Showing 99001 words to 102000 words out of 325075 words
tonama kanki asiri kinji ko, ki wuce ki shafa hodan, idan kuma sokike wani ya sake shigowa to".
Gaban Mirror Nu'aymah ta ?arasa. Ta shafa mai da hoda harda kwalli, duk da dai hakan fuskar dai babu walwala.
Amma sai Kubrah batace mata komaiba suka fito falo inda su Hajarah ke hira tare. Zama tayi kamar yanda Addah dake kallonta ta Umarceta. Su Aunty Basira nata tsokanarta da fa?in ina tsarabarsu ne?.
Tun tana no?ewa dai harta ?an ringa amsasu, amma ta gaza sakin jikinta yanda ya kamata sosai. Duk motsinta Hajarah da Addah na lura da shi, sai dai babu wanda ya iya cewa komai a cikinsu.
___________________________
A ?angaren Yoohan kuwa duk yanda su Hajjo sukaso ya zauna jiran dawowar baba malam ya gaza hakan. Yace musu zai dawo da safe yanzu yanada wani uziri.
Badan hajjo taso ba ta barshi. har ?ofar gida su Yah Ahmad sukai masu rakiyya shi da Manager. Inda su Solomon ke jiransa a mota. Kasancewar basu iske baba malam ba yasa bai shiga dasu cikiba. Yace su jirashi a waje. Dan da ?yarma Su Ahmad suka lalla?ashi ya shiga cikin gidan. Da farko ya ce zai koma tunda baba malam ya fita. Dan dama yaso yin surprise ?insa ne shiyyasa bai sanar masa shigowarsa kanon ba ma.
Har drivern sa ya tada mota ya tsaidashi. Ku?i ya ciro a cikin jakarsa rafa guda na ?ari biyar sabbi ?al ya mi?ama malam ?arami yana fa?in, "Please a bama yarinyar nan barka da salla. Na manta ban bata ba".
Malam ?arami da ya fahimci Nu'aymah yake nufi sai yay murmushi. bai musa ba ya amsa yay masa godiya, dan suma daya basu suka?i amsa a ciki ?ata rai yayi, wai basu ?aukesa ?an uwansu ba. Hakanne ya sakasu amsa tunda yace barka da salla ce.
Duk abinda ke faruwa Solomon na saurarensu. Dama cike yake da haushin sake zuwa wannan gidan. Ya kuma ?auki alwashin suna komawa wannan karon sai ya sanarma madam Chioma. Dan tsaf ya fahimci wa?an nan mutanen zasu iya jan hankalin Ogan nasu tsaf, musamman yanda suke masa hidima kamar wani sarki. Yanzu haka a gabansa aka saka babbar leda a booth wai kayan barka da salla ne aka bama Yoohan ?in a cikin gida. Ya cije bakinsa yana satar kallon Yoohan daya kwantar da kansa jikin kujera ya lumshe idanu kamar mai barci ta mirror.
Babu abinda kema Yoohan kai kawo a zuciya da ruhi sai kalaman Nu'aymah. Kalaman sunyi masifar tasiri a ransa fiye da zaton mai karatu. Sai faman tisasu yake dalla-dalla kamar mai bitar karatu. Duk da ac dake aiki a motar bai hana zufa tsatstsafo masa a goshi ba. Mafarkin da yayi shekaran jiya da baba malam ya kuma sake maimaita shi yau da safe ya shiga tariyowa shima.
