Showing 30001 words to 33000 words out of 325075 words

Chapter 11 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29168

yake baka kishina hakan ko damunka bayayi. To wlhy kama cire wannan tunanin a ranka. Kuma ko a waya ka kira wani cikin iyayenku kace a ?aura maka aure da Nu'aymah shima ban yafe makaba. Idan wannan maganar tasa ka kirani karka sake kirana".
Ta katse wayar batare da ta jira cewarsa ba.

Sosai jikin Abdallah ke tsuma. Ha?oransa har wani bada sautin ?ara suke saboda rawar da bakinsa keyi. So yake ya fa?i sunan Momy amma ya kasa ha?a kalmar waje guda dan tsabar rikicewar da yayi.
"Yah Ab lafiya kuwa?". Adawiya ta fa?a tana ?aura hanunta saman kafa?arsa. A fusace ya ?ago ya hanka?e hannun nata tai taga-taga ta fa?a saman kujera. Ko kallonta baiyiba yay wurgi da wayarsa ya nufi bathroom da sassarfa. Yana shiga ya sakarma kansa shawa ruwan na saukar masa a jiki batare da ya cire kayaba.
Kalmar ALLAH ya isar Momy ce keta masa kai kawo a zuciya har kana hango sama da ?asan da ?irjinsa keyi na.

Adawiya kam tana ganin ya shige ta mi?e idanunta cike da hawaye. Da ?yar ta ?angyasa ?afarta data buge da centre table ta isa inda yay wurgi da wayarsa. Addu'a take ALLAH yasa babu lock. Cikin sa'a kuwa babun, sai dai hoton data fara cin karo da shi a fuskar wayar ne yasata jin wani irin zafi tamkar an soki zuciyarta da mashi.
Hoton Nu'aymah ne da sukayi ranar walimar gama makarantarsu. Tayi masifar ?yau a hoton, dan ?akar doguwar rigar data saka na Material ?inkin yay masifar zama mata a farar fatarta. Ga idanun nan sun bala'in fitowa cikin kwalli har wani ?yalli suke saboda haske. Tayi ?an murmushinta lo?ar kuncinta data gemunta ta fito ra?am. Sosai Adawiya ke faman taunar lips da ?arfi tamkar zata hudasu, duk da tasan hoton tunkan shi Abdallah ma ya gani hakan bai hanata jin zafi mai tsanani ba. Da kyar ta iya danne ranta ta shiga dan son ganin dawa yay waya. A fili tace, 'Momy!. To mita gaya masa daya fusatashi haka har yake neman karya ni a banza?'. Bata da mai bata wannan amsar, gashi kuma batasan inda wayarta takeba balle ta kira wani ta tambaya. Tanajin tsoron yin amfani da tasa kuma yazo ya kamata. Da sauri ta ajiye wayar inda ya jefar jin za'a bu?e ?ofar bayin.
Tsaye yay cak a ?ofar bayin yana binta da kallon tuhuma fusatar zuciyarsa na da?a bayyana saman fuskarsa.............?


Kuyi ha?uri, jiya man kaina ne ya tsiyaye tas yasin na kasa typing??.


_____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________

Wani kaya sai amale ka ?auka??.

SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.

Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ?an gaske.

*_Ina mata masu ?an bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ?ar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ?an ?walisa masu son sabunta gida da kayan ado ?an waje masu sau?in farashi da nagarta!._*

_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ?aya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ?yau da nagarta a farashi mai sau?i kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ?an gayu suma akwaisu babu ?ayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba'a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ?aki basu da tsara_.

Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.

Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ?arin bayani ?ar uwa.

*_Siyen nagari??, maida ku?i gida?? sai SAHFAT PREORDER??????????_*

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________


Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????

Mamu gee??
MIN ?ALB!!????

Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????

Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????

Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????

?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.
[3/14, 2:33 PM] +234 901 860 0202: *_Typing??_*

