Showing 105001 words to 108000 words out of 325075 words

Chapter 36 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29138

malam na zaune yana karatu da azkar kafin ya fara karatu ga magidantan anguwar dakan ?auki karatun safe da baya wuce zaman awa guda.

Yoohan bai zauna ba. Sai ma faman bin massallacin yake da kallo. A ransa yana sake jinjina ?o?arin da su baba malam sukai wajen ginashi. Dan ?aton gaske ne, kuma ya ginu da gini mai ?yau. Gashi an shafesa da farin fenti yanata ?aukar ido tamkar ba'a shiga cikinsa, sai shukoki da suka sake ?awata shi suma. Ko ina kuma a tsaftace yake. Daga wajen da yake tsaye yana sha?o dadda?an ?amshin dake fitowa daga massallacin wanda kullum safiya da maraice Nu'aymah ke zuwa ta sharesa ta saka turaren wuta da kalolin Air Fresheners masu da?in ?amshi..........
Kukan wani yaro ne ya katse masa tunanin nasa. Ya ?an juya inda yake jiyo kukan. Hakan yayi dai-dai da fitowarta daga cikin ajin da take koyarwa ri?e da bulalar dorina. Sanye take da dogon hijjabi mai hannu fari tas dan har yana jan ?asa. Hannunta na dama ri?e da Al-qur'ani, na haggu kuma bulala. Yanda take jijjiga bulalan tana magana da nuna yaron ne ya sakashi shagala da kallonta. A ransa ya raya, 'Ashe kowa ma masifa take masa?'. Jiba dai yanda takema yaro ?arami duk da kuwa bayajin mi take fa?a. Amma yanayinta ya nuna fa?a takeyi dan tama saka yaron kneeling ne a ?ofar ajin.........
"Yahya! kai ne da safen nan?".
Maganar baba malam ta katsesa daga kallon Nu'aymah daya shagala yi. Numfashi ya sauke tare da juyowa ga baba malam ?in. Baba malam daya juya yana kallon abinda Yoohan ?in ya shagala kallo shima ya ?auke kansa ya maido garesa. Sake mai-maita masa tambayar yayi a karo na biyu.
Yoohan da ya sunkuyar da kai ?asa yace, "Uncle, inason sanin minene ni'imomin dake a cikin addininku na musulinci?!".
Ba baba malam da yayma tambayarba, hatta Abban su Abdallah dake fitowa daga massallacin sai da ya taka wani uban birki.
Baba malam da jikinsa ya hau tsuma yace, "Yoohan sake maimaitawa naji".
Babu musu Yoohan ya kuma fa?in,
"Ina son sanin ni'imar dake cikin addinin musulinci?!".

????????? ???? ??????? ???????????? ??????? ????????????? .
Alhamdu lillahil-lazee bini'imatihi tatimmus-salihat.
Godiya ta tabbata ga ALLAH wanda saboda ni'imarsa ce kyawawan ayyuka suke cika.
?????????? ????? ????? ????? ?????.
Alhamdu lillahi ala kulli halin
Godiya ta tabbata ga ALLAH a cikin kowane hali.

