Showing 33001 words to 36000 words out of 325075 words
zauna tana lallashinta amma Nu'aymah sai ta?i saurarenta. Tana cikin darzar kukan Baba malam ya shigo sashen hajjon da daddare bayan ya taso daga wajen karatu a massallaci.
Tsawa yayma Nu'aymah amma ba wadda zata sakata firgitaba. Tai saurin nutsuwa hawaye na sake rige-rigen sakko mata a kumatu.
"K wai kin koma jaririyane a gidan nan yanzu? Da zaki zauna kitama mutane kukan banza da wofi. Ki fita idanuna Nu'aymah tunkan na sa?a miki. Bake kika za?ama kanki hakanba da kanki? To daga yau na baki sati biyu kima shi wanda kika gudu dominsa magana ya turo iyayensa".
Cikin tashin hankali Nu'aymah ke kallon Baba malam. Bakinta na rawa tace, "Abbah wlhy ban guduba, dan ALLAH ka saurareni na fa?a maka yanda akayi". "Bana bu?atar jin komai daga gareki Nu'aymah, dan sa?wannin da kika bar mana sun isheni dukkan amsa. To kin samu yanda kikeso. Kinso tozartamu ALLAH kuma ya hana faruwar hakan ya rufa mana asiri. Abdallah ne dai kince ba?yaso, ALLAH kuma ya canja masa da wa?anda suka fiki alkairi, sai kima wanda kikeson magana ya fito a aura masa ke kuje ku ?arata".
"A....Ab....Abbah!" ta kira sunan Baba malam bakinta na rawa da jikinta. Sosai kalamansa suka nema zautata. 'Yah Ab ?inta ne yay aure da wata ba itaba?. Kai ina bazai yuwuba ma'. Tai maganar a fili tana kallon Hajjo dan baba malam tuni yay ficewarsa ma.
Kamota Hajjo tayi ta rungume tana lallashinta. Tausayinta na ratsata. "Hajjo dan girman ALLAH kimin bayani, wlhy na kasa fahimtar kalaman Abbah gaba ?aya. Da gaske yake Yah Ab yayi aure? Ya auri wata ba ni Nu'aymah ba?. Hajjo fa?amin dan ALLAH, taimakeni ki fa?ain dan girman ALLAH hajjo".
"Ya isa haka Zainabu. Ki nutsu na miki bayanin komai to kinji".
Da sauri Nu'aymah ta shiga ?aga mata kai tana share hawayenta da hannaye biyu. Hajjo ta ru?o hanun nata, cikin nutsuwa tai mata bayanin komai daya faru a ranar bayan an wayi gari babu ita a gidan. Sa?wannin data ajiye musu akan ita ta tafi batason Abdallah sai Ameer.
______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Wannan littafi SARAN ?OYE na ku?ine, yana ?aya daga zafafa biyar, idan kana bu?ata kaima wa?anan numbers ?in magana ka biya ku?insa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka karanta idan baka biyaba, karka kuma ya?a dan ALLAH idan ka gani??????.
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
_______________________
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Mike shirin faruwa dani ni Nu'aymah? Hajjo wlhy kinji na rantse miki bani nabar sa?on nanba. Kuma Ameer da ake magana akansa ni babu abinda ya ta?a ha?ani da shi sai sako da Yah Abdallah ke bashi yana kawomin. Rabon kuma dana sake ganinsa wlhy anfi wata hu?u Hajjo".
"Ah ah! To amma shi kuma Abdullahin yace bai san Ameer ?inba, bai kuma ta?a aiko wani wajenki ba sai Ahmadu".
"Bai ta?a ba Hajjo? Shi Yah Ab ?in da kansa yace haka kuma?".
"Sosaima kuwa, a gaban kowama ya fa?a a randa al'amarin ya faru. Amma kwantar da hankalinki, Zainabu nima dai al'amarin nan ya ?aure min kai matu?a, yanda nasan kike da Abdullahi tayaya zaki aikata wannan abun? To amma iyayenki duk sun kasa fahimtar akwai wani ?oyayyen al'amari daya faru a wannan ranar, musamman ma ?an malam daya ?auki zafi sosai akan al'amarin".
"Hajjo dan ALLAH ki taimakeni, wlhy inason Yah Abdallah fiye da yanda kowa yake tunani, dan ALLAH ku tausaya mani karna rasashi hajjo. Idan na rasashi mutuwa zanyi......"
"Bazaki mutuba Zainabu kinji, ki kwantar da hankalinki muyita addu'a ALLAH na nan, yana sane da komai kuma shine maiyin maganin komai".
