Showing 312001 words to 315000 words out of 325075 words
Sai da suka bashi damar hutun kusan mintuna biyar ya daidaita sannan ya fara bada labari.
"Ni da shi twins ne. Muna tsananin kamanni har takai jama'a basa iya banbantamu inba mahaifiyarmu ta fa?a ba. Duk da itama wani lokacin rikicewa takeyi. Suna ?aya iyayenmu suka saka mana wato Goshpower. Takai inhar ka kira ?aya a cikinmu sai mu amsa maka mu duka. Mamanmu ta ta?a fa?a mana kaifin basira da muke da shi da farar fata tasa har ana dangatamu da wasu sunaye. Wasuko na tsoronmu da fa?in mama debora ta haifi wa?anda ba mayu. Wannan ba sabon a bu bane daga hallayar mutanen ?abilarmu da yankinmu wajen danganta mutum mai fari da ?yawun jiki da suna na tsoro. Mutane basu fara samun basirar banbantamu ba sai da muka fara girma halayenmu suka fara banbanta tsakanina da ?an uwana. Mu duka munada kaifin basira da wayo, sai dai kowa da yanda yake gudanar da tashi. Duk inda gaskiya take zaka samu ?an uwana a wajen, niko sa?anin haka shine za?i na. Kullum cikin takalo rikici nake wa iyayenmu, ?an uwana kuma bai gajiya da bayyana gaskiya idan an tambayesa. A duk lokacin kuma da nai niyyar cutar da shi akan wannan abu da yakemin sai bana samun nasa. Dan ko fa?a zamuyi yafi ?arfina. A haka dai muka kammala primary, akwai sha?uwa mai ?arfi a tsakaninmu, amma bamu cika zaman lafiya ba da zama waje ?aya na dogon lokaci. Bayan secondary skull muka wuce jami'a, inda anan mabanbantan halayenmu suka sake bayyana. Duk da mu duka muna karatu ni a koda yaushe hankalina nakan mata, sannan duk wani abokin banza zaka samu nawane. Hakan na ?atama ?an uwana rai, tun yanamin nasiha da fa?amin gaskiya har yayi zuciya ya daina, daga ?arshema muka raba ?akin kwana, dama ba department ?inmu ?aya ba. Haka dai muka cigaba da tafiya, kafin mu kammala jami'a na zama ri?a?en mara jin magana dan har harkar ?waya na fara, sannan na shiga cikin ?an Cult. Mun kammala degree ?inmu na farko, ta hanyar ogan babanmu muka samu taimakon tafiya ?asar Italy ?aro karatu. Daga nan ne labarin canjawar komai ya fara. Dan watanninmu biyar kacal a makarantar na sake canjawa daga duk yanda aka sanni. Idanuna sun sake bu?ewa sosai harna fara harkar cocaine. Ta hanyar wanda na fara harkar Cocaine ne idanuna suka sake bushewa. Ya kutsa dani cikin manyan mutane konace tantirai dake juya duk wani iya shege na duniya. Nasha wahala ba ka?anba wajen kar?ar horo daga garesu har takai makaranta ma na daina shiga duk da yawan damuwa da kirana da ?an uwana keyi, tare da yawan ?o?arin son sanin abokan mu'amulata. Muna shekarar ?arshe daya kamata mu kammala degree ?inmu na biyu ?an uwana ya ha?u da matashiyar Balarabiyar saudia mai suna Anum. Itama karatu tazoyi, wannan kuma shine zangonta na farko. Sun fara rayuwa kamar abokai a hankali suka riki?e zuwa masoya. Sam bansan da wannan soyayya tasu ba sai da tai nisa, muna ma gab da kammalawa. ko nace ?an uwana na gab da kammalawa. Danni tuni na yaye kaina daga zuwa makaranta. Sai dai nakan shigo lokaci-lokaci saboda har?allar dake tsakanina da ?alibai ta kayan shaye-shaye. A wani shiga da nai cikin makarantar ne na ha?u da Anum, wadda ina cikin tafiyata tazo tasha gabana, a zatonta ?an uwana ne. Da farko na harzu?a matu?a, sai dai ?yawunta yayma idanuna barazana da danne fushina. Cike da tsokana take kallona tana dariyar wai yaushe nasai kayan jikina?, ita dai basu mata ba. Naji haushin kalamanta amma saina fuske na barta akan ?an uwan nawa ne. Kiran wayata da ogana yayine yana min neman gaggawa yasa na sulale nabar Anum da nufin zan dawo gareta. Daga haka bansan yanda ta ?areba bayan taga ?an uwana. Shin ya warware mata mu ?an biyu ne, kokuwa ya kar?a mata matsayin shine ni?. Kwana biyu da yin haka na dawo cikin skull neman Anum sai dai na samu labarin cewa sun wuce saudia ita da ?an uwana. Samakon zuwa da yayunta biyu sukai suka ganta da ?an uwana daba musulmi ba".
