Showing 222001 words to 225000 words out of 325075 words

Chapter 75 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29108

ta mi?e tana gyara gyalen jallabiyar jikinta da ?ayan hannun. Ta gefen da take ?auka labulene kawai ya kaita. Ya zaro handkerchief a aljihu ya zagaya bayanta. Ji kawai tayi ya ?ora mata akan ido alamar zai ?aure.
"Wai kodai saidani zakayi ne?".
Tai maganar tana son ture masa hannu.
Hannunta shima ya ture yana fa?in, "Kina ?ar tamilo ?inan ko an saidaki namanki bazai ishi masu ci ba ai".
Da sauri tace, "To nama fasa".
Shima saurin ri?e mata hannu yayi yana danne dariyarsa ganin bakin ya fara bu?ewa. "Sorry kowa zaici ya ?oshi, kuma zakiyi da?i".
Shiru ta masa, sai dai bakin ya tashi sama alamar ta sha?a. Shiko sai danne dariyarsa yakeyi dan bayason yayi ta birkice masa. Gani nayi ya danna wani abu sai ga labulen wajen dake bango guda ya zuge kansa ya koma gefe da gefe. Glass ya bayyana. Wanda ta cikinsa kake hango ainahin garin Vienna da ya gama ha?uwa da ?ayatattun gine-gine masu ban mamaki da al'ajabi. Kallonta yayi dai-dai ya sake danna wannan abun glass ?in shima ya zuge ?ofar fita ta samu. Hannunta yaja suka fito ?an barandan wajen dan ita dai ta zama makauniya.
Ni kaina sai da na ambaci masha ALLAH a zuciyata ganin yanda aka ?awata barandar wajen domin hutawa kawai da ado na musamman, wanda a kallo ?aya zaka fahimci tsarawa akayi dan wani dalili. Hannu ya saka ya kwance handkerchief ?in daya ?aura mata. glasses ?inta daya cire ya ?ora mata duk da kuwa tana gani abunta ko babu shi, sai dai ba yanda ya kamata ba. Baki ta saki kawai tana bin wajen da kallo, kafin ta sami damar tambayarsa irin flowers ?in ?azun suka shiga zubo musu a jiki ita da shi, sai dai ?amshin wa?anan daban suma. Atare suka lumshe idanunsa fulawoyin na cigaba da sauka musu. A bazata Nu'aymah taji tafi. Saurin waigawa tayi dan tafin yayi dai-dai da daina zubowar flowers ?in a kansu.
Gaba ?aya Doctors ?in da sukai mata aiki ne. sai ?arin mutum hu?u da bata saniba. Biyu mata biyu maza. Sai Solomon da Richard da batasan sanda ya dawo ba. Sai mutum biyu data ta?a gani a wajen dinner ?insu wanda take ?yautata zaton abokansane ko ?an uwansa ma.
A ta?aice dai ?ar ?war?waryar liyafa ce su Rich suka shiryama Aymah da Yoohan na murnar samun lafiyarta da nasarar aiki. Sai dai basu samu damar zuwa Austria ?in su duka ba. Sai Richard daya dawo, sai kuma Osin da Joseph. ?akin ma sune suka kama musu a hotel ?in wai suyi Honeymoon na sati biyu Nu'aymah ta huta kafin su koma tunda hutu Yoohan ya ?auka harna watanni biyu.
Gaba ?ayansu su goma sha biyu ne har Aymah da Yoohan. Hakan yasa komai ya gudana cike da birgewa da nutsuwa. Sunsha shagalinsu na awa ?aya da rabi sannan aka tashi. Su Richard dai tun anan sukaima Nu'aymah sallama. Dan da safe zasu wuce ba lallai ta gansu ba.
Godiya itama ta musu, ta shigo tabar Yoohan na ?arasa magana da su. Bayan su Dr Liam sun wuce, Osin ya shige masaukinsu wai zaiyi toilet??. Solomon ma dai tafiya yayi can nasa masaukin inda suka fara zama da Yoohan. Hakan ya bama Yoohan da Richard damar kasancewa su ka?ai. Maganace a bakin Rich sosai gameda firar papa da Dr Mateo da yaji, sai dai baisan ta yadda zai tunkari Yoohan ?inba kai tsaye tunda Papa mahaifinsa ne.
Ajiyar zuciya Yoohan dake ?an nazarinsa yayi, "Rich kamar akwai magana a bakin nan naka tun kafin ka wuce kwanaki. Sai dai bansan miyasa ka gaza yiba. Duk da nasan dai bazai wuce akan komawata musulmi ba. Na yarda da kai Rich, dan baka ta?a cimin amana ba a tsahon shekaru goma sha shida da mukasan juna. Dan haka zan fa?a maka sirrin komawata mai salla a yanzu koda kuwa bazaka fahimceni ba".
Batare da ya jira amsar Richard ba ya shiga bashi labarin tun farkon ha?uwarsu da su Nu'aymah a ?ofar Orphanage. Fasa masa glass ?in mota da tayi da tilasta musu shiga cikin Orphanage akan yaron da suka bige. Fara mu'amularsa da su baba malam har zuwa musulintarsa da aurensa da ita. Babu abinda Yoohan ya ?oyema Rich. Sosai tsantsar mamaki da firgici ya bayyana ga Richard. Wani irin rauni da ?wa?ayin shiga musulinci ya ringa kutse cikin ?argon jikinsa da zuciya. Sai dai baice komaiba akan hakan sai magana akan ?ullin da akaima Aymah na maganar ciki.