Kai Nu'aymah ta ?agama Hajjo dake share mata hawaye, ta kwantar da kanta a jikinta saboda kanta dake wani irin bala'in sara mata kamar zai tsage. "Hajjo kaina". Hankalin hajjo ne ya sake tashi, dan sam ba'ason ciwon kai ga Nu'aymahr, daboda ciwonta. Saurin tada ita tayi daga jikinta ta kwantar da a kujerar tana fa?in, "Ina zuwa, bara na amso miki maganinki kisha".
Hajjo da kanta ta nufi sashen su Nu'aymah dan yaran duk basu shigoba daga ita sai Nu'aymah ne kawai. Baba malam da Umm suna zaune a falo ta shigo, Muhammad na gefe yana homework.
Da sauri suka shiga tambayarta ko akwai abinda take bu?ata?. Fuskarta babu ko ?igon walwala tace su bata maganin Nu'aymah kanta ke ciwo. Ba ?aramin fa?uwa gaban Umm yayi ba, amma saita danne ta tashi taje ?akin Nu'aymahn ta ?akko ?an box ?in da magungunanta ke a ciki ta kawoma Hajjo. Tanason taje taga mike faruwa da ?iyar tata amma tanajin nauyin hakan. Ga baba malam yay kamar abin bai damesabama, ya cigaba da shan fruit salad ?insa hankali a kwance.
Hajjo dai batabi takansuba ta amsa tai ficewarta. Da kanta ta bama Nu'aymah maganin, sannan ta kamata ta kaita bedroom ?inta ta kwantar. Cikin amincin ALLAH babu jimawa barci yay gaba da ita.
Washe gari da zazza?i Nu'aymah ta tashi ga ciwon kai. abinda ya tada musu hankali Doctor ?inta yayi tafiyar da yace, gashi kuma basu nema wancan likitanba. Andai kaita asibiti wani likitan daban ya dubata, ya?an mata abinda zai iya ya turasu asibitin dawanau. Kamar koda yaushe Baba malam ya?i yarda a kai Nu'aymah dawanau, dan acewarsa yarinyarsa ba ciwon hauka take ba. Yasan dai ance tanada matsala a ?wa?walwa. Hakan yasa ya ?akko file ?in Nu'aymah da shirin neman wancan Doctor ?in. Amma abin mamaki da al'ajabi babu takardar da Numbers ?in take. Anyi ?ai-?ai da file ?in babu ko alamar takardar. Kamar wasa aka bincike littatafan baba malam dake tare da file ?in tas babu takardar dai.
Wannan al'amari ba ?aramin ?aure kan kowa yayiba a gidan. Musamman da ya zam agaban kowa Doctor ya bada takardar da file ?in. Wannan al'amari ya sake ?ata ran baba malam matu?a, amma jarumar fuskarsa ta?i nuna hakan. Sai Hajjo ce keta masifa kamar zata ha?iye harshenta. Dan wannan ?auke takardar ya sake tabbatar mata da akwai mai yin ?ulle-?ulle a gidan da gaske. Sai dai yanda kowa ya nuna damuwarsa akan al'amarin baka isa nuna zarginka kai tsaye akan wane ne ?in ba.
_____¡ï_____
"Maganar gaskiya al'amarin gidannan ya fara bani tsoro Abban Nu'aymah. Anfa da?e ana ruwa ?asa na shanyewa, dolene a wannan karon nasan wanene ke mana SARAN ?OYE. Tunda har aka iya toshe hanyar neman lafiyar Nu'aymah lallai za'a iya kashe mana ita ma". Umm tai maganar hawaye na zuba mata masu zafi.
Zama baba malam daketa kai kawo a ?akin yay kusa da Umm, ya kafeta da idanunsa da sukai jajur shima saboda damuwa. "Jannat idan munce zamu ?auki mataki, akanwa zamu ?auka? Akan kuma mi?".
"Amma Abbah Nu'aymah karka manta musabbabin ciwon Nu'aymah fa fa?o da ita akai daga kan gado tun tana jaririya, kanta ya bugu ta samu ciwo a ?wa?walwa. Badan ALLAH ya ta?aita wahalaba da zata tashine cikin halin rashin hankali kamar yanda Doctor ya sanar mana. Addu'a da hikimar UBANGIJI ce ta cigaba da jagorancin lafiyar Nu'aymah hartakai wannan lokacin cikin hankalinta, sai dai idan ciwon ya motsa tasha wahala. Tun Nu'aymah batasan ma'anar magani ba ake ?ura matashi a ciki, kanaji kwanaki badan ALLAH yasa Doctor ya farga ba hantarta fa harta harbu da ciwo saboda yawan shan magani. Abban Nu'aymah baka tunanin game da al'amarin aurenan akwai wani abu da bamu hasasoba kuwa?".
