Showing 39001 words to 42000 words out of 325075 words

Chapter 14 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29113

basu tsallakoba, tasan Nanah matsoraciyace akan tsallaka titi dama, shiyyasa yanzuma abun ya bata dariya data tuna. Su Yusrah ma dariya suka sanya famhimtar dariyar Nu'aymah da sukayi. Bayan sun kalla ?angare biyu na titin babu mota suka sa kai zasu tsallaka. Da sauri security ?in daya rako yaran nan yasa hannu ya fisgo Nu'aymah dake ?arshen tafiya saboda tahowar wasu motoci guda uku a jere cikin masifaffen gudu.
Ta juya zataima security ?in masifar ta?atan da yayi dukda tasan hakan na halinsu bane sukaji razananniyar ?arar ?aya daga cikin yaran wanda motar farko ta kwashesa yana ?o?arin ?akko gyalen Nu'aymah daya zame ya fa?i lokacin da security ?in nan ke ?o?arin maidota baya.
"?uuuuuwww!!!" motocin suka bada sautin taka birki a tare, yayinda mai napep dake bayansu ya bugi motar ?arshe shima.
A tare su Nu'aymah suka fasa ?ara da rumtse idanu kunnuwansu a toshe da hannayensu, sai da sukaji tsitt sannan suka bubbu?e ido dan son ganin yaya akayi.
"Innalillahi.... Suka shiga ambata kusan a tare saboda hango yaron a kwance ?asa cikin jini. Sunma manta a titi suke, suka tafi da gudu kansa suka rufu masa. Sunkai mintuna uku akan yaron nan suna kuka da jujjuyashi amma ko mutum ?aya bai fito daga motocin nan uku ba balle kai tunanin sunsan ma abinda suka aikata. Cikin tsananin fushi da zafin zuciyar gado Nu'aymah ta rarumi wani dutse dake a gefen titin ta nufi motar tsakkiya dake a saitinta, wadda kuma tafi kowacce ha?uwa da ?yau ta buga dutsen jikin glass ?in.
Ko gezau glass ?in baiyiba, dan haka ta koma na gaba wanda tasan insha ALLAH zata dace ta sake bugawa da iya ?arfinta. Aiko a take ya shiga tsatstsagewa. Ta sake ?agawa zata buga aka ri?e mata hannu. Fisge hannun nata tai ?o?arin yi ta kasa, dan haka ta juyo bakinta cike da tsiwa.
Ido hu?u tayi da manyan garada masu suffar ?an dambe cikin ba?a?en suit da glasess zagaye da ita su shidda, daka gansu kaga cikakkun marasa imani dan babu alamar sunsan ma minene dariya a rayuwarsu, babu tantama kuma zasu iya halaka mutum batare da sunji koda ?ar ba.
A mamakinsu sai gani sukai ta ?aga dutsen ta bugama wanda ya ri?e mata hannu a goshi. Saurin sakinta yay ya dafe goshinsa daya fashe a take ya fara zubda jini.
Kusan a tare suka fiddo bindigu suka nunata da shi. Duk da Nu'aymah tasan zasu iya harbin nata ta mutu kuma, amma sam cikin idanunta babu tsoronsu, saima masifa dake cinta. Haka take ita sam batasan tsoroba. Idan kaga tsoro ga Nu'aymah to duhu ne ko tsawa, ko allura.
?asss! ?asssss!! ?assssss!!!
Sukaji sautin buga yatsu a bayansu. Gani tai duk sunja baya daga kusa da ita amma basu sauke bindugunba, sundai risinar da kawunansu ?asa na alamar girmamawa ga koma wanene mai buga yatsun.
Kamar bazata juyaba sai zuciyarta ta bata shawarar juyawa taga wane shahararran ?wallan mara imanine da mutuncine shi?in...........?

Nidai nama rufe idona bazan gansa ?inba??????.

Yau dai ga dogon page nan ku more harda na jiya na ha?a muku. Saura kuma naji wata tace bai isheta ba??????????????????


__________________________________
_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________


Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????

Mamu gee??
MIN ?ALB!!????

Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????

Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????

Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????

