Showing 54001 words to 57000 words out of 325075 words
?in sanye da rigar wanka Blue, sai hular wanka data kare gashinsa daga ji?ewa, da alama dai baya bu?atar ji?awar. A bakin gadon ya zauna yana mai furzar da iskar daya cika bakinsa da ita, yajawo wayarsa dake a drowar gefen gadon a jiye ya cireta a silent. Dan ya sakata a silent ?inne tun lokacin dazai shiga theatre room. Solomon ya kira, sai akai rashin sa'a ya samu wayarsa a busy.
Kume fuska ya sakeyi alamar baiso hakanba, ya ajiye wayar. ?ayar ya ?auka itama ya cireta a plane mode daya sakata. Kamar jira ake ya cire ?in sai ga kira ya shigo, kafin ya amsa kuma akai knocking ?ofar. Rasa wanne zai farayi yayi. ?aga wayar? Kokuwa bu?e ?ofar?.
"Yoohan!" ya tsinkayi muryar Richard na kiransa. Duk da yayi tunanin akan maganar patients ?in da Rich ?in yay maganar zai dubane hakan bai hanashi tashi ya bu?e masa ?ofaba, sai dai ya sake ha?e fuska alamar da gaske ya gaji baison takura.
Yana bu?e ?ofar yace, "Rich plea....."
Saurin katsesa Richard yay da fa?in, "Yi ha?uri ba wancan maganar bane, akwai damuwa Yoohan, matar da kaima aiki a kano yanzun nan Doctor Sa'ad ke sanar min an samu matsala".
"What?!" ya fa?a hankali tashe. Shima Richard da hankalin nasa ke a tashe ya shiga jinjina masa kai. Juyawa cikin ?akin yay da sauri, yama manta da wata gajiyarsa. Wayarsa ya ?auka domin neman Dr Sa'ad. Ganin ashe shinema ya kirasa ?azun lokacin da Richard ke knocking ya sakashi kiransa. Bugu ?aya kuwa Dr Sa'ad ?in ya ?aga.
Ko gaisuwa basuyi zaman yiba Dr Sa'ad ya shiga masa bayanin dukan abinda ya faru, da halin da matar ke a ciki yanzun.
Hannunsa dafe da kansa cikin tsagwaron damuwa yace, "Dr Sa'ad ta yaya hakan ta faru? Ince duk yanda ya kamata a bata kulawa na sanar muku. Miyasa kuke da sakaci akan rayukan mutane!!?" ya ?are maganar da ?an kaushin murya.
Dr Sa'ad da maganar Dr Yoohan tai masa zafi ya bu?e baki zaiyi magana cikin ?o?arin danne fushinsa, amma sai Yoohan ?in ya kuma dakatar dashi ta hanyar fa?in, "Bana bu?atar jin komai please, zan turo maka hanyar da zakubi wajen fara bata taimako yanzun, nima ina hanyar tahowa".
"Okay Sir" Dr Sa'ad ya amsa masa daga can cikin wata irin murya mai cike da ?aci da takaici. Yaro ?arami dashi yana juyasu dan kawai ALLAH ya basa baiwar da tafi tasu, tabbas idan ba kawar da Dr Yoohan sukaiba a duniya rayukansu da hanyar cin abinsu na a cikin garari.
(Ni dai nace Humm).
Shi Yoohan baima saurari amsawar Dr Sa'ad ?inba, dan tuni yayi wurgi da wayar saman gado cike da takaicin likitoci irin Dr Sa'ad, da a kullum basu da kishin ?asarsu da jama'arsu, burinsu sudai ku?i kawai da ta?ama da aikinsu. Da hanzarinsa ya fito ainhin Office ?in yana fa?in, "Rich Please ka bincika min idan akwai jirgi mai tafiya kano daga nan zuwa mintuna talatin".
Da sauri Richard ya fita daga office ?in zuwa nasa, dan yabar wayarsa a canne. Shi kuma Dr Yoohan yaja Laptop ?insa dake saman tebirin daga tsaye ya shiga dannata da sauri sauri cikin ?warewa. A haka Solomon ya shigo ya samesa, batare daya tsayaba yay saurin shigewa bedroom ?in domin fidda masa kayan da zai saka dan Richard ya sanar masa halin da ake ciki, kuma shi Dr Sa'ad ya fara samu a waya kafin Richard ma.
Dr Yoohan na kammala tura abinda zai aikama Dr Sa'ad ya nufi ?akin shima. bai wani damu da tsayawa duba kayan da Solomon ya ajiye masanba ya ?auka ya fara ?o?arin sakawa, shi kuma Solomon ya fito ya bashi waje.
