Showing 102001 words to 105000 words out of 325075 words
sukari ?wara ?aya kamar yanda yasan Yoohan na bu?ata sannan ya mi?a masa.
"Gashi Sir" ya fa?a da yarensu.
Bu?e ido Yoohan yay a hankali. Sunyi jajur alamar baya cikin nutsuwarsa. Baice komaiba ya amsa tare da yima Solomon alamar yaje. Badan Solo yaso hakanba ya fito yana waigensa. A falo ya ma?ale dan bazai iya zuwa ko inaba yabar Yoohan ?in a haka, kodan gudun ?acin rai mai tsanani da zai iya fuskanta a gurin madam Chioma da Papa.
Yoohan da baisan Solomon bai fitaba ya fara shan coffee ?in a hankali zuciyarsa na cigaba da kai kawo akan abubuwa masu yawan gaske. A haka ya shanye ya sake zubama kansa. Yanzu kam ko sugan ma bai sakaba a haka ya sha kayansa. Koda ya gama kuma nan ya cigaba da zama har tsahon lokaci.
Zuwa can kuma tamkar wanda aka mintsina sai ya mi?e, duk da rigar wanka ce a jikinsa bai damu ba, a haka ya bu?e ?ofar ya fice bayan ya zura Slippers. Tsaye yayi yana kallon Solo dake gyangya?i a falo, kansa ya ?an girgiza ya nufi ?ofa batare da yayi magana ba.
Can ya fita harabar hotel ?in da ko ina ke ?wanyar da haske, mutane nata kai kawo tamkar ba dare ba. Mafi yawansu mazane dake shigowa da mata. Wasu kuma matan su ka?ai ke shigowa alamar masu jiran nasu suna ciki su. Wasu mazan kuma su ka?ai ne suma, dan wasu matafiyane ba she?ancin ne ya shigo dasu ba.
Watsar da komai yay dan shi baya matsama kansa shiga hurumin da banasa ba. Can wajen kujerun da aka tanada dan hutawa ya nufa. Babu mutane sosai a wajen, dan haka ya samu ?aya ya zauna, tare da sake tsunduma cikin abinda ke masa kai kawo a zuciya da ruhi tun ?azun.
A cikin tunanin nasa ne hankalinsa ya fara karkata ga abinda na kusa da shi ke saurare a wayarsa. Duk da ya saka ?arar can ?asa sosai hakan bai hana Yoohan ji ba saboda dare ya fara nisa. Wajen da suke kuma wajene da sam babu hayaniya, dan hotel ?in dama bana ku bayi bane, na manya ne masu ji da ?an canji, inda aka ginasa ma kawai ya isa baka amsa.
Lecture ce da ga bakin Sheikh Fantami yake saurara. Kasancewar da turanci ne sai komai yake shiga kunnen Yoohan ra?am. Bu?e idanu yay a hankali ya kai dubansa ga mai sauraren wa'azin. Matashin saurayine tamkarsa, sai dai kallo ?aya zakai masa kasan kaga ustaz. yayi shiru a wajen tamkar baisan da motsin kowaba yanata sauraren wa'azin sa.
Tsintar kansa yay shima da sake nutsuwa sosai yana saurare. ya shagala sosai da sauraren wa'azin nan mutumin ya mi?e, batare da yayi tunanin wani na tayasa ji ba ya kashe tare da barin wajen ya koma ciki dan ya kwanta ya huta.
Ko ka?an Yoohan baiso hakan ba, dan anzo wata ga?a da duk mai sauraren wa'azin zai so jin ?arshensa. Bin mutumin yayi da kallo harya ?acema ganinsa. Ji yay tamkar ya bisa ya ro?e ya basa ya ?arasa ji. Dan jikinsa wani irin tsuma ya keyi, gashi duk ya mimmi?e masa. Komai ya sake birkice masa, duk yanda yake tunanin tasirin mafarkinsa da maganganun Nu'aymah sai lecture ?in nan daya saurara ta sake fa?a?a rauninsa zuwa ?ololuwar rikicewar tunani da gushewar wani duhu daya fahimci ya jima a cikinsa. Tunanin bin bayan mutumin ya sakashi kallon agogon hannunsa, ya ?an waro idanu waje dan bai ankaraba sai yaga agogo ya nuna ?arfe ?aya saura.
Sake maida idanunsa yay ya lumshe tamkar baiga mi agogon ya nuna masa ba. Sai ajiyar zuciya daya dinga saukewa a jajjere.
A haka Solomon daya sake shiga ?akin nemansa bai gansaba ya fito a rikice nemansa ya iske sa. Duk da wayar dake a hannunsa da alama ta nuna wanine akan layin sai da ya sauke ajiyar zuciya .