?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.[3/17, 9:26 PM] +234 901 860 0202: *_Typing??_*

No. 11
________________________
*ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE*

*_KAJI shahararrun kuma mandiyoyin ?an ?walisar kawo kayan kitchen masu tafiya dai-dai da zamani. Idan nace nadaban ina nufin su?in nadabanne wajen kaya ?an gaske dake ?awata kitchen ?in amarya harma dana uwargida ?ar ?walisa. Ka siya ka tabbatar ka saya ?in ko a gaban tsaranka sai ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. sunan kayansu sa kishiya cin bashi??, dan tana ?yalla ido taga kitchen ?inki tsarin amerikawa tuni zata fara ?wafa da tunanin zuwa gidan delu dillaliliya mai saida kwanika. Sai dai kuma kama da wane akace bata wane, dan haka ku maza ku garzaya ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. domin samun naku kuma. Suna kawo kaya daga ?asashen ?etare akan farashi mai sau?i da rahusa. Suna order ?in products kamarsu, dukan kayan kitchen na zamani, bedsheets, shoes dade sauransu, products ?insu pre-order ne dake zuwa akan lokaci batare da mai kaya ya ?osa da jira ba ko samun matsala. Zaku iya samunsu a Number waya kamar haka ko Location nasu. Phone number: 08102393622. Location Gombe. Amma Zasu iya turawa kowani gari dake a lungu da sa?o na ?asarnan. Sayen nagari maida ku?i gida. Ku garzaya kar ayi babu ku. Da ?yar nasha yafi da ?yar aka kamani inji masu iya magana??????????._*

___________________

................Kamar bazata juyaba sai zuciyarta ta bata shawarar juyawa taga wane shahararran ?wallan mara imanine da mutuncine shi?in,
Abun mamaki babu kowa a wajen, sai dai an sauke glass ?in motar ka?an alamar tanan koma wanene ya isar da sa?on nashi. Jitai zuciyarta ta sake hawa sama fiye da da. Ta yun?ura da nufin nufar motar gayun nan suka sake mata zobe. Kallonsu tai sama da ?asa a wula?ance da fa?in, "Wlhy idan baku matsamin ba ?aya bayan ?aya saina muku fashin goshi da dutsen nan".
Babu wanda ya motsa a cikinsu, da alama ma basa fahimtar yaren datai maganar, dan kallonta kawai suke tamkar wasu zakaru. Dutsenta da har yanzu ke a hannu ta sake ?agawa zata bugama wani again. Da sauri yay baya da ?ana kunamar bindigarsa yana huci. Nu'aymah ta ta?e baki tamkar bata fahimci abinda yake shirin yiba, ta sake ?aga dutsenta ta makama na gefen hannun haggunta a goshi cikin rashin tsamanin hakan daga garesa.
?ara ya saki da du?ewa ?asa bindigarsa na fa?uwa dan abun yazo masa a bazata, babu yanda za'ay kai tunanin shi?in zata bugamawa. ?afa ?aya daga ciki ya saka ya ta?eta tai baya zata fa?i cikin security ?in gidan marayun da suka iso yanzun wajen yay saurin tareta. Ai tanajin bata kai ?asaba tai wani irin ?agowa da sauri ta wulwula dutsin nata sai akan motarnan dai ta ?azun data fasama glass, kuma a gaba ya sauka, dan haka glass ?in ya ?ara tsatstsagewa fiye da ?azun.
A yanzunkam bodyguards ?insa sun tabbatar bazasu iya ha?ura da tsagerancin yarinyarnanba, sai sun ?auki mataki duk da ogansu bai basu damar yin hakan ba. Hannu ?aya daga ciki ya ?aga zai kwasheta da mari iya ?arfinsa, sai dai ganin za'a bu?e ?ofar motar ne ya sakashi dakatawa da nufar motar da sauri ya ?arasa bu?ewa yana saurin cewa, "Sorry Sir"..
Banji an amsashi ba, sai dai motsin da naga anyi daga cikin motar ya bani tabbacin wanda ke a ciki zai fitone. Ba Nu'aymah ka?ai ba, harsu Yusrah sun zuba idone suga mai fitowar.
?afarsa dake cikin ba?in takalmi mai shegen ?yau ta fara bayyana, kafin farin wandonsa. A hankali ya dire sandarsa ?asa itama tare da ?ayar ?afarsa ya fito gaba ?ayansa.
Koni mai ?aukar rahoto saida na furta 'masha ALLAH' a zuciyata. Zu?ar iskar yammaci data fara ka?awa yay a hankali cikin hancinsa ya fesar yana sake tamke farar fuskarsa dake zagaye da ba?in gashin saje si?ik, dan a rayuwarsa ya tsani kallo. Baiko kalli ko sashen dasu Nu'aymah da guards ?insa sukeba ya nufi inda su Nanah suka rufu kan yaron tare da securitys ?in gidan marayun. Hannun Malika dake a saitinsa ya kama ya matsar da ita gefe, hakanne ya sakasu farga da isowarsa duk suka dawo cikin hankalinsu daga kallon ?urullar da suke masa. Baice dasu uffanba yay wani ?an dir?uson gayu gaban yaron tare da kai yatsunsa biyu saitin hancinsa, yakai kusan sakan goma kafin ya janye, sai kuma ya maida kan jijiyar wuyansa dake a saitin kunne. Nanma ya kwashe sakan goma da ?oriya sannan ya ?auke. Mi?ewa yay tsaye, idanunsa dake cikin ba?in glasess akan ?aton symbol ?in da aka rubuta sunan gidan marayun, kafin ya janye ya maida dubansa ga guards ?insa da har yanzu suke zagaye da Nu'aymah kamar wata ?arauniyarsu. Da hannu yay musu nunin su barta, tare da yin wani salo da yatsunsa biyu wanda shi da su ne kawai sukasan ma'anar yaran nasa.
Cike da takaicin rashin ?aukar mataki a kanta sukaja baya kowanne na zuba mata harara a ?asan ido da huro hanci. Gaba ?ayansu garesa suka nufo. ?aya daga ciki ya matso sosai inda yake, A hankali ya furta maganar da babu wanda ya iya jinta a cikinsu Nu'aymah, dan kuwa jajayen la??ansa ne kawai suka motsa ka?an. Ganin haka ya saka Nu'aymah nufosu da sauri itama. Yana ?aga ?afarsa zai bar wajen tana isowa tasha gabansa.
"Kai malam dakata mana! Shin babu zuciyane a ?irjinka kokuwa kana tunani da zuciyar takane bada ?wa?walwa ba?".
Kallonta yake daga sama har ?asa ta cikin glasess ?insa, batare da yama nuna alamar ya fahimci yaren da take maganar da shiba ya ra?ata zai wuce abinsa. Hanzarin ri?o sandarsa tai ?o?arin yi Yusrah ta ri?eta. Cikin magana ra?a-ra?a tace, "Aymah calm down Please, kalla kiga".
Sai da ta zubama bayansa harara kafin ta kalli abinda Yusrah ke nuna mata. Securitys ?in gidan marayun ne tare da guards ?in nasa uku dasu Nanah ta hango harsun kusa shigewa cikin Orphanage ?in ?auke da yaron a hannun ?aya daga cikin guards ?insa. Juyawa tai da sauri ta kalli inda yake shima sai ganin motocin uku tai har sunyi reverse suma da alama gidan marayun zasu shiga.
"Zuciyarki tayi sanyi ko? Iya masifa! ALLAH wataran sai kinsa an maidamu kwalta Nu'aymah, jibesu tamkar wasu bajiman zakuna su da ogan nasu. Da ganinsu kasan ba hausawa baneba ma, ke koma tsoro ba?yaji".
"Mtsoww! Ina ruwana da rashin kasancewarsu Hausawa, inda banyi musu hakanba ai guduwa zasuyi dan tsabar rashin sanin darajar ?an adam. Ko dabba suka bige ai ta cancanci su fito suga lafiyarta balle mutum, shegu masu suffar ba?a?en aljanu".
Dariya Yusrah ta kwashe da ita tana fa?in, "Amma dai banda wannan Handsome ogan nasu ko? Dan wlhy dai kam komai yaji zammm anan kema kin sani".
"Ke kikaga wannan". Nu'aymah ta bata amsa tana fisge hannunta dake cikin na Yusrahn ta tsallaka titi ta barta tana dariya. Dan ta kula bori kawai Nu'aymah keyi itama tasan gayen ya ha?u masha ALLAH, sai dai yanayinsa sam bai mata kama dana Musulmai ba, dan askin kansa kawai da ?aton sar?an Cross na diamond dake a wuyansa, da ?an kunne guda ?aya manne a kunnensa ya isa amsar hakan a garesu.
Hango Nu'aymah har zata shige cikin Orphanage ya sakata saurin tsallaka titin itama ganin babu mota tabi bayanta.

