Showing 147001 words to 150000 words out of 325075 words

Chapter 50 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29155

koyi da baba malam. Cikin harshen turanci yace, "Uncle tanama da ranta, sai dai dama bawai mun mata aikin ainahin matsalarta bane kamar yanda nai maka bayani ?azun kafin mu ta?ata. Aikin da mukai mata zai bata taimakone kawai wajen hana ?wa?walwarta goge komai da take barazanar yi, sannan zai sassauta mata ra?a?in da takeji a duk lokacin da matsalar ta motsa, insha ALLAHU zai hana ta iya rasa hankalinta. Nayi tunanin aikin zai bata kariyar da zamu iya ?aukar kamar watanni biyar kafin ai mata aikin gaba ?aya, dan dole sai an fita da ita waje, a ?asarnan bamu da isassun kayan aikin matsalarta, koma muna dasu zaka samu bana zamani bane tunda shuwagabannin namu bawai hankalinsu nakan abinda ya dace suyi bane. To a yanzu dai matsalar dana fahimta dolene ai gaggawar yimata aikin koda nan da wata ?aya ne insha ALLAH, inba hakaba zata iya loosing memory ?inta a koda yaushe".
?an rumtse idanu baba malam yay yana ambaton sunayen ALLAH, muryarsa da ?o?arin jarumta yace, "Shikenan Yahya, duk yanda kake ganin ya kamata akai kayi tunda aikinka ne, yanzu zamu iya zuwa mu ganta?".
?an jimm Yoohan yayi, kafin yace, "Eh to amma karkuzo da yawa dai". "Babu damuwa". Baba malam ya fa?a yana sauke ajiyar zuciya.

Batare da kowa ya saniba a gidan Umm da baba malam da Hajjo suka tafi asibiti duba Nu'aymah. Yoohan da yake wani irin jin kunyarsu da nauyinsu ne yay musu rakkiya har ?akin da Nu'aymah ke kwance. Ba ?aramin tashi hankalinsu yayiba ganin yanda aka jajjone kan Aymah da na'urori, Hajjo da Umm harda hawayensu. Basu wani jimaba suka fito. Office ?in Yoohan suka sake komawa. Inda ya sake musu bayanin komai dalla-dalla a nutse. Sosai suka gamsu da bayaninsa, wanda a take duk murmushi ya baibaiye fuskokinsu, suka shiga saka masa albarka da jera masa addu'oin fatan alkairi. Har wajen mota ya rakosu, sai da yaga tafiyarsu sannan ya koma ciki, dan yau a asibitin zai sake kwana saboda Nu'aymah zata iya farkowa a kowane irin lokaci.
Zamansa babu jimawa Solomon ya shigo ?akin ?auke da takeaway da yayo masa acan hotel ?in da suke sauka. Dan idan yazo kano abincin can kawai yake ci, sai ko yanzu da suka ha?u da su baba malam. Ganin yana waya ya saka Solomon komawa gefe ya tsaya yana sauraren yanda Yoohan ?in ke wayar a nutse.
Magana suke da wani likita abokinsa dake a ?asar Canada. Yana bu?atar a aiko masa da wasu allurai ne masu matu?ar tsada da zaima Nu'aymah amfani da su. Kuma yana bu?atar sune da gaggawa daga nan zuwa yammacin gobe idan ALLAH ya kaimu. Shine suke maganar ta yanda za'a kaisu airport ?in ?asar a dam?awa wani abokinsa matu?in jirgi da Yoohan ?in yasan kayan zasu iso yanda yake fata. Sai da suka kammala maganarsu har Yoohan ?in yayma Dr Androi transfer ?in ku?a?en allurar take anan masu yawa daga asusunsa sannan ya ajiye wayar.
Solomon dake kallonsa cike da takaici da mamakin ganin ku?in daya biya na alluran tamkar baisan ciwonsu ba yay saurin fa?in, "Good evening sir! Ga abinci na amso maka, naga bakaci komaiba tun breakfast ?in safe".
?an luuuu da idanu Yoohan dake mi?ewa yayi, kamar zai lumshesu sai kuma ya bu?e su akan Solomon ?in. "Karka damu banajin yunwa. Ha?amin coffee kawai is ok for me".
Ganin yanda ya tsuke fuska sosai ya saka Solo amsa masa da "To" kawai. Cikin bin umarni yayi masa yanda ya bu?ata, acan rukunin kujerun office ?in daya koma yana aiki a lap-top yaje ya kai masa coffee ?in. A hankali yace, "Thanks". Shiru office ?in yayi na wasu mintuna, Yoohan nata aikinsa da shan coffee kamar ya manta da Solomon. Sai kuma ya ajiye kofin ya ?ago yana kallon solo ?in. "Kaje ka kwanta, basai kazo nan da safe ba, inaga zuwa dare zamu wuce Abuja, sai ka mana booking ?in jirgi".
Cike da girmamawa yace, "Okay sir". Daga haka yay masa sallama ya fice.

