Showing 36001 words to 39000 words out of 325075 words
"Bazaki ganeba Umm. Daga jiya zuwa yau naje sashenki yafi sau a ?irga amma sai na iske Baba malam na nan. Wlhy na kwana tamkar na ciji kaina dan ba?in ciki. Gaskiya Umm wannan al'amarin bai kamata mu zuba masa idanuba a wannan karon, yanzu dan ALLAH minene na ?aukar Number wayar likita idanba zalunci ba? Lafiyarta ne ba'ason anema kenan ko minene?".
"Humm Addah wlhy nama kaina wannan tambayar yafi sau dubu tsakanin jiya zuwa yau. A a daren jiya har musabbabin ciwon Nu'aymah sai da ya dawomin a rai. Bansan minene laifin yarinyar nanba akeson rayuwarta ta salwanta. Ni harma na rasa wane kalar tunani zanyi Addah, wanene? Miyasa? Mi mukai masa?......"
"Umm nidai tsakanina da ALLAH na fara zargin jama'ar gidan nan fa, idan har mai aikata wannan abubuwan ba'a gidan nan yakeba to daga ina yake zuwa? Nifa dagama jiya na fara tantama akan barin Nu'aymah gidan nan akan maganar aurenta. Shiyyasa ni dama tun farko ban yardaba. ni dama tun jiyan wani shawarace tazomin akan yanda zamu saka ido akan motsin kowa, na tabbatar insha ALLAH a hankali zamu samo bakin zaren".
Kai Umm ta ?aga mata cikin alamar nuna gamsuwa. Addah ta matso kusa da kunnen Umm ta gwargwa?a mata hanyar daya kamata subi. ?ari bisa ?ari Umm ta amince, suka ?aura da addu'ar dacewa. Daga nan suka cigaba da tattauna al'amarin suna ?arama juna haske. Umm bata bar sashenba sai da lokacin salla yayi. Ta koma sashenta tana jin da?i a ranta, koba komai zuciyarta ta rage nauyin da tai mata. Shiyyasa akoda yaushe take sake godema ALLAH daya ha?asu aure gida ?aya ita da aminiyarta. Su kashe su rufe matsalolinsu babu maiji sai ALLAH.
______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Wannan littafi SARAN ?OYE na ku?ine, yana ?aya daga zafafa biyar, idan kana bu?ata kaima wa?anan numbers ?in magana ka biya ku?insa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka karanta idan baka biyaba, karka kuma ya?a dan ALLAH idan ka gani??????.
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
_______________________
_____________
*_DUBAI_*
________
Tun randa Abdallah yay waya da wadda yake zaton Momynsa ce ransa ya sake dagulewa gaba ?aya. Wani lokacin ji yake tamkar ya na?ama Adawiya mugun duka ya cillata jirgi ta koma Najeriya. Sai dai tsoron fushin iyayensa ke sakasa dannewa.
A maimakon kwanaki bakwai ?inma da yay niyyar suyi a kwana na hu?u yasa suka wuce Saudia. Adawiya sai jin da?i takeyi dukda bata ganin koda murmushinsa. Ita kasancewa da shi a ?ar?ashin inuwa ?aya kawai ya wadatar da ita a cewarta.
Ba wannan bane karonta na farko zuwa ?asar saudia, sai dai yanda tazo a wannan karan yanada banbanci da sauran zuwanta na baya. Shiyyasa take wani jin kanta a sama. Wanda kuma takeyi dominsan ma baisan tanayiba. Tunda suka iso gidan da zasu zauna ya nuna mata ?akinta bata sake ganin koda ?eyarsa ba. Tsalle ta dingayi bayan fitarsa, dan ?akin yayi matu?ar ?yau da tsari. Sai dai kalar komar za?in Nu'aymah ne, harda ma manyan frames ?inta guda uku da aka manna a bango, sai na Abdallah guda biyu shima. Dukansu sunyi masifar ?yau. Ta ta?e baki da jan wawan tsaki, stool ?in mirror taja duk ta juya na Nu'aymah dan har cikin ranta ta tsani ganinta, tunda itace sanadin hana tabbatar farin cikinta, saboda Nu'aymah yah Abdallah ya?i sake mata, saboda Nu'aymah ta gagara daraja a garesa matsayinta na matarsa. Saboda Nu'aymah saboda Nu'aymah..... Komanta ya?i dai-daita kamar yanda tai fata, tabar na Abdallah kawai tana faman kuka kashir?an da zagin Nu'aymah da batasanma tanayiba.