"Duk da bana shiri da shi hankalina ya tashi matu?a, dan kodai babu komai shi?in ?an uwanane ai. Duk zatona ko zasu cutar da shi ne? Naso binsu duk da bansan ina suka nufaba sai kuma wani aiki ya sake taso mana zuwa ?asar Germany. Haka na tafi al'amarin ?an uwana na damuna a cikin rai. Kamar wasa sai ga wannan tafiya ta jani tsahon wata hu?u, lokacin da muka dawo ?asar Italy saina samu munyi graduation, course mate ?ina duk sun kama gabansu har ?an uwana. Na bincika Anum sai na samu wai itama tabar makarantar. Daga jin haka sai kawai na nufi Nigeria, a zatona ?an uwana ya koma gida. Amma kash sai na iske sa?anin tunani. An dai tabbatar min yazo wata biyu da suka gabata wajen rasuwar mahaifinmu, nima anta nemana amma ba'a sameniba. Ko damuwa banyi da mutuwar babanmu ba, sai dai jin ogan babanmu ya bama ?an uwana ma?udan ku?in aikin da mahaifinmu yay aiki a ?ar?ashinsa dan yaje ya juya hankalina ya tashi na bukaci sanin ina ?an uwana yake?. Mamanmu bata saniba, abinda kawai ta sanarmin shine ya sake barin ?asar, bakuma susan ainahin ?asar daya tafi ba. Yadai bar musu ku?in da zasu ishesu, tare da musu al?awarin nanda shekara guda zai dawo musu da dadda?an labari. Nayi ?wafa kawai bance komaiba. Daga haka na tattara kayana zan koma. Sai dai kafin na wuce na ha?a har?alla da abokaina akan zanke turo musu kaya insha ALLAHU suna saidawa su tura min ku?in. Sunko amince tare da min al?awarin bazasu bani kunyaba. Daga haka na tattara na koma inda na fito, babu wani zancen nasarar da naci a karatuna dana zauna naima mahaifiyarmu. dan koma ban fa?aba nasan ?an uwana ya gama tona mata dukkan zance a kaina".
"Ban sake sanin ina ?an uwana yakeba, ba kuma mu sake ha?uwa ba sai bayan kusan shekara, ana gab da zai cika al?awarin daya ?aukama iyayenmu na komawa garesu da dadda?an albishir. A lokacin naje kai kaya ?asar Syria ne. Kwatsam zamu shiga wani shopping mail ni da abokin tafiyata sai ga twin Brother ?ina tare da balarabiyar yarinya dana ta?a ha?uwa da ita a Italy a bazata. Da gani har shi babu wanda baima ?an uwansa kallon mamaki ba. Hakama mafi yawan jama'ar wajen kallon mamaki suke mana da al'ajabi. A zahiri dai gashi muna tsananin kamanni, amma a shigar sutura da yanayi bama muyi kama da ?an yanki ?aya ba. Ni na fara sakin murmushi ina kallon jaririn dake rungume a kafa?arsa, sannan na kalli Anum na sake kallonsa. Goshpower kaine anan kuma?".
