Showing 291001 words to 294000 words out of 325075 words
falon. Ta goge mabinta saboda tsagaitawar tarin sannan ta kalli kowa dake falon tana Murmushi mai ciwo a karon farko. Ta kalli ?afarta dake na?e da bandage hawaye na ziraro mata. Dan har yanzu tanajin ra?a?in azabar shigar bullet a karon farko na rayuwarta. Kallon baba malam tayi ta sake sakin murmushi sannan ta maida akan Umm dake a gabanta zaune.
"Ko babu ?arfin iko hukuma dama lokaci yayi da Firdausi! Zata san wacece Fauza a gareta. Dan tun bayan auren Nu'aymah wannan ranar dama nakewa zaman jiran tazo a gareni, dan nasan tana cikin ranakun da ko naso koban soba sai sun riskeni a duniya ko a lahira, musamman daya kasance gajerun kwanaki suka ragemin a duniya. Wannan Fauzar dake gabanku ba Fauza bace ta shekarun baya mai lafiya, hatsabibiya, mai aiki da zuciya kawai bada tunaniba, mai son kanta, mai aiki da hu?ubar shai?an. Wannan Fauzar ma?as?anciyace a gabanku yanzu, mai rauni, mai ?auke da ciwon zuciya da ciwon kansar jini (blood cancer), wadda likita ya tabbatarma watanni ka?anne suka rage mata a duniya. Wannan Fauzar mai dana sani ce da nadama da yin kaico akan ayyukan data tafka batare daku kun saniba saboda iya SARAN ?OYE".
Tarine ya kuma sar?eta da kuka. Nanma tanayi jini na fita, saida ta tsagaita sannan ta sake dubansu. "Da wahala shara'ar al?alin duniya ta iya dacewa da laifukan Fauza, shara'ar UBANGIJI datafi cancanta dani ta fara bayyana a gareni tun daga randa likitanci suka sanarmin sakamakon abinda nakeji a jikina. Amma lallai halina dolene yaje kunnunwan mai saurare ko zai zama izina ga masu irin halin suji tsoron ALLAH su canja kafin lokaci ya ?ure musu".
"Firdausi! Da gaske ni Addah na soki so na gaskiya a zamanin ?uruciyarmu. Duk da ko a wancan lokacin duk randa kika samu abinda ni nafi cancanta da samunsa inajin zafinki a raina. Musamman idan nai la'akari dana fiki komai a rayuwa. Ni ?ar gatace ko a gidanmu, duk wani jin da?i da yaro kan tashi ya samu daga iyaye na samesa. Mahaifina yafi naki komai a rayuwa. Hakama mahaifiyata tafi taki. Hasalima da yawan lokuta ?an gidanku kunaci ne daga alfarmar iyayena. Sai dai kash duk da wannan gatan namu da tarin alfarma kin fini basirar karatu, bama ke ka?aiba duk ?an gidanku ALLAH ya basu wannan baiwar, gashi duk kun fimu ?yau, sannan da wahala ku zauna da mutane basu soku ba. Dan yayyenki ma sunsha ciwo nasarorin dake sa yayuna jin zafinsu, sai dai mahaifiyarmu kan ?wa?emu akan hakan. Nasararki a kaina bata ta?a kaini ga ?ololuwar jin zafinkiba sai a randa Sheikh Soorajidden yazo har gidanmu akan neman aurenki".
Ta share hawaye masu zafi dake gangaro mata har yanzu sannan ta cigaba da fa?in,
"Hakan ta faru dalilin soyayyarsa da taimin shigar sauri cikin zuciya tun a ranar kammala karatunmu. Idan baki mantaba tun a wajen bakina bai hutaba da zance a kansa har kika nuna ?osawarki akan hakan. Mun dawo gida zuciyata na ?unbin begensa, sai dai a randa na bu?i ido na gansa a gidanmu sai labari ya canja salo. Ke! ke! ke!! Firdausi! kin sake yanke igiyar nasarata kamar yanda kika saba a koda yaushe".
Tai maganar da matsanancin kukan da har ya hanata kasa cigaba da magana sai da tai tari mai tsaho. Falon kansa yayi tsit ko motsi kowa ya kasa saboda shock. Da ?yar ta tsagaita kukanta da tarin sannan ta cigaba.
