Showing 57001 words to 60000 words out of 325075 words

Chapter 20 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29161

haifesu ne amma baka haifa halinsu ba, minenema bazasu aikataba tunda basa ganin idon kowa. Ballema Nu'aymah da batajin magana sam, wuyarta dai ta samu sakewa ne kawai, shiyyasa sam banason ko gidanmu tace zataje ta kwana ko wani waje wlhy, danni bansan ina ta ?akko wannan halin nata na tsiwa da rashin kunyaba". Yanda Umm tai maganar cikin ?acin rai yasa Addah saurin fa?in. "Dan ALLAH karki tsaurara harshenki akan wannan abun, mudaibi komai a sannu muji inda matsalar take. Nu'aymah har yanzu yarinyace, kuma sanin kankine duk rashin ji da tsiwar Nu'aymah batayinsa ita ka?ai sai da gudunmawar su Adawiya dama, tunda halin nasu ai duk ?aya ne....."
"Humm Addah kema kinsan indai gaskiya zaki fa?a Nu'aymah ta fisu kaifi, dan duk abinda zasu aikata itace jagora". "To kowa ya zauna akan ra'ayinsa danni bawai yarda zanyi ba, inaga dai bara nakira su Yusrah muji minene ya faru?". Umm dai batace komaiba, tanata kuma ?o?arin danne damuwar dake cizon ranta da kukan dake yun?uro mata a rai. Duk da Alhmdllh zuwan Addah a gareta ya sanyaya mata fushinta bakamar sanda ta shigoba.

Sallamar Yusrah da Amal ce ta saka Umm da Addah ?agowa suna kallonsu. Basai an fa?aba, daga gani kukama sukeyi. Hakan da Umm ta gani sai ya sake karya mata zuciya, tai ?asa da idanunta tana karanto7 addu'ar neman sau?i da sassauci wajen UBANGIJI.
Zama su Yusrah sukai kansu a ?asa suna sharar ?walla. Addah tace, "Kuka ba shi bane mafita Amal da Yusrah, ku sanar mana mikuka sani game da hakan dan musan hanyar data dace mu kama wajen amso ?ar uwarku".
Share hawayensu duk sukai, cikin nutsuwa sukaima su Umm bayanin abinda ya faru aranar ?unshi, sai dai sun ?oye cewa Nu'aymah ta fasama guards ?in kai, sundai ce ta wulwula dutse bisa tsutsayi ya daki glass ?in motar. Hakan da tayine kuma ya saka mutanen tsayawa amma da guduwa zasuyi.
Shiru babu wanda ya iya cewa komai tsakanin Umm da Addah, sai da kusan mintuna uku Addah ta sallamesu suka tafi.

"Umm! Inaga lokaci yayi da zamu fara aiwatar da shirinmu a gidan nan gameda wa?anan abubuwan. Na kula al'amarin ?ara zurfi yakeyi kullum".
Murmushi Umm tayi idanunta akan Addah, ta ce, "Addah wannan ai babu saka hannun kowa a ciki, itace ta jama kanta. Ni wlhy a yanzuma naji bana sha'awar sanin wanda ke aikatawar........."
"Me yasa?"
Addah ta fa?a da mamaki.
Murmushi Umm ta sake yi har ha?oranta na bayyana, tace, "Addah to minene amfanin sanin? Babu abinda sanin zai amfanar sai fitina. Idan a gidan nan yake zai zama sanadin lalacewar zumincin da aka gina bisa ha?uri da juriya. Idan kuma a waje yake za'a jawo masa tsana daga mutane a tozarta iyalansa. Addah hakan baida wani amfani a gareni, dan wlhy bana fatan kwana da wani musulmi a cikin raina koda na kwana ?aya ne, dan bani da tabbacin wayar gari. Koma wanene UBANGIJI ya rufa masa asiri na tsahon lokaci, ya kuma fimu sanin hikimar yin hakan. To mu ha?ura kawai mu barsa da UBANGIJIN ya ishesa komai".
Ba ?aramin ?urama Umm ido Addah tayiba, har sai da takai Umm ?in ta ta?ata da fa?in, "Ina kika tafi kuma?". Murmushi Addah tayi da sauke ajiyar zuciya. Tace na tafi duniyar mamaki ne da tsarkake sunan ALLAH, Umm ki godema ALLAH ya azurtaki da ?ya?y?yawar zuciya wlhy........"
"Kema ai ya azurtaki da ita Addah, dan ina koyi da wasu ?yawawan halayene daga gareki. Hakan yasa ?aunar da nake miki ta dabance a zuciyata wlhy, fatar bakima bazata iya kwatantawa ba, kun bani gudunmawa ke da Baba wadda har na koma ga ALLAH bazan gazaba wajen ro?a muku rahama da yardarsa".
Hawayene ya cikama Addah ido kamar yanda ya cikama Umm itama, suka kama hannun juna suna murmushi cike da ?aunar juna da ta ginu tun ?uruciya..............?