"Kiyi ha?uri Jannat karmu zargi kowa akan al'amuranmu, mu daure mucigaba da ?aukar komai akan jarabawa ne. Duk abinda yay farko nasan zaiyi ?arshe. Da ALLAH na dogara game da lafiyar Nu'aymah nasan kuma shi mai jine mai kuma ganine. Indai bamu da ha??in kowa ALLAH bazai bama kowa damar shiga ha??inmu ba. Ki kwantar da hankalinki, insha ALLAHU zan sake samo Number likitan nata, dan mantawama nai nace masa idan ya tafi ya kiramu".
Kanta ta jinjina masa hawaye na cigaba da sauka mata. Ya saka hannu ya share mata yana murmushin da shima iyakarsa la??ansa ne kawai. Shi ka?ai yasan mi yakeji a ransa. Yana dai ?o?arin dannewane dan yasamu Umm ta kwantar da nata hankalin kodan hawan jininta............?
_____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________
Wani kaya sai amale ka ?auka??.
SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.
Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ?an gaske.
*_Ina mata masu ?an bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ?ar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ?an ?walisa masu son sabunta gida da kayan ado ?an waje masu sau?in farashi da nagarta!._*
_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ?aya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ?yau da nagarta a farashi mai sau?i kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ?an gayu suma akwaisu babu ?ayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba'a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ?aki basu da tsara_.
Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.
Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ?arin bayani ?ar uwa.
*_Siyen nagari??, maida ku?i gida?? sai SAHFAT PREORDER??????????_*
_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????
Mamu gee??
MIN ?ALB!!????
Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????
Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????
Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????
?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.
[3/16, 6:26 PM] +234 901 860 0202: *_Typing??_*
No. 10
________________________
*ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE*
*_KAJI shahararrun kuma mandiyoyin ?an ?walisar kawo kayan kitchen masu tafiya dai-dai da zamani. Idan nace nadaban ina nufin su?in nadabanne wajen kaya ?an gaske dake ?awata kitchen ?in amarya harma dana uwargida ?ar ?walisa. Ka siya ka tabbatar ka saya ?in ko a gaban tsaranka sai *ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE*. sunan kayansu sa kishiya cin bashi??, dan tana ?yalla ido taga kitchen ?inki tsarin amerikawa tuni zata fara ?wafa da tunanin zuwa gidan delu dillaliliya mai saida kwanika. Sai dai kuma kama da wane akace bata wane, dan haka ku maza ku garzaya ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE* domin samun naku kuma. Suna kawo kaya daga ?asashen ?etare akan farashi mai sau?i da rahusa. Suna order ?in products kamarsu, dukan kayan kitchen na zamani, bedsheets, shoes dade sauransu, products ?insu pre-order ne dake zuwa akan lokaci batare da mai kaya ya ?osa da jira ba ko samun matsala. Zaku iya samunsu a Number waya kamar haka ko Location nasu. Phone number: 08102393622. Location Gombe. Amma Zasu iya turawa kowani gari dake a lungu da sa?o na ?asarnan. Sayen nagari maida ku?i gida. Ku garzaya kar ayi babu ku. Da ?yar nasha yafi da ?yar aka kamani inji masu iya magana??????????._*
_________________________
.............Yau Nu'aymah ta tashi jikin nata da?an dama, sai dai rashin ?arfin jiki. Tunda Ahmad ya tafi raka Hajjo asibiti ganin Doctor saboda ?afarta saita dawo sashensu ta kwanta. Barci tai sosai dan har sai gab da azhar ta tashi tai wanka. Shiri tai da ?an sauri-saurinta ta fice zuwa ?akin Umm, dan wani irin maitan awara takeji. Babu kowa a ?akin, sai gyara da yasha yanata uban ?amshi. Tai murmushi da fa?awa saman gadon ta kwanta tana mai sake sha?ar turaren wutar da ?yau cikin hancinta. Tana masifar son ?amshi a rayuwarta. Shiyyasa turare kwana ka?an yake mata ya ?are. Ga baba malam da Yah Ab sun mugun ?aure mata ?ugu wajen siya mata. Sam basa gajiyawa. Kafin wani ya ?are an saya mata wani. Ga khumra da Umm itama take bata ita da Adawiya. Tun Adawiya bata damu da ?amshiba harta fara biyema Nu'aymah saboda yanda take bulala musu shi a cikin ?aki kamar shagon saida shi.........
"K! Kuma yaushe kika shigo nan?". Umm ta fa?a tana kallon Nu'aymah dake kwance a kan gadonta idanu a lumshe.
