Showing 117001 words to 120000 words out of 325075 words

Chapter 40 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29121

baba malam ?in.
Da sauri Yoohan yace, "Papa saboda mi?".
Kallonsa papa yayi da tsananin ?acin rai. Kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru ya sake maida kallonsa ga baba malam dake murmushi.
Baba malam yace, "Kayi ha?uri, dan kai yau sunanka ba?ona. Ka cancanci na karramaka da masauki da abin ci da sha. Dan koba komai kazo ?asata ne, yankina, gidana kuma".
Tsaki papa ya ja. Tare da kallon d.p.o Emanuel yace, "D.p.o kama shi, inason sanin dalilin ala?arsa da yarona".
"What!!?" Yoohan ya fa?a a zabure yana ?arasowa gaban papan. Cikin nuna fusata yace, "Papa mi kake shirin yi haka? Dammi zakasa a kamashi bayan ba'a cikin gidansa ka ganniba. Sannan ba tare da shi ka ganni ba".
"Rufema mutane baki!!. Karna sake jin bakinka anan. Wannan wasane tsakanin manyan daji guda biyu. Ka shiga mota yanzun nan zamu koma Abuja da kai".
"Babu inda zanje papa. Domin aikina ne ya kawoni nan. Banga kuma dalilin dazaisa na barshi ba akan dalili mara tushe. Ku kuma (ya fa?a yana nuna police ?in) duk wanda yay gigin matsowa koda kusa da shi ne na rantse da ALLAH sai ya rasa aikinsa. Idan kunji ?arya zaku iya gwada hakan kuma".

Tashin hankaline ?arara ya bayyana a fuskar d.p.o Emanuel. Dan shi kam an sakashi a tsaka mai wuya. Matsayin papaa a garesa ya wuce duk yanda mai karatu zaiyi hasashe. Sannan ?ansa Yoohan basai an fa?aba, yanada fa?a aji ga gwamnatin kowacce jaha saboda rawar da yake takawa akan harkar lafiya dama matsayinsa na babban likita da duniya gaba ?aya ke ji da gani a yanzu. Dan tabbas yaron yana lokaci da lokacinsa.
"Yahya! Iyaye nada matu?ar daraja ga ?a. Ka daina tsaurara harshenka ga mahaifinka kaji. Karka damu da tsakanina da shi, dan a yau a yanzu ya fini gaskiya tunda a wajena ya sameka. Ba'a wasa da iyaye. Dan haka karka sake maida masa magana kaji". Baba malam ya fa?a idanunsa akan Yoohan dake ta faman ha?iyar zuciya da sauri-sauri.
Kai kawai ya ?aga ma baba malam, dan zuciyar tazo wuya bazai iya magana ba. Ya watsama guards ?insa wani shegen kallo. Kafin ya ra?a papa da baba malam ya bar wajen batare da yayima kowa maganaba.
Papa da yasan minene fushin Yoohan yay saurin bin bayansa yana kiransa. Amma ko kallonsa baiyiba balle ya saka ran amsawa. Ya bu?e murfin motar a fusace ya shiga baya, shima Papa ?ayan gefen ya zagaya ya shiga yana cigaba da kiran sunan sa. Hakanne ya saka drivern sa da Solomon saurin shiga suma, sauran guards ?insa da su Emanuel da suka sami mafita suma suka nufi nasu motocin batare da suncema baba malam komaiba.

Nannauyan numfashi baba malam ya sauke lokacin da mitocin suka harba kan titi. Yayinda can ?asan zuciyarsa ke mamaki da jinjina al'amarin UBANGIJI. 'Yoohan ?an Pastor Goshpower ne da gaske? Lallai UBANGIJI mai yin yanda yaso, a lokacin da yaso, ga kuma wanda yaso'. Baba malam ya fa?a a fili. Yasan tabbas UBANGIJI shike fidda rayayye a cikin matacce, ya kuma fidda matacce a cikin rayayye. Amma al'amarin akwai ?unbin ban al'ajabi a cikinsa, dan yasan abubuwa masu yawa game da papa tun shu?a?en lokaci kafin yakai haka.
Da wannan tunanin baba malam ya koma cikin gidan, inda ya tadda duk jama'ar gidan sun fito sunata tararrabin abinda akace ya faru da Nu'aymah. Su Abban Abdallah ma shirin shiga mota suke zasubi bayansu asibitin.
Ganin baba malam ya sakasu dakatawa, duk suka nufesa hankali tashe suna tanbayar yaya Nu'aymahn.
Tausayinsu ne ya kamashi. dan haka cikin taushin murya ya kwantar musu da hankali, tare da sanar musu shima yanzu zai bisu. Basu zauna ?ata lokaciba suka ?unguma a mota ?aya Omar ya jasu, akabar su Umm a gida na binta da addu'a.