"Naji zafinki a wannan ranar zafin da idan aka bani makami zan iya halakaki. Nayi kuka harna rasa hawayen zubarwa. Amma daga ?arshe sai nayi ha?uri bisa ga shawara da nasihar da babbar yayarmu ta min, a lokacin sai naji na ha?ura na barmiki, duk da dai son nasa na nan ma?ale a raina. A haka aka kammala komai na maganar aurenku ni bani da wani tsayayyen saryima. Har lokacin biki yayi mukasha bikinku. ALLAH ya sani ban ta?a cin karo da rana mai ciwo da ra?a?i ba irin ranar aurenku. Dan aranar na gama yanke hukuncin dolene na shigo gidanki matsayin kishiyarki. Amma sai kash. ?addara ta riga fata, dan kuwa ha?uwata da Mustapha sai ta kasance almakashin daya datse wannan zaren a karo na biyu. Ya nuna yana sona, amma ban amsa masaba a ranar, shi kuma ya zata kunyace ta sani ?in amsawar, dan haka yay amfani da wannan damar yayma rayuwata kutse ta bayan gidan adalilin neman aurena da Sooraj yaje yayima ?aninsa a gidanmu tamkar yanda yayima kainsa. Babana kuma babu wani tsayawa ja'in-ja ya bashi. Na sake shiga ru?ani a karo na biyu, amma sai yayata dai ta sake ?orani akan mizanin hankali da nasiha kamar wancan karon. Ta kuma tabbatarmin Mustapha shine mijina dama ba Sooraj ba, tanada ya?inin kuma shine zai zama mafi alkairi a gareni insha ALLAHU. A wannan karonma taci nasara. Dan duk da babu son Mustapha a raina na aminta zan auresa kodan darajar jini da suka ha?a da Sooraj, sannan a fuska ma suna kammani da juna".
Ta share hawayenta tana murmushi da kallon Umm.
"Firdausi! Shigowata gidan nan shine ya sake canzama zuciyata salo a kanki. Dan tun a yanayin taron aurena da Mustapha na fahimci a wannan ga?arma kin sake min tsere. Ban sake tabbatarwa ba sai da na tabbata ?aya daga cin wannan ahalin. Zamantakewar ki da Sooraj tana ?aya daga abinda ya dagula min tunani. A zahiri mutane ?auka suke tsoron Sooraj kikeyi, amma wanda zai ganku a sashenku ka?aine zai goge wannan tunanin a ransa saboda soyayya da tattalin da kike samu daga garesa. Sannan kasancewarsa babban ?a a gidannan duk wata daraja ta matar gida kin kwashe a sama da tamu. Wannan yasa ita kanta Momyn Abdallah kejin zafinki ganin anan kikazo kika sameta. Abinda ya ?an sakamin sassauci a kanki lokacin haihuwa dana rigaki yi kuma namiji, har takai sai da na jera hu?u sannan kika samu ciki. Maganar gaskiya bazan ?oye mikiba naji matu?ar jin kishi akan samun cikinki duk da kuwa inada ?a?a har hu?u a lokacin. Dan idan ina ?aunar mutuwata to ina ?aunar bu?ar ido naganki da wani cigaba daya ?ara nawa a rayuwa, dan na tsani cikin nan naki tun yana ?an tayinsa. Duk da ban ta?a tunanin cutar dake ba adalilin cikin nan zuciyata ta fara rayamin hakan, dan kullum hu?uba takemin na ?arar da cikin kawai kowa ya huta. Sai dai ina shirin aikata hakan a gareki Sooraj ya ?aukeki kuka wuce saudia, nayi ba?in ciki nayi takaici irin wanda bazai misaltuba. Gashi baku dawoba sai gab da zaki haihu. Koda kuka dawo ban fasa aiwatar da ?udirina akan cikinki ba, sai dai babu wata makamar yin hakan dana samu har ALLAH ya saukeki lafiya a wani dare. Hankalina ya tashi ganin kema da namiji kika fara, zuciyata ta sake bushewa da kangarewa akan na kashesa kawai tun yana jaririn........."
Cikin ?acin murya Baba malam ya katse Addah da cewar, "Fauza kenan kece kika kashe mana yaro?".