Sai ya dur?usa a ?asa yay sujida hawaye na sauka masa a fuska.
Yoohan dake binsa da kallo yay saurin du?awa shima yana zaro manyan idanunsa a waje. dur?ushewa yay gwiwa bibbiyu yana kallon malam harya ?ago daga sujidar da yay.
Fuskarsa ?auke da murmushi ya kama Yoohan suka mi?e tare, sai kawai ya jawosa jikinsa ya rungume.
Duk da ba yaune karan farko da aka fara yima Yoohan irin wannan rungumar ba sai yaji ta yau ?in kamar daban ce a rayuwarsa. Kamar ba irin wadda Papa da sauran mutane ke masa bace. Kamar girman ta yau ?in na musamman ne.
Baba malam ya ?agosa da sauri tare da ri?e hannunsa. Yace, "Lallai yau zaka fara sani da ga rahamar UBANGIJINA, domin kuwa, *HASKE da RAHAMAR UBANGIJIN* al'arshi ta bayyana a zuciyarka da harshenka Yahya!. Sai dai bazaka ta?a fahimtar tarin ni'imomin dake cikin musilinci ba daga wajensa har sai ka shigo cikinsa".
Yoohan da bai fahimcesa ba yay shiru yana kallonsa ?asa-?asa. Sai kusan seconds goma ya ?ago ka?an ya kalli baba malam ?in da ?yau, sai kuma ya sake maida kansa ?asa. "Uncle ban gane mikake nufi ba".
Murmushi baba malam yayi, ya sake gyara tsaiwarsa cikin harshen turancin da suke magana yace, "Ina nufin bazaka ta?a fahimtar ni'imomin dake tattare da wannan addini mai daraja ba har sai ka kasance musulmi Yoohan. Ta wannan hanyar ne kawai zaka ?wan?wa?i madarar ni'imar UBANGIJI fiye da zaton hasashen ka".
Babu ko tantama Yoohan yace, "Inhar zan sani ?in ta wannan hanyar zan biya ko nawane na shiga addinin naku dan na sani, dan na tabbatar idan ban sani ?inba natsuwa zata cigaba da yin nisa da ni har abada".
"UBANGIJI kai ne gagara misali a tunanin hankali ko hasashen zuciya. Tabbas kai mai ikone ga wanda kaso, a kuma lokacin da kaso. Yahya shiga addinin musilinci ba'a biyan ko sisi. *_ALLAH ma?aukakin sarki ya halicci halitta ne domin su bauta masa, kuma ya sawwake musu abinda zai taimaka
musu na arzikinsa, ALLAH ma?aukakin sarki yana cewa:_*
_"Kuma ban halicci aljan da mutum ba sai domin kawai su bauta mini. Bana neman wani arziki daga gare su kuma bana bukatar da su ciyar da ni. Lalle ALLAH shi ne ka?ai mai azurtawa kuma ma'abocin karfi sosai"._ Suratuz Zariyat, aya ta:56-58.
*_Mutum a halittar da ALLAH ya yi masa zai bautawa ALLAH ne shi ka?ai inda za'a bar shi, ya zama mai son ALLAH ya na bauta masa ba ya yi ma sa shirka, sadai abinda ya
?ata wannan (dabi'ar) kuma yake karkatar da ita shi ne abin she?anun aljanu da na mutane su ke ?awata mata na abinda sashin su yake yi wa sashi wahayi na ?awatacciyar Magana kawai don ru?i, shirka wata aba ce da ta zo daga baya kuma ta kutsa kai ga halittar da ALLAH
ya yi wa mutum, ALLAH ma?aukakin sarki yana cewa:_*
_"To, ka tsayar da fuskarka ga wannan addini kana mai kaucewa shirka, halittar ALLAH wacce ya halicci mutane a kan ta, babu mai canza halittar ALLAH"._ Suratur Rum, aya ta: 30.
*Kuma Ma'aikin ALLAH (S.W.A) ya ce: "Dukkan abin haihuwa ana haihuwarsa ne akan musulunci, to iyayan shi ne su ke yahudantar da shi, ko su Nasarantar da shi (kiristan da shi) ko su majusantar da shi". Bukhari da Muslim ne su ka ruwaito.*
Dan haka Yahya UBANGIJI baya bu?atar ko sisi da ga gareka face amsa kalmar *_La'ilaha illallah......._*".
Sosai abin ya bama Yoohan mamaki da wannan bayani na baba malam. dan haka ya gya?a kansa yana mai gyara tsaywarsa da fa?in, "Na shirya amsar wannan kalma Uncle".
Murmushi sosai ya sake fa?a?a a fuskar baba malam, batare da ya sake cewa komai ba ya kama hannun Yoohan sukabi ta ?aramar ?ofa zuwa cikin gida. Abban su Abdallah na biye da su zuciyarsa fal tunanin inda ya ta?a sanin mai kama da Yoohan ?in a wasu shekarun baya..
Sashen mahaifinsu kai tsaye suka nufa, ko ina fes yake dan ana gyarawa saboda sukan zauna a ciki musamman randa sukaso nisha?i. Duk hidimar bikin salla ma jiya a ciki sukayita su hu?un. Sai da duk suka zauna, Yoohan da Abban Abdallah kowa nama ?an uwansa kallon sani baba malam ya katsesu da fa?in.
*_"Shaidawa Babu Abin Bautawa Da Gaskiya Sai ALLAH, Kuma Muhammadu MANZON ALLAH ne"_*.
_"Waannan kalmomin shahada guda biyu, sune ?ofar shiga musulunci, sune kuma rukuninsa mafi girma, kuma ba a yin hukunci da musulusncin mutum, sai da furuci da su, da kuma aiki da abin da suka ?unsa, da wannan ne kuma kafiri yake zama musulmi._
1-Ma'anar kalmar shahada: Ma'anar shaidawa da cewa babu abin bauta da gaskiya sai ALLAH, shi ne yin furuci da ita tare da sanin ma'anarta, da kuma yin aiki da abin da ta ?unsa, zahiri da ba?ini, malamai sun ha?u akan cewa furuci da kalmar shahada, ba tare da sanin ma'anarta ko yin aiki da abin da ta ?unsa ba, ba shi da amfani, kai sai dai ma ta zama hujja a kansa, kuma ma'anar (La Ilaha Illallah) shi ne babu abin bautawa da gaskiya sai ALLAH shi ka?ai matsarkaki ma?aukaki.
_Rukunan wannan kalmar (shahada) sune: (korewa da tabbatarwa), wato kore ha??in bauta daga wanin ALLAH, kuma tabbatar da shi ga ALLAH shi ka?ai ba shi da abokin tarayya. Haka kuma wannan kalmar ta ?unshi kafircewa ?agutu (shi ne dukkannin abin da ake bauta masa wanda ba ALLAH Ma?aukaki ba, ko da kuwa ya kasance mutum ne (tare da yardarsa da bautar da ake masa), ko dutse, ko bishiya, ko son zuciya, ko sha'awa), da nuna masa ?iyayya da yin ku?uta daga gare shi._
*_Wanda ya fa?i wannan kalmar (shahada da bakinsa) amma bai kafircewa abubuwan da ake bauta
musu wanin ALLAH ba (a aikace), to tamkar bai fa?eta ba. ALLAH Ma?aukaki ya ce: "Kuma abin bautarku abin bauta ne guda ?aya.
Babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. Mai rahama Mai jin ?ai".(Ba?ara: 163)._*
*_Kuma Ma?aukaki ya ce: "Babu tilastawa game da (shiga) addinin
(musulunci), ha?i?a shiriya ta bayyana daga ?ata, saboda haka wanda ya kafirce wa ?agutu kuma ya yi imani da ALLAH, to ha?i?a ya ri?i igiya amintacciya, (wadda) ba ta yankewa. ALLAH kuwa Mai ji ne, Masanine"._* (Ba?ara: 256)
_Kuma kalmar (Ilah) tana nufin abin bautawa da gaskiya, duk wanda ya ?udurci cewa abin da ake nufi
da kalmar (Ilah) shi ne: Mai halitta, Mai arzutawa, ko wanda yake da ikon ?ir?ira, kuma ya ?udurci cewa yin
imani da wannan kawai zai wadatar, ba tare da ka?aita ALLAH da ibada ba, to ha?ika fa?in kalmar (La Ilaha
Illallahu) ba za ta amfane shi ba, a nan duniya wajen shiga Musulunci, kuma a Lahira ba zata kubutar da shi ba daga azaba madawwamiya._
ALLAH Ma?aukaki ya ce: "Ka ce (da su): "Wane ne yake arzuta ku daga sama da ?asa? ko kuma wane ne yake mallakar ji da gani?, kuma wane ne yake fitar da mai rai daga matacce, ya kuma fitar da matacce daga mai rai? Wanene kuma yake tsara al'amura?" To za su ce: "ALLAH ne". To ka ce (da su): yanzu ba za ku ji tsoronsa ba?"
(Yunus: 31).
*_ALLAH Ma?aukaki ya ce: "Ko wane ne ya halicci sammai da ?assai, ya kuma saukar muku da ruwa daga sama, sannan (da wannan ruwan) muka tsirar da (shukokin) gonaki
masu ?ayatarwa, ba kuwa za ku iya tsirar da bishiyoyinsu ba?, shin akwai wani abin bautawa tare da ALLAH, A'a, su dai mutane ne da suke kauce wa (gaskiya)". (Naml: 60)._*
Kuma ALLAH Ma?aukaki ya ce: "Kuma lallai idan ka tambayesu, "Wanene ya halicce su?, Lallai za su ce: "ALLAH ne" To, yaya ake juyar da su (daga bauta wa ALLAH)?" (Zukhruf: 87).

