Showing 114001 words to 117000 words out of 325075 words
zata fa?a yay azamar saka hannu ya sake toshe bakinta da manneta sosai a jikinsa yanda bazata iya ko motsawa ba.
"Wa'iyazubillah!! Iskancin naku da rashin tsoron ALLAH yau har a falon malam?" Kubrah data shigo falon tamkar an jehota ta fa?a hannu bisa kai tana mai waro idanu waje..
Tashin hankali, tsabar ru?ewa Nu'aymah harda guntun fitsar ta saki a wando, batama san ta saka gwiwar hannunta ba ta kai ma Yoohan duka. Sai ko ya sauka a gefen cikinsa.
Saurin sakinta yay yana fa?in "Ouch!!!" dan harga ALLAH yaji zafi. Yay saurin ?oura hannun nasa bisa cikin ya ri?e yana watsa mata mayun idanunsa masu haske da cikar gashi.
Nu'aymah dake ja da baya tana hawaye da kallonsa da kallon inda Kubrah take tsaye tace, "?an iska kawai, ALLAH ya isa ban yafeba. Wlhy daga yau ka sake ?o?arin ta?amin koda hannu sai na illata maka wannan fuskar taka mai kama da jan ?osai, na tsane ka wl........"
"Hhhhhhh! K! ?ar iska bar wani pretending kinji!". Kubrah ta fa?a tana ?arasa shigowa cikin falon sosai.
Nu'aymah dake kuka tamkar ranta zai fita tace, "Aunty Kubrah wlhy ba abinda kike tunani bane. Wlhy tallahi kinji na rantse by mistake ne hakan ya sake faruwa yau ma, shine fa y....."
"K dalla saurara mani! Mahaukaciya kika maidani irinki komi? Na ganki da idona saman cinyarsa kuna tsotsar bakin juna sannan ki hau mini wani rsantse-rantsen banza. Kinsan ALLAH, inhar kika sake fa?in tak saina kwarara ihu yanzun nan kowa yasan halin da kuke ciki".
?asa Nu'aymah ta dur?ushe tana ?ara sakin kuka maiban tausayi. Yayin da Yoohan da sam bai fahimci mi Kubrah ke fa?a ba ya zuba musu idanu kawai yana kallonsu.
Juyowa Kubrah tayi garesa, sai dai wani shegen kwarjini da cikar haibarsa tai bala'in cika mata idanu. Mu?ut ta ha?iye maganar tata ?irjinta na wani irin bugawa da sauri-sauri. Cikin su?utar baki ta firta 'Tsarki ya tabbata ga ALLAH'.
Sake ?aure fuska Yoohan yayi fiye da da, dan a rayuwarsa ya mugu-mugun tsanar kallo, musamman ma irin wanda Kubrah ke masa na ?urulla a yanzun. Duk da ma bawai yaji mi take fa?aba ne ?azun, sai dai ya fahimci ba magana mai da?i takema Nu'aymah ba. Dan haka ya watsa mata wani mugun kallon da manyan idanunsa yana mi?ewa.
Ganin ya nufita ya sata saurin zabura tai baya, sai dai kuma a mamakinta yama ?auke kai daga gareta gaba ?aya, ra?ata yay ya nufi Nu'aymah dake dur?ushe har yanzu tana kukan tashin hankalin datasan a yau babu makawa sai Kubrah ta tona mata asiri.
Handkherchief ya ciro a aljihunsa tare da tsugunawa gabanta, murya ?asa-?asa yace, "Hello!".
A razane Nu'aymah da batasan da isowar tasaba ta ?ago danjin maganarsa gab da ita. Ta waro idanu waje sosai da saurin duban inda Kubrah ke tsaye tana kallonsu kamar ta samu television.
Kamo hannunta yay, da sauri ta dawo da dubanta garesa tare da fisgewa da ?arfi. Sai dai ko gezau baiyiba balle tai tunanin ?wacewar. "Kai wane irin......"
Yatsansa ?aya ya ?aura akan baki. "Shiiii!!!" ya fa?a cikin katseta da zazzaro mata idanunsa sosai.
Ruf. Tai saurin rufe bakin kuwa. Dan wani irin shakkarsa da tsoronsa da bata ta?a fuskantaba daga gareshine ya shigeta yau ?in. Ga wani irin kwarjini mai bala'in cika idanu da yay mata. Batare da yayi magana ba ya saka mata handkherchief ?in cikin tafin hannunta tare da matso da fuskarsa gab da tata cikin wata irin raunanniyar murya yace, "Silly girl".
