Showing 237001 words to 240000 words out of 325075 words

Chapter 80 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29137

ya bu?e ya amshi abinci ya koma ciki. Sai da ya gama kimtsawa tsaf sannan ya tasheta zaune. Kuka ta sanya masa duk da kuwa yanzu zafin ya ragu, sai dai zazza?i da jikinta da takejin na mata ciwo na bala'i. Kasancewar yunwa takeji sai gashi taci abincin daya bata da kansa. Ya bata maganinta daya tabbatar zai taimaka mata tunda zatai barci. Ayko bata rufa mintuna biyarba sai barci. Da ?yar ma ya samu ya ta yarda ya saka mata kayan barci ya taimaka mata ta koma kan gadon. shima dai kayan barcin ya canja ya kwanta dan jikinsa sai karkarwar zazza?i ya keyi. Ga ciwon kai tamkar ana ?ara masa shi.
Sai gashi ita Aymah ta samu barci mai nauyi, shiko dake rungume da ita ya kasa rintsawa. Ga zazza?i da ciwon kai. Sau biyu yana zuwa yay amai. Hakan yasaka shi sake galabaita fiye ma da farko.
Yau ma Alarm ne ya tadasu, koma nace ya tada Nu'aymah dan shi dai Yoohan bama barcin yayiba. Garama gabannin asuba ya?an fara figarsa sama-sama sai kuma ya farka. Daga haka bai sake komawaba har alarm ?in ya buga. Sosai jikin Aymah da sau?i dan zazza?in nata ya sauka ita. Sai dai rashin jin da?i jiki da sabon al'amari ya haifar. Sai ciwo ?afafunta dake mata. Jinta take fayau kamar iska zata ?auketa ta kayar. Bakinta ko ?aci, ?an-?an?anon data fara samu yana dawo mata ya sake guduwa. Yanda take tsananin jin kunyar Yoohan ?inne ya sakata tashi zaune batare data yarda ta kalle sashin da yake ba, sai faman matse baki take dan can wajen kam da zafi har yanzun.
A hankali ta dinga tafiya tana hawaye har bathroom, Yoohan na kwance yana kallonta cike da tausayi, duk yanda yaso ya yun?ura ya sake taimaka mata ya kasa saboda ciwon da kansa ke masa ga zazza?i irin wanda shikam a rayuwarsa zai ce ya mata rabon da yayi zazza?i mai zafi irin wannan.
Aymah na shiga bayin ta fashe da sabon kuka mai sauti tana kiran baba malam da Umm suzo su taimaketa. Ta kai mintuna hu?u zaune a a?an step ?in hawa wajen bathtub ?in kafin ta mi?e da san?a ta nufi madubi wani da?i na ratsata na hango wayar Yoohan a jiye. Da alama dai a daren jiya ya manta da ita kenan.
Umm ta riga da ta mata tarbiyyar duk abinda ya sameta ita take fara sanarmawa, sai dai a yanzu abinda naga Aymah na shirin aikatawa ya sake tabbatar min da tsabar wautar dake a kanta, dan kuwa number ?in Umm ta shiga lodawa cikin wayar tai dailing. Kuka ta sanya da dariya a lokaci ?aya jin kiran ya shiga.
Daga can Nigeria kam Umm na idar da sallar magriba kiran ya shigo. Da mamaki take kallon Number dan bata kawo Aymah a rantaba. Tunda tasan indai zasu gaisa a wayar baba malam mijinta ke kira sai shi kuma ya bata su gaisa. Tana gab da tsinkewa dai tai ?uru ta amsa, tare da kaiwa kunne tai sallama. Maimakon mutuniyar taku ta amsa sallanar sai kawai ta fashe ma Umm da kuka. Shiru kawai Umm tai tana saurarenta dan ta gane abarta. Sai da ta barta tayi kusan na minti ?aya sannan tai gyaran murya. "Mike faruwa?". Umm ta jefa mata tambayar.