"Ashe kana anan sir?!". Solo yay maganar yana sake sauke numfashin ru?anin da yake ciki na rashin ganin nasa da farko.
Yoohan da tun isowar Solomon wajen yana kallonsa ta ?asan ido ya bu?e idanunsa ya watsa masa wani shegen kallo mai cike da garga?i.....
"I'm sorry sir. Madam ce".
Kafesa da ido sosai yayi, duk da kuwa yasan Momy Solomon ?in ke nufi. Bai amshi wayarba, bai kumace komaiba ya mi?e yabar wajen. Solo dake binsa da kallo yay saurin bin bayansa hankali a tashe.
Koda suka koma ?akin bai gajiya ba sai da ya sake maimaita masa maganar amsar wayar sannan ya mi?a masa hannu alamar ya bashi. Yana amsar wayar ya nunama Solo toilet da hannu.
Duk da bai fahimcesa ba haka ya nufi toilet ?in dan ya duba. Shi kuma ya ?ora wayar saman kunnensa muryarsa mai amo da kauri ?in nan ta fara fidda sauti. "Hello Mom".
Ajiyar zuciya mai ?arfi madam Chioma ta sauke da ga can, kafin cikin ?asa da murya sosai tace, "My boy!".
"Humyim".
Ya fa?a a hankali cikin ma?oshi.
Murmushi mai sauti ta sake da ga can tana mai ?an?ame filo a ?irjinta da lumshe idanu. Cikin sake narke murya tace, "Mike damunka?".
Shiru yay na wasu sakanni. kafin ya furzar da ?an huci yana sauke idanunsa da ga table ?in. "Ba komai Mom, bakiyi barci ba?".
Sake narke murya tayi kamar zatai kuka. Tace, "My Boy tunaninka ya hanani barci. Kai kasan muna tsananin bu?atar ganinka tare da mu ni da papan ku dama ?annenka gaba ?aya. Amma duk da ?okin dawowarka da mukeyi wannan karon, bayan tsahon sati biyu da ka ?auka bakanan shine kai wucewarka wani gari batare da ka fara sauka Abuja mun ganka ba".
"Am so sorry Mom". Ya fa?a a ta?aice kawai.
Matse filo ta sakeyi sosai a ?irjinta. Dan ji take jininta na wani masifar yamutsawa tamkar zaiyi tsartuwa ya fito. Kafin ta samu damar sake magana ta sake tsinkayar muryar Yoohan na fa?in, "Mom goodnight, zan kwanta". ?itt ya yanke wayar.
"My b......" tai yun?urin fa?a sai kuma taji ?itt. Da sauri ta ciro wayar daga kunnenta ta kalla. A take fuskarta tai masifar tsukewa hawaye na taruwa mata cikin idanu. Filo ta sake jawowa zata ?an?ame papa ya shigo ?akin nata.
"Wai lafiya kika ma?ale anan bayan inata jiranki a can?".
Wani irin takaici da ba?in ciki ne ya kumeta a zuciya. Ta ?an hararesa a kaikaice tana maijin wani irin zafinsa da ?aci a ranta. Amma a zahiri sai tai ?an murmushi da cewa, "Ka bari kawai. Solomon ne ya kirani wai yaga kamar John a damuwa. Shine fa nasa ya ha?amu dan wayoyinsa duk basa tafiya. Amma yaron nan sai ya amsa ni sama-sama. daga ?arshe ma ya yanke wayar".
?ar dariya Papa dake hawowa gadon yayi. ya jata jikinsa ya rungume yana fa?in, "Kema kinsan halin yaronki ai. Minene zai ?ata miki rai a ciki. Maybe yana bu?atar hutawa ne shiyyasa ya kashe".
Kafin ta samu damar basa amsa ya ha?e bakinsu waje guda. Duk yanda taso ta ?wace kanta ya hanata wannan damar. Dan dama inhar ALLAH ya bashi sa'a a kanta baya wasa da damarsa. Saboda duk lokacin da zai bu?aci kasancewa da ita sai sunsha uwar rigima, wani lokacinma ?arfi yake nuna mata ya samu nutsuwa. Yakan rasa miyasa take masa hakan tunda shi dai yasan auren soyayysa sukayi. ada can kuma sam bata masa wannan halin sai a shekarun nan da bazasu gaza goma zuwa sha ?aya ba.
To komadai minene yau ya moreta da ?yau. Daga ?arshe ya koma lallashinta sabida kuka da take masa tamkar wanda yay mata fya?e. Da ?yar ya samu kuwa tai shiru sukai barci duk da shi ya rigatayi kafin itama ya sacetan.
