Showing 138001 words to 141000 words out of 325075 words
ta kawo nannauyan numfashi alamar dama suma tayi. Kusan a tare duk suma suka sauke numfashin, musamman ma baba malam da ke jin kamar an tsundumasa a aljanna.
Ba ?aramin fa?uwa kuma gabansa yayiba ganin kiran ?an uwansa, amma sai yay ?arfin halin ?agawa ya saka a kunne. "Rudwan ta rasu ko?".
Da dauri Abban Abdallah yace, "A'a Yaya tana da ranta". Da ga haka yayma baba malam bayanin halin da ake ciki. Kamar baba malam bazaice komaiba. sai kuma ya nisa ka?an da fa?in, "Shike nan ina zuwa".
¡ï¡ï¡ï¡ï
Bayan saka hannun baba malam Yoohan da wasu likitocin biyu sai Dr Aysha ta uku suka shiga theatre room da Nu'aymah da ko ma?iyinta ya ganta a wannan lokacin sai ya tausaya mata.
Tun suna irga mintuna har suka koma awanni, dan anyi sallar magrib har isha'i su Yoohan basu fitoba. Duk jikinsu ya kumayin sanyi. amma saboda ?arfin hali irin na baba malan haka ya bama matan da samarin ?a?an nasu umarnin suje gida su huta haka nan. Basu da ikon masa musu akan hakan, amma a kallo ?aya zaka fahimci ba haka suka so ba, dan Abdallah kasa daurewa yay kansa a ?asa yace, "Abba da ku kuje kawai, ni zan zauna har su fito insha ALLAHU".
Da sauri Naser shima yace, "Abba nima ina nan harsu fito dan ALLAH". Ta ?asan ido Abdallah ya ballama Naser harara, amma dai baice komai ba.
Shiru kawai baba malam yay yana dubansu, dan shi harga ALLAH tausayi suke bashi. Kafin baba malam yace wani abu Hajjo tace, "Ai mu duka ma tafiyar tamu bamai yuwuwa bace ba, dan ya kamata muga fitowarsu ko ma tafi da ?an ?warin gwiwa. ALLAH dai ya bata lafiya".
Duk da Amin suka amsa mata. Daga haka kuma babu wanda ya sake cewa komai, suka sake cigaba da zaman jiran tsammani.
Sai kusan ?arfe tara na dare dai-dai su Yoohan suka fito, duk su baba malam suka mi?e tsaye don son jin yaya ake ciki? Su Doctor Aysha ne kawai suka tsaya musu bayani, dan Yoohan yana ?akin bai fito ba tukunna.
A tare suka shiga fa?in Alhmdllhi, Koba komai sun?an sami kwanciyar hankali duk da ba cewa akai Nu'aymahn ta tashi garas bane ba.
Su Dr Aysha da suma fuskokinsu ke nuna alamar nutsuwar jin da?in yanda aikin ya kasance suka sanar da su zasu iya tafiya gida. Dan Doctor yace babu wanda zai iya ganin Nu'aymah a yanzu, hasalima ba'a bu?atar kowa a gareta.
Duk da ba haka suka so ba sun gamsu da bayanin Doctor Mubarak ?in, dan haka baba malam yace su wuce ?in kawai, dama gashi sun baro Umm ita ka?ai a gida sai su Hajarah da ke a tare da ita.
¡ï¡ï¡ï¡ï?¡ï¡ï¡ï¡ï
Kamar jiya yau ma baba malam ba shine yaja salla a massallaci ba, hakama bayan an idar bai zauna wajen karatu ba ya shiga gida.
Tun a daren jiya ya gama yanke shawarar da ta dace akan wannan al'amarin, dan haka koda ya shigo gidan waya ya ?auka, ya rubuta gajeren text massege ya tura. Umm na zaune na azkar tana kallonsa. Yanda baice mata komaiba itama batace ?inba har sai da ya kammala ya ?ago yana kallonta.
?an Murmushin ?arfin hali tai masa ta du?ar da kanta. Shima sai ya ?an murmusa cike da jarumta ya kirayi sunanta a hankali. ?agowa tai ta sake kallonsa. Muryarsa a sanyaye yace, "Ki ?ara ha?uri Jannat kinji, nasan kina cutuwa matu?a, amma inason ki ?auki komai matsayin jarabawa, kinsan ita duniya dama UBANGIJI bai yita dan ta kasance abin jin da?in ?an adam ba a kullum".
?wallar da suka cika mata idanu ta ha?iye da ?yar, ta maida kanta ?asa dan karya gani tana fa?in, "Insha ALLAHU, ALLAH ya bamu ikon cinyewa".
"Amen ya rabbi" ya amsa mata shima.