Rayuwarsu ta saudia tana kadaran kadahan ne, baya shiga harkarta bakuma ya takura ma rayuwarta. Sai dai har yanzu ya hanata wayarta, idanma zata gaisa da Addah da Abbanta ko wani a ?an gidan nasu saita wayarsa. Kuma yay tsaye a kanta har saita gama ya amshe abarsa. Hakanna bata haushi, amma sonsa da tsoronsa ya hanata ta nuna masa koda a fuska.
A haka suka kwashe watanni biyu a gidan. Shirye-shiyen makarantarta ya gama kammaluwa ta fara zuwa. Da farko bata shiga harkar kowa ta maida hankalinta a karatu kamar gaske. Tana wata na biyu da fara karatunta tai ?awa mai suna Abida, sai da ana kiranta Maman Aaida, itama matar aurece harda yaranta biyu, asalin Mamana Aaida itama ?ar Nageriya ce, amma yanzu iyayenta na nan Saudia. Ta girma Adawiya da kusan shekara uku zuwa biyar, dan itakam zatai 22years. Maman Aaida irin matan nanne masu shegen iyayi dason gayu, ga ?wan?wanin tsiya kamar jikar ?aruna, kullum cikin bama Adawiya labarin mijinta take a zatonta Adawiya budurwa ce. Adawiya dataga iyayin Maman Aaida yayi yawa saita fito ta nuna mata itama ai tanada auren. Sosai Maman Aaida tayi mamakin hakan, danta tabbatar saita shirya zuwa gidan Adawiya a wani weekend. Babu wani ja'inja Adawiya ta bata address ?inta. A kuwa ranar Alhamis saiga Maman Aaida har gida ita da maigidanta da yaransu biyu, da yake Abdallah na gida sai har mijinma ya shiga. Abdallah dai bai wani sake musu ba, bai kuma wula?antasuba aka gaisa da ?ar hira suka wuce, bayan tafiyar tasu kuma bai cema Adawiya komaiba akan zuwan nasu ba duk da yasan ya dace ace yayi hakan.
Sanadin ha?uwa da Maman Aaida fa idanun Adawiya ya ?ara bu?ewa. Dan tunda Maman Aaida ta bigi cikinta taji yanda akai aurenta da Abdallah sai ta shiga ?orata bisa wasu hanyoyi da zata ringa jan hankalin Abdallah, ciki harda abubuwan irinsu turaren jan hankali da sauransu. Tun Adawiya najin tsoron yin hakan harta fara hawa kan network da sha'awar fara gwadawa ko zata dace Abdallah ya manta da Nu'aymah.
A ranar farko da ta fara bu?e jikinta da turare Abdallah bai kwana gidanba, yamayi tafiya bata saniba. Da yake sai ya gadama take ganinsa sai bata fahimci baya nanba, washe gari ta wuce makaranta. Data dawoma bata gansaba bata kawo komai a ranta ba har dare, lokacin kwanciya ta sake shanana turare ta nufi ?akinsa. Sai dai kuma wayam. saida ta le?a har toilet sannan ta lurama ba'ai amfani da toilet ?inba ma kwata-kwata. A take kuma sai tsoro ya kamata duk ta tsure, le?e-le?e ta shigayi cikin gidan kamar wata zararriya. Data ga dai lallai babushi a gidan saita fara kuka, ta koma ?akinsa ta ?ulle ?ofa ta ?udundune a bargo. Ta kusa awa guda a haka sannan ta fara jin motsin za'a bu?e ?ofa. Sake rikicewa tayi da kuka catake wanine ya shigi. Cike da mamaki Abdallah daya shigo yake sauraren kukan nata dan baiyi zaton ganinta a ?akin nasa ba. ?arasawa yay gaban gadon ya yaye bargon. Tako dage zata kwarara masa ihu dan ru?ewa ya hanata nutsuwa taga wanene. Saurin hayewa gadon yayi ya rufe mata baki ruf da hannunsa yana kallon yanda jikinta ke rawa.