Yoohan kam koda ya yanke wayar sai yay jifa da ita saman kujerar dake gefensa. ya sake maida kansa jikin kujerar ya lumshe idanunsa tamkar ?azun.
A haka Solomon da ya kammala tattare kayan da Yoohan ?in ya baza a toilet ya fito ya samesa. Baiyi magana ba, ya lalla?a kawai ya ?auki wayarsa ya fice da ga ?akin. Duk da Yoohan najinsa bai motsaba, haka ya cigaba da zama a wajen har tsahon lokacin da shima kansa baisan ya kai ba, dan barci ne mai nauyi ya kwashesa a wajen, tare da fa?awa cikin nannauyan mafarki maiban tsoro da al'ajabi a garesa.
Gabannin asuba ya farka a firgice, da ?yar ya iya motsa wuyansa da ya ?age, cikin dauriya da jarumta ya shiga jujjuyasa yana matse fuska saboda zafi. Sai da yaji ya ?an sake masa sannan ya mi?e tsaye yana sauke tagwayen ajiyar zuya. Duk da a zuciyarsa yayi mamakin barcin da yay a zaune na kusan awa hu?u sai baiyi magana ba ya taka a hankali zuwa gaban Window. Idanu ya rufe zai fara addu'a kamar yanda sukeyi a addininsu sai kuma yay saurin bu?ewa. Hannu ya saka ya bu?e Window ?in. Sassanyar iskar asubahi ta feso masa, tare da ?wala kiran sallar farko da ga wani massallaci da alamu suka nuna yana gab da hotel ?ine ko kuma a cikin hotel ?inma yake . Wani wawan numfashi ya sauke tare da lumshe idanunsa. Haka kawai sai ya tsinci kansa a wani irin nisha?a na musamman..............?
_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????
Mamu gee??
MIN ?ALB!!????
Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????
Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????
Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????
?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.[5/18, 3:08 PM] Ummuanwar??: *_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.
No. 28
............Sake bu?e idanun yay ya saukesu bisa giza-gizai dake yawo cikin hasken sararin samaniya na yanayin asubahi. Karan farko a rayuwarsa da zuciyarsa ta tafi wajen tunanin da girmama UBANGIJI da ya halicci sammai, gata dai babu icce ko ?aya daga kowacce kusurwa ta duniya da zakai zaton ta ri?eta. Sannan babu wata sar?a ko ?arfe da suma suke amsa sunan ginshi?i a gareta. Da rana hasken *_Rana_* ya mamayeta. Da dare hasken *_Wata_* ya ?awata ta da adon taurari. da *_Damuna_* na _Giza-gizai_. Lokacin asubahi takan canja kala zuwa sky blue da wasu ado masu ban mamaki da al'ajabi. Hakama da yammaci lokacin fa?uwar rana takan ?awatu da kalar sky blue da na yanayin fa?uwar rana. Duk wannan hikima da rahamar akan azurtamu da sune babu ko naira ?aya. Babu ku?in haraji babu na ?arshen wata. To miyasa wanda ya azurtamu da ita bai ta?a jiran mu biyasa da ko taro ba? 'saboda shi ?in *_(SARKI NE GAGARA MISALI DA BAUTA KAWAI AKE KA?AICE SA)'_*
Wani yanki na zuciyarsa ya bashi wannan amsar.
Samun kansa yay da sake lumshe idanu ya sauke wasu tagwayen ajiyar zuciya saboda wata kalma data fa?o cikin kunnensa daga massallacin da aka kira salla dan sun saka tafsir ne.. (Kana son sanin ni'imar dake cikin addinin musulinci?). Furicin ya fito daga bakin Sheikh Sooraj Hashim jibiya (Baba malam) dan sun saka tafsir ?in nasa ne.
'Tabbas ina son sanin ni'imar dake cikin addinin musulinci?'. Ya amsa tamkar shi ?in akeyima tambayar kai tsaye. yana mai cigaba da kallon yanda wata keyin ?asa cikin giza-gizai alamar lokacin fa?uwarsa yayi, zai bama rana guri itama tazo ta cika umarnin ALLAH (S.W.A) akan aikinta.
Tabbas wannan tambaya ta tsayama Yoohan a zuciya. Dan da ita ya ?arasa sauran daren daya rage masa. Akan kunnensa har aka kira assalatu akai salloli a massalatai. Sai da gari yay haske sosai sannan ya iya barin jikin Window ?in zuwa toilet.
Ji yake a ransa bazai ta?a samun nutsuwa ba sai ya dangane da gidan baba malam a safiyar nan. Dan tabbas yana bu?atar sanin (Hanyar fahimtar ni'imomin dake cikin addinin musulinci? A yau).
