Showing 3001 words to 6000 words out of 325075 words
shashancine wannan kikema mutane haka Adawiya?!!".
Adawiya da sai yanzu tasan da shigowarta ta taso da gudu ta fa?a jikinta da sake fashewa da wani sabon kukan, "Addah Wlhy ina sonshi, idan baku auramin shiba mutuwa zanyi, wlhy saina kashe kaina Addah. Dan nafita sonshi ku taimakeni............."
Ta fashe da wani irin kuka tana zamewa zata fa?i ?asa jikinta na rawa. Da wani irin kallo Addah ta bita harta zube ?asan yaraf, ta?anja jikinta baya tana jan tsaki zata ra?ata ta wuce. Saurin tashi Adawiya tai zaune ta ri?o hannunta. "Wlhy Addah inhar baku aura masa niba saina kasheta!!".
Baya Addah tai da sauri zata fa?i ?asa tana mai waro idanu waje sosai akan Adawiya, bakinta na ?ari tace, "Ki kasheta Adawiya?!".
"Da hannun nan nawa kuwa". Adawiya ta fa?a tana zazzaro idanu waje itama da ?aga hannunta tana nunama Addah............?
Hummmmm!!!! Tur?ashi. Masu karatu wannanfa shine ana dara sai ga dare yayi??. Mi kuke tunani akan wannan labari? Wacece Adawiya? Sannan wacece Nu'aymah? Wanene Kuma Abdallah?. yaya zata kasance? Minene zai faru kuma? Wace amsa Addah zata bama Adawiya?......
Amsar wa?anan tambayoyin duk suna a Littafin SARAN ?OYE!! da ke cikin tawagar littatafai biyar na zafafa 2021 dake shirin zuwa muku insha ALLAHU nan bada jimawa ba????.
Wlhy karku bari ayi babuku, dan ZAFAFA BIYAR 2021 fa da zafinsu suke tafe, na tabbatar muku tafiyar wannan shekarar ta dabance MASOYAN AMANA??????????.
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????
Mamu gee??
MIN ?ALB!!????
Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????
Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????
Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????
?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.
[3/4, 5:46 PM] +234 901 860 0202: *_Typing??_*
*_SARAN ?OYE!!_*
*_Bilyn Abdull ce????_*
Free page??
No. 2
.................Tsaki Addah taja tana ballama Adawiya harara, ta tsallaketa ta wuce tana fa?in, "Sai kije ki kashetan shashasha kawai mara tunani".
Kuka sosai Adawiya ta sake fashewa da shi. Ta rarrafa har inda Addah take shirin kabbara salla ta ri?e mata ?afafu. Cikin fushi Addah ta ?wace ?afafunta tana nuna Adawiya, "Wlhy idan baki shiga hankalinkiba Adawiya zan bala'in sa?a miki, wai wane irin iskancine wannan? Ki shiga hankalinkifa tunkan nai miki abinda zakiyi dana sani a taron bikin nan. Dalla tashi ki ficemin anan, ba kashe Nu'aymah ba ki babbakama gidan wutama mu ?one ?arewar hauka. Wawuya kawai!!".
Yanda Adawiya taga ran Addah ya ?aci tasan zata iya cin ubanta kamar yanda ta fa?a, tana ganin ta kabbara salla saita tashi ta fita tana kukanta. Addah mace ce mai yawan wasa da fara'a, idan har kaga fushinta to lallai an kaita ma?ura, shiyyasa idan tai fushin dolene kaji shakkarta. Su kansu ?a?anta tana rayuwa da sune tamkar ?awayenta, hakama sauran yaran gidan. Wannan halayar tata tajan yaran a jiki yasa kowane yaro yazama ?an ?akin Addah a gidan, suna sonta sosai, hakama iyayensu sunajin da?in yanda take son ?a?ansu da basu lokacinta.
Can bayan ?akunan sashen samarin gidan Adawiya ta nufa, dan tasan canne kawai babu mutane. Waje ta samu ta zauna tasha kukanta, yayinda zuciyarta ke shirya mata mugayen abubuwa game da Nu'aymah da matakin da zata ?auka a kanta na dakatar da wannan auren, tayi al?awarin kota halin ?a?a saita mallaki Abdallah a safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu. Sai kuma ta rabashi da Nu'aymah, idan kuma har hakan bata tabbata ba to sai dai suyi zaman kishi ita da Nu'aymah kokuma kowa ya rasa. Dan ko sama da ?asa zata ha?e bazata barma Nu'aymah Abdallah ba wlhy........
"Adawiya! Adawiya!!". ta jiyo ana ?wala mata kira. Tsaki taja mai ?arfi kafin ta mi?e tana kakka?e jikinta daya ?an ?aci da ?asa, duk da ma ita ko shiryawa batayiba. Fitowa tai inda zata iya ganin mai kiran nata. Da sauri taja baya saboda karo da suka kusa ci da Yah Abdallah. ?irjinta yay wani mugun harbawa, a take ta fara neman nutsuwarta ta rasa. Kwarjininsa da matsanancin son da take masa suna neman birkitata gaba ?aya ta kasa ri?e kanta....