Kuka Addah ta sake fashewa da shi kanta a ?asa ta kasa kallonsu. Ga tari ya kuma sar?eta har jini na fita guda-guda yanzun.
Ko batace komaiba sun fahimci shirunta na nufin haka ?inne. A take gaba ?aya falon suka ?auki salati. Umm kam ido kawai ta tsurama Addah hawayenma sun tsaya cak. Hakama baba malam kallon ?asa kawai yake ya gaza koda motsi. Abba Mustapha zai mi?e Hajjo ta hanashi, dan har yanzu ai ba'azo inda take bu?atar ba.
Jay ne ya katse shirun nata da fa?in, "Ke muke saurare". Yay maganar yana kallon agogon hannunsa.
Da ?yar Addah ta tsagaita kukanta ta cigaba da fa?in, "Na sha?a masa maganine, irin wanda naso sha?ama Nu'aymah aka samu akasi Rabi mai aikinki ta kusa rutsani, dan a lokacin kin tafi wanka Nu'aymah kin barta ta dinga le?ata a ?aki, ni kuma saina aiketa domin aiwatar da ?udirina, sai akai rashin sa'a kafin na sha?ama yarinyar maganin Rabi ta shigo, motsin nufowarta bedroom. Wannan shine dalilin tsoratata na saketa a ?asa kanta ya bugu. A take ta suma, ni kuma nai saurin ?oyewa dan kar rabi ta ganni gakuma kema naji yanda kika rikice a toilet kina ?o?arin fitowa. Sai da ta fita da gudu tana ihun kiranki saboda rikicewar da tayi ni kuma na samu na fita a sashen, daga baya na shigo cikin matan gidan muka shiga jajen yaya akai a tare. Kowa yama zata Nu'aymah ta rasu, sai dai hajjo ta matsa a kira likita. Zuwansane ya tabbatar mana da suma tayi, ba haka nasoba, amma lokacin da aka dawo da ita daga asibiti da tabbacin sanadin fa?uwar tata ta samu ciwo a ?wa?walwa sai naji da?i a raina saboda bushewar zuciya da hu?ubar she?an".
"Likita ya fara ?usa zargin yaddota akai daga gado, kema kuma Firdausi kin tabbatarma kowa kina toilet kinji motsin shigowar mutum bedroom ?inki, sai dai kin zata Rabi ce, sannan kuma kinji sanda yarinyar ta fa?i ?asa ta bugu. hakan yasa aka tuhumi Rabi, amma kuma saita rantse da iya gaskiyarta ba ita bace dan nama aiketane ta dawo,, tana shigowa taji ?arar Nu'aymah datai sau ?aya kafin ta suma. Maigadi ne ya sake wanke Rabi a wajen kowa. Haka kawai na tsargi kaina akan karfa asirina ya tonu, dalilin da yasani saurin ?aukar mataki kenan na saka malamin da ya bani abinda zan sha?ama yarinyar rufemin bakin kowa a gidan nan akama bar wani hasashe-hasashen son sanin yaya akai Nu'aymah ta fa?o a gadon?. Ban sake yun?urin cutar da yarinyarba, dan a ganina ciwon data kamu da shi ya isa kai rayuwarta ?arshe. Sai dai na saka an da?e bakin mahaifarki yanda bazaki sake haihuwa ba. ALLAH kuwa ya amincemin baki sake samun ciki ba sai bayan haihuwar Nu'aymah da kusan shekaru biyar, hankalina ya sake tashi na nufi malamina. Saina iske ALLAH ya masa rasuwa. Lallai nayi gamo da tashin hankali na ha?i?a a wannan lokacin, dan zan iya cemuku daga wannan lokacin ban sake samun malamin da yaymin aikin da yaci a kanku ba......."
"Mtsoww!! Malami ko boka dai". Abban Abdallah ya fa?a a fusasce.
Wani irin kallo Addah tai masa, sai kuma ta kwashe da dariya ta ?auke kanta kawai. Hakan da tayi kuwa yaba kowa mamaki. Amma sai babu wanda yayi magana. Har shima Abban Abdallah ?in bai sake cewa komaiba.