Shiru ?akin yayi kowa na nazari a zuciyarsa, a haka har gari ya ?arasa wayewa tangaran. Duk da Umm bazata iya aiki ba haka ta fita cikin dauriya ta lissafama Rabi abinda zatayi. Ita kuma ta koma ?akin baba malam inda ta tarar zai shiga wanka.
¡ï¡ï¡ï
A ?angaren Abdallah kam tun a daren jiya ya kar?a Number Yoohan a wajen Ahmad. Babu irin tambayar da Ahmad ?in bai masa ba akan mizaiyi da Number amma ya?i fa?a masa. Dan haka ya ?yalesa kawai yay kwanciyarsa.
Tun a daren ya fito harabar gidansu ya kira wani abokinsa SSS, bayani ya kora masa akan taimakon da yake son yay masa, babu musu kuwa ya amsa zaiyi. ya bu?aci Number Yoohan a take ya tura masa ita da ?ara jaddada masa dan ALLAH zuwa gobe yake bu?atar result.
A safiyar yau kam kusan ?arfe bakwai da kwata sai ga kiran abokin nasa. Bayan sun gaisa da ?an tsokanar juna kamar yanda suka saba ya sanar masa aikinsa ya kammala, yaya yakeso ayi?.
"Wow gaskiya na gode matu?a Mahmood, amma nayi mamakin jin mai Number wai yana a kano, kasan a yanda naji Abuja yake da zama".
"Eh to, zata iya yuwuwa kanon yazo, dan a yanzu hakama sai da na sake tabbatar da yana a inda muka gansa jiya sannan na kiraka, dama wannan shine amfanin tracing ?in ai".
"Gaskiya kam, aiko nagode sosai. Abu nagaba shine zanzo mu ha?u yanzun, dan ina bu?atar a kama min shi ne".
Dariya sosai Mahmood ya keyi, yace, "Shegen sama mi yayi maka ne? Halan wata har?allar kuka ?ulla ya doje?".
"Ai har?allar dake tsakanina da wannan shegen ta wuce duk yanda zakai tunani wlhy Mahmood, kai dai fa?amin inda kake nazo na sameka kawai".........
¡ï??¡ï
Sai ?arfe shida da wasu mintuna ya farka na safiya. ya tashi a ?an firgice bakinsa ?auke da addu'ar barci da ALLAH ya bashi ikon ri?ewa a lokaci ?an?ani kamar yanda baba malam ya koyar da shi. Tunda ALLAH yasa ya musulinta yau ne karan farko da zaiyi sallar asubahi a makare. Dan alarm yake sakawa gudun karya makara. Sannan kuma baba malam duk asubahi sai ya kirasa ya tadashi. Hakan na masa da?i, yana kuma ?ara masa ?warin gwiwa. Dalilin makarar tasa ta yau ma dan bai kwanta da wuri bane, dan tun bayan fitowarsu theatre ya du?ufa ne akan binciken matsalar Nu'aymah. Dalilin binciken nema ya sakashi kwana a asibitin, Solomon ne kawai yaje Hotel ya kwana.
Bayi ya shiga ya ?auro alwala ya fito, ya bu?e jakka ya ciri sallaya da yanzu bai rabo da ita a kayansa duk inda zaije, shimfi?awa yayi sannan ya zura jallabiya ya tada salla. Yana idarwa sa?o na shigowa wayarsa, sai dai baibi takai ba ya mi?e ya fita dan yana son duba patient ?insa.
Kusan mintuna ashirin ya ?auka a ?akin da Nu'aymah take sannan ya fito ya koma office. Yanzunma baibi takan wayarba dai ya shiga wanka. Bayan ya fitone ya ?auka wayar saboda ganin screen ?in yana haske. Missed calls ne har uku yaci karo da su duk na Mumynsa. Bai kirata ba sai ?o?arin duba sa?on da ya gani yay cike da mamakin ganin baba malam ne.
Yana gama duba sa?on yay ?o?arin kiran baba malam ?in. Cikin sa'a kuwa ya ?aga. Tamkar yana a gabansa haka ya rissina da girmamawa ya gaida shi, shima kuma da ga can baba malam ya amsa masa da kulawa tamkar yanda ya saba.
"Uncle dama naga massege ?inka ne, ina fatan dai lafiya?".
"To Alhmdllh Yahya, kawai dai inason ganinka ?inne, ina fatan bazan shiga aikinka ba?".
"A'a Uncle babu damuwa, dan yanzu hakama ina cikin kano, insha ALLAHU zuwa anjima zan shigo".
"Masha ALLAH, ALLAH ya nuna mana".
