?arfinta suka koma ciki inda suka tarar duk wanda zai fita sai yaje ya jefa ku?in baikon sa tare da kar?ar wani abu da papa ke saka musu a baki sannan mutum ya fice.
Matsawa madam Chioma tai kusa dashi tai masa magana a kunne, kansa kawai ya gya?a mata yana murmushi. Ita kuma ta juya ta fito yaranta da su Mira na biye da ita. Koda suka fito sai manyan mata suka zagayeta anata mi?a gaisuwa ga matar Pastor, harma da mazan da matasa kowa burinsa ya gaisheta. Yayinda wasu keta tambayar ina Yoohan dan sun riga duk sun gansa ?azun. Da yake shi dama zuwan nasa bawani sosai bane saboda yanayin aikinsa sai yazam duk sanda yazo sai su maidashi tamkar wani tauraro mai fitowa a daren sha biyar.
Cike da ya?e madam Chioma ke basu amsa da cewar wani uzirin gaggawa ya sakashi tafiya, amma wani satin zai tsaya yay gaisuwa da kowa.
Da ?yar ta samu kanta daga wajensu, gashi rabin hankalinta duk yana ga Yoohan da Rich keta faman kira ya?i ?aga waya. Daga ?arshe ma wayar bata shiga.
Tun shigowar motocinsu ?aton harabar gidan suka fahimci Yoohan ba gida ya zo ba, dan babu ko mai kama da motar da ya shigo acikin jerin mitocin dake gidan. Sai da suka gama fita sannan Madam Chioma ta ?walama maigadi kira cikin ?araji. Jikinsa na ?ari ya ?araso gareta cikin cika umarni.
Kafinma takai ga jefa masa tambaya Miracle ta rigata. Mai gadi yay saurin basu amsa da cewar Yoohan baizo gida ba. Gaba ?ayansu hankalinsu sake tashi yayi, kowa ya fiddo waya suka shiga nemansa..........??
????Mufa an ishemu kamar wani ?an gwal????.
_____________________________
Koda Yoohan yabar gidan wani ma'aikata ya nufa, duk da kuwa da ?yar yake jan motar saboda nauyin jiki dana zuciya da rashin baccin ya haddasa masa.
Yana tsaida motar a inda ta dace ya ?an kife kansa a sitiyarin motar na wasu sakkani, zuciyarsa ce keta faman masa kai kawo akan abinda yake shirin aikatawa. wani ?angaren na ?arfafasa akan dai-dai, wani kuma na raunana masa niyyar tasa. A haka dai ya kwashe mintuna har biyu kafin kiran daya shigo masa waya ya maidashi cikin hankalinsa. ?agowa yay a hankali yana yamutsa fuska, ganin mai kiran nashine ya sakashi ?agawa tana gab da tsinkewa.
"Na shigo" ya fa?a kawai cikin harshen nasara. Bansan amsar da aka bashiba. ya dai yanke kiran tare da bu?e motar ya fita.
Wani matashin saurayi da zasu iyayin sa'anni ya fito daga cikin ginin ma'aikatar fuskarsa ?auke da murmushi. Kallo ?aya zakai masa ka shaida shi?in musulmine, dan yana sanye cikin shadda bara sol dataji ?inkin tazarce, ga ?aton tambarin salla a goshinsa ya kuma murza ba?ar dara mai taushi.
Tunda ya tunkaro Yoohan ?in kallonsa yake ta ?asa ido cike da nazari. amma ba kowa zai fahimci yana kallon nasaba musamman idan akai dubi da yanda yay wata tsayuwar basarwa yana busar iskar dake ka?awa ta hantsi mai gauraye da ?umin rana.
"Ina fatan dai ba?o nane?". Saurayin yay maganar fuskarsa ?auke da fara'a duk da kuwa tun daga nesa ya gama shaida Yoohan ?in ba musulmi bane.
Duk da Yoohan yana mu'amulat da musulmai batun yanzuba, a mabanbanta ?asashe da yarurruka kuma, baya iya sakin jiki da su. Dan shi kullum yana cikin yin taka tsantsanne karsu cutar da shi kamar yanda aka ?orasa a hakan tun ?uruciya. Ya dai yarda zai ?yautatama mai bu?atar taimakonsa ko a wane irin yare yake ko addini, zai kuma gudanar da aikinsa da gaskiya ga kowa. Amma bai aminci da yayi dogon aminci da musulmin ba.
Sai dai kuma gashi yau a karan farko na tarihin rayuwarsa matsashin saurayi ya burgesa, harma da shigar kamalar dake a jikinsa. Duk da babu ?igon fara'a kota sisin kwabo tattare da shai sai ya jinjina kansa cikin lumshe ido yana mai mi?ama saurayin hannu.