Addah ta cigaba da fa?in, "Tunda na fahimci aikin malami ya daina tasiri sai na koma la?e da son zubar da cikinki, to ALLAH ya tabbatar Muhammad sai ya sha?i iskar duniya sai gashi kin haihu lafiya duk da ba haka nasoba. ta wannan hanyar la?e ne nakejin duk wani abinda ya shafeku, dan duk da amintarmu firdausi ke mutumce mai zurfin ciki. Nakan fa?a miki sirrikana kai tsaye ko kema zaki warwaremin naki babu shamaki. Amma sai da na fara muku la?e na fahimci kina bala'i-bala'in rainan hankali. Dan babu wani sirrinki mai muhimmanci da kike sanarmin sai ?ananu kawai. Hakan yasa nima na ?auki ?ammarar bi dake ta yanda kikazo min".
Ta kai dubanta ga Abban Abdallah. Wanda a take mood ?insa ya canja ya wani zazzaro mata idanu kamar zai ha?iyeta da su. Murmushi tayi da ?auke kanta ta cigaba da fa?in, "A dalilin son halaka Muhammad na ha?u da babban makirin daya ?ara fa?a?a ?wa?walwata akan ?iyayyarki da zuri'arki. Dan ta sanadinsa ne wasan ya canja salo daga soyayyar Sooraj zuwa wani abun daban. Ba kowa nake nufiba sai Lurwan ga shinan". Tai maganar tana nuna Abban Abdallah da tun fara maganar tata ya zabura zai mi?e a fusace amma Hajjo ta ri?oshi cikin fushi.
Babu wanda bai zaro ido ba a jama'ar falon. Abban Abdallah ya sake zabura yana ?o?arin ?wace hanunsa daga hajjo. "K ba?ar annamimiya, makira, azzaluma. dan ubanki sharrin naki da makirci yazo kainane kenan komai?".
Dariya sosai Addah tayi tana kallonsa, tace, "Lurwanu ai ka fini iya makirci, dan kaine malamina a wannan fanin kuwa. Da farko ta hanyar malami kawai nake samun nasara akan Firdausi, amma ha?uwata da kai ya sani hutawa daga zuwa wajen kowanne irin malami, dan kai kafi malamin hatsabibanci ma. Yau ranace mai kama da ranar hissabi, yanda nasan cewar ayyukanmu bazasu ?oyu ba a wannan rana dake jiranmu to ina tabbatar maka yau ?in nanma tun a duniya zan fara fallasasu dan kowa ya yaji. Dan wlhy yanda duniya tasan waceceni a yau, ?a?ana sukaji shukar danayi, mijina yaji, dolene kaima uwarka da yayanka da matarka da ?a?anka da sauran ?an uwanka susan kai wanene a cikinsu".
Sake zabura yay kanta kuwa da ?arfin tuwo ya fisge hannunsa a cikin na hajjo, amma sai Dawood yay azamar shan gabansa da bindiga. "Ka kama girmanka, inba hakaba zan maka irin tabon dake a ?afarta kaima. Ka nutsu ka ri?e sauran mutuncinka".
Jikin Abban Abdallah rawa yakeyi sosai, dan bai ta?a kawowa a ransa tone-tonen Addah zai iso kansaba musamman da yasan irin garga?in da yay mata kafin ya yarda su fara aiki tare, da kuma kalaman datai amfani dasu a yau wajen shimfi?a labarinta. Yayi zaton zata rufa asirinsa ne.
A hankali baba malam ya yun?ura ya mi?e hawaye na sakko masa akan fuska. Yasa babbar rigarsa ya share sannan ya dubi jama'ar falon. "Inaga dan ALLAH mubar maganarnan gaba ?aya, wannan tone-tonen a ganina sam bashi da amfani. Sun aikata abinsu a ?oye sai mu barsu kawai da nauyinsu suje can su ?arta. Bana bu?atar jin abinda Rudwan ya aikata ku barni haka, n......."
"Dolene kuwa kaji ?an malam, dan haka koma ka zauna". Hajjo tai maganar cike da bada umarni. Baya iya ?etare maganar mahaifiyarsa. dan haka ya koma jagwab ya zauna yana mai dafe kansa da hannaye biyu saboda jirin dake kwasarsa.