Daga haka sukai sallama Yoohan na cigaba da mamakin ganin nasa da baba malam ke bu?atar yi, dan ya ?ara fahimtar kiran nasa nada muhimmanci sosai. Bai kira Momy ba sai da ya shirya cikin ?anun kaya. Daga wandon har riga duk ba?a?e ne, sai suka sake fito masa da ainahin farar fatarsa daketa ?yalli da ?aukar idanu. Ya?an saka turare tare da gyara gashinsa da a yanzu yake ?auke da aski na mutunci, sai sajensa dake kwance luf masha ALLAH.
Jin motsi a office ?in nasa ya sakashi ?aukar p-cap ?insa jaa ya ?ora a kai, sannan ya zauna bakin gado ya saka takalmansa suma ba?a?e da ?an kwalliyar ja ka?an.
Harya ?araso cikin office ?in da aka gyara tsaf yana zuba ?amshi Solomon na kallonsa ta ?asan ido, a ransa kuwa yaba iya ado da kwalliya irinta ogan nasu ya keyi, sai dai yana mamakin ganin a ?an kwanakin nan gaba ?aya ya daina saka sar?a, hakama ?an kunne baya sakawa. Saurin katse tunaninsa yayi cike da girmamawa ya mi?e tsaye yana fa?in,
"Good Morning sir".
A ta?aice Yoohan yace, "Same". Yana zama a kujerarsa. ?an kallon Solomon ?in yayi ya ?auke kansa da fa?in, "Bani Coffee".
Solomon na cikin ha?a coffee ?in akai knocking ?ofar. Izinin shigowa ya bada idonsa akan file ?in Nu'aymah daya tattara na binciken jiya. Dr Aysha ta shigo hannunta ?auke da basket. Saman table ?in ta ?ora tana fa?in, "Good morning Doctor".
Ka?an ya kalleta ya ?auke kansa zai maida ga file ?in, sai kuma ya sake dubanta ya dubi basket ?in yana fa?in, "Morning. How are you?".
"Alhmdllh sir" ta fa?a tana sake fa?a?a murmushinta ganin yanda yake kallon basket ?in data ajiye. A ta?aice tace, "Breakfast. ban saniba ko zaka iya cin jagwalgwalon hausawa".
?an lumshe idanu yay ya bu?e yana maida kansa ga abinda yakeyi da fa?in, "Thanks" a ta?aice.
Bata damuba, sai ma murmushi da ta sakeyi tana amsa gaisuwar da Solomon ke mata fuskarsa a murtuke kamar ma shine boss ?in. Coffee ?in daya ha?a ya ajiye gaban Yoohan.
Nanma "Thanks" ?in Yoohan yace masa batare da ya kallesa ba. Sai da yaja wasu sakanni sannan ya rufe file ?in ya gyara zamansa da ?yau yana ?aukar kofin coffee ?in da ?an kallon Dr Aysha da har yanzu take a zaune.
"Matsalar yarinyarnan babbace, ina bu?atar magana da mahaifinta".
"Sir kana nufin aikin da akai mata jiya ba shine na ainahin matsalarta ba kenan?".
Sai da ya kur?a coffee ?in sannan ya girgiza mata kai, "No ba shi bane dai kai tsaye, dan tana da matsala a ?wa?walwa, wanda shine musabbabin yawaita haddasa mata matsalar saurin suma da wasu matsalolin da akai mata aiki a kansu jiya".
Cike da tausayawa Dr Aysha tace, "ALLAH sarki, ALLAH ya bata lafiya, gata yarinya ?arama dan da alama bata wuce 17years zuwa 18 ba". Yoohan baice komai ba dai. Ganin haka Dr Aysha ta mi?e dan ta bashi damar cin abincin idan yana so. "Bara naje to Doctor, zan duba ko wani cikin ?an gidan nasu ya shigo".
Kansa kawai ya ?aga mata. Ta juya ta fita itama tana jinjina hali irin na Dr Yoohan a ranta. Amma ita duk da haka sam baya ?ata mata rai, sai ma birgeta da ya keyi.
Da harara kuwa Solomon dake can gefe ya raka bayanta.
Dr Aysha na fita su Abdallah na isowa bakin ?ofar office ?in Yoohan su biyar, dan bayan Abdallah akwai Mahmood da yaransa su uku, sunbar biyu a mota kuma. Mahmood ya ?aga wayarsa yana fa?in, "Nan shine alama ta nuna, kuma da alama shi ?inne" ya ?are maganar yana nuna masa rubutun dake a saman office ?in mai ?auke da sunan *_Dr Yoohan Goshpower_*.
Wani Murmushin mugunta da jin da?i Abdallah yayi, batare da ya jira sunyi knocking ba ya tura ?ofar office ?in kawai ya shige.
Duk da a yanda aka bu?e ?ofar Yoohan baiko motsaba balle yabar abinda yakeyi. Sai Solomon ne ya mi?e zumbur yay magana cikin daka tsawa. Cikin harshen nasara yace, "Kai wanene zaka shigo nan babu neman izini?".