Sassanyan Murmushinsa ya sakar mata yana ?an ware idanunsa a kanta, "Oh Hassanar amaryace haka bata ko shiryaba?". Duk da maganarsa batai mata da?iba saita saki masa murmushi, ta matsa kusa da shi tana sha?ar ?amshin turarensa mai da?i, "Yah Abdallah dama ka iso?".
"Ya za'ayi ki sani tunda ance kina nan kinata kukan rabuwa da Husainar ki". Baki ta bu?e zatai magana sai kuma ta fasa tana kallon Amal data rako Yah Abdallahn. "Kiranmi kike ?walamin ke kuma?". Baki Amal ta?an ta?e tana cigaba da latsa wayar hannunta, "Kiranmi zan miki ni kuwa, dama Yah Abdallah ne ke nemanki, shine akace anga kinyo tanan".
Kafin tace wani abu Yah Abdallah yace, "Nine na sakata, wani aiki zakimin, Amal jeki abinki". Kai Amal ta jinjina masa, tai gaba abinta batare data sake kallon inda Adawiya take ba. Sai da tai nisa da su sannan Abdallah ya sake kallon Adawiya, ganin shi take kallo sai yay murmushi.
"Yaya dai ?awar amarya na canja miki ne?". "Sosaima kuwa Yah Abdallah". Adawiya ta fa?a cike da yanga tamkar ba itace ta gama darzar kukaba yanzun.
Murmushi yayi yana ?auke kansa da fa?in, "To na gode. Kinsan aikin da zakimin?". Kai ta girgiza masa batare da tace komaiba. "Sonake kije wajen Walimarcan ki satomin amaryata nan inason ganinta". Wani takaicine ya soki zuciyar Adawiya har fuskarta sai da ta nuna hakan. Da mamaki Abdallah yace, "Yaya dai?". "Babu komai Yah Abdallah" ta bashi amsa da rawar murya.
"Okay, to maza ki shirya saiki ?akko min ita, karfa ki bari kowa ya ganki musamman ma Hajjo". Kanta ta ?aga masa kawai, dan tasan idan tai magana kukane zai ?wace mata. Da kallo Abdallah ya bita harta ?acema idanunsa, haka kawai tausayin yaran ya kamashi, kowa yasan irin sha?uwar dake tsakanin Adawiya da Nu'aymah tun ?uruciya, sun tasone tamkar tagwaye a gidan, komai tare ake musu shi, yanzu kam ace zasu rabu rana tsaka ai dolene kaji tausayinsu.
Adawiya kam koda ta bar wajen sashen Hajjo kakarsu ta nufa, babu kowa duk ana wajen walima, dan ana idar da salla kowa ya koma, daga cikin gidanma kana jiyo lecture ?in da aka fara. Kwanciyarta tayi dan ta rantse bazata kira Nu'aymah ba.
¡ï¡ï¡ï
Tun Abdallah na kallon hanya na jiran ?ullowar amaryarsa Nu'aymah da Adawiya harya koma duban agogo. Kamar wasa sai ga mintuna ashirin sun shu?e babu Adawiya balle Nu'aymah, abinda zuciyarsa kawai ta basa Hajjo ta hana Adawiya ?akko Nu'aymah ne, maybe kuma tanacan tana wayon yanda zasu baro wajen. ?an murmushi yayi yana lumshe ido, sosai yake cike da ?oki da ?aguwar son ganin Nu'aymahr sa, yanason yaga yanda ta sake komawa yanzun........
Kiran da ake masa a wayane ya katse tunaninsa, ya zaro wayar daga aljihun gaban rigarsa ya duba. Zaid ne, kamar bazai ?agaba sai kuma ya amsa tare da ?orawa a kunnensa. "Hello Jibiya wai kana inane?". Kamar bazaice komaiba sai kuma yay guntun tsaki da kallon agogon hannunsa. "Ina cikin gida mana, miya faru?". "Cikin gida kuma? To mi kakeyi acan bayan kowa duk yana nan har amarya. Gashi nan Baba malam na nemanka to". Baice masa komaiba ya yanke wayar. Badan yaso ba ya baro cikin gidan ya koma wajen walimar.
Inda Nu'aymah ke zaune kusa kakarsu Hajjo ya kalla, tana zaune a yanda ya barta tun ?azun, babu kuma alamar Adawiya a wajenma. ?an tsaki yayi a ransa ya ?arasa inda Baba Malam yake.