ya sauke wani irin nannauyan numfashi yana sake tariyo mafarkin nasa da yayi a karo na biyu kenan,
*Ya kanga kansa a mafarkin a gaban wani kogo ?aton gaske, cikinsa akwai wani irin wuta dake ci mai ban tsoro, dan duk iya hasashensa ya kasa kamanta ?arfin wutar da zafinta a zahiri. Aduk lokacin da yake a gaban wannan kogon dake zuwa masa a mafarki, ya kan tsinci kansa cikin matsanancin mawuyacin hali da ru?u, sai dai kuma abin mamaki sai ya ga baba malam acan gefensa cikin shiga ta kamala, a wasu irin korayen ciyayi masu bada ni'imtaccen yanayi yana masa murmushi da mi?a masa littafin nan na musulmai (Al-Qur'ani), yakan ringa ce masa_______*
*_"Yoohan wannan shine zancen ALLAH, littafi dake ?unshe da kowane irin sirri, littafin da aka aiko MANZONMU ANNABI MUHAMMADU (S.A.W) da shi. kanada sauran daman ri?o dashi domin ka samu tsira daga wannan narkon azabar dake gabanka. Kazo gareni, zan nuna maka hanyar sanin UBANGIJINA kamar yanda ya aiko MANZONMU ANNABI MUHAMMADU (S.A.W) a garemu ya nuna mana muma, ya kuma koyar damu. Ni Sooraj bin Hashim, na rantse maka da ALLAH, babu wani addini na gaskiya sai musulinci, babu wata hanya ?ya?y?yawa sai ta bin UBANGIJI, babu wani abin ta?ama da ri?o sai MANZON ALLAH. Inhar kabi ALLAH, kai koyi da koyarwar MANZON ALLAH, ka ri?e gaskiya da amana, ka tsare gangar jikinka daga sa?ama ALLAH, ka nema dukiyarka ta hanyar halak, kaji tsoron zalintar mutane, ka kiyaye jinka da ganinka daga haramun, ALLAH bazai jarabceka da shiga wannan taskar azabar dake a gabanka ba. Domin UBANGIJI ya tanadi gidaje guda biyu, WUTA DA ALJANNAH, ya kumayi al?awarin cikasu da mutane. Dan haka Yayha kazo gareni, kazo ka kar?i kalmar LA'ILAHA ILLAH, MUHAMMADURRASULULLAH (S.A.W)._*
A wancan ranar da yay wannan mafarki ya wayi garine a yanayin sanyin jiki, da tunane tunane kala-kala. Ya kuma yini zuciyarsa na rinjayarsa da amsa wannan kira. Sai dai daya tuna wani gagarumin al'amari sai yay azamar ?wa?ar kansa harma da al?awarin nisanta kansa da su baba malam ?in. Dan yau ?in nanma da ?yar manager ya lalla?a shi sukazo nan ?in. duk da kuwa yana a cikin kanon yau kwanansa biyu kenan ma.
Kafin su ?arasa hotel ?in daya sauka sosai ya tsinta kansa cikin ru?anin kalaman Nu'aymah da mafarkinsa. Sai ?unbin takaici da dana sanin abinda ya aikata ma yarinyar yakeyi, wanda sam ba halinsa bane yin hakan, amma yasan ita da duk wanda zai iya ji ko ganinsu a lokacin bazai ta?a yarda da shi ba. Ya ?an ciza le?ensa na ?asa da ?arfin tsiya, ?irjinsa na sake masa zafi.
Motocin na tsayawa baiko jira an bu?e masa ba ya bu?e da kansa ya fice. Daga Solomon har sauran guards ?insa tsaye kawai sukai suna kallonsa cike da mamaki da tsoron yanayin nasa. Da sauri Solomon yabi bayansa shima dan yasan ba lafiya ba dai. Gashi key ?in ?akin Yoohan ?in yanama a hannunsa ne.
?an gudun da yayine ya sakashi cimmasa. Dan haka suka ?arasa ?ofar ?akin tare. Solomon ya bu?e masa tare da matsawa ya bashi hanya dan ya shiga.
Batare da yace masa komaiba ya shige, shi ma Solomon ?in sai ya bisa yana fa?in, "Sir lafiya kuwa?".
Cak Yoohan ya tsaya da ga yun?urin shiga Bedroom ?in da ya keyi, batare da ya juyoba ya ?agama Solomon ?in hannu da masa alamar ya barsa.
Da baya-baya Solomon ya rin?a tafiya harya fice da ga ?akin, yaja masa ?ofar a hankali gabansa na fa?uwa da yanayin ogan nasu.............?
????????Tofa, Dr Yoohan yaya dai?????
_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????
Mamu gee??
MIN ?ALB!!????
Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????
Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????
Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????
?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.
[5/18, 3:08 PM] Ummuanwar??: *_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta_*.
No. 27
............Zubewa Yoohan yayi a saman gadon tare da saurin dafe kansa dake barazanar rabewa biyu, sai kuma ya ?an naushi gadon da fa?in, "Noooo!!!". Da ?arfi kamar mai magana da wani.
Tashi yay zaune zumbur yana huci, so yake abinda ya faru yabar ransa, amma tamkar ana ?ara kusanto masa da hotonsa ne a zuciya. Da ya rufe ido babu abinda yake gani sai yana kissing ?in yarinyar da ko sunanta baima sani ba. Mi?ewa yay daga gadon ya shiga toilet ?in dake cikin ?akin, ko takalman dake ?afarsa bai cireba balle kuma kaya, ya ?arasa gaban shower ya tsaya, tare da kai hannu ya murza makunnar da ?arfi, tamkar itace tai masa laifi.
Shaaa!!! Ruwa ya fara sauka masa bisa gyararren gashinsa yana gangarowa fuska. Lokacin da ya gangara cikin jikinsa ya wani saki sassanyar ajiyar zuwa tare da lumshe idanunsa ya dafe bangon da hannunsa duk biyu. A haka ruwan ya cigaba da sauka a kansa, kafin wani dogon lokaci ya gama ji?ewa sharkaf. Sai da yay kusan mintuna ashirin a haka sannan ya kashe shower ?in yana sauke numfashi a jajjere, kafin ya ?arasa saman toilet sit ya zauna yana mai ri?e kansa da hannu biyu....