Baya taja jikinta, dai-dai da sakar mata hannu da yayi ya mi?e shima. Batare da ya kalli ko inda Kubrah take ba ya ?auka jikkar da Nu'aymah tai tuntu?e ya fice abinsa. Ya tabbata idan ya cigaba da zama a falon to lallai zai iya aikata abinda shi kansa bazai yafema kansaba. Dan duk da baiji mi Kubrah ta fa?aba ya fahimci ba abune mai da?i ba musamman yanda Aymah take kuka.
Yana ficewa Kubrah ta bi bayansa da sauri.
"Aunty Kubrah!" Nu'aymah ta fa?a da hanzari tana mi?ewar itama. Amma sam Kubrah batako jiyoba balle ta nuna zata saurareta ta ficewarta.
??????????? ??? ?????? ?????? ??? ?????????? ??????? ???????? ???????? ????????? ????? ?????? ???????.
Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahlan, wa anta taj'alu-l-hzana idha shi'ta sahlan.
Ya Allah! Babu wani abu mai sauki sai abin da Ka sanya shi ya zama mai sauki, kuma Kai kana sanya tsanani idan Ka so ya zama sauki.
Nu'aymah dake jin wata hajijiya na neman zubar da ita ?asa ta fa?a tana mai dafe kanta da sauri. Da ?yar ta iya kai hannu domin lalubar bango. Sai dai kuma ina bai kai ga bangonba wani duhu ya mamaye idanunta. a take ta zube ?asa jikinta na karkarwa saboda wani bala'in sara mata da kanta yayi lokaci ?aya..............?
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????
Mamu gee??
MIN ?ALB!!????
Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????
Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????
Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????
?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070*_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.
No. 31
..............Ta ?aramin gate Yoohan yay ficewarsa. Hakan yasa Kubrah data biyo bayansa ta rasa ina ya nufa. Har babban gate taje bayan ta gama dube-dube a harabar gidan bataga wata ba?uwar mota ba duk saina ?an gidan.
Yanda ta iso gate ?in a rikice tana tambayar maigadi sai abin ya bashi mamaki. Amma sai kawai ya bata amsa da cewar babu wanda ya fita.
"What?! Yama zakace dani babu wanda ya fita a gidan nan? Bayan nasan tabbas idan ba fitaba babu inda zai nufa".
"Hajiya Kubrah wlhy babu wanda ya fita kamar yanda na sanar miki. Shin kodai ?arawo ne ya shigo gidan ban sani ba?".
Wani takaicine ya sake tu?e Kubrah, batare data bashi amsaba ta bar wajen tana zuba masa harara. Shima tsit yayi bai sake magana ba, sai dai zuciyarsa fal sa?e-sa?e.
¡ï¡ï¡ï¡ï
Yoohan na fitowa waje yay turus dan mamakin ganin motocin gidansu da alamu suka nuna tsayawarsu kenan. Dan yanzu suke ?o?arin fitowa. Mamaki yay masifar sake kamashi ganin papa harda d.p.o Emanuel da yaransa. Tsuke fuska ya sakeyi ya nufesu ganin yanda suka tafi kai tsaye ga gate ?in gidan dan su basu ganshi ba.
"Papa!" ya fa?a dai-dai lokacin da papa ya kai hannu zaiyi knocking gate ?in. A kusan tare duk suka juyi garesa domin shigar muryarsa mai amo da kauri cikin kunnuwansu.
Wata wawuyar ajiyar zuciya suka shiga saki a jajjere, musamman ma guards ?in Yoohan da suka san suna a cikin gagarumin tashin hankali inhar ba'a samesa anan ?inba.
Papa har yi yay tamkar zai kifa dan saurin zuwa ga Yoohan ?in. Yay wani bala'in rarumosa jikinsa ya rungume yana fa?in, "Thanks you lord. my son are you okay?
"Yes Papa! What is happening? Mi kakeyi anan? Miya kawoka kano?". Yoohan ya jerama papa tambayoyin yana zare jikinsa daga nasa tare da bin guards ?insa da ?an sandan dake zagaye da su da kallon tuhuma suma.
Sake jawosa jikinsa papa yayi, batare daya bashi amsar ko ?aya daga tambayoyin ba, ya shiga duba jikinsa sama da ?asa kamar mai tunanin an masa wani abu. Sai kuma ya kama rigar shaddar jikinsa yana fa?in, "Yoohan minene wannan?".
Wani irin luuuu da idanu Yoohan yayi tare da huro iska daga bakinsa. Cikin ?osawa da abinda ke faruwa yace, "Papa kaya ne mana. Wai mi kukeyi anan wajen ne? Miya kawoka kano?".
Cikin tsananin nuna ?acin rai papa yace, "John! Yau kaine da kayan hausawa a jiki? Mike damun kanka da tunaninka?".