Masha ALLAH, anyi taron walima an tashi lafiya, inda malamai suka ragargaza lectures masu ratsa jiki ga ma'abocin saurare. Gaba ?aya an gina sune akan zaman aure da kurakuran da muke tafkawa a cikinsa da hanyoyin magancesu, inda amarya da angonta sukasha addu'oin fatan alkairi da zaman lafiya.
______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Wannan littafi SARAN ?OYE na ku?ine, yana ?aya daga zafafa biyar, idan kana bu?ata kaima wa?anan numbers ?in magana ka biya ku?insa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka ya?a dan ALLAH idan ka gani??????.
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
____________________________
Tunda aka tashi jikin Nu'aymah sai ya sake yin sanyi, maimakon ta nufi ?akinsu da suke zaune da ?awayenta sai ta nufi wajen Umm. Kanta tsaye ?akin Umm ta wuce, sai dai bata ciki sai ?an uwanta. Gaishesu tayi suna tsokanarta da amarya-amarya, ita dai kanta a ?asa ta sulale ta fito. Sashen baba malan ta nufa, dan tasan Umm bazata wuce tana a canba ko wajen Addah.
Tun shigowarta corridor ?in daya shiga tsakanin falon Baba malam dana Umm taga takalman Umm da Addah, ?an murmushi tayi tana sake jinjina wannan irin ?auna ta iyayensu, ?ofar falon ta ?arasa tare dayin sallama, daga ciki suka amsa mata da bata iznin shiga.
"Ah ah! amarya da kanta. Miya farune?". Addah ta fa?a tana murmushi. Kallon Umm da batace komaiba Nu'aymah tayi, sai kuma ta du?ar da kanta hawaye na cika mata ido. Addah tace, "Kinga zonan". Takawa tai a hankali zuwa garesu, ta zauna a ?asa jikin ?afafun Umm data cigaba da abinda takeyi tamkar batasan da shigowar Nu'aymah ba.
"?ar albarka miya farune? Ko kewar Umm ne ya motsa?". Maimakon Nu'aymah ta bama Addah amsar tambayarta sai hawaye suka gangaro mata a kumatu, ta kwantar da kanta bisa cinyar Umm tana jan ajiyar zuciya a jajjere.
Dauriya kawai Umm keyi dama, taja ?oyayyen ajiyar zuciya da girgiza kanta tana kallon Nu'aymahn. "Ke kuma wannan shashancin fa?......"
"A'a babu wani shashanci Umm". Addah ta fa?a tana kamo hannun Nu'aymah cikin nata. "Baby fa?amin miya faru? Ko har yanzu tsoron dai?". Kai Nu'aymah ta ?aga mata, sai kuma ta ?ago ta kalli Umm da itama kallonsu takeyi. "Umm dan ALLAH ni banason auren a fasa kawai".
"Afasa kuma Nu'aymah?! Miyasa?".
"Addah wlhy ni naji banaso yanzun kawai".
Sosai abin ya bama Addah dariya, ita kanta Umm sai da tai murmushi tana girgiza kai, dan babu komai a maganar Nu'aymah sai zallar ?uruciya da sakarci. Umm ta janyeta a jikinta tana mi?ewa da fa?in, "Wannan shashancin ba daniba, Addah bara nayi nan kinji".
Sauri ri?eta Nu'aymah tayi tare da sake cukuykuye ?afafunta tana kukanta, "ALLAH Umm nidai banaso, gara na zauna a wajenku Please".
"Oh ALLAH, Nu'aymah banason sakarci kinji, sakarni naje nayi abinda zai amfaneni".
Kallon Umm Addah tayi, cikin magana da yaren ido taima Umm alamar ta lallasheta Please. Umm zatai magana Addah ta girgiza mata kai tana mi?ewa ta fice ta barsu. Ajiyar zuciya Umm ta sake saukewa a sanyaye, kafin tai guntun murmushi da komawa ta zauna a inda ta tashi. Kama Nu'aymah tai ta tadata ta maidota kan kujerar kusa da ita ta zaunar. Hakan ya bama Nu'aymah damar fa?awa jikin Umm ta rungumeta.
Karan farko Umm tai ?ar dariyar ?arfin hali da rungume ?iyar tata itama. "Ke wai bakisan kin girmaba Nu'aymah? Aurefa za'a ?aura miki gobe idan ALLAH ya kaimu amma kike halin yara har yanzun?".
"Umm ni wlhy na fasa, zan zauna a wajenku nayi karatun kawai". Dariya Umm ta sakeyi da ?ago fuskar Nu'aymah ta share mata hawayenta. "To naji ya isa haka nan kukan ko". "To Umm za'a fasa ?in?". "Tambayi Abbanki ga shinan". Umm ta fa?a tana kallon Abba daya shigo kusan mintina biyu kenan harya zauna kusa da Nu'aymahn bata saniba yana kallonsu kawai. Tashi Nu'aymah tayi daga jikin Umm takoma jikin Abbanta.