A gaggauce ya gudanar da komai. Kamar ko yaushe yay shirinsa cikin ?ananun kaya. Blue jeans da farar shirt mai gajeren hannu. Sai ya ?ora suit jacket fara tas itama. Yau dai bai saka necktie ba, ma?allin shirt ?inma ba duka aka rufe ba. Cikin ?amshinsa ya baro cikin hotel ?in batare daya nema inda su Solomon suke ba.
Safiya ce sosai a garin, hakan yasa da ?yar ya samu keke napep, shima da mutum ?aya a ciki. Bai damu ba, duk da kuwa wannan shine karan farko a tarihin rayuwarsa da zai shiga napep ?in. Lokacin da mai napep ya tambayesa ina zasa? Da ?yar ya iya ha?a hausan ya bashi amsa da sunan baba malam kawai. Dan dama bawai ya iya hausan bane yana dai jin abubuwa sosai saboda mu'amula da mutane marasa lafiya akan aikinsa. Sai dai bai iya maidawa, bayan gaisuwa sai abubuwan da baza'a rasaba suma ?ai-?ai ne.
Sai da aka fara ajiye wanda ya tarar a ciki kafin shi a kaisa. Kusan dubu uku ya mi?ama mai napep ?in. Da mamaki shiko yake kallonsa, yama rasa mizai ce masa dan ya fahimci hausa ba isarsa tayi ba. Sake mi?o masan da yayne ya saka mai napep ?o?arin ha?a ?an turancinsa ya sanar masa naira ?ari da hamsin ne ku?insa. Duk da dai turancin bai ha?u da ?yau ba Yoohan ?in ya fahimci mi ya fa?a. Dan haka ya ajiye masa ku?in a jiki yana fa?in, "Na baka ne duka". Yanda yay maganar da hausa abin dariya, harma mai napep ya kasa ha?uri sai da ya dara.
Yoohan baibi takansa ba ya nufi ?ofar gate ?in su baba malam kansa tsaye, kai kace gidansa yazo.
Sau uku yay Knocking sannan maigadi ya bu?e ?aramar ?ofar ya le?o yana tambayar "Wai wanene haka da farar safiyar nan?" dan yasan su Baba malam ta ?aramin gate sukaje massallaci yau.
Bai gane Yoohan ba. Dan duk zuwan da yay har sau biyu bashi ka?ai ya shiga ba sai da jagorancin masu gidan. Sai da ya gama ?are masa kallo sama da ?asa kafin yace, "Samari lafiya kuwa? Mikake nema ko bu?ata anan?".
Sam Yoohan bai fahimta ba, bayan kalmar (lafiya da wasu ?ai-?ai) babu abinda ya gane a zancen maigadi. Sai yay shiru yana kallonsa cike da nazarin miya kamata ya ce da shi. Maigadi da haushi ya kama ya sake maimaita masa tambayar?. Nan ?inma dai ba fahimtar yayi ba. Sai ma ya jefa masa tambaya da turanci shima.
"To bakajin hausa kenan?". Maigadi ya fa?a a hankali. Sai kuma ya kalli Yoohan yay masa alama da hannu (wai yana zuwa). Kafin Yoohan ?in yace wani abu maigadi ya koma ciki. Saurin yun?urowa Yoohan ?in yayi zai tsaidashi sai dai tuni ya rufe ?ofar.
Cike da damuwa ya dafe kansa. Sai kuma ya juya yana kallon titin anguwar. babu mutane sosai, sai tsilli-tsilli dake fitowa cikin massallacin. Sai kuma sautin karatun yara da shima alama ta nuna daga harabar massallacin ne.
Nufar gate ?in massallacin yayi, kasancewar shi a bu?e yake sai ya samu damar shiga kansa tsaye. Sai dai bai kai tsakkiyaba wani cikin almajiran malam ya tsaidashi da sauri, dan kallo ?aya zai tabbatar maka Yoohan ?in ba musulmi bane.
Anyi sa'a almajirin malam najin turanci, sannan kuma duk zuwan da Yoohan yayi gidan sau biyu ya gansa. Ba ?aramin da?ine ya kama Yoohan ba jin cewar almajirin malam najin yaren da shima yake ji. Cikin sau?i suka gaisa ya sanarmasa wajen malam yazo. Kuma yana cike da ?aguwar san ganinsa domin dalilin babban uziri.
Duk da almajirin malam yayi mamaki hakan bai hanashi yarda zaima Yoohan ?in iso ba. Dan haka ya nuna masa wani ?an dakali alamar ya zauna ya jurasa. Shi kuma ya juya cikin massallacin inda yasan