_______________________
Duk yanda Nu'aymah taso sakewa a sashen Addah ta kasa hakan. Gani take kamar kowa yasan abinda ya faru tsakaninta da Yoohan. Kamar an tsikareta ta mi?e daga zaunen da take kusa da Kubrah. Dukansu da kallo suka bita har suna rige-rigen tambayarta lafiya.
Sai da ta?an saci kallon Addah da tai banza dasu kafin ta amsa musu cike da in-ina. "Um.....u.... Zanje su Aunty Zulfah na jirana". Bata jira amsar su ba tai wuf ta nufi ficewa da ga falon tamkar zata kifa dan sauri.
Karo suka kusan ci da Malam ?arami da ke shigowa. Tai saurin komawa da baya tana fa?in, "Yi ha?uri Yaya, bansan ka taho ba".
Murmushi ya mata da cewa, "Karki damu Aymah. Ashe dama kina nan naje nemanki wajen Umm". ?an kallonsa tayi kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Ya sake fa?a?a murmushin sa, "Dama ba wani abu bane, ba?on da kika ganmu tare a sashen Hajjo ne ya bada barka da salla a baki. Shine naje kai miki na Iske ba?ya nan. Amma na bama Umm ta ajiye miki".
Tunda ya ambaci ba?o gabanta ya sake tsananta fa?uwa. Ta tsaresa da manyan idanunta dake wani mar-mar na rashin gaskiya. Sai kuma ta ?an juya ta kalli sashen da su Addah suke. Su dukansu hankalinsu na wajen. Sai taji hankalinta ya sake tashi. Tai saurin fa?in, "Ni banaso Yaya".
Kafin yayi magana ta fice da gudu daga falon. Shi malam ?arami ma dariya abin nata ya bashi. Hakama su Hajarah. Dan haka suka shiga ?yal?yala dariya banda Kubrah da tai shiru tana kallon wani waje daban.
Hajarah ce ta fara farga da yanayin Kubrah, dan haka ta tsagaita da tata dariyar tana fa?in, Aunty Kubrah ALLAH dama nasan ba ciwon kai Nu'aymah keyiba. Inagafa sabon siriki ta samo ma su Addah shine duk take a ru?an nan".
Uffan Kubrah batacema Hajarah ba. Sai ma mikewa tai ta bar falon tana wani ?an murmushin da su duka basu fahimci ma'anarsa ba......
Nidai nace, "Humm".
"K lafiya? Kika shigoma mutane tamkar wadda aka koro!". Umm ta fa?a a tsawace tana kallon Nu'aymah data shigo falon a guje.
Du?ar da kai tayi ?asa tana ?o?arin ha?iye kukan da ke son zubo mata. Cikin rawar murya tace "Umm babu komai fa, zanje toilet ne". Bata jira amsar kowa ba a cikinsu ta shige ?akinta da sauri.
Dariya su Aunty Zulfah sukayi, sai dai banda Umm da tabi Nu'aymahn da ido dan sam bata yarda da abinda ta fa?a ba.
Tana shiga toilet ?in ta maida ?ofar ta rufe harda murza key. Jingina tayi da ?ofar ta fashe da kuka maiban tausayi. A ranta tana fa?in yaya zatai da wannan abin kunya da takaici da mutumin nan ya aikata a gareta? Ita namiji yayma kiss, namijinma kafiri da baya bautama ALLAH. Baisan idan ya sa?ama UBANGIJI ba ya nema gafara. Baisan haramci ba baisan halacci ba, balle yasan hukuncinsu. Bakinda bai ta?a ambaton ALLAH ba sai shan giya da zina, bakin dake ambaton wanin ALLAH (Shirka) shine yau akan nata. 'ALLAH ya isa bazan ta?a yafe makaba'. Ta fa?a a fili tana sake rushewa da kuka. 'Na shiga uku ni Zainab, ni.........'
"Nu'aymah!". Muryar Umm ta hanata ?arasawa. Saurin toshe bakinta tayi dan kar Umm taji shashshekar kukanta.
"Nu'aymah wai ba?ya jinane?".
Umm ta sake fa?a tana matsowa jikin bayin.
Da sauri Nu'aymah tai gyaran murya. Kafin ta mi?e da sauri gaban tap ta fara wanke fuskarta, kallo ?aya taima mirror tasan idan Umm ta ganta a haka akwai matsala, to amma kuma bata da wani ikon ko dabarar yin wanka tunda yanzu nan tayi sa. Towel tasa ta tsane fuskar tata sannan ta bu?e ?ofar a hankali ta fito.