Addah tai murmushi mai ciwo da cigaba da fa?in, "Lurwanu shiya canja tunanina daga fushin rasa masoyi zuwa na mallakar dukiya, dan hu?ubarsace ta fahimtar dani cewa ina dukan taiki ne kawai ina barin jaki, haukana kawai nake akan nafi Firdausi ?a?a nafita nasara yanzun. sai dai ashe dukiyar da mijinta ya mallaka a cikin ?an uwansa ta ninka wadda nawa mijin ke da shi sau fiye da bakwai. Kaso biyu na dukiyar gidan nan mallakarsace, kaso ?aya ne na mazajenmu da Hajjo. Gaba ?aya komai ya susuce min a lokacin nama nema rasa makamar tunani da hankalina. Amma sai ya dinga kwantarmin da hankali ta hanyar nunamin inhar zan taimakesa muyi aiki tare to lallai dukiyar baba malam zata koma ?ar?ashin ikonmu ne. Nace masa ta yaya kenan?. Ya bani tabbacin ta hanyar Abdallah. Tunda akwai sha?uwa sosai tsakanin Nu'aymah da Abdallah hakan na nufin nangaba ka?an soyayya zata iya bayyana a tsakani duk da ?uruciyarsu. Dan bazaiyi wasaba wajen ?ora Abdallah akan matakin daya kamata game da Nu'aymah. ?ari bisa ?ari na yarda da hakan a wancan lokacin. Saboda a yanda ya fa?a?a min bayanansa na fahimci inba ta wannan hanyarba babu ta inda zamu mallaki wannan dukiyar. Wannan shine sanadin dun?ulewarmu waje guda ni da Lurwan muka fara aiki tare. Amma wlhy kullum hankalinmu cikin ?ara tashi yake gameda ha?aka da dukiyar Sooraj keyi abun tamkar ro?o. Shima kuma sake ?aukaka yakeyi fiye da sauran ?an uwansa akan ilimi da soyayyar mutane. Wanda ?aukakar tasa itama tana ?aya daga cikin abinda ke ?ara ?ora Lurwan ga son cutar da shi. Haka muka cigaba da tafiya munama Sooraj *SARAN ?OYE* da iyalinsa harma da duk wanda tsautsayi ya sakko a tarkonmu. Dan kuwa dai Rabi na ?aya daga cikinsu. Mun sakata tana mana wasu ayyukan akan dole wasu ko bama tasan muna amfani da ita munayiba musamman ta wayarta. Akwana a tashi mun cigaba da tafiya wataran muyi nasara akan aikinmu wataran su tsallake tarkonmu. A haka maganar soyayyar Abdallah da Nu'aymah ta fito, har takai Nasir yayi zuciya yabar gidan nan dan shima yana sonta. Da gaske Abdallah tsananin son Nu'aymah yakeyi, kamar yanda itama sonsa takeyi saboda tsananin sha?uwar dake a tsakaninsu, amma a hankali muka fara canja tunanin Abdallah muna kwa?aita masa dukiyar Sooraj. Tun yaron nan baya fahimtar mi muke nufi yana bijire mana harya hau kan hanya saboda ?aukesa da iyayensa sukayi zuwa wajensu. Dan mun fahimci zamansa da Firdausi ne ke mana illa komin masa hu?uba itake wargaza mana komai ta hanyar ?aunar da take nuna masa ta gaskiya. Gaba ?aya mun tattara shirinmu ne akan auren Nu'aymah da Abdallah, shiyyasa duk likitan da aka samo da tabbacin zai mata aiki akan matsalarta sai munbi duk hanyar da zamubi wajan da?ile hakan saboda wani likita ya tabbatar mana da wahala ai mata aikin nan ta tashi, mukuma burinmu muyi amfani da wannan damar sai bayan aurenta da Abdallah aimata aikin ta she?a mu samu abinda muke bu?ata, dan inhar muka gama da yarinyar kauda ?aninta abune mai sau?i a garemu. Har ALLAH yasa burinmu ya cika aka tsaida ranar auren Abdallah da Nu'aymah. Sai dai Abdallah baisan da shirinmu akan bayan aurensa da Nu'aymah so muke ta mutu ba. Wannan daga ni sai mahaifinsa ne muke shirinmu. Amma kash tarihi sai ya nema maimaita kansa tsakanin Adawiya da Nu'aymah tamkar ni da Firdausi. Dan kuwa dai Adawiya soyayyar Abdallah ce tai mata shigar sauri, tanata ?oyewa har takai ta gagara hakan