Ya janye hannunsa da ga dafe kan da yayi yana duban Yoohan da ke kallon wani waje da ban. "Ka yafemin Yoohan".
Juyowa Yoohan yayi yana dubansa. Cikin ?an lumshe idanu yace, "Akan mi? Ni bakamin laifin komaiba ai".
"Niko na maka laifi X-man. Dan na zargeka akan abinda ba haka yake ba. Sannan na zargi in-lows ?inka suma. Da ga yau na maka al?awarin tayaka wannan ya?in, zan taimakeka wajen cikama iyayenta al?awarin daka ?auka na bayyanar gaskiyar maganar cikin da suke zargin ta zubar".
Kallonsa Yoohan yake cike da so da ?auna. Ya ri?o hannun Rich cikin nasa yana fa?in, "Nagode sosai Rich, kai ?in na dabanne a gareni koda bakina bai furtaba".
"Ba nine na daban a garekaba Yoohan, kai ne na daban a gareni. Dan kamin abubuwa da yawa da ni kaina bansan hanyar da zan iya saka maka ba. Indai ni ?in ?an halak ne dolene na kasance a cikin ya?in nan daka ?auki al?awarin yi. Sai dai zan baka shawara ?aya zuwa biyu".
Numfashi Yoohan ya furzar da lumshe idanu ya bu?e akan Rich. "Ina jinka".
"Ka ajiye maganar ?an?antar matarka ka fara nuna mata ?unbin soyayyar da kake mata. Waddama bata kaita shekaruba tana ?aukar namiji balle ita dana fahimci tanada wayo sosai. Kaifa likitane, kasan sirrin mace duk da kuwa karatun likitancinka ba'a kansu kayisa ba. Amma na sanka da bincike, ta wannan hanyarne kawai kaima kanka zaka fahimci gaskiya ko akasin abinda Doctors ?in suka fa?a a wancan karon, tare da naka gwajin, sai ka bita a sannu yanda kake bu?ata........."
"Amma Rich......."
"Karkace komai Mr X. Wai shin kai baka tunanin shekarunka ?aruwa suke ba raguwa ba? Ya kamata kasan sirrin dake cikin wannan tafiyar. Ko dai baka da lafiya ne Yoohan?".
Harararsa Yoohan ?in yayi kawai ya kauda kansa. Rich ya kwashe da dariya yana fa?in, "Kai ?inne kana abu kamar dutsi oga. Ga dama ka samu a hannu amma kana son kasa damawa. Idan da kace kana ?yan?yami da gudun matan waje wannan dai matarkace ai ko......."
"To naji mai shegen surutun tsiya. Muje shawara ta gaba". Yoohan ya fa?a yana talle ?eyar Rich.
Shafa ?eyar Rich yayi da fa?in, "Mugu, ashe dai kanaso. Shawara ta ta biyu itace karku koma Nigeria da ita yanzu har sai na binciko maka duk yanda komai ya kasance".
"Taya zaka binciko abinda baka saniba. Sannan wannan abun nasu yayi kama dana family, kai da ma ko sakin jiki ka kasayi da Uncle ?in kanata faman jin haushinsa".
Murmushi Rich dake kallonsa ya keyi, a ransa kuwa yanason hana Yoohan komawa Nigeria da Aymah ne saboda abinda ya jiyo a wajen papa a wannan komawar da yayi gida. Saboda hirar papa da Dr Mateo ta kasa barin ransa tun wancan karon. A wannan zuwan koda suka koma dasu baba malam a abuja ya sauka shi. Anan ya ?anbi diddigin papa shine ya sakejin kwangilar kashe Aymah da ya bada ayi masa saboda wai ya ganta a cctv ta shigar masa ?aki. Duk da basusan mitayiba a ciki saboda cctv ?in iyakarta parlornsa ne, (Tab, kenan randa Aymah taje ?akin papa. Ya salam?????¡â?) Abinda yasa suka gaza gane mitayi su basuga komai a hannuntaba. To amma shi papa ya tabbatar ta ga sirrinsa shiyyasa yake bu?atar a kauda masa ita kafin bakinta ya fa?ama wani. duk da yana zargin ta fa?ama baba malam, yaso kuma ?yaleta yabi a hankali harya gano abinda tayo a ranar amma su Uncle Mike sukaita tunzurashi aka ya kasheta kawai, shine ya bama Dr Mateo kwangilar kasheta a wajen aiki batare da an zargesaba, dan Yoohan ya sanar masa a inda za'ai aikin da masu tayasa. shine aikin ya gagara kuma.
Wannan abu da Richard yajine ya sakashi zaunar dasu G-boy akan su ha?a ku?i su saka Yoohan zaman Honeymoon a Austria. Sai dai su basu san dalilinsa nayin hakanba dan bai fito fili ya fa?a musu ba........
Ta?ashin da Yoohan yayine ya sakashi dawowa hayyacinsa. Ya sauke numfashi, cikin son kauda tambayar mi yake tunani da Yoohan yay masa yace, "Yoohan ka bani dama. Zanyi bincike nane iyakar likitocin da suka gwadata. Sai kuma ?ar aikin da kace an kawo muku tunda kace ka saka mata abin ?aukar magana a ?akin da kuka ajiyeta".
"Okay Rich, sai dai banason ka saka kanka a ha?ari Please".
"Karka damu kamin addu'a kawai. Kuma ai tare zamuyi aikin ma da kai".
Murmushi Yoohan ?in yay masa suka rungume juna cike da so da ?auna. Daga haka Rich ya korashi wai yaje madam na jiransa shima zaije yay video call da tashi dan gobe ma wajenta ya nufa, tare zasu wuce 9ja daga can..........???


ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????

Mamu gee??
MIN ?ALB!!????

Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????

Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????

Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????

?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.
[6/22, 12:42 PM] +234 901 860 0202: *_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.


No. 59

..............Sosai yanzu ta nutsu ta ?arema lungu da sa?o na ?akin kallo, dan an kashe wa?ancan fitulun ansa ainahin fitilu da suka ?arama ?awata ?akin. Lallai duniya budurwar wawa. Idan bakayi wasa ba irin wa?anan abubuwan tuni suke shagaltar da kai ma ga bautar ALLAH. Shiyyasa wasu mutanenmu dasun samu irin wannan damar sai kaga addininma an fara walagigi da shi. Zama tayi tana jiran shigowarsa dan taji wai yayama za'ayi? taga ?aki daya ne. Nashi ne nan ko nata?. Dan kuwa dai ba yarda zatai su zauna a ?aki ?aya ba ehe.
Tayi kusan zaman mintuna goma sha biyar sannan ya shigo ?auke da ?yaututtukan dasu Dr Sophia Suka bata. Yi tai kamar batasan ya shigoba. Shima kallo ?aya yay mata ya ?auke kansa. Sai da ya ajiye kayan hannun nasa sannan ya nufo inda take. Zama yay a kujerar dake kallon tata ya zaro wayarsa dake ring ya sa a kunne fuska ?auke da murmushi. Sun kwashe tsahon mintuna a haka yana waya tana satar kallonsa harya kammala.
Kallonta yay ta kauda fuskarta gefe. 'Yarinyar nan rigimanta yawane dasu' ya ayyana a ransa yana lumshe idanu da bu?ewa a kanta. Ganin bazatayi manar daya fahimci takeson yiba sai ya mike ya shiga toilet ?in ?akin bayan ya ciri kayan barci a cikin kayansa da Solomon ya kawo ya ajiye rigar a saman gado ya ?auki wandon kawai.
Duk da Aymah najin sanda ya shiga bayin ta kasa ?agowa. Haka ta cigaba da zama zuciyarta na tattaro mata abubuwa masu ?unbin yawa a kansa, ga ?okin son komawa gida da takeyi, dan wula?anci yau ma gaba ?aya bai kira mata Baba malam ba kamar yanda ya saba.
Duk da?ewar da yay a bayin a yanda ya barta haka yazo ya isketa. Da alama ma dai barci ta fara. Gaban kujerar ya matsa yana mai tsane sumar kansa ta gefe-gefe dan ba ji?ata yayi ba. Le?a fuskarta yayi, hakan yasa ruwan da bai gama tsanewa ba a jikinsa ya ?isar mata a gefen fuska.
Motsawa tai tare da bu?e idonta dan da gaske barci ta fara. Suna ha?a ido tai saurin jan gyalen jallabiyarta ta rufe fuska. "Oh God! Dama babyn nan mai bakin tsiwa tanada kunya ashe?. Tom tashi kije kiyi wanka".
Bata iya ta motsa ?in ba sai da taji motsin barinsa wajen. Ta gabanta ya zagayo inda Wadrobe ?in ?akin take. Tabi bayansa dake ra?ar ruwan wanka da kallo, dan dogon wandone kawai a jikinsa babu riga, sai towel ?in dake a hannunsa ?arami. harya bu?e Wadrobe ?in da akwatin kayansa ke a ciki, harma da nata kayan a ha?e da batasan da zamansu ba idonta a kansa. Ajiyar zuciya ta?an sauke da mikewa ta nufi bayin dan tana bu?atar yin wankan da ruwa mai ?umi ko zataji da?in jikinta, taga alamar kuma guy ?in nan ba kunyace da shi ba. Ka?anma daga aikinsa yace a gabanta zai Shirya. Bara tai wankan sannan tazo taji yanda zasuyi akan zaman ?aki.
