Showing 111001 words to 114000 words out of 325075 words

Chapter 38 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29120

zunubanka damu baki ?aya".
A tare suka sake amsawa da amin.

__________¡ï¡ï¡ï¡ï__________

A hotel kam hankalin su Solomon a matu?ar tashe yake da rashin ganin Yoohan. Gaba ?aya sun tada hankalin ma'aikatan hotel ?in da barazanarsu. Saboda maigadi ya tabbatar shi baiga fitar Yoohan ba. Hakama wanda yake a reception yace baiga fitarsa ba. Ga kuma motocinsu duk suna ajiye alamar Yoohan bai fitaba a fahimtarsu.
Ganin ?aramar magana na neman zama babba Solomon ya kira papa ya sanar masa halin da ake ciki. Cikin matsanancin tashin hankali papa yace su kira layin Yoohan ?in mana.
"Sir! Duk wayoyinsa na nan cikin ?akin, shiyyasama muka fahimci bada kansa ya fitaba kenan". Solomon da jikinsa har tsuma yake ya bama papa amsa murya na rawa. Wata wawiyar tsawa papa ya sake daka masa daga can, tare da sakin wani irin ihu tamkar zai fasa gidan.
"Solo!!!!!! Inhar yarona ya shiga wani hali na rantse muku da ALLAH duk sai na kasheku da hannuna, na baku awa biyar kacal akan nemansa. Idan har kuka bari na iso kano kuyi kuka da kanku!!...."
?it ya yanke wayar batare da ya bari Solo yay ko ?wa?waran numfashi ba.

Sosai hankalin Solomon ya sake ?ololuwar tashi, hakama na sauran ?an uwansa. Dan sunsan wanene Pastor Goshpower, sun san kuma abinda zai iyayi, musamman ma akan Yoohan da duk duniya bai ha?a sonshi dana kowa ba.
Suna cikin tashin hankali da tararrabin mafita sai ga ?an sanda kusan mota uku sun iso hotel ?in bisa jagorancin D.p.o Emanuel.
Su masu hotel babban tashin hankalinsu kar sunansu ya ?aci. suko su Solomon sune sukasan babban tashin hankalin da zai iya samunsu da su kansu masu hotel ?in indai har ta tabbata anyi kidnapping ?in Yoohan a hotel ?in ne, kamar yanda kowa yake tunani da hasashe.............?
[5/18, 3:08 PM] Ummuanwar??: *_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.



No. 30

................Lokacinda su Solomon ke acan cikin tashin hankalin tsoron cikar lokacin da papa ya basu akan sanin inda Yoohan yake, shi yana nan suna shirin tafiya massallacin juma'a shi da su baba malam.
Kowa ya kalli baba malam ?in a yau zai fahimci yana cike da tsantsar farin ciki. A cikin nisha?in daya shiga da shi cikin gidan nasa ya sake fitowa shi da Umm data taimaka masa yay shirin massallaci.
?ar tsokanar da ya kema Umm yasa Nu'aymah dake zaune a falon tana gyaran fruit ?in da Umm ta sakata ?agowa tana kallonsu. Cikin washe baki tace, "Abbah yau dai kana cikin farin ciki ALLAH, naga tun safe fuskarka sai annuri takeyi".
Da ga Umm har baba malam dariya sukayi, ya matsa kusa da ita tare da kai hannu ya shafa kanta. "Tabbas yau ina cikin farin ciki mamana, saboda wannan farin cikin yau har ?yauta ta musamman na shirya miki ke da Muhammad, dan haka kafin na dawo ki shirya fa?a mini abinda kike so".
Sosai farin ciki ya sake kamata. Ta shiga jera masa godiya da addu'ar fatan dawowa lafiya. Daga shi har Umm amsa mata suke cike da kulawa. Kowannensu najinta a ransa sosai, dan daga Umm har Baba malam ba ?aramin so sukema Nu'aymah ba. Suna dannewane kawai saboda ?arfafama kansu tarbiyarta. Ga ?unbin tausayinta dake mamaye da ruhinsu game da matsalarta. Dan har yau da muke ?in nan baba malam bai gajiya ba wajen cigaba da neman likitan nan, yana kuma gayama UBANGIJI da neman taimakonsa a kowane da?i?a.