Solomon na isa hotel ?in wayar Papa ya fara kira. Ba a ?auki lokaciba kuwa ya ?aga. Bayani ya shiga yimasa da yarensu wanda sam ban fahimci akan minene ba. Sunja lokaci mai tsaho suna wayar sannan ya kira madam Chioma itama. Itama ?in dai magana sukai ta tsahon lokaci da wani yaren ba irin wanda sukai da papa ba. Batun yau ba na fahimci Solomon najin yare ba ?aya ba. Kamar yanda na kula shima Yoohan ba yare ?aya kawai yake jiba bayan turanci. Shiyyasa a lokuta da dama nakan gaza banbance shin su wane yarene wai?.

*_WASHE GARI_*

Washe gari da safe ?an gidan su Nu'aymah sukaje asibitin suka duba Nu'aymah data sake farfa?owa. Sai dai har suka gama abinda zasuyi suka taho basuga Yoohan ba. Yana office yana duba marasa lafiyar da suke da tsananin bu?atarsa duk da da da farko baiyi niyyar hakanba.
Suna dawowa gida kuma suka iske ba?in da basu san da zuwansu ba. Kakar Nasir data haifi babansa ce tazo daga katsina mai suna Hajiya Hassana. Sai dai suna kiranta Ananah, yayar Hajjo ce uwa ?aya uba ?aya, wadda ita ka?ai ce ta rage mata a duniya. Hajjo na tsananin girmamata dan itama tana ?aunar hajjon, batason abinda zai ta?a hajjo da zuri'arta, ta zame mata tamkar uwa da uba. Itama ta tsufa sosai fiye ma da Hajjo, sai dai da yake ALLAH ya basu lafiya sosai ga jin da?in rayuwa, ko ina suna zuwa, garama hajjo tana fama da ciwon ?afa. Ananah kuma idanuntane dan sai da galashi take gani da ?yau.
Tare take da jikokinta da yaranta biyu ?annen mahaifin Nasir ?in mata. Dama duk babbar salla anan take salla kano, ita kuma hajjo sai gab da azumi take zuwa mata can katsina tai kamar wata guda. Hakan na sakasu farin ciki sosai.

'To yanzu kuma Nasir ya ?a??ago Ananah akan batun Nu'aymah. Ko yaya zata kasance?. saimu bisu muga wane mai rabo ne zai ?auki wannan allurar ta cikin ruwa???'.

Ba ?aramin farin ciki hajjo dama duk jama'ar gidansu Nu'aymah sukaiba da zuwan Ananah. Dan yanda take son kowa a gidan haka kowa ke sonta da ?aunarta har surukan Hajjo. Take gidan ya rikice da murna dan duk tunaninsu ta iso da wurine saboda bikin su Kubrah nan da kwanaki goma. Ciwon Nu'aymah ne ma ya?an sanyaya shirye-shiryen da akeyi.
Cikin ?an?anin lokaci aka shirya abinci gabansu kala-kala daga kowanne sashe. Da mamaki Ananah tace, "Wai ni banga ?awalliyata ba ita?". Kowa yasan Nu'aymah take nufi. dan suna shiri sosai-sosai da Ananah, saboda Nu'aymah nada sunan hajjo ma take cemata ?awalliya.
Rufaidah ce tai caraf ?in cewa "Ananah tana asibiti babu lafiya" a rikice Ananah take tambayar, "Asibiti kuma? Miya sameta ni Hassana ?iyar malam Haruna". Shiru kowa yayi ya gaza bada amsa. Sai hajjo ce tai ?an murmushi da cewar, "Ciwonta ne ya motsa, amma Alhmdllh da sauki ma".
Cikin jimami Ananah ta share ?ar ?wallar data taru mata a ido, tace, "Kai duk wanda yay sanadin shigar wannan yarinya a bala'innan yayi asarar rayuwarsa wlhy, ALLAH ya saka mata, ko wanene kuma ALLAH ya hanashi farin cikin duniya dana lahira".
Kusan a tare duk falon suka amsa da amin.