Lallai indai da ranka kallo baya ?are maka ba. Dan toilet ?in kansa ma wata aljannar duniyace. Tsabar ?aurema ?arya ?ugu harda television a ciki. Baki ta ta?e tana fa?in, 'Kunga aljanu ai sun samu nayi. Kayi tsirara ga tv ana nunawa ai al-amari sai wanda kuma ido ya gani'. Da wannan mitar ta shiga wajen wankan na glass shima dake a mulmule. Wankanta tayi, sai da ta gama ne kuma tunanin kaya yazo mata a rai. Kanta ta dafe cike da damuwa tana fa?in 'Oh Stupid me. Miya shiga kaina ne?'. Fitowa tai gaban ?aton mirror ?in da aka shirya towels a wani ?an drawern glass shima. Fatanta ta samu bathrobe. Cikin sa'a kuwa tana ?aga ta farko sai taga rigace. Ajiyar zuciya ta sauke ta warwareta ta saka. Tako wuce mata gwiwa, hakan ya sata jin da?i ta ?aure igiyar sannan ta na?a ?aramin towel a kanta dan duk ta ji?a gaban goshin da ?eyar. Kayanta data cire da nasa daya ajiye ta jefa cikin washing machine ?in ta wanke. Ta sakasu wajen busarwa ma ta busar sannan ta ninke abunta ta fito dasu a hannu duk da harga ALLAH tanajin nauyin fitar saboda Yoohan. Amma da yake bawani jikinta bane a waje sai ta fuske akan zata ?akko kaya ta dawo toilet ?inne ta saka.
Zaune ta iskesa a bakin gado yana danna tab. Yana sanye da kayan barci farare ?al. Baiji fitowarta ba saboda a hankali take tafiya da san?a, ita wayonta wai karya ganta. Sai ko akai rashin sa'a tana zuwa saitinsa ya ?ago ido ya kalleta. Cak ta tsaya tana cika baki da iska kamar zata fasa kuka. "Ni dai banason kallo". Tai maganar da alama dai an ?ure mata gudu ne.
Idanunsa ya lumshe yana sake bu?esu a kanta. Baki ta kuma cunawa gaba ta juya masa baya.
A hankali yace, "Silly girl!". Yana maida kansa ga tab ?in.
Cike da munafurci Aymah ta?an karkato ta kallesa. ganin ya maida kansa ga tab taci gaba da tafiyarta kai tsaye yanzun. Bayansa taje ta tsaya ta ?ayan ?angaren gadon. Kamar zatai kuka tace, "Banda kayan sakawa ni fa".
Batare daya juyo ya kalleta ba yace, "Tom aro zan baki ne?".
"Hu'um. ?ato da kai tayaya kayanka zasumin. Kana kallon kanka kuwa a mirror? Sai kace ?an dambe".
'Yarinyar nan ko' ya fa?a cikin ransa yana juyowa ya kalleta. Saurin juya masa baya tayi dan itafa batason kallon. Shima ya fahimci kunya takeji, hakan ya sakashi yin murmushi. Wannan ?abi'ar ta kunya tana abu na farko da yaren hausawa ke burgesa da shi. Ko abu ke damunsu sukazo gabansa matsayin likita sunta ?unshe-?unshe kenan.
Mi?ewa yay ya zagayo inda take. Ganinsa kawai tayi a gabanta. Hakkanne ya sakata zabura tai baya kamar wanda tai gamo da abun tsoro. Tai saurin sake juya masa baya a daburce.
Hannayensa duka biyu ya tura cikin aljihun wandon kayan barcinsa yana fa?in, "Uhyim! Tom nama fasa bada aron kayan. Garama ki lalla?ani fa, koki kwana da bathrobe. idan kuma kinaso juyo ki kalleni".
Ji Nu'aymah tai kamar ta fasa ihu dan takaici, gashi harga


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login