(Nazata bazata iya fa?aba fa??) sai kawai Aymah ta gyara zama ta fara fa?in, "Umm dan ALLAH kuce ya maidoni gida. wlhy ban ta?a iskanciba. Na rantse da ALLAH Umm ba laifina baneba, sai da naita ro?onsa karyayi banaso, amma shi mugune sai da yayi. Gashi na kasa tafiya, wajen kamar zai fita, ciwo yake min, gashi inajin fitsari inajin tsoron yi Um........"
Harga ALLAH dariya ta bama Umm, amma sai ta danne abinta tai saurin fa?in, "To ya isa zubaina sarkin magana. Wai nikam yaushene ranar hankalinki Nu'aymah?. Kai ALLAH na gode maka ni Firdausi. Yanzu shi mijin naki yana ina kike zubamin zance haka?".
Baki ta kumbura na haushin ba'a barta takai ?arshen labariba tace, "Yanacan ?aki bai tashi ba. Ni kuma ina toilet asuba fa tayi anan". Ta ?are maganar hawaye na silalo mata.
Ajiyar zuciya kawai Umm ta sauke hawayen farin ciki itama na silalo mata. Koba komai dai ta fahimci yarinyarta takai mutincinta gidan aurenta. ALLAH ya ?ara wanketa a garesu ga ?azafin da akai mata. Hawayenta ta share. Tace, "Ki shiga ruwan zafi kinji ko, ki daure duk zafinsa ya ratsaki sosai zakiji da?i".
"Umm wlhy jiya daya sakani kamar zan mutu. Dan ALLAH ki fa?amin wani maganin sai nace ya sayo min zansha. Amma dan ALLAH kice Abbana ya kirashi ya kawoni gida yau".
"To naji, yanzu ki ?ara shiga ruwan zafin bazakiji zafin kamar na farkoba kinji ?ar albarkana".
Cikin jin da?in sunan ?ar albarka da Umm ta kirata tace, "To Ummuna. In kiraki video call ki ganni, ?ila zakifi ?arajin tausayina ma". Da sauri Umm tace, "A'a jekiyi abinda na sakaki, kije kiyi salla lokaci na shigewa".
Fuska ta ?wa?e zatai wani sabon kukan, zatai magana Yoohan da shirunta ya sakashi a damuwa ya taso da ?yar ya biyota yay azamar zare wayar daga hannunta dan yaji maganar video call da taima Umm, sai dai baisan amsar data bataba da ga can.
Zabura tayi dan batasan da shigowar tasa ba. Shi kuma ya zaune a step din yana dafe kansa da fa?in, "Acshh!! Kaina". Mi?ewa ta nemayi duk da ganin yanayinsa ya bata tsoro, yay saurin dam?o hannunta ya maidata ya zaunar. Hannunsa dake akan goshinsa ya cire yana dubanta da idanunsa dake jajur. "Zeeynab baki da hankali wa kika kira? Ba dai Uncle ba?".
Tana cika kumatu da iska tace, "Ni ban kira Abba ba, Ummna na kira na fa?a mata abinda kaimin. Nace tasa Abbah yasa ka maidani gida".
Tuni ya manta da maganar ciwon kai, ya waro idanu waje yana fa?in, "Kin kasheni Zeeynab. Kika fa?a matafa kika ce?".
"To wa yace kayi? Gobe ma ka ?ara kaga idan bankira harda Hajjo da Abbana da Addah duk na fa?a musu ba ALLAH. Kai harma Ananah sai tasan halinka".
Gaba ?aya kunya ta lullu?e Yoohan, ji yake tamkar yana a gaban Umm. cike da ?arfin hali yace, "Yarinyar nan ALLAH har yanzu kanki da motsi, dole na sake maidaki wajen su Dr Liam".
Umm da duk take saurarensu da ga can ta yanke wayar tana dariya. Dama ta tsayane ta sake gaskata zancen Nu'aymah. Wayar ta ajiye tana fa?in, "Yaron nan kaga takanka indai Nu'aymah ce. Bayan motsin ciwo dake a kanta akwai ma na hali wlhy. Ni harma ka bani tausayi".....