¡ï¡ï

Bayan sallar magriba Ananah sukaje asibiti suma suka duba Nu'aymah, a lokacin Yoohan yaje airport amso sa?on da aka aiko masa daga ?asar canada. Hakan yasa har suka kammala suka wuce yanzunma basu ha?u da shi ba. Sai bayan wucewarsu da kamar awa guda ma ya dawo.
Kansa tsaye ?akin da Nu'aymah take ya nufa. Solomon biye da shi ?auke da wata madaidaiciyar bag. A ciki ya samu Nurse ?in data gama gogema Nu'aymah dake barci jiki.
Da girmamawa ta gaida shi, Solomon kuma ya ajiye bag ?in ya fice. Matsawa yay gaban gadon lumsassun idanunsa akan Nu'aymah da fuskarta tai wani irin fayau. Sai uban haske data ?ara tamkar mai yaron ciki. Ya kafe La??anta da sukayi wani irin jajur gwanin sha'awa, gashi ta?an tsuke bakin ya sake komawa mitsitsi.
Huci ya ?an furzar ya janye idanunsa daga kallonta, yana fa?in 'Bakin tsiwa' a zuciyarsa. ya gyara kujerar gefen gadon ya zauna tare da ?aukar bag ?in da Solo ya ajiye ya bu?eta. Madaidaicin abu ya fiddo cikin kwali mai kama da kula, ya bu?esa sai ga ?an?ara a sama tanata huci. a ?asan ?an?arar ya zaro kwalaben alluran kusan guda guda bakwai ?an ?ananu, yanda kwalaben suke ?an mitsitsi sai ka ?auka wani tarkacen banza ne. Nanko ku?a?ene masu shegen nauyi zaune da ?afafunsu. Sai da ya gama duba takardar dake a cikinsu kafin ya maidasu ciki ya fiddo ?aya kawai.
Mi?ama Nurse ?in dake a ?akin yayi, murya a da?ile yace "Kiyi mata allurar nan yanzun nan". Amsa tayi da girmamawa. A gabansa ta bu?e syringe ta kwashe ?an ruwan allurar da ko ganinsa bama ayi sosai cikin syringe ?in. Shine ya nuna mata a inda zatayi. (A raina nace da idon Aymah biyu sai anyi ?aramin ya?in duniya na uku kafin ayi allurar na kuwa??).
Mintuna uku ba'a rufa dayin allurarba wani irin mahaukacin zufa ya fara tsatstsafowa a kowacce ?ofar gashi ta jikin Nu'aymah. Kafeta da kallo Yoohan dake zaune ?afa kan ?aya ya har?e hannayensa a ?irji yayi. Yanda take wani irin mutsu-mutsu kamar macijiya mai tsohon ciki ne ya sakashi sakin wani tattausan murmushi daya ?awata cikar haibarsa da kwarjinin bautar UBANGIJI. Ya ?an lumshe idanunsa ya sake bu?ewa a kanta yana jan ajiyar zuciya.............?

'Saura naji wani yace ?an ka?an ne????. Da gobe saina ?ara rage mudu????????'.


______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________


Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????

Mamu gee??
MIN ?ALB!!????

Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????

Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????

Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????

?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p.


*_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.


No. 41

.............Tunda su papa suka koma Abuja Suka kasa zaune suka kasa tsaye shida ?annensa da aminansa. Sunyi zaman mitin kuwa yafi sau goma.
A kuma kowanne zama babu abinda suke tisawa da tirzawa sai kalaman baba malam masu cin zuciya da farin ciki.
A yanzun ma dai suna zaune ne su duka bakwai da suka kasance aminan juna kuma shaki?ai. Papa daketa kai kawo hannunsa goye a baya ya girgiza kansa idanunsa tamkar zasuyi aman wuta saboda jaa. "Bazai yuwuba. Dolene sai mun cimma burinmu akan Hausa man ?in nan. Dan abinda ya shu?e tsakanina da shi shekaru kusan ashirin da takwas yana a ransa daram babu abinda ya manta. Idan kuwa har ya tabbata bai manta ?inba tofa ku sani, ni da ku duk muna cikin........"
Da sauri Uncle Mike ya ?aga ma papa hannu. Muryarsa cike da barazana yace, "Karma kace komai Pastor. Ba'a haifi mahalukin daya isa hanamu cimma burinmu ba bayan wahalar da mukai ta tsahon shekaru. Duk da ku?in da kuke tunanin hausa man ?in nan nada shi wannan ba komai bane. Ni inada hanyar da zamuyi amfani wajen cinsa da ya?i batare da shi kansa yasani ba. Zamu ruguzashi shi da duk zuri'arsa ta hanyar SARAN ?OYE. Ni dai fatana shine ku bani ha?in kai kawai na nuna muku hanya mafi sau?in ?ullewa".
A take duk suka dubesa zukatansu na samun nutsuwa ka?an. Ba komai yasa hakanba sai sanin da sukaima Mike wajan iya ?ulla talalar rufta duk wanda suka sakama kahon zu?a a rayuwarsu. Dan haka babu wani kace na ce duk suka shiga sauke ajiyar zukata.
Hannunsa ya ?aura saman tebirin gabansu yana dubansu. Papa ne ya fara aza nashi akan na Mike ?in. Sai Godwin. Sauranma duk sai suka shiga ?orawa ?aya bayan ?aya alamar tabbatar da mubayi'arsu akan idea ?in da Mike zai kawo musu wadda suke fatan ta zama hanyar da zasu ?ulle akan baba malam.