*_"Ma'anar Shaidawa Lallai MUHAMMADU MANZON ALLAH ne:_*
_Ma'anar shaidawa lallai (Annabi) Muhammadu
MANZON ALLAH ne shi ne a yi masa biyayya cikin abin da ya umarta, da gaskatashi a kan abin da ya ba da
labari, da nisantar abin da ya hana kuma ya yi tsawa a kansa, kuma ba za a bautawa ALLAH ba sai da abin da ya
shar'anta._
*_Tabbatar Da Shaidawa Lallai MUHAMMADU MANZON ALLAH ne:_*
_ MANZON ALLAH ne: Shaidawa lallai (Annabi) Muhammdu Manzon
ALLAH ne tana tabbata ne da yin imani da cikakken ya?inin cewa lallai (Annabi) Muhammdu tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi bawan ALLAH ne, kuma Manzonsa ne ya aiko shi zuwa ga Aljanu da mutane gaba ?ayansu, kuma lallai shi ne cikamakin Annabawa da Manzonni, kuma shi Annabi tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi bawa ne makusanci a gurin ALLAH ba shi da komai daga siffofin ALLAH, kuma (wannan shaidar tana tabbata ne) da yi masa biyayya da girmama umarninsa da haninsa, da lazimtar
sunnarsa a baki, a aikace, kuma a ?udurce._
*_ALLAH ya ce: "Ka ce: ya ku mutane lallai ni MANZON ALLAH ne
zuwa gare ku gaba ?aya" (A'araf: 158). _*
_Kuma ya ce: "Ba mu kuma aiko ka ba face zuwa ga mutane baki ?aya, kana mai garga?i da bushara" (Saba'a: 28)._
_Kuma ya ce: "(Annabi) Muhammadu bai kasance uban ?aya
daga mazajenku ba, sai dai (shi) Manzon ALLAH ne kuma cikamakin Annabawa" (Ahzab: 40)._
_Kuma ya ce: "Ka ce tsarki ya tabbata ga Ua
UBANGIJINA, ni ba
kowa ba ne face mutum kuma Manzo" (Isra'i : 93)._
Wannan (tabbatar da shaidawa Annabi Muhammadu Manzon ALLAH) ya ?unshi al'amura kamar
haka:
Na farko: yarda da Manzoncinsa da ?udurceshi a ?oye cikin zuci.
Na biyu: yin furuci da haka da harshe a bayyane.
Na uku: koyi da shi da yin aiki da abin da ya zo da shi na gaskiya, da barin abin da ya hana na ?arya.
*_ALLAH Ma?aukaki ya ce: "Sai ku yi imani da ALLAH da Manzonsa, Annabi Ummiyyi1, wanda yake imani da ALLAH da kalmominsa, kuma ku bi shi don ku shiriya" (A'araf:
158)._*
Na hu?u: gaskatashi a kan dukkan abin da ya ba da labarinsa.
Na biyar: Mutum ya so shi sama da son kansa da dukiyarsa da ?ansa da mahaifinsa da mutane baki ?aya; domin shi MANZON ALLAH ne, kuma ha?i?a sonsa yana daga cikin son ALLAH, da so saboda ALLAH Ha?i?anin son MANZON ALLAH shi ne yi masa biyayya wajen bin umarninsa da nisantar haninsa da
taimakonsa da jibintarsa.
*_ALLAH ya ce: "Ka ce: idan kun kasance kuna son ALLAH, to ku bi
ni, sai ALLAH ya so ku, ya kuma gafarta muku" (Ali Imran: 31)._*
Kuma ANNABI tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi ya ce: "?ayanku ba ya zama mumini har sai ya soni fiye da mahaifinsa da ?ansa da mutane gaba ?aya" Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi daga hadisin Anas ALLAH ya yarda da shi.
*Kuma Allah Ma?aukaki ya ce: "Saboda haka wa?anda suka yi imani da shi, suka kuma girmama shi, suka kuma taimake shi, suka kuma
bi hasken da aka saukar a tare da shi, to wa?annan su ne marabauta" (A'araf: 157).*
Na shida: ?udurce cewa sunnarsa asali ce ga shari'ar musulunci, kuma ita sunnar kamar Al?ur'ni mai girma take (wajen dogoro da aiki da ita), saboda haka ba a sa?a mata domin hankali ya ci karo da ita.
Na bakwai: yin aiki da sunnarsa da gabatar da maganarsa a kan maganar kowa, da mi?a wuya zuwa
gare shi, da yin hukunci da shari'arsa da yarda da ita.
*_ALLAH Ma?aukaki ya ce: "Na rantse da girman UBANGIJINKA ba za su yi imani ba, har sai sun sanyaka mai hukunci game da abin da ya faru a tsakaninsu, sannan kuma ba su sami
wata ?unci ba a zukatansu game da abin da ka hukunta, su kuma mi?a wuya gaba ?aya" (Nisa': 65)._*...............?