Yoohan da tunda suka tafi ya ?i kula papa daketa so yayi magana yay kwance jikin kujera hannunsa dafe da goshinsa cike da tsananin takaicin abinda ya faru tsakaninsa da Nu'aymah yauma. Yarasa mike jan hankalinsa ga aikatama yarinyar nan wannan banzan ?abi'ar?. Abinda ba halinsa ba amma yana ?o?arin ?abi'antar da shi a gareta. Saima yaji na yau yafi masa zafi a rai fiye da na jiya.
Da sauri ya kwanto jikin papa saboda wata hajijiya-hajijiya dake neman kwasarsa. Sake rikicewa papa yayi. A matu?ar ru?e ya shiga girgiza Yoohan kai kace gani yay baya numfashi.
Sosai takaici da hayaniyar papa ta sake rufe Yoohan ?in, amma sai ya daure cikin taushin murya da sanyayata yace, "Papa Please relax. Ina lafiya fa".
Da sauri ya rungumeshi yana sauke numfashi a jajjere. Su dai su Solo suna kallon ikon ALLAH daga gaba. A haka suka ?arasa hotel ?in da har yanzu akwai sauran yaran Ema... Da taimakon papa Yoohan ya fita, shine ya kamasa har ?akin da yake. Su kuma su Solomon suka dakata wajen manager ?in hotel ?in suna musu bayani akan anga Yoohan ?in su kwantar da hankalinsu.

Papa na zaune kusa da Yoohan dake kwance idanu a lumshe, hannunsa har yanzu dafe yake da kansa. Yama rasa wane kalar tunani ya dace yayi akan matsalarnan guda biyu. Ala?alar Papa da Baba malam. Abinda ya aikatama Nu'aymah a karo na biyu. Bu?e idanunsa yay a hankali kan papa da yay shiru shima yana wani tunani can daban, sai da yay masa kusan kallon sakan goma kafin cikin nuna kulawa ya kamo hannunsa cikin nashi da fa?in, "Papa!".
Firgigit ya dawo hankalinsa tare da kallonsa. Yoohan ya sake lumshe idanu ya bu?e a kansa. "Papa dama kasan malamin nan ne?".
"Yoohan! Wannan tambayar taka bata da muhimmancin samun amsa. Kai ya kamata nasan minene ala?arka da shi?".
Kamar Yoohan ya fa?i ainahin gaskiya sai kuma wata zuciya ta garga?esa dayin hakan. Yun?urawa yay ya tashi zaune sosai ya jingina da fuskar gadon. Hannunsa ya sake maidawa cikin na papansa, cikin kwantar da murya yace, "Papa akwai abinda nake bu?ata a wajensa, shiyyasa na kwantar da kaina nake binsa a sannu harna cimma burina. Sai dai kuma gashi kai kazo cikin mintuna goma kacal kana shirin rusamin shiri na. Miyasa zaka biyema su Solomon da shirmensu? Ai koda suka sanar maka na ?ata ko tunanin inda za'a'a sameni kamata yayi ka jira harna dawo kaji ta bakina. Haba papa da girmanka a ?asarnan amma kake abu tamkar wani mara......."
Saurin katsesa papa yayi ta hanyar ?aga masa hannu. hakanne ya saka Yoohan ha?iye sauran maganar tasa. Papa ya gyara zamansa sosai da cewa, "Naji nayi kuskure, amma kaima harda laifinka. Miyasa tun tuni baka sanarmin ba, bayan kasan ni?in mai baka goyon bayane akan kowanne irin business naka musamman a wannan yakin".
"Nima naji nayi kuskure to. Amma ina da dalilin ?oyewar ai. Da ace na sanar maka mi nake shirin yi zaka iya ?atamin aiki dan kanada gaggawa papa. kai kafi son komai da zafi-zafi a lamarinka. Hakan kuma na ta?iyeka daga nasarorinka. Yanzu da ace bakazo ba da cikin satin nan zan kammala aikina. Amma yanzu kaga ka kawo min togaciya dan zai fara kokwanto a kaina. Kaga kenan saina sake sabon ginin da zai ?ara yarda dani hundred percent kamar farko".
Cikin tsananin jin da?i papa ya rungume Yoohan yana fa?in, "I am sorry my sweetheart, kai ?inne ba'a gane kanka sai kaso. Yanzu dai na maka al?awarin da kaina zan gyara abinda na ?ata a yau ?innan kaji".
?agowa Yoohan yay da sauri, yace, "Papa da gaske kakeyi?".
"?warai kuwa my dear son".
Wani lallausan murmushi Yoohan ya saki najin da?i. Dan ya fahimci lallai sai ya nunama papa akwai manufa a tafiyarsa da baba malam sannan zai samu nutsuwar samun damar fahimtar ilimin addinin islama da zai kare kansa anan gaba a wajensu dama duk wani dake a cikin ahalinsa da yasan zai kawo masa togaciya. Amma a yanzu yasan duk yun?urin da zaiyi sai sun ta?esa saboda rauninsa na kasancewa sabo cikin addini mai ?unbin haske irin musulinci. A yau kawai daya kasance a ciki jinsa yake tamkar sabon mutum. Tamkar darajarsa ta ?aru. Duk wani nauyin zuciya da ?unci da yakan tsinta kanshi a ciki a baya yau sai yaji tamkar ansa kwano an kwashesu tas.
Jikin papa ya sake lafewa tare da lumahe ido. Papa ma dake jin da?in Yoohan ya fara ?aukar hu?ubarsa ya shiga shafa kansa cike da jin da?i da annashuwa. Dan shima har zuciyarsa ta gama shirya masa babban aiki akan baba malam tsaf............?