"Waye ya bada tausayi?". Cewar baba malam dake shigowa ?akin. Dan dawowarsa kenan gidan. Juyowa tai tana cigaba da dariyarta. Ya zauna a bakin gadon ya ri?o hannunta. "Jannat da alama dai kina cikin farin ciki, zoki ?an sammini nima muyi tare". Sosai take ?ara fa?a?a dariyarta. Ta shiga bashi labarin kiran da Nu'aymah tai mata da drama ?in data gama ji tsakaninta da Yoohan a ?arshe. Shi kansa baba malam sai da ya dara.
"Ai Jannat lamarin mamana sai ita. Yarinya tamkar goyon kaka. Amma koba komai ni hakan yamin da?i tunda munji cewar dai sharri dai akai mata kamar yanda zukatanmu ke fa?a mana. Wannan shine amfanin ka bama yaro tarbiyya akan duk abinda ya shafesa ya sanar maka. ALLAH yay musu albarka su duka. Ya azurtasu da zuriya masu albarka da alkairi. Wadda zata zama maijin ?ai a garesu damu baki ?aya".
"Amin ya rabbi. Sai dai kuma naji muryar mijin nata kamar wanda baida lafiya ma. Dan da ?yar yake magana".
?an jimmm baba malam yay yana sauke numfashi. Yace, "To inaga dai bara na sanarma yaron nan abokinsa shi sai ya nema wanda zaije ya duba halin da suke cikin, dan yanzu ni idan na kirashi a kunya zan sake sakashi tunda mamana ta ?allo masa aikin data iya na wauta".
Dariya Umm tayi shima yana tayata. A take ya kira Richard dan yanzu yana da Number sa. Sai dai bata shiga ba. hakan na nufin Rich baya Nigeria kenan kokuma wayar a kashe. ya barsa akan zuwa anjima zai sake gwadawa kawai.

A nan Austria kam Yoohan da ?yar ya iya taimakama Aymah ta sake shiga cikin ruwan zafi. Sai dai yau batai rakin jiyaba. Hawayene dai kam tanata abunta. Baiyi maganaba dan shima takansa yakeyi, da alama ma yafita jin jiki yanzun. Tana ganin ya shiga wajen wanka tai alwala ta fice daga bayin tana ?ingishi. Yau ko jiransa ya jasu salla batayiba. Tana idarwa yana fitowa. Komawa tai kan gado ta kwanta.
Bazai iya salla a tsayeba saboda jiri yake gani ga ciwon kai. Hakan ya sakashi yinta a zaune, yana idarwa shima gadon ya koma ya sake kwanciya. Wayar landline ya ?auka da nufin kiran yima Aymah order ?in breakfast saboda shan maganinta sai yaga wayarsa na haske. Hotel ?in ya fara kira, kafin ya ?auka wayar tasa dan silent take dama. Richard ya gani, cike da mamaki ya amsa kiran dan alamu sun nuna Rich ?in yana a cikin Austria tunda da Number ?asan ya kirashi.
Ko gaisawa basuyi ba Richard ya fara jera masa tambaya a rikice saboda jin muryarsa, cikin son kwantar masa da hankali Yoohan yace, "Ciwon kai ne kawaifa. Dama kana Austria?".
"Jiya da dare na iso, yanzu dai idan ba damuwa bara nazo ?akin naku na dubaka hankalina zaifi kwanciya". Murmushi kawai Yoohan yayi da fa?in "Okay". Daga haka ya ajiye wayar ya juya yana kallon Nu'aymah data juya masa baya. Ta na?e a cikin bargo alamar sanyi takeji. Maida idanunsa yay ya lumshe tunda yasan akwai kaya jikinta.