Shirin yake ransa duk a jagule da takaici, yana kammalawa ya fito jacket ?in suit ?insa a hannu, necktie ?inma haka. Gashinsa kansa yau sama-sama ya samu gyara. Haka yake shi, a kullum matsalar al'umma itace tashin hankalinsa da damuwarsa. Da kaga damuwa a idanunsa to patient ?insa na cikin matsala ne. Baiko kalli inda Solomon ke tsaye da jikkarsa a hannuba ya nufi hanyar fita fuskarnan babu alamar wasa.
Kusan cin karo sukai da Richard dake ?o?arin shigowa ya sanar masa an samu jirgi, kuma cikin amincin ALLAH zai tashi nan da mintuna goma sha bakwai ne, da ?yar akama samu ticket ?in guda biyu. A yanda Dr Yoohan yasan garin Lagos da yammaci irin haka yasan kafin su isa airport ma lokacin tashin jirgin ma ya wuce, dan haka ya yanke shawarar su tafi a Ambulance kawai zasufi samun hanya da sauri.
Rich kansa yayi na'am da wannan tunanin na Yoohan, dan haka yama yanke shawarar kaisu da kansa ko Yoohan ?in zai kuma samun nutsuwa.............?
_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????
Mamu gee??
MIN ?ALB!!????
Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????
Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????
Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????
?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.
??.________________________
*ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE*
*_KAJI shahararrun kuma mandiyoyin ?an ?walisar kawo kayan kitchen masu tafiya dai-dai da zamani. Idan nace nadaban ina nufin su?in nadabanne wajen kaya ?an gaske dake ?awata kitchen ?in amarya harma dana uwargida ?ar ?walisa. Ka siya ka tabbatar ka saya ?in ko a gaban tsaranka sai ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. sunan kayansu sa kishiya cin bashi??, dan tana ?yalla ido taga kitchen ?inki tsarin amerikawa tuni zata fara ?wafa da tunanin zuwa gidan delu dillaliliya mai saida kwanika. Sai dai kuma kama da wane akace bata wane, dan haka ku maza ku garzaya ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. domin samun naku kuma. Suna kawo kaya daga ?asashen ?etare akan farashi mai sau?i da rahusa. Suna order ?in products kamarsu, dukan kayan kitchen na zamani, bedsheets, shoes dade sauransu, products ?insu pre-order ne dake zuwa akan lokaci batare da mai kaya ya ?osa da jira ba ko samun matsala. Zaku iya samunsu a Number waya kamar haka ko Location nasu. Phone number: 08102393622. Location Gombe. Amma Zasu iya turawa kowani gari dake a lungu da sa?o na ?asarnan. Sayen nagari maida ku?i gida. Ku garzaya kar ayi babu ku. Da ?yar nasha yafi da ?yar aka kamani inji masu iya magana??????????._*
_______________________________
15
.................Ka?an ya rage su makara a hanyar zuwa airport, ALLAH dai ya taimakesu suka isa gab. Sai da Richard ya ga tashin jirgin sannan ya bar Airport ?in yana mai kiran Dr Sa'ad ya sanar masa ga Dr Yoohan nan ya taho su kwantar da hankalinsu.
Duk da Dr Sa'ad baiso hakanba sai ya amsa masa harda addu'ar isowarsu lafiya. A ?asan ransa kam ji yake kamar zuciyarsa zata babbake da wuta dan takaici da tsanar Dr Yoohan ?in da bai ta?a tare masa komai a duniyaba bayan nusar dashi ya san kansa kawai.
Yana sauke wayar daga kunnensa kiran Madam Chioma na shigowa. ?agawa yay da hanzarinsa, dan yasan dai bai wuce ta kira Number Yoohan ?in bata shigaba ko bai ?agaba. Ya gaidata cikin girmamawa kamar yanda ya saba, kafin ya ?ora da fa?in, "Mom lafiya dai ko?". Daga can tace, "Eh Richard, lafiya, amma na kira abokinka sau uku bai ?agaba, nayi zaton ko yana akan aikine idan ya kammala zai kirani, sai dai har yanzu banga kiransaba. Na kuma nemesa yanzu da kaina wayarsa bai tafiya. Shine nace ko lafiya?".
Murmushi yay yana ?ara jinjina ?aunar wannan uwa da ?a a zuciyarsa. Cike da kulawa yay mata bayani yanda zata fahimta, sai dai yanda tai azamar katsesa jin ya ambaci kano sai abin ya nema firgitashi. Kafin ya samu damar tambayarta dalili harta yanke kiran.
*_ABUJA_*
Hankalin Madam Chioma a tashe tai kiran Guards ?in Yoohan dake shirin tahowa da Nu'aymah Abuja. Cikin azalzala ta sanar musu karsu taho su ajiye Nu'aymah a police station ?in maza su nufi airport su tarbi Yoohan gashi nan ya taho da ga Lagos. Tai mugun basu garga?i akan inhar wani abu mara ?yau suka bari ya faru da Yoohan ?in yau to su tabbatar a bakin aikinsu kenan, bayan horo mai tsanani da zasu fuskanta kuma.