Sake shiga wani takaicin shima Yoohan ?in yayi, dan a take fuskarsa ta sake nuna fusata. Tayaya yana tambaya amma batare da an basa amsaba papa kuma na masa wasu tambayoyi mara kangado sai kace wani ?aramin yaro. A tsawace ya kalli su Solomon da fa?in, "Mi kukazo yi anan nace?!!".
Yanda ya daka tsawar basu Solomon kawai ba, hatta Emanuel da yaransa duk da suke ?an sanda saida suka razana. Balle kuma ?an anguwa da suka fara taruwa kallo. Gashi Yoohan yayi maganar ne da yare.
Solomon ne cikin rawar jiki data baki ya fara masa bayani,
"Sir! Dama mun zata ko wani abu mara ?yaune ya sameka. Tunda muka tashi muka fahimci baka a cikin hotel ?in. Gashi an duba ko ina amma babu alamarka. Ma'aikatan kuma duk sun tabbatar mana basuga fitarka ba, ga kuma wayoyinka mun samu baka fita dasu ba. To shine mukai tunanin ko anyi kidnapping ?inka ne shine muka kira boss muka sanar masa......."
"To da kuka kawosu nan, sune sukai kidnapping ?in nawa kenan?". Yoohan ya fa?a cikin katse Solomon.
Kasa bashi amsa Solomon yayi, dan harga ALLAH ba ?aramin gulma da munafincin su baba malam sukai wajen papa ba akan gaba ?aya sun janye ra'ayin Yoohan ?inma, amma sunyi bakin ?o?arinsu suga tun a zuwan farko bai sake zuwa gidanba sai dai hakan ya gagara. Kuma jiya a yanda suka bar gidan yana cikin wani yanayi yasa sukai suspecting ?in kosu baba malam ?inne suka turo aka saceshi. Shiyyasa papa na isowa maganar gidan suka fara fa?a shiyyasa yace su kawosa.......
¡ï¡ï
Baba malam da Kubrah kusan a tare suka shiga falon. Shi ya fitone wajen Yoohan ?in dan yanason su tattauna ta yanda ya kamata Yoohan ya fara neman ilimin dazai taimakamasa wajen bautar ALLAH. A tunaninsa zuwa lokacin ya kammala cin abincin da Nu'aymah taje kai masa. Dan rashin dawowar tata baisa sun zargi komaiba da ga shi har Umm. A tunaninsu ko bayan takai masan ta shiga sashen Hajjo ne ko kuma Addah.
Da sauri ya ?arasa ga N'aymah daya hango ?asa wanwar, ga kuma falon babu alamar Yoohan ?in sai ?amshin turarensa kawai. Tiren abincin data kawo yana a ajiye a inda ta ajiyesa.
"Ya ALLAH! K lafiya kuwa mamana? Mikikeyi kwance anan haka?!". Baba malam ya fa?a yana kai hannu ga Nu'aymahn. Da sauri ya zabura dan jin jikinta yayi sanyi ?alau ya saki. Yay azamar maida yatsunsa biyu wajen ?ofar hancinta. 'tabbas bata numfashi' ya ambata a zuciyarsa yana ?agota gaba ?ayanta.
Hakan yayi dai-dai da ?arasowar Kubrah da tun shigowar baba malam tana biye da shi, sai dai shi bai gantaba sai yanzun data ?araso garesu da dauri tana fa?in, "Abbah lafiya? Miya faru da ita ne?".
Cikin tashin hankali baba malam yace, "Ban saniba nima Khadijah, kinga mi?o ruwa dan bata numfashi".
A hanzarce ta ?akko masa ruwan da Yoohan yasha ya bari, ya mi?a hannu ta tsiyaya masa. shafama Nu'aymah yay a fuska. sai dai ko motsi batayiba balle ai tunanun zata farko. Hankalin baba malam ne ya sake tashi matu?a. Ya ?ago idanunsa da sukai jajur ya kalli Kubrah.
"Khadijah maza kiramin Ahmad ko malam ?arami ko Omar. duk wanda kakaci karo dashi cemasa ya fiddo mota".
Amsawa tai da to tana fita da sauri. Sai dai maimakon ta wuce aiken da akai mata saita samu waje ta la?e abinta tana wani ta?e baki da sakin murmushin mugunta. Zuciyarta fes take akan halin da Nu'aymahr ke ciki. Ita ta mutu kota rayu hakan ba damuwarta bace a yanzu. Dan ita ka?ai tasan miyasa take bala'in jin zafin yarinyar.