Nu'aymah da har yanzu keta faman jan tsakin takaicin mutanen ta nufi clinic ?in gidan kanta tsaye, tasan dai bazai wuce can suka nufa da yaron ba. Kasancewar tafiyar tata sai a hankali, ba wani sauri ta iyaba kuma akwai tazara tsakanin gate ?inma da clinic ?in saiga Yusrah harta isketa. A tare suka ?arasa batare data kula Yusrah daketa son taga ta sakko ba. Tsaitsaye suka iske su Nanah a reception da guards ?in mutumin, sai bah-bah hindatu ?aya daga cikin masu kula da yaran, da kuma Abban Adawiya da ashe tun ?azun yana a cikin gidan marayun su Nu'aymah basu saniba.
Waige-waigen inda zataga gayen ta farayi, sai dai babu ko mai kama da shi a wajen. Wani takaicine ya sake dirar mata a zuciya, cikin ranta ta ayyana 'Wato shi yamafi ?arfin shigowa kenan? To ai idan yasan wata baisan wataba'. Ta nufi hanyar fita tana surutunta a zuciya.
Yusrah da tunaninta ya bata Nu'aymah zata iya zuwa ta sakemusu ?arna a motoci tai saurin ri?o hannunta tana fa?in, "Ina kuma zakije?".
"Yusrah sakeni, bakiga wannan mai shegen taurin kan bai biyosu ba". "Oh ALLAH, to minene idan bai shigo ?inba, baga guards ?insaba, nasan ai zasu wakilcesa. Ki tunafa ba shine ya buge yaron ba ma, cikin guards ?in nasane tunda shi yana a motar tsakkiyane, sannan ba shinefa ke tu?inba".
"Wannan matsalarsace kuma, ai wanda ya bige ?in dai yaronsane ko? To ya zama dole shina ya kasance a wajen wlhy dan ya ja masa matsala".
Kafin Yusrah ta samu damar mata magana sai gashi ya fito daga ?aya a cikin ?akunan clinic ?in, Dr Safwan biye da shi a baya, taku yake cike da nutsuwa irinta zaratan samari masuji da lokacin ?uruciya da kwanciyar hankali. Handglop ?in dake a hannunsa taga yana zarewa ya jefa cikin shara. Har yanzun dai idanun nasa a toshe suke da Google ?in, kuma fuskar a tamke, tana ?o?arin janye idanunta daga kallon nasa caraf suka sauka bisa kan ?atuwar sar?ar Cross ?insa da a?azun masifa baisa ta ganta ba.
Cikin su?utar baki tace, "Ashe Arne ne shiyyasa baida imani".
Karaf wannan magana a kunnensa. Sai dai yanza yazo ya gittata ya barta da ?amshin turarensa mai sanyin da?i batarr da ko kallon inda takeba ne, zaka fahimci da wahala ace yamaji mitace, maybe ma bayajin hausar sam.
Wajen Abbah dake zaune ya ?arasa, suna ?an nesa dasu ka?an shiyyasa bazasu iya jin mi suke fa?a ba. Ta ta?e baki da nufar Dr Safwan tana tambayarsa yaya jikin yaron?.
"Jikinsa Alhmdllh, ai bama wani ciwo yaji sosai ba, yadai bugune a kansa da hannunsa na haggu, insha ALLAH kuma fatan komai zaiyi normal da wuri".
Duk da taji da?in hakan sai bataji ranta ya huce daga haushin mutuminda ita kanta shaidace tasan ba shine ya aikata laifin ba. 'Amma kuma ai ogan wanda ya aikata ?inne' ta raya a cikin ranta cike da gamsuwa da jawabin zuciyarta.
?akin da yaron yake kwance suka nufa suka dubashi duk da ansa masa ruwa barci ya ?aukesa. Lokacin da suka fito basu iske mutanenba har motocinsu. Hakan ya bama Nu'aymah tabbacin sun wuce kenan.
Suma nufar hostel ?in yaran sukai suna sake tattauna abinda ya faru, tare da yin gulmar mutumin dako sunansa basu saniba. Nu'aymah dai uffan bata cewa, dan ita takaicima suke ?ara mata a kanshi kawai.