A hankali ta bu?esu akan Umm dake kallon yanda tai rama cikin kwanaki ka?an. Tai ?an ?ata fuska kamar zatai kuka. "Umm dan ALLAH awara zanci". Kai Umm ta?an girgiza da nufar gaban mirror ?inta ta ?auki ?aramar wayarta da tazo ?auka. "Indai banda fitina ni ina naga awara yanzu Nu'aymah? Ke dai inhar kikai zazza?i sangarta iri-iri kin iyata mara dalili, ko Muhammad baya iya shegenki a gidan nan".
"Umm Please!". Ta sake fa?a cike da shagwa?a kamar zatai kuka. Zama Umm tai a bakin gadon kusa da kanta. Ta?an shafa goshinta a hankali, "Nu'aymah banson rigimar nan, yanzu dai kinsan baza'a samu awaraba ko? Sai ki bari sai anjima, bara dai na bama Saude takai ku?in gidan ?an awaran".
Kai Nu'aymah ta ?agama Umm tana murmushi, sai kuma ta tashi zaune ta rungumeta tana ?ar dariya. Zame hular kanta Umm tai ?o?arin yi. Da sauri Nu'aymah takai hannu zata ri?e dan tasan mi Umm ?in zata duba. "Umm kainafa ke ciw....."
"?aniyarki keda ciwon kan, wai Nu'aymah bazaki daina wannan shegen ?azantan nakiba na rashin son ?itso? Kalla kiga fa kanki gashinki duk ya lalace saboda rashin kula. Tashi maza ki wuce wajen Adda ta kama miki kai kafin na ?ata miki rai".
?walla cike da idonta ta kalli Umm, "Umm dan ALLAH ba yau ba". "Kin rainani ko?". Umm ta fa?a tana ?ata fuska.
Muhammad dake ?o?arin shigowa ya ?yal?yale da dariya yana fa?on, "Umm ALLAH fa ta rainaki, inba rainiba ya zakice taje kitso ta zauna shagwa?a......"
Filo Nu'aymah ta ?auka ta wurgama Muhammad ?in. Ya goce yana dariya. "Wlhy idan na kamaka a gidannan saina tsiyayar maka da man kai tas. Umm ki fa?ama yaron nan nifa ba sa'arsa bace". Yanda tai maganar idanunta cike da ?wala ya saka Umm yin ?aramar dariya itama, tai saurin saka hannu ta rufe bakinta tana ha?iyeta ganin hawayen harsun sakko a guje.
"Uhghumm!" Umm tai gyaran murya tana ha?e fuska da wurgama Muhammad harara. Hannayensa ya ha?e waje guda fuskarsa da murmushi yace, "Am Sorry aunty N". Ya ?are maganar da mata gwalo ka?an. Harara ta zuba masa ta koma ta kwanta da juya masu baya shi da Umm ?in.
Hannu Umm ta bashi suka tafa, kafin ya haye gadon yana fa?in, "Banace kiyi ha?uri ba Noorunnisa". Juyowa tai fuskarta ?auke da murmushi ta dungure masa kai tare da ja masa hanci tana fa?in, "Yaro 1-0".
Dariya sukayi a tare. Umm ta mi?e tana murmushi ta bar musu ?akin.
¡ï¡ï¡ï¡ï
Sashen Addah Umm ta nufa, dan tanason su tattauna game da al'amarin nan na Nu'aymah tun jiya, sai dai rashin lokaci yasa bata shigaba. Tasan itama Addahn bata shigo bane saboda taga baba malam ya wuni a gida jiya, yauma ya da?e bai fitaba.
Kubrah kawai ta iske a falon tana yankan ?umba. Ta gaidata cike da girmamawa kamar yanda suka saba. Dan bayan mahaifiyarsu Umm itace mace ta biyu a gidan da suke ?auka tamkar mahaifiya. Fuskar Umm ?auke da murmushin itama ta amsa mata, "?iyata saike ka?ai a gidan kenan?". "Eh Wlhy Umm, daga ni sai Addah kawai. Hajarah da su Jafar sun fita aika". "To ALLAH ya maidosu lafiya. Ina Addan?". "Umm tana ?aki ki shiga mana".
Kafinma Umm ta amsa mata Addah ta fito daga ?aki. "Haba nifa ince kamar muryar Umm, ashe kuwa kece?". "?yaface haka mana, tun jiya rabon danaga idonki a gidannan Addah. saboda kinga ?arki ta samu lafiya".
"Wacefa lafiya Umm, anason a ganmin bayanta". Addah ta fa?a cikin ?acin rai. Murmushi Umm tayi da kama hannunta, dan tasan Addah dama bata barin saita kwana sam. "Kinga nidai muje sarkin hawa".