Saurayin ya sake fa?a?a fuskarsa da murmushi yana fa?in, "Ina godiya ?warai da amsa wannan gayyata tawa da banyi zaton zata kar?u ba. Sunana Hamza Ibrahim khalil, manager mai aiki a wannan kamfani namu mai albarka". Yanda matashi Hamza yay magana da harshen ingilishi haka Yoohan dake binsa da kallo kwarjininsa na sake cika masa ido shima ya mayar masa da murtani cikin harshen nasaran. "Dr Yoohan Goshpower". Ya fa?a a hankali kamar bayason maganar, sai dai hakan bai hana voice ?insa mai amo fita da ?yau ba. "Ina sake godiya da amsar gayyata ta a karo na biyu Doctor".
"Karka damu" Yoohan ya fa?a a ta?aice. Hamza Ibrahim da kansa yayma Yoohan jagora har cikin office ?insa dake a ha?e masha ALLAH, dan babban kamfanine dake fidda kayan masarufi masu ingaci da lafiya ga jikin al'umma.
Sai da Yoohan ya zauna kafin Hamza Ibrahim ya kawo masa lemo, ya tsiyaya a cup tare da ajiye masa gabansa a kan table ?in. Godiya Yoohan ?in ya masa. Hamza Ibrahim ya sake yin murmushi yana gya?a kansa tare da yima kansa mazauni shima.
Sun sake gaisawa a karo na biyu. Yoohan ya sake bin ba'asin kiran da ya samu daga garesu. Babu wani ?oye-?oye Hamza Ibrahim yay masa bayani cikin nutsuwarsa, tare da mi?a masa envelope yana fa?in, "Wannan itace takardar da suka aiko da ita a baka, abinda yasa ban badata kai tsaye taje garekaba saboda gudun ha'incin mutane, zata iya yuwu akai takardar amma ta?i isa gareka. Shiyyasa na bu?aci dama nazo ni gareka da kaina na kawo maka. Sai ma kace min zakazo da kanka.
Yoohan daya gama duba takardar ya ?an ?ago kansa yana kallon Manager, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya ha?iye abinsa a rai yana ?o?arin maida takardar cikin envelope ?in.
Duk da Hamza yayi mamaki da ganin Yoohan ?in a matsayin wanda yaketa faman hidimtawa bayin ALLAH haka ya ha?iye mamakinsa, dan yayi imani da UBANGIJI na fidda rayayye a cikin matacce, kuma ana samun mutanen kirki a cikin kafiranma, wanda wasu musulman mu sukan gaza gyara zukatansu su zama haka duk da addininmu ya koyar damu komai. cikin hikima irinta masu ilimin addini dana zamani yace, "Yalla?ai ina fatan dai zaka amsa wannan gayyatar? Dan suma mutanene masu karamci da mutunci kamar kai, na tabbata alkairinkane kuma yake sake girmamarsu shiyyasa suka shirya wannan liyafar a gareka domin nuna girmamawarsu a kanka".
Karan farko a rayuwar Yoohan da kalaman hikima sukai masa da?i a rai, har yay wani ?an motsi da la??ansa mai kama da murmushi amma ba murmushin bane ba. Idanunsa ya ?an lumshe na wasu sakanni yana nazari. Ba zuwan bane matsalarsa, ciwonsane damuwarsa. Bayason kowacce kalar hayani, ba kuma ya bu?atar shiga cikin kowanne irin mutane gudun ?untatama wani. To amma kuma maganar Manager tai tasiri a ransa harma da tunaninsa.
Bu?e idanunsa yay a hankali ya ?an gya?a kansa, "Babu damuwa zanje ?in, sai daifa ka shirya ayi tafiyar tare da kai". "Ni kuma Doctor?". Manager ya fa?a yana ?an waro idanu. "Indai kace bazakajeba nima kam zan fasa, dan saboda kaine dama zanje. Banyi musu komai dan su damu da sanina ba, sannan wanna shine karo na farko da aka bu?aci yimin karamcin da bai shafi aiki na ba ko yarena ko addinina ba. Shiyyasa nakeson na halarta ko zai shiga tarihin farko da ?arshe na rayuwata".
Manager ya gya?a kai a ransa yana fa?in 'daga ganin wannan a Christians ?inma inaga ?an ?ari?ar Catholic ne, ALLAH yasa ina ?aya daga mutanen da zasu jagoranci duhunsa ya samu haske' a zahiri kuma sai yay murmushi da fa?in, "Babu damuwa, indai kana bu?atata a tawagar masu rakkiya bazan ?i ba".
Hannu Yoohan ya mi?a masa tare da yin godiya, kafin ya mi?e alamar zai wuce dan yasan hankalin families ?insa nacan a tashe da rashin ganinsa.
Har mota Manager yay masa rakkiya yana ?ara masa godiya sosai, dan yana cikin mutanen da ayanzu company ?in ke jin da?in shigowarsu cikin manyan Customers.
¡ï¡ï¡ï
Lokacin da Yoohan ya iso gidansu ya iske kowa a birkice, dan har papa ya baro church yayo gida. Harma yana shirin kiran police station yay report.
Tun a harabar gidan ya fuskanci akwai abinda ke faruwa a gidan, dan yaga ba?in motoci da yake ?yautata zaton na Uncles nashi ne. Sannan yanda yaga Guards ?insa da sauran securitys ?in gidan na sauke