______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Wannan littafi SARAN ?OYE na ku?ine, yana ?aya daga zafafa biyar, idan kana bu?ata kaima wa?anan numbers ?in magana ka biya ku?insa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka karanta idan baka biyaba, karka kuma ya?a dan ALLAH idan ka gani??????.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

_______________________

Tunda suka baro cikin Orphanage ?in ya kwantar da kansa jikin kujera yay shiru idanunsa dake da cikar ba?in gashi da gira a sama suna a lumshe. Sai faman juya glasess ?insa dake a hannunsa na dama yake tamkar zai karyasa. Gaba ?aya abinda ya farune ke dawo masa cikin zuciya daki-daki. Ya yarda yaran Arewan nan basajin magana tamkar yanda yakeji ana shan fa?a. Jibafa yanda ?ar yarinya ?arama sa'ar ?anwarsa Victoria ta tsaya agaban bindiga tana musu raini tamkar wasu sa'anninta. A karan farko yaja ?aramin tsaki da furzar da iskar daya cika baki da ita yana maijin takaicin komai a ransa. A hankali ya bu?e idanunsa ya kai dubansa ga glass ?in gaban motar tasa da Papansa yasa ma?udan ku?i wajen siya masa. Yau shine hawansa na farko da motarma gaba ?aya, dan sati biyu da suka wuce papa ya bashi ita a birthday ?insa matsayin gift. Amma sai gashi cikin sakanni an mata walmakalifatu, kamar Mom tasan hakan zai faru tace bata yarda yazo kano a mota ba daga Abuja, shi kuma gashi yanada uzirin da bazai yuwu ya fasa tafiyarba, dan dama zaibi jirgine kamar yanda ya saba sai akace jirgi bazai tashiba dan yanayi babu ?yau yau. Shinefa ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login