A take yanayin nata ya juye masa tamkar na Nu'aymah, dan duk lokacin da abu ya tsoratata haka zakaga jikinta na rawa duk ta fita hayyacinta, daga haka kuma saita suma. Yanda zuciyarsa ke ?awata masa Nu'aymah sai tunaninsa ya gushe zuwa gareta harya rungume Adawiya batare daya fargaba. "K malama ki nutsu nine?".
Sosai Adawiya ta sake ma?an?ale masa dan a rikice take sosai, amma taji da?i da taji shine.
Tun Abdallah na sha?ar ?amshin turaren data saka matsayin ?amshi kawai harya fara canja masa yanayi. Hancinsa ya ?aura bisa wuyanta yana shinshina da lumshe idanu, kafin a ?auki tsahon lokaci jikinsa ya fara tsuma, sai ya sauya salon ri?on da yay mata. Anan nefa Adawiya ta dawo hankalinta da ?yau. Da farko nisha?in abinda yake matan ta farayi. Sai dafa taji al-amarin bawai wasan yara bane sannan ta fara kuka da ro?o da magiya. Da al-amari yay zurfi saiga hajiya malama mandiya ?ar ?walisar soyayya Adawiya na tsinema Maman da jamata ALLAH ya isa??????.
Oho, Abdallah baisan tanayiba, morewarsa yakeyi dai-dai gwargwado, yama manta dawa yake tare. Iya wahala ya bama Adawiya batare da tausayawaba, kafin ya koma gefe ya barta ko numfashin kirki bata iya yi.
Tun daga wannan ranar Abdallah ya maida Adawiya abar hutawarsa. Daya samu biyan bu?atarsa kuma ya watsar da ita tamkar bai ta?a sanin daga inda ta fitoba. Sam ta gagara gane kansa balle inda ya dosa. Komai nasa yana yinsane da kulawa da lura. Abincinta dama kam bai ta?a ci ba, zai dai ajiye mata duk abinda ta bu?ata ya kuma bata ku?i. Amma babu wani farin ciki da kulawa kamar yanda Maman Aaida ke fa?a mata. Duk iya dabarun Maman Aaida cikin gwadasu take ga Abdallah amma saiya yi kamarma baisan tanayiba. ba shiga ?akinta yakeba, ko abu zai bata sai dai yay knocking ta fito ta amsa. Idan yana bu?atar moranta ma zai mata knocking ne idan tana ?aki yace ta samesa nasa ?akin.
A haka rayuwar auren nasu ke tafiya tare da karatun Adawiya da ta fara saka shiririta saboda damuwarta kawai itace Abdallah ya sota a yanzu.
*_NAJERIYA_*
Rayuwa ta shu?a, kwanaki nata gangarawa, inda ake neman watanni na takwas kenan da lalacewar auren Nu'aymah da Abdallah. Tana cikin tsananin damuwa da begensa, kullum dare sai tayi kuka, tana sonsa matu?a, dan ta rayune da son nasa. Yawan damuwar da take a cikine ya haifar mata da yawan yin ciwo, saboda ciwonta bayason damuwa sam. A duk sanda ta takura kanta da tunani da damuwa yakan yawaita motsa mata akai akai, tana kuma matu?ar shan wahala.
Gaba ?aya a awatannin nan lafiya ta?i wadatarta, haka taketa fama yau fari gobe tsumma. Gashi baba malam kullum cikin mata jan ido yake akan ta kawo Ameer yay musu aure. Tayi kuka tayi rantsuwar akan Ameer ba saurayinta bane amma sam ya?i ya saurareta. Umm kanta wannan al'amari na tada mata hankali. Amma babu yanda ta iya ta zuba musu ido kawai taga iya gudun ruwan mijin nata.