Ha?a ido sukai da Umm da ke a tsaye tana jiran fitowar tata. Tai saurin kauda idanunta zuwa ?asa da fa?in, "Umm yi ha?uri, ALLAH toilet ne".
"Toilet ko kuka?".
Da sauri ta ?ago ta kalli Umm ?in. Muryarta na rawa tace, "Umm toilet ne ALLAH".
"Toilet ?in ki kai ma kuka kenan?".
Baki ta?an tura gaba, "To Umm gudawa fa ce".
"Mtsoww! K dai bansan randa zaki bar wannan shashancin ba wlhy. Idan gudawan ne bazaki iya zuwa ki amshi magani ba".
"Kiyi ha?uri Umm".
Juyawa Umm tayi ta fice batare data tanka mataba. Itama sai ta sauke ajiyar zuciya tanabin mahaifiyar tata da kallo. Ta tabbatar yau da tasan mita aikata da saita fasa mata baki. Dan Umm tana da zafi idan aka ?ureta, sam bata ?aunar halin banza.
Duk da tana bu?atar ka?aici haka ta daure ta sake gyara fuskarta sannan ta fito falon. Dan bata fatan wani ya gano halin da take ciki. Musamman ma Umm data kasance mace mai saurin fahimta akan rashin gaskiyar yaranta. Ba komai ya jawo hakanba kuwa sai saka musu ido da takeyi a duk motsinsu kwarai da gaske. (Iyaye ya kamata mu kasance haka. muzama kowanne motsin yaranmu nakan idanunmu da zukatanmu kodan gudin yin tuf?a da warwara akan tarbiyyarsu. ALLAH ya kare mana su dai damu baki ?aya).
Tana zama aunty Rafi'a tace, "Hummm! Aymah ina kika samo wannan turaren mai shegen da?i haka?".
Gaban Nu'aymah yay mugun fa?uwa. Ta ?ago da dauri tana kallon aunty Rafi'a. Sai taga har Umm ma ashe kallonta take tamkar yanda su Aunty Zulfah duk suka xuba mata idanu. Ta bu?e baki zatai magana su Nanah suka shigo cikin uhun sallama.
Wata muguwar ajiyar zuciya Nu'aymah ta sauke a ?oye. Tare da saurin mi?ewa zumbur ta nufi su Nanah ta rungume.
Zuwan su Nanah gidan ne ya shashantar da maganar turare. Amma ga Umm sam abin ya?i barin ranta. Dan sai da tai duk dabarar da uwa ta gari ya dace tayi wajen sha?ar ?amshin a jikin Nu'aymah. Ta kuma jisa, ta tabbatar duk gidan kuma batasan kowa da wannan ?amshin ba. Amma sai bataima Nu'aymah maganar ba. Dan tuni su Nanah sun janyeta ma sun fice su da su Amal daga gidan.
____________________
Ya jima zaune matu?a akan toilet sit kafin ya mi?e ya fara zame ji?a??un kayan jikinsa. Wanka yayo, ya fito sanye da Bathrobe fara mai ?an tsaho. Dan ta wuce gwiwarsa ka?an. Towel ?arami ya ri?o a hannu ya fito yana goge fuskarsa da sumarsa.
Kallo ?aya yayma Solomon daya kasa ha?uri ya dawo ?akin duk da korar da yay masa ya ?auke kansa. Kan Solo a ?asa yace, "Kamin afuwa Sir, bazan iya nutsuwa ba bayan kai kana cikin wani hali".
Yanzun ma uffan baice masa ba. Ya dai gitta ta gabansa ya wuce zuwa gaban kujeru biyu dake a ?akin. Zama yay cikin ?aya ya ?ora ?afafunsa saman table ?in dake a gabansu tare da na?e towel ?in hannunsa saman kansa ya jingina bayansa da kujerar ya lumshe idanu.
Shi dai Solomon na tsaye yana cigaba da kallonsa cike da damuwa. A can ?asan ransa kuwa zargine fal ciki akan su baba malam. Gani yake kamar yau rashin bin Yoohan cikin gidan yasa aka cutar da shi........
"Ina bu?atar coffee". Ya katsema Solomon tunaninsa cikin yin magana a da?ile.
Da sauri Solo ya dawo hankalinsa. Ya amsa da "Okay sir" yana matsawa inda telephone ?in ?akin take yay kira domin yin order ?in coffee ?in da Yoohan ya bu?ata.
Ba'afi mintuna uku zuwa hu?u ba kuwa sai ga cikin ma'aikatan yay knocking. Solomon ne ya je ya bu?e ya amso. Ya dawo inda Yoohan ?in ke zaune ido a lumshe ya ajiye tray ?in ?asa dan ya ?aura ?afarsa akan table ?in. Saida ya tsiyaya masa, tare da saka