Wannan zama shine ya samawa papa ?ar nutsuwa, duk da a kallo ?aya zaka fahimci yana tare da fushi har zuwa yanzun. Wayarsa ya ?auka yay kiran Yoohan da a yau ya wuce birnin Lagos. Bai ?aga ba harta tsinke. Hakan ya sashi tunanin ko baya kusa. Dan haka bai sake kiraba ya ajiye wayar gefe ya cigaba da kora giyarsa.
Kusan mintuna goma sai ga kiran Yoohan ?in ya shigo masa. ?auka yay fuskarsa cike da fara'a, dan har cikin ransa yana ?aunar ?an nasa. A duk irin fushin da yake ciki inhar ya kasance da Yoohan sai yaji ya samu nutsuwa ta musamman.
Yanda Yoohan ?in ke gaishesa cike da shagwa?a ne ya sakashi sakin murmushi. Cikin muryar ?an mayen daya fara tasiri a kansa yace, "My sweet John yaya dai?!".
Cike da ?ar shagwa?a Yoohan dake zaune a office tare da Richard yace, "Papa na gaji ne, barci nakeji. Kaga tunda nazo Rich bai barni na hutaba sai laftamin aiki yakeyi kamar wani jakki".
?ar dariya papa yayi yana kur?ar giyarsa. "Oh my Darling kaifa gwarzon namiji ne. karka karaya da sauri haka mana a gaban Richard".
"Papa kai masa magana to ya tayani".
"Hhhh to babu damuwa zan masa. Kasan miyasa na kiraka?".
A nutse Yoohan daya gyara zama yace, "A'a papa, sai ka fa?a".
"Humm" papa ya fa?a yana mi?ewa. Ya kur?a giyarsa saboda ?acin ran baba malam na sake dawo masa sabo a zuciya. muryarsa cike da kaushi yace, "Jiya mukaje kano wajen wancan hausa man ?in".
Sosai gaban Yoohan ya fa?i. Ya ?an ture files ?in gabansa yana fa?in, "Kana nufin Sheikh Sooraj jibiya".
"Yes! My son".
Mi?ewa Yoohan yayi da sauri. Ya tura kujerarsa ta zama baya ya bar gaban tebirin Richard na binsa da kallo. A wani irin yanayi yace, "Papa mi kukaje yi wajensa?".
Batare da papa ya ?oyema Yoohan ?in komaiba ya sanar masa cewar sunje nema masa auren Nu'aymah ne. shine dan wula?anci baba malam yake sanar musu wai shi yarinyarsa bata isa aure ba. Idanma ta isa bai shirya aurar da ita ba........"
"Oh my GOD papaa! Miyasa baku sanar dani ba kafin kuje?. Nifa koda nace muku zan aura ?arsa bawai ina nufin yanzu ba. Da gaske yarinyarfa ?aramace. Shekararta sha bakwai ne kacal fa......."
"My son! kai kake ganinta a ?aramar, sufa sunama yaransu aure suna shekara goma ko sha biyu. Kawai dai ya shirya wula?anta mune saboda......." sai kuma yay shiru bai ?arisa ba
Yoohan da ransa ke a dagule yace, "Saboda mi papa? Ko dai ba neman auren ne ya kaiku ba dama?!. Papa kuna son ku ?atamin aiki nane kawai kudai. Idan ba hakaba tayaya zaku tafi nema min aure batare da shawarata ba. Inada tabbacin kuma su Uncle Godwin ka kwasa kukaje sukaita masa gadaran da sukema mutane. Shifa wannan ya wuce duk yanda kuke zato, yanada iliminsa yasan mi yake yi. Sannan baya ?aukar wula?anci ga kowa shiyyasa nakeyi komai cikin taku da taka tsantsan a kansa. Idan ku?i kuke ta?ama da shi shima ya tara su. Idan mabiya ne shima yana dasu bama a Najeriya kawai ba. Kaga kuwa tunkararsa sai an shirya".
Jikin papa ne yay sanyi. Dan haka murya a sanyaye yace, "Tabbas na sake tafka kuskure na biyu Yoohan. Gaba ?aya farin cikinka ne ya rufe min idanu na kasa fahimtar zuwa dasu zai iya haifar da matsala. Yanzu dai kayi ha?uri mu nemo mafita zan sake gyarawa da kaina. Kuma zan kiyaye".
Duk da ran Yoohan a jagule yake har yanzun sai ya sauke ajiyar zuciya yana gyara tsaiwarsa. "Karka damu zamuyi magana. Yanzu ina kan aiki ne. Amma papa Please ka daina biyema su Uncle Mike suna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login