Burin Nu'aymah cigaba da karatu a yanzun, amma Baba malam yay banza da maganar karatun nata, bayan kuma kowa a gidan yasan burinta a rayuwa shine ta zama likita ko Nurse tun tana yarinya. Addu'arta kullum itace Baba malam ya ha?ura a sake nema mata makaranta kafin ALLAH ya dawo da hankalin Abdallahnta gareta, dan ita duk ?aukarta Abdallah fushi yake da ita akan ta gudu ran aurensu, shiyyasa ya?i nemanta koda a wayama. Ta dage da azumin litinin da alhamis da sallar dare tanata gayama UBANGIJI kukanta.
Ana cikin wannan yanayin su Baba malam suka gama shirya gagarumar walima na saukar Al-Qur'anin yaransu na gidan marayu, tare da aurar da wa?anda suka samu mazan aure. Wasunsu anan cikin gidan suka dai-daita kansu. Wasu kuma a waje suka samu mazajen aure da mata.
Shirye-shirye ake babu kaman hannun yaro, dan shinema ya ?auki Baba malam Busy sosai ya samawa Nu'aymah lafiya daga takurar zancen fiddo mijin aure. Duk da dama dai yana matane kawai dan hukuntata ta cikin ruwan sanyi akan abinda ya faru. amma ta ?ar?ashin ?asa neman hanyar ganin likitan nan kawai yakeyi da nema mata makaranta batare da ko Umm ta san da hakan ba.
Ana saura sati ?aya su Yusrah suka iso, washe gari kuma su Amal. Hakan ba ?aramin da?i yayma Nu'aymah ba, koba komai ta rage ka?aicin da ta tsinci kanta a cikin a wa?annan watanin ai. Abinda ya ?ara fa?a?a farin cikin natama shine Amal da Yusrah bazasu komaba, dan zasu zaunan zana jarabawar ssce anan. Cikin kwana biyu kacal da dawowar tasu ta fara komawa cikin walwalarta.
Tuni suka fara addabar gidan da ?iriniyarsu da bata ?arewa, sau?inma babu Adawiya, amma hakan baisa sun fasa abinda suka saba yiba. tun ana saura kwana uku suka saka Hajjo ta ro?a musu baba malam komawa cikin gidan marayu har sai an kammala komai. Dan yawancin ?ammatan da za'aima auren duk ?awayensu ne, duk da dai a shekaru gaskiya zasu girmesu da kusan shekara bibbiyu ko ?ai-?ai.
Bai hanasu ba, dan gidan marayun nan nada matu?ar muhimmanci a garesa dama family ?in gaba ?aya. Yanda suke ?o?arin dagewa akan tarbiya da karatun yaransu haka suke dagema yaran gidan marayun nan suma. Shiyasa suma yaran suna tsananin ?aunar wannan family, su suke ?auka danginsu da komai a rayuwa.
¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï
"Wai wannan akwatin da kika lodama kaya duk na miye Nu'aymah?". Umm data shigo ?akin Nu'aymah ta fa?a tanabin Nu'aymahr daketa shirin kaya da kallo.
?agowa tai ta kalli Umm cike da ?oki, "Umm yo na bikine mana, sati guda zamuyi a can". "To lallai, ashema kune iyayen bikin kenan?". Dariya Nu'aymah tayi dajin zancen Umm, Umm kam daga haka bata sake cewa komaiba ta ajiye mata magungunan ta tana fa?in, "Gasu nan, saura kije kita wasa da shansu Nu'aymah, dan ALLAH ki kula da kanki, duk abinda kikasan zai zame miki matsala ki kujesa, ku kuma ri?e mutuncin kanku, na kira Baba Habi a sashenta zaku zauna kafin Hajjo ta iso gobe idan ALLAH ya kaimu, saura naji wani abu mara ?yau na shegen tsiwanki, ALLAH saina ?ata miki rai".