(ALLAH ya bar ?auna Umm da Addah??????)

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________


Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????

Mamu gee??
MIN ?ALB!!????

Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????

Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????

Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????

?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.[3/26, 1:01 PM] +234 901 860 0202: _____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________

Wani kaya sai amale ka ?auka??.

SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.

Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ?an gaske.

*_Ina mata masu ?an bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ?ar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ?an ?walisa masu son sabunta gida da kayan ado ?an waje masu sau?in farashi da nagarta!._*

_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ?aya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ?yau da nagarta a farashi mai sau?i kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ?an gayu suma akwaisu babu ?ayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba'a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ?aki basu da tsara_.

Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.

Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ?arin bayani ?ar uwa.

*_Siyen nagari??, maida ku?i gida?? sai SAHFAT PREORDER??????????_*

_____________________________
*_SAUDIA_*

.............Kai kawo taketa faman yi a falon nasu dake wadace da sanyin ac da ?amshi kai kace safa da marwa take gudanarwa. Ta canja sosai, dan komai na jikinta ya ?ara girma da cika. Daman can duk tafi su Nu'aymah girman jiki kasancewar ta ?akko jikin Addah. Yanzu kuma darajar aure saita sake bata damar bu?ewa tamkar ba ?ar shekara goma sha takwas ba.
Tabbas tana samun ci da sha da sutura duk irin wadda ta bu?ata, sai dai a watanni tara kenan da aurenta da Yah Abdallah babu wata rana da zata ware ta dangantata da farin cikinta. Idan har ta samu kulawarsa to na wasu awoyine da zai biya bu?atarsa. Baya son zaman gidan sam, ita kanta har mamaki take da al'ajabin ina yake zuwa bayan makaranta da harkar kasuwancinsa?.
Duk yanda taso fahimta ko gano hakan ya gagara, babu kalar dabaru da maman Aaida bata koya mataba duk kuma ta bisu daki-daki amma ta gaza samun haske. A yanzu haka wata ?ura ta fahimta baibaye da ita game da mijin nata shine dalilin kaiwa da kawowar tata.
Tun daga randa Abdallah ya fara kusantarta ba'a cikin hayyacinsa ba a washe gari ya ha?ata da wasu ?wayoyin magani guda biyu. Daga haka kuma duk sanda zai kusanceta sai ya batasu ta sha. Tun bata ta?a kawo komai a ranta game dasu ba harta fara zargar wani abu. Ba komai ya kawo mata zarginba kuma sai haihuwa da akullum maman Aaida ke kawa?aita mata ta sanadinta zata iya samun soyayyar Abdallah, tunda sunyi dukkan wasu dabaru ya?i hawa network. Da farko Adawiya batason ta haihu yanzu, amma da taji wannan magana daga maman Aaida sai taji ?wa?ayin hakan itama dan tana masifar son Yah Ab. To amma sai me? Har yanzu babu ciki babu alamarsa a gareta, har zuwa asibiti tayi a ?oye aka dubata Doctor ya tabbatar mata inhar bata daina sha maganin hana ?aukar cikiba bazata ta?a samun ciki ba.
Wannan magana ta daki zuciyarta, dan a ?an hasashenta ta fahimci kenan maganin da Yah Ab ke bata kullum na hana ?aukar cikine? Duk da zuciyarta ta?i aminta da hakan sai taji tana ?wa?ayin dubawa ta tabbatar. Wannan shine dalilin kai kawonta tana nazarin hanyar data dace tabi wajen binciken maganin a ?akinsa batare daya saniba ko ya ganta. Saboda haka ta?i zuwa makaranta yau ta zauna gadin fitarsa. Sai dai kuma har yanzu bataji ko motsin alamar zai fitoba balle tayi tunanin fitar tasama kamar yasan mi take shirin yi....

(Humm muje zuwa baby Adawiya????).