Sanin Madam Chioma zata aikata fiye da abinda ta fa?a inhar akan Yoohan ne ya saka guards ?in Yoohan bin dukkan umarninta. Har an fito da Nu'aymah da ko harara babu wanda yay mata a station ?in, hasalima tana a office ?in d.p.o tunda aka kawota suka sanarma d.p.o halin da ake ciki game da umarnin mahaifiyar uban gidansu.
Babu musu ya amince da ajiye Nu'aymah har suje su dawo, su kuma suka shiga motocinsu suka bar station ?in zuwa airport ?akko Dr Yoohan da suka san nanda mintuna ?alilan ne jirginsu zai sauka.
Murmushi Nu'aymah tayi tana mai bu?e tafin hannunta ta kalli ?ar takardar da baba malam ya saka mata lokacin daya kamo hannunta. Takardar ta sake bu?ewa ta karanta addu'ar dake ciki tana murmushi, wata irin ?aunar mahaifinta da tausayinsa na ratsata a zuciya da ?argo. A yau ta ?arajin ?warin gwiwa akan shirin mahaifin nata. Wanda daga ita sai shi sai ALLAH daya hallicesu sukasan da shirin. Amma ko Umm yaja mata garga?i mai ?arfi akan karta bari ta sani, bakomai yasashi yin hakanba sai wani dalilinsa da itama yace ba yanzu zai sanar mataba sai nan gaba.
______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Wannan littafi SARAN ?OYE na ku?ine, yana ?aya daga zafafa biyar, idan kana bu?ata kaima wa?anan numbers ?in magana ka biya ku?insa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka ya?a dan ALLAH idan ka gani??????.
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
______________________¡ï
Gaba ?aya Yoohan ji yake kamarma jirgin baya wani sauri, duk bayan mintuna sai ya kalli agogon hannunsa yayi ?aramin tsaki da Solomon ne kawai ke jinsa, yay masifar ?osawa yaga sun sauka. A yanda hankalinsa ke a tashe har sai da Solomon yaji tausayinsa ya kamasa. Yana mamakin yanda Dr Yoohan sam babu wani ?yashi ko ?abilanci a ransa, game da aikinsa bai ta?a banbanta kai ?an wane addini bane ko kai ?an wane yankine. Kansa tsaye yake ?o?arin sa, shiyyasa a kullum ALLAH ke sake ?aukaka darajarsa, dan kullum bayin ALLAH cikin masa addu'oi suke a zahiri da ba?inin zuciya.
Duk da burinsa nason jirgin yay saurin sauka ahakan bai hanashi fita cikin nutsuwa ba lokacin da jirgin ya ta?a ?asa. Yanda yake tafiya kawai ya isa abin kallo ga mutane. Duk da fuskarsa kullum a cinkushe take hakan bai hana ya ?auki hankalin masu kallonsa daga maza har mata ba.
"Welcome sir". Yaji an fa?a Lokacin da suke isowa wajen masu taxi shi da Solomon dake a bayansa. Kamar zai share sai kuma dai ya juya. A bazata idanunsa suka sauka akan guards ?insa wa?anda baiyi zato ko tsammanin ganiba.
Da sauri suka ?araso gabansa zuciyarsu na dukan ?ari-?ari ganin kallon da yake musu na tsagwaron mamaki da tuhuma, cike da girmamawa suka shiga gaishesa ?aya bayan ?aya, kafin su ?ora da masa bayanin Mom ce tace suzo su tarbesa.
Duk da akwai magana a bakinsa game da ganin nasu a kano sai ya share bai yiba. Ya nufi inda ?aya daga cikinsu ya bu?e masa mota ya shiga.
Sai da suka fito da ga airport ?in gaba ?aya suka hau kan titi sannan ya jefama driver da Solomon ke kusa da shi tambaya a bazata.
Cikin harshen nasara yace, "Miya kawoku kano?". Cikin fa?uwar gaba driver ya kallesa ta madubi. Sam bama kallonsu yake ba, hankalinsa nakan waya yana dannawa. Cikin ?an rawan baki na rashin gaskiya driver ya bashi amsa da fa?in, "Sir M... Madam ce ta aikomu". "Yin me?".Yoohan ya fa?a da ?ago fararen idanunsa ya zubama drivern cike da nazari. Sosai kallon ya firgitashi, dan anyi sa'a lokacin da Yoohan ?in ya ?ago idanu yayi dai-dai da ?agowar driver shima ya kallesa.