"Shima Murmushin ya saki a karo na farko yana girgiza min kai, yace my twin bro, wannan suna yanzu na bar maka. A yanzu sunana IBRAHEEM ne, wannan matatace Anum, ga yarona Abdul-Maleek. Woow!! Na fa?a ina dariya da tafa hannu, kafin na mi?a hannun ya ?oramin jinjiri Abdul-maleek. Yaro ?ya?y?yawa mai tsananin kama da mahaifiyarsa, sai dai ya kwaso kamannina nima ni da ?an uwana ka?an. Ganin dai da gaske munsan juna abokin tafiyata ya barni tare da su yana fa?in mu gaisa shi zaije ya kai kayan zuwa anjima saimu ha?u. Na amsa masa da jin da?i, dan koba komai ina bu?atar ke?ancewa dama da ?an uwana dan naji yaya batun ku?in daya amso a Nigeria suke. Dan ko ka?an banji wani damuwa da fahimtar ya koma musulmi ba. Kamar ya shiga raina kuwa. Sai ya bu?aci mizai hana muje gidansa kawai, ashe nan yake da zama yanzun. Mun shiga dan?areriyar motarsa dani da ke wahalar nema da shiga ha?arin rayuwa ko wadda bata kamitaba bani da ita. Wannan abu ya sosamin rai, amma sai ban nunaba muka shiga, suna gaba shida matarsa niko ina baya tare da jaririnsu a hannu. Al'amari bai kuma tadamin hankaliba sai da muka isa ?aton gida da yaji kayan more rayuwa a matsayin wai nashine. Lallai nasha kallo, cikin mintuna kalilan kuma matarsa ta gama cika gabanmu da kayan ciye-ciye. Sai bayan munci mun ?oshi mukai gaisuwa da tambayar bayan rabuwa. Bai ?oye min komaiba daya shafesa bayan rabuwarmu".
Yace, (?an uwana kamar yanda na sanar maka wannan itace matata, mun ha?u a jami'ar Italy daka?i nutsuwa ka ?arasa. Da farko tsakanina da ita abota ce, sai daga baya muka fahimci muna son juna. Sai dai ta tabbatarmin babu yanda aure zai kasance a tsakaninmu saboda addinimu ba ?aya baneba. Hankalina ya tashi domin ina tsananin ?aunarta. Nai al?awarin inhar zata yarda mu zama ma'aurata zan koma addininta. Ta sake tabbatarmin indai saboda aurenta ko soyayyar da nake matane zan zama musulmi wannan bazaisa ta yarda ta aureniba. Na musulinta kawai domin ALLAH badan tarayyarmu ba. A hakanma na yarda na amince, a randa muke shirin zan karbi shahada aranar ?an uwanta biyu sukazo dubata. Sun nuna mata tsantsar ?acin rai nayin tarayya dani, harma yanda ake musalta musu a cikin makarantar mun zama tamkar wasu miji da mata. Dagani har ita hankalinmu ya tashi muma. Dan tunda nake da ita ko maganar banza bata ta?a shiga tsakanina da itaba. Bata ta?a yarda ko zama gab da juna munyiba balle akai ga aikata wani abu mara ?yau. Ni bamma ta?a kawo wani mummunan al'amari tsakanina da itaba kamar yanda nasan itama hakanne daga gareta. Kawai dai ALLAH ya ha?a jininmune kawai, kuma ina koya mata karatu. Duk yanda mukaso su sauraremu sunki, daga karshe ma suka tattarata wai zasu wuce da ita. Banyi ?asa a gwiwa ba wajen tattara duk abinda nake da shi na bisu batare da sun saniba. Sai da muka dira ?asar saudi-arebia suka fahimci jirgi ?aya ma muka shiga da su. Sun nuna jin zafin binsu da nayi, amma sai basu hanani na bisu har gidansu ba. Koda muka isa gidansu sunma iyayensu bayani akan dukkan ala?ar dake tsakanina da Anum. Maimakon nai zaton za'a koreni sai naga sa?anin hakan, dan kuwa sun yarda da bukatata ta zama mai salla. Amma babu zancen aurena da Anum, dan suncemin yarinyarsu karatu takeyi. Duk da na shiga tashin hankali saina amince a hakan zan musilinta ?in. A take kuma na amshi shahada. Komawata musulmi ya sake canja komai, dan kuwa sunmin gagarumar ?yauta maiban mamaki ta ma?udan ku?a?e wai na ri?e kaina, tare da ha?ani da wani malami dazan dinga ?aukar ilimi a hannunsa a ?asar Italy. Satina biyu a saudia na dawo saboda karatuna. Amma daka ganni kasan bana cikin hayyacina saboda rabani da akai da masoyiyata. Duk na rame na fita hayyacina, amma hakan