No. 9

.................Sosai Adawiya ta tsorata da mugun kallon da Abdallah ke jifanta da shi. Jan jikinta ta farayi baya a hankali ganin ya fara takowa yana nufota. "Y...y..Yah Ab wlhy babu abinda nayi da wayarka, Please dan ALLAH karka dak......"
Ta kasa ?arasawa saboda kiran wayar da akayi. Shima cak ya tsaya daga bin nata yana kallon wayar. (Sweet Momy) ya hango ?aro-?aro yana yawo akan fuskar wayar kamar yanda yay saving. Iska mai zafi ya busar daga bakinsa yana lumshe idonu. Tsinkewa wayar tayi aka sake kira. Yanda bai motsaba haka ma Adawiya ta kasa motsawa. Kallon wayar take kawai daga nesa tamkar yanda yake kallonta shima. Sai ka ?auka gamo sukai da bomb.
Sai da Momy ta jera ma Abdallah kira har biyar bai ?aga ko guda ?aya ba a ciki. Daga ?arshema saiya nufi wayar a fusace ya takata da ?afarsa. A take screen ?in ya shiga bada sautin fashewa.
Baya Adawiya tai da sauri tana mugun waro idanu da bu?e bakin mamaki. Al'amarin bai ?ara firgitataba sai da taga ya ?auka wayar ya zare sim card ?in ya karyashi biyu. ya kuma nufi toilet ya jefashi yay flushing a take.
Da sauri Adawiya ta koma inda take da ta tsaya zuciyarta na mata wani masifar bugu, ga wani irin tsoron Abdallah daya sake shigarta mai ?arfi. Sam batai tunanin yanada zuciya irin hakaba. Duk da tasan ?an gidansu kowa yanada wannan shegen zuciyar amma tazata tashi mai sau?ice ganin yanda bata cika ganin fushinsa ba. Ta gabanta yazo ya fice ko kallon inda take bai sake yi ba. Ya bugo mata ?ofar da ?arfi har saida ta zabura jikinta na karkarwa........

*_NIGERIA_*

Cike da mamaki Momy ke kallon wayar tata tamkar idanunta zasu zubo ?asa. A ranta take raya 'To miya samu wayar Abdallah? Ta shiga bai ?agaba, daga ?arshema wayar ta jita a kashe'.
"Momy lafiya?". Omar daya shigo falon ya fa?a idanunsa akan Momy dake tsaye tana ta faman juya waya.
Saurin ?agowa tai ta kallesa, sai kuma cikin sanyin murya tace, "Omar yayanku ne wlhy, ya kirani bana kusa inaga ko cikin su Amal wani ya ?aga, shine yanzu dana fito naga alamar ya kira an ?aga saina kirashi. Amma har missed calls biyar na jera masa bai ?aga minba, yanzu daga ?arshema wayar a kashe take".
Murmushi Omar yayi yana zama da fa?in, "Oh Momy ?ila to baya kusa ne, kinsan hidimar Yah Abdallah ba ?arewa takeba. Nasan zai kiraki shima".
Kai Momy ta girgiza masa, "Omar ba rashin ?aga kiran bane damuwata, jin wayar a kashe bayan kuma duka kiran danai sun shiga".
"Momy Please ki kwantar da hankalinki, nasan insha ALLAH babu wata damuwa. Koma baida cajine kokuma network".
Kamar zata sake magana sai kuma tai shiru ta?an jinjina kanta. Tashi tai ta maida wayar a caji dan fama cajin ta saka ta shiga kitchen tun ?azun. Yanzuma tana maida wayar a caji saita koma kitchen ?in suka cigaba da aiki ita da masu aikinta su biyu tabar Omar daya kwanta cikin kujera yana canja chennal a falon. Sai dai kuma abin ya?i barin ranta sam.