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????

Mamu gee??
MIN ?ALB!!????

Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????

Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????

Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????

?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.
[5/18, 3:08 PM] Ummuanwar??: *_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.


No. 29

............."Na fa?a?a maka muhimmanci kalmar shahada ne domin kasan addinin musilinci ba abin wasa bane, sannan bautama UBANGIJI shi ka?ai bashi da abokin tarayya shine cikakken imani. Gujema shirka babba da shirka ?arama domin dawwama da tsira wajen bautama ALLAH shi ka?ai da tabbatar da soyayyar MANZONMU a zukatanmu wajibine. Zaka kar?i kalmar shaha yanzun nan Yahya, da ga haka ka tabbatar kabar kafircema ALLAH har abada, ka tsarkake ranka da zuciyarka cewa babu wani sarki sai ALLAH, ANNABI MUHAMMADU kuma MANZON ALLAH ne".
Kai Yoohan ya jinjina a hankali, zuciyarsa na wani irin tsitstsinkewa, tsigar jikinsa na tashi batare da yasan dalili ba. Hakama jininsa gudu yake a cikin jijiyoyinsa da sauri-sauri. Wannan yanayin sai ya saukarma jikinsa da kasala da wani rauni da bai ta?a tsintar kansa a ciki ba.
Baba malam na fa?ar kalmar shahada yana maimaitawa,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login