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Wannan littafi SARAN ?OYE na ku?ine, yana ?aya daga zafafa biyar, idan kana bu?ata kaima wa?anan numbers ?in magana ka biya ku?insa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka ya?a dan ALLAH idan ka gani??????.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

_______________________
________________________

Dr Yoohan ya bama matar da yazo kano dominta dukkan gudumawar data dace har ALLAH ya bashi nasarar dai-daita komai da taimakon Dr Aysha. Sai dai fa Dr Sa'ad yasha masifa dan tabbas harda sakacinsa. Ba komai ya sashi sakacinba kuma sai kasancewar matar talakace, hasalima Dr Yoohan shine ya biya mata ku?in aikin dukda kuma shine yayi aikin. Ya kuma bama marayun ?a?anta wasu ?an ku?a?e tare da bu?atar takardun makarantar babban yayansu dake ri?e da gidan da ?ar sana'arsa ta saida ruwa a cikin kasuwa. ALLAH ya taimakesa tun mahaifinsu nada rai ya ha?a diploma ?insa da ?yar da si?in goshi. Wannan alkairi nasa a garesu ya sakasu cigaba da jera masa addu'oin fatan alkairi da nasara a rayuwarsa. Tare da fatan ALLAH yasa yanada rabo cikin addinin islama.
Tunda Dr Sa'ad yaga Dr Yoohan ya wuce sai ya fara sakaci da kula da matar yanda ya kamata saboda takaicin ?arta data bijire masa tun farko. Da farko shine zaima matar aiki akan matsalarta, ya bu?aci ku?a?e masu nauyi daga wajensu na aikin amma suka tabbatar masa basu dasu. Sunta ro?onsa ya taimakesu ko rabi su bada kafin ta warke sai su cika ya nuna bazai iyaba, sai kuma ya koma ta bayan fage ya nema yarinyar matar akan inhar zata bashi kanta shiko zaima mahaifiyarsu aiki ?yau bama sai sun biyaba. Itako tace bazata aminceba, dan ran mahaifiyarsu a hannun ALLAH ya ke, sun kuma dogara da shi.
Wannan shine farkon matsalar. Lokacin da Dr Sa'ad ke bibiyar yarinyarnan saiko karaf a kunnen Dr Aysha, hakanne yasa ta koma a ?oye ta kira Dr Yoohan da ro?on ya taimaki yaran inhar yanada halin yin hakan. Da yake tasan yana Abuja yana hutun kwanaki uku. Sanin ?ya?y?yawan halin Dr Aysha ya saka Dr Yoohan yarda ya baro Abuja ta mota ya nufo kano. Da taimakonta sukaima matar dukkan hidima, ya tafi yabar amanar kulawarta a hannunta ita da Dr Sa'ad. dan Dr Aysha ta ?oyema Yoohan sunansa dan kare masa mutuncinsa.
Da Dr Sa'ad ya fahimci Dr Aysha ta ?oyema Dr Yoohan sunansa da ainahin gaskiya sai yay shirin ?ata aikin da akaima matar saboda jin zafin rashin ha?in kai da bai samuba na yarinyarta. Dr Aysha dake taimaka musu kuma data fahimci hakan ta tabbatar masa saita sanarma Dr Yoohan ?in komai. Wannan shine yay masifar tada hankalinsa kafin ta sanar?in shi ya kira ya sanar.

Yunwa da gajiya taima Dr Yoohan rumusu zuwa yanzun, haka ya fito a matu?ar wahale Dr Aysha biye dashi tana masa bayani akan nasarorin da suka samu game da sauran aikin da yayi a wancan zuwan kafin yima wannan matar aiki. Sosai yaji farin ciki a ransa, dan haka ya biye mata suka shiga zagaya ?angarorin da marasa lafiyar suke yana dubasu.
Duk inda ya gitta addu'a ake binsa da shi, duk da wasu da an masa addu'ar zakaji sunce. Arne ne fa. Jin hakan kansa wasu jikinsu yay sanyi. Wasu kuma suce dan arne ne baza'a masa addu'a ba bisa ga ?yautatawarsa?.
To shidai baimasan sunayiba, dan farincikine shimfi?e a ransa ganin nasara na kuma ziyartar aikinsa a koda yaushe. Amma duk da wannan farin ciki sam babu fara'a kota sisin kwabo a fuskarnan tasa saboda halittarsace haka rashin fara'ar.
Suna kammala zagayawa ya kalli agogon dake a tsintsiyar hannunsa. Ganin yaci a wanni uku a cikin uku da rabi na hutunsa ya sauke ?oyayyen ajiyar zuciya. Bashi da tabbacin samun jirgi mai komawa Lagos yanzu, dan haka ya yanke shawarar nufar Abuja a mota kawai, sauran patients ?insa kuma sai dai Richard ya dubasu.
Da wannan tunanin yayma su Doctor Aysha sallama ya fito batare da ko office ?insa yay tunanin shiga ba. Amma duk da haka sai da Doctors ?in dake matu?ar yinsa suka firfito suka gaishesa, sannan suka yo masa rakkiya zuwa wajen guards ?insa da basuyi tunanin fitowar tasa ba a yanzun. Dan Solomon suke ta bama labarin abubuwan da suka faru game da kama Nu'aymah da aka turosu yi.