Tofa masu karatu. Yanzu za'a fara wasan?? dan haka kumuje zuwa filin daga????????.



ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????

Mamu gee??
MIN ?ALB!!????

Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????

Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????

Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????

?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.

????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.*_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.


No. 32

............Tun isowarsu asibitin aka fara bama Nu'aymah dake a sume taimakon gaggawa. Sai dai harsu baba malam suka isa asibitin bata farfa?o ba. Hakan sai ya sake ?aga hankalinsu. musamman ma Hajjo dake ta faman shar?ar hawaye. Cike da kulawa baba malam ya zauna kusa da ita duk da kunyar ?an fari dake tsakaninsu. Murya a tausashe da nuna ?unbin kulawa da ladabi ya fara lallashinta da fa?a mata kalamai masu taushi da nutsuwa irin na masu ilimi. Ya nuna mata koda rasa Nu'aymah sukayi su zama masu ha?uri da godema ALLAH. Dan lokacin da ya basu ita baiyi shawara da suba. A yansu kuwa idan ya kar?eta ya fisu bukatarta ne.
Haka ya cigaba da mata nasiha harta samu nutsuwa tai shiru. Abba Musbahu yazo gabanta ya dur?usa tare da saka handkherchief ya share mata hawayen.
Ana haka Doctor ya fito daga ?akin da aka sanya Nu'aymahn. Ya bu?aci ganin ?aya daga cikinsu cikin nuna girmamawa a garesu. Abban Abdallah da Abban su Adawiya ne suka bisa office. Dan baba malam ya nuna kawaicin nasa da ya saba kamar ko yaushe. Amma zuciyarsa cike take da tsoro da rauni. Yana ta dai ?o?arin danneta ne da ambaton ALLAH wajen ?arfafa imaninsa.

A office ?in likita kuwa ya nutsu ne wajen rubuce-rubuce a wata takarda kafin ya maida hankalinsa gasu Abbah.
"ALLAH ya gafarta malam zan fara da muku albishir ?in farfa?owarta. Sai dai kuma kamar yanda kuka sani raunin dake a cikin ?wa?walwarta shine ya motsa mata. Kuma gaskiya a bincikenmu yarinyarnan tana matu?ar bu?atar son ganin babban likita. Idan ba hakaba a koda yaushe zata iya fuskantar gogewar komai na ?wa?walwar ta. saboda tana ?ara girma ciwon na da?a fa?i. Musamman ma daya kasance kamar tana sakama kanta abubuwa masu nauyi a cikin rai. A duk kuma lokacin data shiga ?unci ciwon na mata ku?a a cikin kanta, ba dan ma tana samun kulawa da kuma addu'oi ba da gaskiya bana zaton yarinyarnan zata kai wannan shekarun batare data tsinci kanta a ciwon hauka ba. Duk da komai na ALLAH ne, babu wani bawa daya isa canja ?addarar wani bawa daga yanda tazo a littafinsa. Amma a wannan karon ayi himmar sadata da likitan daya dace da matsalarta, munan taimako kawai muke bata na dakatar da ra?a?in a gareta a lokacin daya taso. Amma matsalarta sake hauhawa takeyi gaskiya".
Su Abba da duk jikinsu yay sanyi sukaima Doctor godiya sosai. Tare da tabbatar masa insha ALLAHU a wannan karon zasuyi abinda ya dace.
Yaji da?in hakan sosai. Ya sake ?an musu wasu bayanan da suka dace akan yanayin kula da Nu'aymahn kafin ALLAH yasa a dace da samun Doctor ?in daya fa?a. Dan ya basu note dazai taimaka musu samun ganin makusancin likitan da lokaci-lokaci yake shigowa cikin kano. Baya kuma duba marasa lafiya a ko ina sai a General hospital. Dan haka ya basu abinda zai taimaka musu ganawa da wata likita dake aiki a General hospital ?in, wadda yake da tabbatacin ta hanyarta zasu iya ganin Doctorn.
Godiya sukai masa sosai, sannan suka fito. Sai dai basu ma su baba malam bayanin komaiba, a ?o?arinsu nason yin wani ho??asa akan jinin yayan nasu da a kullum hidimarsa ke ?arewa a kan su da nasu iyalin. Suma wannan karon sunason nuna tasu bajintar akan ?aya daga cikin jininsa guda biyu da ALLAH ya bashi.