Bayan Umm tama baba malam rakkiya ta dawo. A inda tabar Nu'aymah nan ta sake isketa tana ?alular gyara fruit ?in.
"Nikam naga takaina da wannan hali naki Nu'aymah! Mutum yayta abu sanyi-sanyi tamkar bazai ?aresa ba. Yanzu maimakon ki zauna kiyi aikin nan a kitchen shine kika taho nan kuma dan salon neman ?ata guri?".
Baki ta tura gaba tana ?ata fuska, "Yoni Umm idanfa na zauna a kitchen wlhy Rabi damuna zatayi da surutun ta, kin sani dai ko redio haka ta ganta ta ?yale akan zanc........"
Bammm!. Umm ta make mata baki, hakanne ya hanata ?arasa fa?a. Da sauri ta saki wu?ar hannun nata hawaye na taruwa mata a ido. Umm dake hararta tace, "Saunawa zan fa?a miki karna sake jin wannan maganar banzan a bakinki Nu'aymah? Rabi bata girmeki ba? K wai yaushe ne zaki bar tsiwa da rashin kunya? Ita?in sa'arki ce?".
"Kiyi ha?uri Umm bazan sakeba ALLAH ".
"Kima sake mana, mara wayau kawai". Umm ta fa?a tana hararta da barin wajen. Harta kusa ?ofar sashen baba malam ta juyo. "Kiyi ki tashi a wajen nan kuma kafin na fito, ga man-shanu can a kitchen ki ?auka ki kaima Addah, kuma idan kinje ki zauna shiririta karki dawo ki ?arasa aikin dana sakaki kinji ko".
Sake ?ata fuska Nu'aymah tayi hawaye na zirara mata. Sai dai batace komaiba har Umm ta shige ciki. Dan zuciyar gadon tazo mata wuya.