"Maman nan nawa dai shagwa?anta yayi yawa". Ya fa?a fuskarsa ?auke da murmushi yana shafa kanta. ?agota yayi ya zaunar sosai, tare da saka hannu ya share mata hawayenta gaba ?aya. "Kinga fa?amin miya faru?".
"Abbah a fasa kawai".
Waro idanu ya ?anyi cikin mamaki, "Mamana mi za'a fasa?". "Abbah aur....." sai kuma ta kasa ?arasawa tai ?asa da kanta.
"Ina jinki fa?amin mana!".
"A...Abbah auren, ni yanzu na fasa".
Kallon juna sukai shi da Umm dake kallon Nu'aymah cike da damuwa, Sosai ta basu tausayi da dariya, amma duk sai suka danne kayansu. Abbah ya ri?e hannayenta da sukasha ?unshi cikin nasa, cikin muryar lallashi yace, "Mamana kin daina son yayan nakine?". "A'a Abbah". Ta fa?a kanta a ?asa. "To miyasa kikeson a fasa?". "Abbah banason rabuwa daku nidai".
Murmushi Abbah yayi tare da sauke ajiyar zuciya, "To ai ba rabuwa zakiyi damuba Nu'aymah, kuma shima Abdallah ai ?an uwankine mai gatantaki ma fiye da kowa a gidan nan, duk kuma sanda kikeso ya kawoki wajenmu zai kawoki". Idanunta cike da kwalla ta kalli Abbah, "To Abbah ina zai samu ku?in jirgi yayta kawoni kullum tun daga Saudia?". "To ai dama ba kullum ba Mamana, keda zakiyi karatu tayaya za'ace za'a kawoki gida kullum koda anan zaku zauna ma. Duk dai sanda kuka sami hutu sai ya kawoki, kuma muma zamu dinga zuwa ganinku ai ko". Shiru tai batace komaiba, sai hawaye keta sake mata zarya.
Cikin hikima da wayo Abbah da Umm sukaita mata nasiha da ?ara ?arfafa mata gwiwa harta daina kuka ta koma dariya kamar ba ita ba, kusan awarta ?aya da rabi a wajensu sannan ta tafi kiran da hajjo ta aiko Farida tai mata.
Tafiya take tana ?un?unin haushin Hajjo, dan tasan kiran datai mata bai wuci sakata shiga cikin ruwan lalle ba, itako ta tsani abun dan ?yan?yami takeyi, amma jarabar kakar tasu bazai bari ta fito ta fa?a ba.
Gabanta ne ya fa?i jin an kamo hannunta, ta juyo a firgice zata wage baki tai ihu aka rufe bakin.
Cikin muryarsa mai sanyi da nutsuwa yace, "Matsoraciya nine. Na gaji da wasan ?uyar da kikeyi dani malama".
Ajiyar zuciya Nu'aymah ta sauke jin Yah Abdallah ne, ya saketa yana cigaba da ?awata fuskarsa da murmushi da ?are mata kallo daga sama har ?asa. "Saboda kinsan kin sake ha?uwa fiye da da shiyyasa kiketa faman ?oyemin kanki ko?".
Hannu Nu'aymah tasa ta rufe fuskarta da shi tana murmushi, "Yah Ab banfa san kazo ba".
"Kutt!". Ya fa?a yana zaro idanu waje, "Wato bama kisan nazoba?". Kai ta jinjina masa da ?yal?yalewa da dariya.
"Lallai yarinya na yarda kin girma kam, idan ba tsoroba bu?e fuskar ki fa?amin ido da ido mana". "A'a ai basai na bu?eba tunda dai kaji na farko". "Hahyh! Zaki min bayani gobe idan ALLAH ya kaimu ai".
Kasa cemasa komai tai a kan hakan, saima ta risina kawai ta gaidashi. Ya amsa mata cike da kulawa idanunsa na cigaba da yawo a jikinta, duk da akwai ?aramin hijjabi tare da ita, rayawa kawai yake a ransa 'anya baiyi gangancin ?aukar alwashin rinon Nu'aymah ba kuwa? Kai da sakel wai anbama mai kaza kai'.......
"Yah Ab bara naje hajjo ke kirana".
Maganarta ta dawo dashi hayyacinsa. Ajiyar zuciya ya sauke da?an kallon gefensu, sai kuma ya kalleta sosai yana gyara tsaiwarsa. "Babie kinga manta da tsohuwar can kinji, musamu guri mu zauna mu?an zanta na yaushe gamo, ke koma ?okin ganina ba?yayi bayan kuma shekara biyu kenan baki ko ganniba".
Murmushi tayi tana ?an kallonsa ta gefen ido, a ranta godiya takema ALLAH daya mallaka mata Yah Ab matsayin masoyi, gobe idan