________¡ï¡ï

Ganin lokacin sallar la'adar ya gabato Yoohan ya bu?aci ka?aicewa dan ya huta. Hakanne ya saka papa fita ya barsa shima ya nufi ?akin da aka kama masa.
Yoohan ya ?an sauke ajiyar zuciya yana mi?ewa. Zuwa yay ya sakama ?ofar ?akin key. Kafin ya nufi bayi yayo alwala kamar yanda baba malam ya koya masa. Duk da zuciyarsa na kwa?ayin zuwa massallaci yay salla cikin jam'i kamar yanda suka gabatar ?azun a massallacin juma'a haka ya ha?ura ya daure yin tasa shi ka?ai a cikin ?akin kamar yanda aka koyar da shi.
Bayan ya idar da sallar a tsanake yay addu'a gwargwadon abinda ALLAH ya hore masa. Waya ya jawo yay kiran baba malam. Cikin sa'a kuwa bugu biyu aka ?aka. Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke wadda har baba malam ya jiyota.
"Banyi zaton zaka ?agaminba Uncle. Nazata zakayi fushi dani bisa kuskuren papa".
Baba malam da fitowarsa kenan daga massallacin cikin asibiti sun idar da salla kiran ya shigo masa yay sassanyan murmushi, ?aunar Yoohan ?in da ?yawawan ?abi'unsa na sake dulmiyasa a ?aunar yaron. Cikin kulawa yace, "Haba Yahya! Mizaisa nayi fushi da kai? Ai koshi bazanyi fushi da shiba dan ya fini gaskiya. Da farko ina fatan dai ka gabatar da sallar la'asar. Na biyu kuma ina fatan babu wata matsala tsakaninka da mahaifinka a dalilin ganinka da yay a wajena?".
Lumshe idanu Yoohan yay a hankali yana jingina bayansa da kujera, cikin so da ?aunar baba malam dake ratsashi shima yace, "Alhamdulillahi Uncle. Yanzun nan na idar da salla, sai dai banje massallaci ba, ina fatan hakan ba laifi baneba. Dan nayi hakanne saboda ahalina, banason su fahimci ni musulmi ne tun yanzu dan zasubi hanyoyi da dama wajen kaini ?asa. Amma idan na sami wadataccen ilimin addini musulinci duk ta inda suka ?ullo zan kare kaina".
Baba malam dake murmushi ya sauke ajiyar zuciya. "Tunaninka mai ?yau ne Yahya. Sai dai salla cikin jam'i tanada matu?ar muhimmanci, dan haka kar kayi sakaci da samun ladan dake cikin jam'i kaji".
"Zan kiyaye Uncle".
"Alhamdulillahi haka ake so. Mahaifinka fa?".
"Karka damu da shi Uncle. haka yake da zafi, amma da an fahimtar da shi yanada saurin fahimta. Munyi magana da shi ya kuma fahimceni, kafin ma ya wuce zai shigo wajenka yacemin".
Hakan ya bama baba malam mamaki matu?a. Amma sai bai nunama Yoohan ba ya amsa masa kawai. Sannan sukai sallama.

Lokacin da Yoohan ke waya da baba malam a can papa ma yana ?akinsa suna waya da Uncles ?in Yoohan ?in su Uncle Godwin. Ba akan komai suke wayarba sai akan baba malam. Kamar yanda papa ya girgiza da ganin Yoohan da farko haka suma suka girgiza dajin Yoohan a wajen baba malam. amma daga baya sai bayanin da Yoohan yayma papa ?in ya?an sanyaya musu rai.
Uncle Mike yay wata dariyar mugunta yana fa?in, "Wannan ?an nakafa shegen kansane, inaga akwai aikin da yakema turawan nan ta ?ar?ashin ?asa shiyyasa kullum bai damuwa da lamarin kowa sai wannan aikin nasa. A da ba ?aramin haushi yake baniba akan hakan, amma jin wannan maganar ta yau sai naji ?aunarsa da son ha?a tafiya da shi. Sai dai matsalar ?aya ce yaron yanada taurin kai, nasan bazai ta?a yarda musan cikinsa gaba ?aya ba. Amma ni a ganina mizai hana muma muyi namu aikin akan wannan hausa man ?in, dan fa multi millions ne. Kawai dai baya nunawa ne".
Papa ya kwashe da wata dariya, kafin yace, "Mike! tunaninmu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login