Showing 258001 words to 261000 words out of 325075 words

Chapter 87 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29182

farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????

?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.[7/1, 2:17 PM] +234 901 860 0202: *_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.


No. 67

............Juliet taso kiran Yoohan ta sanar masa amma Aymah ta hana. A cewarta ta barsa wai dama ta saba irin wannan zazza?in duk shekara. Asibiti ma ta?i yarda suje sai magani data amsa tasha. Daga haka ta fara ?an ?arfafa kanta duk dan ta kwantarma Juliet ?in da hankali ganin ta damu. Gashi itama fama take da kanta dan cikine da ita ?an wata kusan takwas.
Dole Juliet ta barta, sai dai duk motsinta na akan idonta. Ita har mamakin yanda Nu'aymah ke bankar coffee takeyi babuji babu gani. Gason yawan kwanciya bisa tiles wai sanyin take so.
A hankali tama daina cin abinci, dan kotaci sai tayi amansa take samun sau?i. Hakan na damunta, sai dai ta kasa fa?ama ko Juliet ?in balle Umm da Hajjo da Addah da kusan kulumm sai sunyi waya. Ko sun kirata ko ita ta kirasu sai taita ?arfafa kanta yanda babu mai ganewa. Sai dai Uwa dabance. Dan Umm kan tambayeta anya tana lafiya kuwa? Dan a muryarta da yanayin sanyin da tayi na rage surutu da rawar kai Umm takan ji kamar Aymah na cikin wani haline. Amma sai take cemata babu komai, kawai yanayin wajene.
Juliet nada coffee powder a gida, sai dai kota ha?ama Aymah bata sha sai dai suje shagwan shan coffee ta sha tayo guzirinsa kuma. A duk sanda sukai waya da Yoohan ko video call kam sai taita ?arfafa kanta harda masa ?arfin halin tsiwa wai karda ya fahimci halin da take ciki.
Batasan kallonta kawai yakeba, dan tun kafin akai haka ya gama fahimtar shigar ?an tayin cikinsa a mahaifarta. Sai dai ya barma ransa har ALLAH ya bayyana ikonsa da kansa tunda shima hasashene kawai da shegen ganin ?waf irin na likitanci bisa baiwar da UBANGIJIN al'arshi ya azurtasu da shi.

_________________

Kwanan Yoohan hu?u a ?asar Oman ya wuce Nigeria. A abuja ya sauka, sai dai maimakon ya tafi gida direct sai ya sauka a hotel ya kama ?aki. Dan dama babu wanda yasan da zuwansa ?asar a cikin su papa. Yama toshe duk wata hanyar da zasu iya samunsa a waya tun barinsu Austria. Ya fi son yazo su fuskanci juna akan maganar Solomon ?in fiye da suyi magana ta waya.
A daren ranar ya samu aka samo masa Number ?an sandan nan da ?yar ta hanyar wani abokinsa da shima ?an sandan sirrine babba.
Gajiyar daya kwaso ce ta sakashi yin barci da wuri ranar ko waya da Aymah baiyiba. To itama dai da yake ranar zazza?i ya mata rigif ko nemansa batayiba ma.