"Umm insha ALLAH bazakiji komaiba ma". "ALLAH yasa". Umm ta fa?a tana juyawa ta fice daga ?akin..
Bayan sallar azhar su Nu'aymah sukai sallama da kowa suka wuce, Yah Abubakar ne ya kaisu. Da yake shima irinsu ne ?an taraliya saida ya kaisu sukai shopping sannan ya wuce dasu gidan marayun.
?aton gaske ne, sannan an ?awatashi ta ko ina babu makusa. Akwai makaranta da asibiti da duk ma abinda masu rayuwa da iyayensu suke samu. Makarantarsu ta fara tun daga noziri har zuwa sakandire. Ana koyar da boko da arabic, idan kaji yanda yaran ke larabci da turanci sai kasha mamaki da al'ajabi. Rayuwarsu suke cike da farin ciki da jin da?i wadda ko wasu masu iyayenma basa samu. Gasu da tarbiyya abin birgewa.
?ata lokacine zama bayyana muku yanda gidan marayun nan ya ginu da tsari mai ?yau, kusa a ranku kawai ya ha?u. Dan sosai su baba malam ke samu taimakon manyan mutane dama masu mulki game da ri?e gidan. Ga kuma suma kansu masu nemane basu zauna jiran na sadakaba. Kaso mafi yawa na ?unbin dukiyarsu yana tafiyane wajen tattalin rayuwar marayun nan da kulawa da su. Shiyyasa Alhmdllh da wahala ace sun nema abu sun rasa. Sai dai ace yau da gobe sai ALLAH, komai arzi?inka dama wani abun sai ya gagareka.
A yanda su Nu'aymah suka sami tarba zai tabbatar maka da sanannune a gidan, kuma ba wannanne farkon zuwansu su kwanaba. Dan rigima aka shigayi musamman ga sa'anninsu, kowa na fa?in sashinsu su Nu'ayma zasu sauka. Bayan ansha ta?addama dai kowa ya ha?ura zasu zauna a sashen da amare suke, wato sashen baba habi da Umm ta fa?ama Nu'aymah tun a gida.
A yau kowa ya kalli Nu'aymah yasan tana cikin farin ciki sosai, ha?oranta sun kasa rufuwa. Tsiyarsu sukaita tsulawa uwa ba kwa?a uba babu tsanani, dan suna son suga sunzo gidan nan, shiyyasa wani lokacin baba malam da kansa yake cewa suzo suyi weekend ?insu anan, dama anan duk yaran gidansu ke karatunsu tun daga noziri har zuwa sakandire, shiyyasa sukeda sha?uwa sosai da yaran gidan marayun fiye da zaton mai tunani.
Washe gari Nanah tace suma gasunan zuwa ita dasu Suhailat, hakan yasa bayan sallar la'asar ana tsaka da musu ?unshi dan ranar itace suka saka ranar ?unshin, Nanah ta kira wayar Yusrah ta sanar musu gasu a bakin titi suzo su shiga dasu dan baza'a barsu su shigaba kai tsaye.
Nu'aymah da Yusrah da biyu cikin ?ammatan gidan suka fita shigowa da su Nanah dansu ?unshinsu harya bushe sun wanke, Nu'aymah ce kawai bata wanke nata ba amma ya bushe. da ?ar tafiya tsakanin gate da gidajen yaran, amma haka suka taka a ?asa suna hira har suka iso. suna a gab da fitane suka ha?u da yaran gidan maza da bazasu gaza shekaru sha biyu ba kusan su bakwai wai wajen ball suka tilla ?wallon waje ta katanga shine zasu zagaya ?akkowa. Security ?aya ne tare dasu zai rakasu. A tare suka fita dasu Nu'aymah da zasuje tarbar su Nanah.
Gidan marayun yana akan babban titine, shiyyasa sam ba'a barin yaran fitowa ko ina su ka?ai koda hakan ta kama sai da security.
Dariya Nu'aymah tai ganin su Nanah acan ?ayan tsallaken