Saurin ri?e sitiyarin yayi jin zai ?wace masa, dan har motar sai da tayi ?an tanga?i ka?an. "I am sorry sir" driver ya fa?a da sauri ?irjinsa na dukan tara-tara ganin yana neman zubar dasu a ?asa. Shiru Yoohan bai tanka ba, hasalima ya ?auke kansa tamkar baiga wani abu daya faru ba. Sai ma ya ?auka waya yay kiran Dr Sa'ad da kai hannu saman kunnensa ya gyara Bluetooth ?insa na fama dake a ma?ale.
Solomon da duk ya fahinci akwai wani abu dangane da zuwan ?an uwanasa kanon ya ha?iye yawu da ?yar shima yana satar kallon madubin, ganin hankalin Yoohan ?in baya garesu sai yay saurin maidawa ga drivern. ?yaftama juna idanu sukai, alamar dai sun saba da yaran. Solomon ya ?an gya?a kansa yana gyara zama.
A haka suka isa asibitin batare da kowa ya sake magana ba. Tun kafin a bu?e masa shi harma ya bu?e ya fice abinsa. Da yake yau zuwan bazatane Dr Sa'ad kawai ya san zaizo sai Dr Aysha, sauran Doctors ?in basu fito sun tarbesa ba kamar yanda suka saba.
Sai dai tun shigowar motocinsa wasu daga ma'aikatan asibitin suka fahimci shine. Yayin da gefe guda kuma da ya zama abin kallo ga mutane. Musamman ma yanda yake tafiya Guards ?insa na take masa baya. Wa?anda suka sanshi nata fa?in, "Dr Yoohan yay zuwan bazata, yaukam za'asha masifa musamman akan ma'aikatan dakeda sakaci akan aikinsu.
Duk da ya fahimci yanda wasu a cikin ma'aikatan ke ta guje-gujen sanarma iyayen gidansu zuwansa basuko ishesa kalloba. dan abinda ya kawosa shine kawai a gabansa ba su da shirmensu ba.
Tunda su Solomon sukaga shigewarsa sai yaja hannun ?aya daga cikin Guards ?in suka fito, sauran kuwa na tsaye ?i?am tamkar an dasasu gadin duniya????, sai zazzare idanu suke sun hana masu kai kawo ta wajen sukuni. Ba marasa lafiya da ?an uwansu kawaiba, hatta ma'aikatan asibitin a takure suke. Masu sanya da aikinsu duka sun dage saboda jin zuwan Dr Yoohan. (ALLAH ya ?yauta. Bazakaji tsoron UBANGIJIN daya halicceka ya baka amanar wannan aikin a ranka ba sai wani shasha mutum irinka, ba kuma komai ke kawo tsoronsa ba sai gudun karka rasa aikinka????, ya salam. Musulmai ina muka ajiye gaskiyar tamu? Ina muka ajiye koyarwar addinin namu? Ina muka ajiye tausayi dajin ?an da aka san mumini da shi?. Ku dubafa Dr Yoohan ba musulmi bane, ba?an yankinku bane, ba yarenku bane? Amma yana nuna fushinsa akan sakaci da cigabanku, yana nuna damuwarsa akan ?an uwanku, yarenku addininku, yayinda ku son zuciya da burin tara duniya ya rufe jinku da ganinku. Kaje asibiti kaga ana wula?anta marasa ?arfi dan kawai sunzo neman lafiya. Babban abin takaicinma yafi yawa a ?angaren mata masu haihuwa. Kaga ma'aikatan asibiti nacin zarafinsu dan kawai sun kasance ?auyawa ko talakawa. Haba ?an uwana, wannan aikinfa da kike cin zarafin wasu dashi tamkar mabu?ine na gida guda biyu. Wuta ko aljannah, ya rage naki/nak ka za?ama kanka wanda kafi bu?ata. ALLAH ya shiryar damu dai, ya rabbi kai ri?o da hannun ma'aikatanmu masu ?yawawan zukata domin rahamarka da alfarmarka??????).
__________________________
Tunda Addah ta isko Umm a ?aki basu iya cema juna uffan ba. Kowa ya zabga uban tagumi ne yana sa?a mai fishshesa. Sun kwashi tsahon mintuna sha biyar a haka kafin Addah ta katse shirun nasu da fa?in, "Ni nama rasa abin fa?a wlhy akan wannan al'amari, har nawa Nu'aymah take da ?an sanda zasuzo su tafi da ita? Mi ma to tayi musu? Sannan miyasa yaya malam zai yanke wannan hukuncin mai tauri haka?".
"Wannan sune tambayoyin da nake taima zuciyata Addah, amma sam na gaza samo amsar ko guda a ciki. Ina ?yautata zaton a tafiyarsu bikin nan koma miye ya faru acan ya faru, dan........"
"Haba Umm miyasa zakice haka? Naga dai su a cikin Orphanage suke? To mima zata aikata da har ace mu bamujisa ba?".
"Addah yaran nan kafa