Har dare Momy na jiran kiran Abdallah shiru, ta kuma sake nemansa itama amma har lokacin wayar switch up. Tun tana danne damuwarta harta bayyana fili. Abbah da tun ?azun yake kula da yanayinta ya tambayeta ko lafiya?. Batai nauyin bakiba tai masa bayanin abinda ya faru.
Shi dariyama ta bashi ganin yanda duk tai wani iri kamar ance Abdallahn ya rasu ne, dan haka ya?an murmusa yana girgiza kansa, batare da ya ce mata komaiba ya cigaba dacin tuwonsa.
"Abban Abdallah dan ALLAH ko zaka kira min shi da wayarka?". Sake kallonta yayi da ?yau, sai kuma yay gyaran murya da ?auke idonsa. "Khadija ki rage ru?iyarnan taki, yanzu dan ALLAH Abdallah ?aramin yarone halan? Maybe baida caji ne kokuma ya shiga wata sabgar. Kiyi ha?uri kiga zuwa safiya idan ALLAH ya kaimu idan bai kiraki ba".
A sanyaye tace masa "to" kawai badan hakan ya mata da?iba. Sai ma ta tattare kwanikan daya kammala cin abincin ta fice da su. Saida takai kitchen sannan ta nufi ?akin su Amal. Zaune ta iskesu suna karatu, Amal na ?arama su Imran. Duk shiru sukai suna kallonta. Itama kallon nasu takeyi.
"Amal wanene a cikinku ya ?aga kiran yayanku ?azun?".
"Kira kuma Momy? Wlhy bansan Yayah ya kira wayabama ni, dan tun ?azun danace miki zanje na sake duba Nu'aymah ina can wajenta ?angaren Hajjo ni da Yusrah. Amma wani abune ya faru?". Kai momy ta girgiza mata tana kallon su Imran suma. Da ?ai-?ai suka shiga bata amsar suma duk basu baneba.
Kanta ta?an dafe zuciyarta na neman fa?awa a ru?ani, lallai yaran sunada gaskiya, dan idanma tai dubi da lokacin da Abdallah ya kira ai duk basa gidan ma suna islamiyya. Kasancewar yau lahadi sunayin harta safe zuwa uku a tashesu, to indai suna garin suma yaran suna zuwa anan ma. Kuma tunda safen duk suka fita. Amal ce kawai batajeba saboda ta tashi da ciwon mara, daya ?aga matane tace zataje ta duba Nu'aymah. Sai da ta fita da kusan awa ?aya ma Abdallah ya kira.
Ficewa tai taja musu ?ofar tanason tunano ko wani ya shigo a wannan lokacin, to amma kuma babu wanda ya shigo ?in, daga ita sai ?an aikinta. Abba ma baya nan, Omar ma ganin datai masa bayan kiranne ya shigo gidan, dan tare suka fita da baba malam tunda safe.

Momy da taga tunaninta na kaita wasu nazari daban sai kawai ta ajiyesa gefe, ta barsa akan uzirine yayma Abdallah yawa. Waya kuma ?ila sanda yake kira cikin sauran ?annensa yaran gidan wani ya shigo ya gani ya ?aga.
Washe gari da safe batabi takan kiran Abdallah ba ta cigaba da hidimominta kamar yanda ta saba. Abin mamaki kuma har dare bai kirantanba, sai itace dai da dauriyanta ya gaza ta nemesa kusan ta?was na dare. Switch up dai ?in yauma.
Ganin yanda ta zuba tagumi yasa Abba jin tausayinta. Wayarsa yasa ya kira Abdallahn, amma sai yaji layin a rufe. maida kiran yay a ?ayar Number Abdallah ta business. Bugu biyu kuwa ya ?aga. Bayan sun gaisa yace masa ga Momy.
Jimmm Abdallah yay kamar bazaice komaiba, sai da Abbah yace, "Nace ga Momynku ko bakajiba?".
"Amm sorry Abbah network ne, bata to".
Mi?ama Momy Abbah yayi, ta amsa zuciyarta na mata sanyi, dan tana matu?ar ?aunar Abdallah sosai a cikin ?a?anta, sai dai tana ?o?arin dannewa gudun saka ru?ani a tsakanin ?a?anta.

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Wannan littafi SARAN ?OYE na ku?ine, yana ?aya daga zafafa biyar, idan kana bu?ata kaima wa?anan numbers ?in magana ka biya ku?insa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka karanta idan baka biyaba, karka kuma ya?a dan ALLAH idan ka gani??????.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

_______________________

Da ?yar Abdallah ya danne zuciyarsa ya gaida Momy da fuskarta ke shimfi?e da murmushin farin cikin jinsa. Ta amsa masa cike da kulawa tana tambayarsa yaya suke? Ina Adawiya?.
Muryarsa a ?an cinkushe yace tayi barci, shima shirin kwanciya yakeyi.
"To Alhmdllh tunda dai lafiya kuke. amma jiya miya samu wayarkane? Na kira har sau biyar baka ?aga ba, daga baya kuma saima naji switch up".
Ba ?aramin haushine ya kama Abdallah ba dajin maganar Momy, bayan shara?in data gindaya masa mai ?arfi akan abinda yake tsananin so shine kuma zata kirasa?, yanzu kuma dan taga tana kusa da Abbah take nuna kamar batai komaiba. To mizata fa?a masa bayan wanda ta fa?a masan kuma?............
"Abdallah lafiya kuwa?". Momy ta katse masa tunani. "Babu komai Momy, wayarce ta fa?i a cikin ruwa bayan mungama waya jiya shiyyasa".
"Abdallah ai ni bamuyi way......."
Zare wayar Abba yay daga kunnen Momy yana fa?in, "Haba Khadijah tunda kinji lafiyar tasu ya isa haka. Bakiga dare yayiba ne? Yanzu kuma Abdallah yanada iyali".
"Afuwan Abban Abdallah na shafa'ane wlhy. Ni saima naji muryarsa kamar wanda bayajin da?i".
Kallonta Abba yay sosai, sai kuma ya matsota jikinsa ya gwargwa?a mata magana a kunnenta. Idanu ta ?an zaro waje, sai kuma tai saurin mi?ewa tana kare fuska da hannu alamar maganar tasa ta bata kunya.
Murmushi Abba yay yana binta da kallo harta shige toilet. Ya?an girgiza kansa yana gyara kwanciyarsa.