Cike da farin ciki Solomon ke wata shegiyar dariya, ya ?yal?yale da ita yana fa?in, "Inason kafin kuje abuja da ita kuci ubanta a hanya ta ?arasa da ?afa ?aya. Kai bama nason taje da numfashi gaba ?aya. ku kaita da rabin rai yanda oga zai ?arasata da kun isa, dan bana fatan kafin mu dawo Abuja boss yaji koda ?ur?ushin labarin abinda ya farune. Kunsansa ?an hana ruwa gudu ne. Shi a dole masoyin ?.........."
Da sauri Solomon ya ha?iye sauran maganarsa jin ?amshin turaren Dr Yoohan ya cika wajen. Yay azamar juyawa kamar yanda suma sauran duk suka juya a tsorace.
Ganin yana maganane da Doctors ?in da sukai masa rakkiya ya sakasu sauke ajiyar zuciya. Dan sun tabbata baiji komaiba.
Dr Yoohan yay sallama da abokan aikinsa kafin ya shiga motar da aka bu?e masa yana nai ?aga musu hannu hamar yanda suke ?aga masa. A haka motocin suka fito daga cikin asibitin.
"Sir! Zamu koma airport ne?". Cewar Solomon fuskarsa ?auke da murmushin jin da?in kama Nu'aymah da har yanzu ya gaza barin fuskarsa.
Shiru Yoohan ya musu tamkar bai jiba, yama maida hankalinsa kan files ?in daya fiddo a jikkarsa yana dubawa. Sake maimaitawa Solo yayi.
Nanma sai da yaja wasu sakanni kafin yace, "Police station".
Ji kake ?iyyyyy!!! Driver ya taka wani uban birki a firgice, tare da ha?a baki shi da Solomon waje. fa?in, "Police station kuma sir?!".
(??????An yanka ta tashi ko masu gadi?).

Idanu ya zuba musu na wasu sakanni fuska a matu?ar ?aure. Sai kuma ya ?auke kansa ya cigaba da abinda ya keyi. Ganin gaba ?aya wutar kansu ta ?auke a fusace ya sake kallonsu "Kona canja yaren da nai maganar da shi ne bakuji wannan ba?".
Da sauri suka shiga bashi ha?uri, driver ya ?arama mota gudu zufa na keto masa ta ko ina a sassan jikinsa. Kai kace motar babu ac. kallo ?aya zaka fahimci tsagwaron tashin hankali da ?acin rai tattare da su. Driver bashi da wata hanyar daya wuce ya ?auki hanyar police station ?in da suka bar Nu'aymah. Acan kuma ?asan ransu shi da Solomon tunanin mafita sukeyi.
Sunci rabin tafiya wani dabara yazoma Solo a rai, dan haka ya ?auka wayarsa ya rubuta text ya turama Madam Chioma. Mintuna uku ba'ayi cikakkuba sai ga kiranta ya shigo wayar Yoohan.
Idanunsa ya ?ago daga abinda yakeyi ya kalli fuskar wayar. Duk da yaga sunan Mom ?aro-?aro a jiki sai ya ?auke kansa ya cigaba da abinda ya keyi. Kiran ya yanke wani ya sake shigowa. Yanzun kam maimakon kallon wanene sai ya lumshe idanunsa ma, sai da sukai kusan sakan goma a rufe sannan ya bu?esu akan su Solomon dake a gaba suna addu'a da fatan ya ?aga wayar kafin su isa station ?in.
Lip ?insa na ?asa ya?an lasa da harshe ya sake maida idanunsa ya lumshe bayan ya kife wayar alamar dai bazai ?aga ?inba..
"S...S sir ana kiran wayarka fa". Solomon ya fa?a da rawar baki.
Tamkar yayi magana da dutse, dan Yoohan yi yay kamarma bai jisa ba, kuma sarai yaji miya fa?a ?in.

A haka suka iso station ?in, bai fitaba sai da yaja wasu mintuna, ta cikin motar ya gama ?arema station ?in kallo har su Solomon da suka fita suka bu?e masa. Solomon yay ?asa da kansa ganin banzan kallon da Dr Yoohan ?in ke masa. Batare da yace da shi uffanba ya zuro ?afafunsa ?asa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login