Duk yanda Umm tace tayi haka tayi, sai dai data shiga kitchen Rabi tasha harara, dan a ganinta saboda itane Umm ta Mammangare ta. oho ita batama san tanaiba, dan aikinta takeyi koda ta shigo bama ta kalli inda Nu'aymahn takeba tunda tasan basa doguwar magana lafiya sai sunyi fa?a.
Manshanun ta ?auka zuwa sashen Addah. Sai da tai sallama kusan sau uku kafin a amsa mata ciki-ciki. Bata damuba ta shige tana ?aure fuska dan har yanzu akwai haushin fa?an Umm tare da ita. Kubrah kawai ta iske zaune a falon, tunkan ta ?araso ciki take jefo mata harara.
Jitai kamar ta juya dan haushi, amma sai ta daure ta ?arasa da fa?in, "Aunty Kubrah Umm ce ta aikoni wajen Addah?".
Banza tai mata tamkar bata jitaba, har Nu'aymah ta fara yanke shawarar juyawa sai ga Hajarah ta fito daga ?akinsu hannunta ?auke da Al-qur'ani.
"A'a Aymah ce a wajen namu?".
Ajiyar zuciya Nu'aymah tayi da maida kallonta gareta. Fuskarta da ?an damuwa tace, "Aunty Hajarah Umm ce ta aikoni wajen Addah. Amma ina tambayar Aunty Kubrah tamin banz....."
Kafin ta ?arasa taji saukar duka a bakinta, Kubrah da tai dukan ta nunata da yatsa cikin magana ?asa-?asa tace, "K dan uwarki ni sa'arki ce ko?".
"Kai haba Aunty Kubrah daga tambaya, yanzu dan ALLAH mita miki zaki dakar mata baki? Minene abin laifi anan to?". Hajarah ce mai maganar dai-dai tana ?arasowa inda suke ta kama hannun Nu'aymah dake hawaye, dama bakin bai gama mata zafiba akan dukan da Umm tai masa yanzu. Ga kuma Kubrah ta ?ara mata wani.
Cikin masifa Kubrah ta kalli Hajarah, "Kozaki rama mata ne?".
"Bazan rama mata ba, amma ALLAH zai saka mata. Tunda duk wanda ya zalinci wani ALLAH na kallonsa. Nu'aymah jeki Addahn na ?akinta kinji ko".
Kai Nu'aymah ta ?agama Hajarah tana share hawayenta. Batare datace komaiba ta nufi ?akin Addah zuciyarta na mamakin yanda Aunty Kubrah kejin zafinta a ?an kwanakin nan, duk da dai dama ita babu wani sha?uwa sosai tsakaninta da ita tun da can. Sai dai bata ta?a nuna mata banzan hali irin na wannan karonba. Tana gab da shiga ta tsinkayo muryar Kubrah na fa?in, "?ar iskar yarinya ki taka a sannu dan a tafin hannuna kike wlhy, inba hakaba saina tona asirin iskancinki a gaban kowa yasani a gidan nan".
Sosai gaban Nu'aymah yay bala'in fa?uwa, dan tasan inhar Kubrah ta fa?i abinda ta gani tsakaninta da Yoohan ranar tata ta ?are. Da ?yar ta iya ha?iye kukan daya taho mata.
Da mamaki Hajarah ta kalli Kubrah, "Haba Aunty Kubrah wace irin maganace haka? Wai nikam minene ya ha?aki da Nu'aymah mai zafi a kwanakin nan dan ALLAH?".
"Ki sha?eni in fa?a miki mana". Kubrahn ta fa?a a harzu?e.
"ALLAH ya baki ha?uri". Hajarah ta fa?a tana barmata wajen ranta fal tunane-tunane kala-kala akan ?ar tsamar yayar tata da Nu'aymah data gaza fahimtar tushenta a kwanakin nan sam.

Sai da Nu'aymah tai sallama Addah ta bata izinin shiga sannan ta shiga ?akin. Tsaye ta isketa tana ninke abin salla alamar sallar ta idar. Ganin Nu'aymah na sharar hawaye yasa fara'ar fuskar Addah gushewa lokaci guda. "Lafiya Nu'aymah? mi akai miki?".
"Babu komai Addah, Umm ce tace na kawo miki wannan".
Sam Addah bata yarda da maganar Nu'aymah ba, dan haka tai shiru tana cigaba da kallonta kawai batare data amshi man-shanun ba. "Nu'aymah bana son shirme, fa?amin gaskiya mi akai miki?".
"Addah wlhy aunty Kubrah ce ta dakar mata baki dan hawai tacemin ta tambayeta kina ina ta mata banza". Hajarah dake shigowa ?akin ta bama Addah amsa.
Cikin ?acin rai Addah tace, "Kubrah?!".
"Eh wlhy Addah, ni bama dukan ya ?atan rai ba, bakiji yanda take fa?ama Nu'aymahr maganar banza ba. A kwanakin nan dama na kula tana matsama yarinyar nan a gidan nan, haka ?azun a islamiyyar asuba dan kawai Nu'aymah ta fiddo Fahad ?in maman Sadiya daga aji saboda suna fa?a da wani yaro wlhy bakiga abinda tai mataba. Alhalin baikamata taima Nu'aymahn maganaba tunda yaran duk ?an ajintane, ta fita sanin halin kowa a cikinsu".
Kama hannun Nu'aymah Addah tayi suka fito ranta a ?ace. Hakan yasa Hajarah biyo bayansu da sauri itama.
"Kubrah!!". Addah ta ?wala mata kira ganin bata a falon.
Da sauri ta fito daga kitchen hannunta ?auke da plate ?in abinci.
"Ubanmi Nu'aymah tai miki kika daketa?!".
Sake tsuke fuska Kubrah tayi, ta kalli Nu'aymah data du?ar da kai tana hawaye har yanzun. Wani ?an murmushin mugunta tayi kafin ta kalli Addahn. "Addah catai na daketa?".
"Ni na fa?a ba ita ta fa?aba, tunda a gabana akai komai". Hajarah ta bata amsa kafin Addah tai magana.
"Mtsooow!! Munafuka kawai. Addah ni ban daketa haka kawaiba, rashin kunya zataimin shiyyasa........"
"To amma shine zaki ce mata ?ar iska, kuma sirrinta a tafin hannunki yake. Idan kinso zaki tona mata asiri agaban kowa".
"Wlhy Hajarah zan sauya miki kamanni, wai ni sa'ar wasanki ce?".