Kusan a tare Richard da ma'aikaciyar hotel ?in suka iso. Rich ya amshi abinci kawai sannan ya danna door bell. Mi?ewa Yoohan yayi da ?yar hannunsa dafe da kansa. Ya gyarama Aymah ?an kwalin kanta daya zame sannan ya nufi ?ofar ya bu?e. Saurin ri?esa Rich yayi ganin yanda yake layi, duk ya rikice masa da fa?an yaya zai zauna da ciwo irin haka baije asibitiba?. Amma yana fa?in wai ciwon kai ne kawai. Murmushin ?arfin hali kawai Yoohan yay masa shi dai, ya zaunar da shi a kujera yana sake jera masa sannu.
Kansa ya ?aga masa yana magana cike da ?arfin hali. "Shine zaka shigo baka sanar min ba?".
Rich da damuwa duk ta baibayesa yace, "Manta da batun shigowata fa?amin mike damunka Please X-man".
"Kai dai ka cika ru?iya. Ciwon kai ne kawai da zazza?i".
Hararsa Rich yayi da fa?in, "Shine bazakaje asibiti ba? Ina madam?".
Da idanu ya nuna masa gadon da cewa, "Gata can, itama bata da lafiyar".
"Oh GOD. Miya faru haka?".
Murmushi kawai Yoohan yayi baice komaiba. Hakan yasa shima Rich ?in bai sake magana ba ya mi?e ya fita yana fa?in, "Ina zuwa Please".
"Okay" Yoohan ya fa?a da jingina jikin kujerar ya lumshe idanunsa. Yanason tashi yaje ya tada Nu'aymah data fara barci taci abinci amma jiri da yake gani ya hanashi motsawa. Har tsahon mintuna sha biyar Richard ya dawo da kayan magani. Sannu ya sake yima Yoohan ?in sannan ya zauna yay allurai a cikin drip. Yana gamawa ya dubi Yoohan.
"Ya kamata ka koma kan gado sai a saka drip ?in". Idanu Yoohan ya bu?e da ?yar, batare da yayi magana ba yay ?o?arin tashi tsaye. Taimaka masa Rich yayi har kan gadon. Aymah nata barcinta batasan hidimar da sukeyi ba ita dai.
?aura masa ruwan yayi, sai da ya tabbatar ya fara shiga jikinsa sannan yace, "Ita kuma yaya zamuyi da ita?". Isaka Yoohan ya ?an furzar idanunsa a lumshe yace, "Inaga ita barta kawai, dan allura ya kamata ai mata kuma bazata tsaya ayi da arzi?i ba. Dan bata ?aunar allura sam".
"Okay, idan ka tashi kayi mata. Sai dai akwai alluran a wajenka ko sai an siyo?".
"Sai an siyo".
Ya bashi amsa a yanayin barcin daya fara fisgarsa. Sai kuma ya fa?ama Rich ?in sunan allurar da yake bu?ata.
Idanu Richard ya ?an waro waje jin allurar da Yoohan ?in ya fa?a. Cike da neman magana ya shuri ?afar Yoohan ?in yana fa?in, "Shegen sama, ashe kasan tsiyar daka aikata".
Shi dai Yoohan baice masa komaiba dan barcin ya fara masa Nauyi, Richard ya fice cike dajin da?in ?an uwansa ya zama babban mutum yau.

Yanayin rashin jin da?in jikin ya sakata kasa barci yanda ya kamata, ta bu?e idanunta a hankali kansa. Barci yake sosai yanzun. Ganin kamar ana ?ara masa ruwa ya sakata tashi a?an zabure. Cike da ru?ewa ta kai hannunta ta ?ora a bisa kansa. Har yanzu kan nasa bai gama hucewa ba da zafi. Sosai damuwa da tausayinsa suka bayyana ?arara a fuskarta. A fili tace, 'Bawon ALLAH, ashe shima bashi da lafiya, shiyyasa ?azun yaketa magana da ?yar. ?an balarabe ALLAH na zata duk muguntar da kaimin ce ta sakaka komawa kalar tausayi ai'. Ta ?are maganar da ?ora kanta bisa ?irjinsa hawayena cika mata idanu ganin an saka masa allura a jiki. Dan itafa ba'a ta?a mata ?arin ruwa cikin hankalinta dan bazata yardaba. Inhar yazam za'a ?ara mata ruwa to lallai sai an bata maganin barci ko an mata allurar barci saboda tsabar ?iyayyar dake a tsakaninta da allura.