Wani banzan kallo Abdallah yayma Solo, sai kuma ya maida idonsa ga Yoohan da har yanzu bai ?ago ya kallesu ba, baima nuna alamar yasan da shigowar tasu office ?in ba. Hakan sai ya sake fusata Yah Ab, shima a tsawace yace, "Tsaya matsayinka na bodyguard yaro, dan ubangidanka ne dai-dai da ni".
Solomon zaiyi magana Yoohan da har yanzu ?in bai ?ago ba ya ?aga masa hannu alamar kar yace komai. Shirun kuwa Solo yayi ransa na masa ?una da takaicin rashin sauran ?an uwansa.
Cike da ?asaita Yoohan ya ?ago fuskarsa da ada p-cap ta rufe kusan rabi saboda kansa da ke a du?e. Manyan idanunsa ya sauke akan Abdallah, sai kuma ya maida kansu Mahmood da ke tsaitsaye suma. Batare da yayi magana ba yay musu nuni da wajen zama cike da basar da yanayin da ya ga fuskokinsu.
Abdallah ne yaja tsaki da ?arasawa gaban table ?in Yoohan ?in, cike da kaushin murya yace, "Ba zaman shan ac da kallon syringe ya kawomu ba, munzo arresting naka ne".
?an jim Yoohan yayi kamar bazaiyi magana ba, sai kuma ya motsa la??ansa a hankali yace, "For......?". A takaice cike da rainin wayo
A hasale Yah Abdallah ya jefa masa farar envelope ?in hannunsa.
Da farko Yoohan baiyi niyar dubawa ba, sai dai ganin tsantsar kamannin Abdallah da su baba malam ya sakashi ?aukar Envelope ?in, hotunan ciki ya fiddo. A karon farko ?irjinsa ya ?an buga saboda cin karo da abinda baiyi tsammanin gani ba. Da kafin ya musulinta ne akazo masa da wannan hoton da yake kissing ?in Nu'aymah bazai nuna ya damuba, amma a yanzu yana matu?ar sake ?yamatar wannan ?abi'ar, idan kuma ya tuna ya aikata akan kuskure yana jin matu?ar takai ci. Kallon na biyu da na ukun yay su ma, amma duk da haka sai ya dake, ya sake tsuke fuska fiye da yanda suka sameta yana jifan Abdallah da yake masa kallon tsana da ?yama shima da kallo wula?anci.
Kafin wani a cikinsu ya samu damar cewa wani abu Dr Aysha ta shigo office ?in ita da Dr Mubarak, dan sunyi knocking har sau biyu basuji ya amsa ba. A zatonsu ko yayi busy ne shiyyasa suka shigo kawai tunda sunsan babu wani mara lafiya da zai duba bayan Nu'aymah kamar yanda ya sanar musu tunkan yazo.
Da mamaki suke bin su Abdallah da kallon tsoro, sai kuma suka kalli Dr Yoohan ?in shima. Ganin yanda ya tsuke fuska ya sakasu kasa masa tambayar dake a bakunansu, sai Dr Mubarak ne ya kalli Solomon da ya gama tsumewa da ba?in ciki. "Solomon mike faruwa anan ne?".
Solomon zai basu amsa Yoohan ya katsesa da fa?in, "Mi kuke bu?ata?". Shiru Solo yayi dan ya fahimci Yoohan ?in baya bu?atar ya fa?a. Suma jin hakasai duk suka sake maida kallonsu garesa, cike da ?arfin hali Dr Aysha tace, "Dama mahaifin yarinyar ne ya zo, shine nace a shigo da shi?".
Kansa kawai ya gya?a mata, sannan ya maida dubansa ga su Abdallah "Zaku iya fita ga ?ofa ko". Ya fa?a cike da tsantsar rainin hankali. Abdallah zaiyi magana Mahmood ya matso da sauri yana nunama Yoohan I'd card ?insa. Hakan yayi dai-dai da shigowar Baba malam office ?in bisa jagorancin Dr Aysha.
Mahmood da ya fara fa?in, "Mu?in jami'ai ne daga hukumar s......" ya kasa ?arasawa saboda tozali da baba malam. Yoohan ma mamakin ganin baba malam ?inne ya sakashi sakin hotunan hannunsa saman desk ?in.
Baba malam kuma da duk ke binsu da kallon mamaki ya sauke idanunsa kan Yoohan a ?arshe. Takawa yay a hankali zuwa gaban tebirin, ya kai hannu ya ?iba hotunan dan tun daga inda yake yana hango komai na cikinsu. ?auka yay ya sakasu cikin envelope ?in. Kafin ya samu damar fa?in wani abu saboda nauyi da bakinsa yay masa Abdallah yace, "Abba munafukin nan ashe likita ne anan, dan hak......."
Baba malam yay saurin girgiza masa kai,