"Kai!! Ya isheni haka, banason rashin mutunci. Bazan ?auki wannan wawancinba kunji na fa?a muku. Shin ku?in yaran goye ne da kullum baku da wani buri sai na samin ciwon kai? Kusani daga yau na sakejin makamancin wannan banzan al'amarin wlhy sainayi ?ololuwar ?atama mutum rai a gidannan. Banda k kullum girma kike kinacin ?asa Nu'aymah ce kuma ta zama abar tozartawarki Kubrah? To daga yau na ji wani abu ya sake fitowa makamancin wannan zakiyi nadama a gidannan kinji na fa?a miki". Ta ?are maganar da matu?ar zafin rai tana sake yima Kubrah garga?i da hannu.
Sai kuma ta juya ga Nu'aymah dake sauke ajiyar zuciya a jajjere. "Nu'aymah jeki wanke fuskarki kinji kuma kar naji wannan maganar a wani waje, kiyi ha?uri".
Kai Nu'aymah ta jinjinama Addah, babu musu ta shiga toilet ?in dake a falon ta wanke fuskarta ta fito. sallma tai musu ta fice batare data sake yarda ta kalli sashin da Kubrah take ba. Harga ALLAH hankalinta a tashe yake matu?a da kalaman Kubrah.
Koda ta koma sashensu ?akinta ta shige ta shiga raira kuka, Nu'aymah yarinyace da bata da tsoro sam. Amma yanda tai matu?ar damuwa da faruwar abin nan na jiya daya kasa barin ransta saita baka tausayi. Tasan tabbas wannan laifin na jiya yasha banban da kowane irin laifi, kuma duk wanda zaiji abinda ya farun sai yayi ALLAH wadai da ita, ?ilama baba Malam da Umm su tsine mata albarka.
Sake rushewa tai da kuka kamar zata shi?e wajen jan zuciya. A haka ta tsinkayo muryar Umm na ?wala mata kira. Da sauri ta mi?e ta shiga share hawayen, harta nufi ?ofar fita sai kuma tai saurin dawowa. Toilet ta shiga ta sake wanke fuska tazo gaban mirror tasa hoda da kwalli sannan ta fita.
Zaune ta iske baba malam da Umm a falo. Cikin raunin murya taima baba malam sannu da dawowa. Duk kallonta sukai shi da Umm, baba malam yace, "Lafiya kuwa? Naga idonki kamar wadda tai kuka? Mamana!".
Kafin tayi magana Umm dake hararta tace, "Saboda namata fa?a akan rashin kunyar data iya". (dan ita tazata fa?an datai matane ya sakata fushi har yanzun).
Baba malam baice komaiba sai maida kansa da yay ga tv kawai. Fuska a ?aure Umm ta nuna mata trayn dake a kan centre table. "Ki ?auka ki kaima ba?o a falon baba".
Kai kawai ta jinjina mata ta koma ?akinta ta ?akko hijjab. Batare datai maganaba ta ?auka tiren ta fice. Sai da ta fice gaba ?aya sannan baba malam ya ?auke kansa daga kallonta. maidawa yayi ga Umm da itama take kallon nata.
"Addu'a ya kamata ki cigaba da mata bawai nuna fushinki da zafi fiye da kima ba. Har yanzu Nu'aymah yariyace ?arama, sannan kinsan lalurar dake tare da ita sam bata bu?atar yawan takura. Ki fahimci ita wannan tsiwar itace tata ?uruciyar".
"Amma Malam ka tunafa ?a mace ce ita. Gidan wani fa zataje. Bandama ?addara daba yanzu tana ?akin miji ba. Wlhy sam bana son tsiwarnan tata, bansan a ina ta kwaso wannan banzan halinba nikam".
Murmushi baba malam yayi yana mi?ewa, "To ayi ha?uri zata daina insha ALLAH, nima zan zauna da ita anjima ALLAH ya huci zuciyarki".
Yanda yay maganarne ya saka Umm yin murmushi, dan ta sake tabbatarwa yau mijin nata yana cike da nisha?i sosai kam, musamman data san yafi kowa ?in jinin tsiwar ?iyar tasu.

¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï

Murya a sanyaye tai sallama a ?ofar falon har kusan sau uku. jin shiru ba'a amsaba ya sakata tura kanta ciki da haushi. Takaicin rashin amsa mata sallamar da ba'ayiba ne ya sakata ?in kallon ba?on ma balle tasan wanene.
A gabansa ta dangwarar da trayn, murya a cinkushe batare data kallesa ba tace, "Ina yini".
Shiru yanzuma ba'a amsaba, wani sabon takaicin ya sake lullu?e ta. Har tayi niyyar dubansa ta sauke masa takaicinta saita tuna yanzufa Umm ta gama mata fa?a harda duka akan tsiwa, sannan kuma bai kamatama tayi wani abun rashin hankali ba tunda batasan wanene ba?on nasu ba. Zata iya yuwuwa babban mutumne sa'an baba malam ko cikin yayunta. Ha?iye haushinta tai ta nufi hanyar fita zata bar falon.
Yoohan da tun shigowarta idonsa nakan wani littafi da baba malam ya bashi ya duba ya ?an ?ago kansa dan sam baiji sallamarta ba balle shigowartaba ma shi, sai gilmawarta kawai ya gani yanzu da take ?o?arin fita. Cikin tsautsayi ta bigi ?aramar jakkar dake gefensa da ?afa. baya tai taga-taga zata fa?i cikin sa'a yay saurin saka mata ?afa dan son kareta bisa tsautsayi sai gata a cinyarsa ?are-?are.
Duk da ya canja kayan jikinsa mayataccen ?amshin turarensa na nan manne da shi. Sha?a ?aya Nu'aymah tayi tai azamar ?agowa cikin tashin hankali da tsantsar takaici.
Idanunsu ne ya shige cikin na juna, cike da firgici Nu'aymah ta sake waro masa idanunta da kware baki zatai ihu saboda harga ALLAH ta tsorata da ganinsa. Saurin saka tattausan hannunsa yay ya rufe mata bakin ruf yau ma, tare da sake manneta a jikinsa sosai shima a cikin ?an firgice.
Wani irin mugun bugawa ?irjinta ya sakeyi, jikinta ya hau ?ari tamkar wadda aka jefa cikin garwashin wuta ko akan wayar lantarki. Ta shiga mutsu-mutsun ?wace kanta tana kai masa duka.
"Oh my God! Just relax. Please calm dawn". Ya fa?a yana janye hannayensa duka daga jikinta.
Cikin rawar jiki hawaye na zirara ta mi?e, sake bigewa tai da kujera ?afarta ta tuzgu?e ta sake yin gaba kuma zata kifa yay azamar ri?o mata hannu ta sake dawowa jikin nasa.
"Wayyo Abbana ?an isk........." ta wage baki da iya ?arfinta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login