baisa nayi sakaci da karatuna ba. Na cigaba da neman ilimin addini da zana jarabawar ?arshe data rage mana na tsahon watanni biyar. Har muka kammala jarabawa banji labarin kaba. Na bincika ance bakaje Nigeria ba. Hankalina ya tashi matu?a. Amma yaya zanyi. Bayan yin graduation ?inmu na tattara zan koma gida ?asata. Amma maimakon nayi 9ja direct saina kasa ha?uri na nufi Saudia wajen Anum. Nayi mamakin tarbar dana samu daga iyayen Anum da ita Anum ?in kanta daya kasance tazo hutu, dan lokacin karatunta ya dawo nan ?asar Syria. Albishir na farko da suka faramin shine bani auren Anum, ashe dama sun gwadanine dan suga da gaske nakeson komawa addinin islama kokuwa dan son ?arsu?. Shiyyasa suka ha?ani da malamin dake koyar dani batare da nasan bayanai yake basu ba a kaina. Nayi farin ciki nayi kuka dan da?i. Sai dai da aka nema na gabatar da iyayena na fito fili na tabbatar musu akwai matsala. Dan nasan kaf danginmu babu wanda zai amshi canjawata matsayin musulmi balle kuma auren musulma kai tsaye. Naji tsoron Anum zata sake ku?ucemin sai gashi ba hakaba. Dan duk da abinda na sanar musu sai gashi sun amince sun bani aurenta. Bayan ?aurin aurena da Anum an bamu wajen zama kafin ta koma makaranta. Watanmu ?aya da tarewa ta koma makaranta, ni kuma naje gida Nigeria, sai dai kowa ya tambayeni ina kake sainace kanacan baka ?arasa naka karatunba sai next year. Na tarar jikin babanmu yayi tsamari, amma sunki kaisa asibiti. Inada ku?a?e masu nauyi a accaunt dana samu saboda musilintar da nayi, dan haka nai amfani dasu wajen kaisa babban asibiti aka fara bashi kulawa. Sai dai kash, kwanakinsa hu?u a asibiti ya rasu. Bayan rasuwarsa da kusan sati biyu nace musu zan koma domin yin kasuwanci. Ananne ogan daddy ya bani ku?a?en daddy, wai yace a bamu idan munzo, tunda mune manyan ?a?ansa maza. Na amsa ku?i na basu wanda zasu wadacesu na koma saudia. Mahaifin Anum shine ya ?aurani akan harkar kasuwanci acan ?asar Syria, ya bani shawarar na koma can kusa da matata ina kasuwancina tana karatunta. Naji da?in wannan shawara kuwa. Tafiyata Syria ta zama tushen nasarata, dan ina zuwa na iske matata na laulayin ciki. Nayi farin ciki matu?a, harma bansan yaya zan musalta makaba. Haka na zauna kulawa da ita tare da fara kasuwancina. Cikin amincin ALLAH sai gashi dan danan na ha?aka. Saboda na farane da ku?a?e masu nauyi. sannan kuma ta hannun babban mutum irin mahaifin Anum. A haka cikin Anum ya shiga watan haihuwa, tana gab da haihuwa na sayi wannan gidan da nake ciki, tare da motar hawa. Sannan na zauna na banbance dukiyar da take matsayin mallakina, na kuma fidda wadda ta kasance ta mahaifinmu. Kwanaki uku da yin haka Anum ta haihu namiji, wanda yaci suna Abdul-malik. bansan yaya zan bayyana maka ?unbin farin cikinaba ?an uwana. Amma babu abinda zancema ALLAH sai godiya. A yanzu haka watan Abdul-maleek uku a duniya, muna shirin zuwa Saudia ne domin nunasa ga dangin Anum dan babu wanda ya ta?a ganinsa sai mahaifinta da yazo mana nan sanadin harkar kasuwarsa. Daga Saudia kuma zamu wuce Nigeria na nunata ga dangina, na kuma sanar musu na zama musulmi duk da a tsorace zuciyata take. Dan yanzu haka maganar da nake makama nayi cinikin wani gida a Lagos, idan munje can zamu ?an zauna kafin hutun Anum na ?arshen shekara ya ?are. Wa?anan takardun sune takardun shaidar company na dana mallaka da dukiyata. Insha ALLAHU kuma zan mallakashi ga Abdul-maleek ne. Dan haka kaima inason ka zama shaida, kaimin signing anan wajen, a duk lokacin da yakai shekaru talatin na girma zan mallaka masa shi. Wannan kuma sune takardun dukiyar mahaifinmu, idan nazo Nigeria mu dukanmu zamu ha?u mu saka hannu alamar tabbatarwa da banawa bane ni ka?ai).