Ta da?e jikinsa kwance kafin ta tashi ta zauna, tagumi tayi hannu bibbiyu ta zuba masa idanu kaikace television ta samu. Ta shafe kusan mintuna talatin a haka kafin ta mi?e saboda fitsari da takeji. bayan ta fito kuma idonta ya sauka kan abincin. Yunwa takeji bana wasaba, dan haka ta zauna ta faraci dan ta fahimci natane dama. Tanaci tana kallonsa harta kammala dan ka?an ma taci saboda rashin da?in bakinta, cike da son ?arfafa kanta da rashin da?in da jikinta ke mata ya sakata ?aukar magungunanta tasha kamar yanda taga yana bata kullum. Kasancewar barcin da suke sakata idan tasha ya sa ta ?ara ?ingirewa barcin a wajen.

¡ï¡ï¡ï¡ï

A hankali Yoohan ya bu?e idanunsa saboda ka?awar alarm alamar lokacin sallar zuhur yayi. Hakan kuma yay dai-dai da farkawar Aymah dake can kan sofa itama. Sai dai har Yoohan ya mi?e zaune ita ?in bata tashinba tana kwancenta. Inda take ya kalla yana sake lumshe idanu da bu?ewa. Sosai ciwon kan nasa yay ?asa. Zazza?in ma kuwa duka ya sauka. Ya zare drip ?in da ka?an ya rage ya ?are. Fuskarsa a yamutse na alamun wanda ya tashi a barci ya sauke ?afafunsa ?asa yana ambaton Alhmdllhi a cikin ransa. Sai da yay kusan minti uku a zaune sannan ya mi?e zuwa inda Nu'aymah ke kwance.
Da sauri ta maida idanunta ta rufe, shikam batare da yasan idanunta biyu ba ya ?ora hannunsa saman kanta. Alhmdllh ya fa?a jin babu zafi. Ya ta?a wuyanta ma nanma sanyi ?alau. Maganganun data sha ya dudduba yaga tashasu dai-dai, hakan ya sakashi mi?ewa ya nufi bayi zuciyarsa sakayau da farinciki da nisha?i. Jinsa yake tamkar wani sabon mutum a duniyar mutane. Aymah na ganin ya shige ta tashi zaune fuskarta a curku?e kamar zatai kuka. Gaba ?aya jitake tama rasa abinda ke mata da?i a duniya. Babu abinda tafi bu?ata kamar ta ganta a gaban Umm ?inta. Ta ha?iye ?wallar daya cika mata idanu tare da zabga uban tagumi.
A haka Yoohan ya fito ya sameta. Kallo ?aya tai masa tai azamar maida kanta ?asa saboda ganinsa da ga shi sai boxer da ?aramin towel a hannu. Direct yayo kanta yana fa?in, "Kin tashi?". Kunya ta hanata masa magana, sai kai kawai ta ka?a masa. Bai damuba dan ya fahimci kunyarsa takeji. Ya zauna a hannun kujerar yana cigaba da goge wuyansa idanunsa a kanta. "Mike miki ciwo yanzun?".
Murya na rawa tace, "Komai ma".
A ransa yace, 'Abin nemafa ya samu ga iya madam hajjaju malamar tsiwa da shagwaba'. A fili kam sai yace, "Oh so sorry Mrs Yoohan. Jekiyi wanka sai na duba wajen na gani".
Da sauri ta ?ago tana hararar sa kai kace idanun fa?owa zasuyi ?asa. Gashi dama sun kumburo saboda kukan data sha sannan akwai ja a cikinsu. Da sauri ya kauda kansa gefe gudun kar dariya ta kufce masa ya ?ara laifi. Mi?ewa tai tabar wajen tana ?un?unin da baisan mitake fa?aba a ciki saboda hausa takeyi. Ya ?an lumshe idanu ya sake


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login