Baba malam da baisan Kubrah bata tafi aikansa ba ya ?akko Nu'aymah gaba ?ayanta ya fito. Da sauri Kubrah data hangosa ta sake ma?ewa tana zaro ido waje. dan batai tunanin baba malam zai fito da Nu'aymah ba yanzun, a tunaninta ko saita kira ?aya daga cikin wanda ya aiketan.
Oho shi hankalinsa ma bai kai gareta ba. Jikinsa na tsuma bakinsa na ambaton ALLAH ya nufi harabar gidan. cikin sa'a kuwa sai hakan yay dai-dai da fitowar malam ?arami daga sashin su Kubrahn hannunsa ?auke da leda da key ?in mota.
"Abba lafiya? Miya sameta?". Malam ?arami ya fa?a a ru?e yana nufo baba malam dake ?auke da Nu'aymah.
Da sauri baba malam ya bashi amsa da, "Maza bu?emin mota malam ?arami, yanzu ba lokacin sanin mafari bane ba". Cikin sauri malam ?arami ya cika umarnin baba malam. ya karasa ga motarsa ya bu?e. Baba malam na ?o?ari sakata a ciki Kubrah ta ?araso wajen. Tamkar an kira Hajjo sai gata itama ta fito daga sashenta ita da Husnah da alama ma fita zatayi.
A rikice ta nufesu tana tambayar ba'asi. Dan taga yanda baba malam ya saka Nu'aymah a motar tamkar bata da rai. Babu yanda baba malam ya iya dole yayma Hajjo bayani a ta?aice. Kubrah na ?o?arin shiga motar dan a tafi da ita Hajjo ta tureta gefe ita ta shi. Yayinda Husna ta ?ir?ira cikin gidan da gudu tana ?walama Umm kira tana kuka. Dan ita a zatonta Nu'aymah kota mutune. Yarinyace ?arama bata wuce 9years ba. Itace autar amaryar Abbah Musbahu.
Fara fitowar mutanen gidan saboda ihun Husna yay dai-dai da ficewar motar da aka sakata daga gidan. Sai dai suna fitowa idon Baba malam ya sauka akan su Yoohan. Da mamaki ya tsaida malam ?arami dake ?o?arin hawa titin layin. bu?e motar yay ya fita yana fa?in, "Malam ?arami kuje asibitin ina zuwa. da alama wajen nan babu lafiya dan kamar Yahya ne".
Daga malam ?arami har Hajjo dake baya ri?e da Nu'aymah tana faman jijjigata da tofa mata addu'a basu fahimcesa ba. Sai malam ?aramin yabi umarni.
Cikin nutsuwarsa ya ?arasa garesu tare da yin sallama duk da alamarsu bai nuna na wa?anda ya dace yayma sallamarba. Sai bai saniba ko akwai musulmai a cikinsu. Ai ko cikin sa'a sai gashi wasu daga cikin ?an sandan sun kar?a masa. Harda ma risinawa suna gaishesa dan darajar da ALLAH yay masa ta babban mutum kuma jagora.
Ya amsa musu ne idonsa akan Papa da sukema juna kallon sani. Kusan a tare papa da baba malam suka ambaci sunan juna.
"Pastor Goshpower!".
"Sheikh Sooraj Hashim!".
Sai kuma kawai sukaga Papa ya kece da dariya yana tafa hannu. Ya sake nuna Baba malam yana fa?in, "Da gaske Sheikh Sooraj nake gani anan?".
Kafin baba malam dake kallonsa fuskarsa babu yabo babu fallasa ya bashi amsa Solomon yace, "Sir! Ai shine mutumin da......."
Malalacin kallon da Yoohan ke masane ya hanasa ?arasawa, yay saurin du?ar da kansa ?asa yana ha?iye sauran maganar.
Kallon Yoohan baba malam yayi. Sai kuma ya sauke wani lallausan murmushi. Cikin halin dattako irin na masu ilimi da sanin ya kamata yace, "Yahya ka sanshi ne?".
Kai Yoohan ya jinjinama baba malam, kafin a hankali yace, "Mahaifina ne".
Sosai alamar mamaki ya bayyana ga baba malam, dan fuskarsa ta nuna ?uru-?uru. Yace, "Yahya da gaske?".
Kafin Yoohan yay magana Papa da yay matu?ar tsuke fuska ya matso gaban baba malam ?in yana fa?in, "Mizaisa ya maka ?arya?".
Kamar baba malam zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ya sauke ajiyar zuciya a hankali yana sake dai-daita nutsuwarsa. Kusan sakanni goma kafin yace, "Okay! Alhmdllh. Inaga to mu?arasa ciki tunda yau gashi kazo gidana....."
"Never!". Papa ya fa?a cikin saurin katse