"Rungumesa nai a lokacin, na nuna masa tsantsar jin da?ina da wannan ?o?ari nashi, tare da bashi goyen baya akan zamansa mai sallah. Yaji da?in yanda na bashi goyon, hakama matarsa. Sai dai ni a cikin zuciyata ?ulla ta yanda zan kwashe wa?anan takardun nakeyi, tare da damfare duk wata dukiya da yake fankamar ya tara. Banbar gidanba sai dare, na tafi da ?udiri kala-kala a cikin raina da zuciyata".
"Washe gari ma naje na samesu, shine ya ?aukeni ya zagaya da ni duk inda companys ?in suke guda biyu. Na ?ara girgiza da wannan al'amari, dan dukiyace bata wasaba ?an uwana ya tara. Tofa sai tunanina ya ?ara fa?i da girmama. Dan koda nabar wajensu a ranar kasa barci nayi, har takai na fito na bayyanama abokin tafiyata. Yace na bashi dama zaiyi tunanin ta yanda dukkan wannan dukiya zata zama tawa, amma sai nan da kwana biyu mun gama abinda ya kawomu zai fa?amin hukuncin daya yanke. Naji da?i, na kumayi murna. Sai dai wayewar garin ranar al'amari ya canja salo, dan bamusan yaya akaiba aka kama wanda muka kawoma kayan cocaine. Har bincike yazo ta kanmu. Da farar safiya mukaji jiniyar motocin ?an sandan ?asar. Hankalina ya tashi matu?a ni da abokin tafiyata, cikin zafin nama muka samu nasarar tserewa ta bayan gidan kafin ?an sanda su gama shigowa gidan. Muna barin gidan muka rabu nida abokina, domin wannan gudune na ceton rai, kuma hakan abune da kowa ya sani daga tsagera. Idan bala'i ya tunkaro kowa takansa yakeyi. Ba'a sauraren dukiyar da aka tara balle abokantaka. Cikin ki?ima na nufi gidan ?an uwana, dan duk da wannan bala'i da nake a ciki ban manta da batun takardu ba. Ina isa na samesu a tsakar gida suna hutawarsu cikin kwalliya. Dakewa nai daga ru?anin da nake ciki na amshi jaririnsu, tare da fa?ama matarsa nifa inajin yunwa. Dariyar tsokana suka dinga min, ?an uwana na fa?in to nazo nayi aure, yafimin wannan gararin, danshi sofa yake na dawonan tare da shi mu ha?a ?arfi wajen kula da kasuwancinmu. Murmushi kawai nayi, na shiga daga ciki ?auke da yaron. Matar ta shigo ta bani abinci. Tana kammala ha?amin komai ?an uwana ya shigo, kallonta yay cike da so da kauna, yace tunda ga bro yazo kizo muje muyi shopping ?in nan da bamuyiba jiya, sai mubar Maleek tare da shi dan harmu dawo da wahala ya farka. A take ta amince da shawararsa. Yayinda ni kuma kaina ya kawomin wuta a take. Jacket ?in jikina na cire jin yana fa?in bara ya karo riga a saman kayansa. Nace bro indai rigace ga wanann ka saka nasan zata maka ?yau, dan yanzun nan dazan fito na ganta a wani shago na siya. Nama tambayi biyu akace babu. Cike dajin da?i ya amsa, dan shi mutumne mai saukin kai. Sannan bashi da saurin zargi. A gabana matarsa ta taimaka masa ya saka suna dariya da yaba ?yan da rigar tai masa. Murmushi nayi ina dubansa na ajiye yaronsu na tashi ina gyara masa rigar, cikin dabara na saka masa wayata da wallet ?ina a aljihu, na zare tasa wayar da wallet ni kuma. Sunmin sallama sun wuce bayan sun tambayeni abinda nake bu?ata a siyomin nima, dan yace idan ya dawo zamuyi magana akan zamana a gidan. Suna fita na kulle ?ofar falon, na bar yaron anan na shiga cikin ?akinsu binciken takardu dama duk wani