________________

Jikin Nu'aymah yayi sau?i sosai Alhmdllh, sai dai har yanzu bata koma sashensu ba tana sashen hajjo. Tana dai zuwa ta gaishesu da safe, ta kuma taya Umm aiki kamar yanda aka horesu. Babu wanda yay mata maganar Yah Ab a gidan, itama tayi ?o?ari ta danne tana jira taji daga garesu kamar yanda Yusrah ta bata shawara data dameta da tambayar yanda akayi.

Kwana biyu da samun lafiyar Nu'aymah su Momy sukai shirin komawa Abuja saboda karatun yara. A wannan karon Nu'aymah jitai batason tafiyar su Yusrah da Amal, dan suna ?auke mata kewar Adawiya sosai. Tasan kuma idan suka wuce zata koma ita ka?aine babu wani abokin ?iriniyarta kamarsu a gidan, daga yayu sai ?anne sai iyaye.
Babu yanda ta iya, a washe gari su Amal suka fara wucewa Lagos da safe. Da yamma kuma su Yusrah. Nu'aymah harda hawaye. Hajjo da taji tausayinta har tayi tunanin ko Nu'aymah tabi cikinsu Yusrahn, sai kuma ta tuna ashe akwai shirin zuwa ganin Doctor da sukeyi. Zama tayi taita lallashinta harta saki jikinta, yayinda su Hajarah da sukazo sashen Hajjon suka ?an rage mata kewar tafiyarsu Amal ?in.

¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï

Kwanaki sun shu?a, jikin Nu'aymah yayi garas, gidan ya koma kamar da sai su ka?ai. itama harma ta tattara ta koma ?akinsu ita da Adawiya dake a sashensu. Sosai takejin kewar Adawiya, musamman ma idan tazo kwanciya ko zata shiga toilet. Dan ?a'idane kullum sai sunyi fa?a akan bargo da filos, hakama shiga wanka sai sunyi fa?a. Haka sabo yake turken wawane.
A yanzun kam sai Muhammad ?aninta ya zame mata abokin hira. Daya dawo makaranta koda yaushe suna tare, duk da dai ta dage wajen maida hankali a karatunta na islamiyya itama. Dan a ?an tsakanin nan ba ?aramin ?o?ari takeyi akan haddar Qur'aninta ba. Ga sauran littatafai ta dage sosai suma.
Wannan karatun shine ya ?auketa busy matu?a. Tunma rashin sakewar da su Umm suke mata yanzu yana damunta har abin ya fara raguwar mata a rai. Dan tasha tambayar Umm ?in kota musu wani laifine?. amma sai Umm ta shashantar da zancen ta?i bata amsa, haka shima Baba malam baya cemata komai akan hakan. A yaran gidan ma duk wanda taima tambayar ina Adawiya taje? Sai suce mata makaranta, Yah Ab kuma ya koma Saudia.
Takanyi shiru taita tunanin miyasa za'akai Adawiya makaranta ita ka?ai a barta? Bayan kuma tunda suka taso komai tare sukeyi, makaranta da komai da komai tare ake sakasu, kuma tare ake musu komai. Wannan tafiya makaranta da taji na Adawiya saida ya sakata kuka, daga ?arshe ta ha?ura da fatan ALLAH yasa haka shine mafi alkairi. Tana kewar Yah Ab sosai a zahiri da ba?ini. Gashi yanzu bata da waya, ta kuma kasa aron ta wani ta kirashi koda ta Umm ce. Dan da idan tanason suyi magana wayarta babu caji data Umm take amfani. Shima daya kira yaji bai sametaba zai kira Hajjo ko Umm a bata. Amma a wannan karon ganin shima ko sau ?aya bai nemeta ba sai al'amatin ke ?aure kanta da bata mamaki. Da taga dai zuciyarta na neman ?untata sosai sai taje ta tsare Hajjo da tambaya tana kuka.
Hankalin Hajjo ya tashi sosai. Ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login