Washe gari ?arfe goma na safe Omar (Rich) ya iso hotel ?in daga birnin Lagos. Ya iske Yoohan ?in cikin shirin suit royal blue da sukai masa masifar ?yau. Musamman yanzu da yay wani ?an ?ul-?ul dashi saboda madarar angwanci data hudashi. Rungume juna sukai cike da so da ?yauna da begen juna. Kai kace basa waya kullum. Bayan sun gama ?ar chapter ?insu da suka iya suka fito gwanin sha'awa zuwa motar Omar ?in. Omar ne ya jasu zuwa headquarter ?an sanda na jami'an tsaron sirri suna ?ar hirarsu.
Sai da suka gama shan tambayoyi da uban bincike kafin su sami damar shiga da taimakon abokin Yoohan ?in da aka sanarma zuwansu daga baya.
Da ?ar dariya Dawood yake kallon Yoohan daya ciskule fuska saboda haushi binciken da akaita musu yana fa?in. "Yi ha?uri bokan turai, wlhy banyi tunanin zakuzo a yau bane da nazo na tsaya a gate ?in na jira isowarku ai. Tunda aka ?ora mana adalin shigaba a hukumarnan tamu tsaro ya ?ara tsauri dan sam bashi da wasa".
Dariya shima Omar yayi yana ta?e baki. Yace, "Kai Dawood manta da lamarinsa kewar matarsa ke ?awainiya da shi badan wannan binciken yake fushi ba".
Hararsu Yoohan yayi su duka amma baice komaiba. Da haka suka ?arasa can sama inda office ?in oga kwata-kwata na hukumar DSS yake. Duk da Dawood yay masa bayani akan zuwan su Yoohan ?in sai da suka jira shi ya fara shiga office ?in sannan ya fito yay musu iso.
?ya?y?yawan dattijo ne da a shekaru a ?alla zai iya kaiwa 64 Zaune a kan kujerar office ?in hankalinsa gaba ?aya akan Computer ?in dake saman desk ?insa. Batare da ya ?ago ba ya amsa musu sallamarsu cike da nutsatstsiyar muryarsa mai tarin kamala da dattako.
Sosai kwarjininsa ya cika zukatan su Yoohan duk da bai ?ago sunga fuskar tasa ba da ?yau. Da hannu ya?an nuna musu kujerun yana fa?in, "Bismillanku".
Kusan a tare Omar da Yoohan suka sauke ajiyar zuciya da duban Dawood dake ?ame a tsaye. Kai shima ya jinjina musu alamar su zauna ?in. Zaman sukayi tare da ha?a baki wajen fa?in, "Good morning sir".
Cikin ?an fesar da iska Boss *_Jawaad Abdul-aziz Yusif tafida_* ya ?ago gaba ?ayansa fuska babu walwala kamar ko yaushe yace, "Good Morning". yay maganar da mi?a musu hannunsa alamun suyi musabuha.
Omar ne ya fara mi?o masa hannun suka gaisa, kafin ya mi?ama Yoohan da shima zuciyarsa ke wani bugawa da harbawa da sauri-sauri. sai dai cike da dauriya ya fa?a?a fuskarsa da murmushin ?arfin hali.
Da ga shi har Boss Jay zukatansu suka buga da ?arfi. Hannun Yoohan ya dinga rawa dan yama kasa ?arasawa da shi inda na Jay dake ?o?arin zare glass ?in idonsa yake.
Hakan yayi dai-dai da shigowar wata kamilalliyar mace da shekarunta zai kai kimanin 53 cikin office da sallama, hannun ta ri?e da takardu. Sanye take cikin doguwar rigar jallabiya ba?a. Shigar tata ta ?ara fidda kamalarta da mutuncinta ga mai kallonta.
Akan mijin nata ta fara sauke idanunta da mamakin yanayin data gansa. Sai kuma ta maida dubanta ga abinda yakema kallon ru?ani da tsoro. Baya tayi da sauri har takardun hannunta na watsewa a ?asa. Saurin sunkuyawa Dawood da ke binsu da kallon mamaki yayi yana tattare takardun da fa?in, "Am sorry maa".
Bilkisu bata iya cewa komaiba sai takawa da tai da sauri inda Jay yake. Zatai magana yay saurin dam?e hannunta alamar shi ya dawo cikin hankalinsa. Girgiza mata kai yayi alamar kartace komai. Sai ma wayancewa yayi da fa?in, "Wai nikam da gaske likitan da naso gani ruwa a jallo shekara ?aya data shu?e ne amma hakan ya gagareni a gabana?".
Duk da Yoohan yaji sam a ransa ba wannan batun bane jefa adalin ma'aikacin cikin ru?anin ganisa sai shima ya sauke ajiyar zuciyar da sam bata samun nutsuwa bace. Cike da ladabi ya jinjina kansa yana murmushin ?arfin hali. Dan wani masifar kwarjini da Jay ya masa. Yace, "I'm very sorry sir. Nasan ni mai laifine sosai a gareka".
"No no no son. Inama mutane irinka uziri sosai ni a rayuwa. Dan haka manta kawai da wancan batun, tuni an kauda matsalarma". Jay ya fa?a yana maida glasess ?insa akan ido.
Cike da jin da?i Yoohan yace, "Thanks you Uncle". Sai kuma ya ?an kalli Bilkisu da alamu suka nuna har yanzu tana a cikin ru?ani ita dai yace, "Good morning maa".
Da wani irin sanyi tace, "Good morning dear". Shima Omar (Rich) da al'ajabi ya cika gaisheta yayi. Ta amsa masa da kulawa shima tana duban Jay da har yanzu idanunsa akan Yoohan suke. Kauda kansa yayi ya ?an dubeta saboda ta?a masa kafa?a da tayi. Murmushin ?arfin hali yay mata da nunama su Yoohan ita fa?in, "My wife. Itace naso na kawo maka a wancan lokacin muka gagara samun dama. Itama ma'aikaciyace a wannan hukumar. Amma Alhmdllh, daga baya mun fahimci babu waccan matsalar da mukai zargi".
Cike da girmamawa Yoohan da Omar sukace masha ALLAH. ALLAH ya ?ara kiyaye gaba.
Amin suka amsa musu. Bilkisu data fahimci zamanta a wajen zai iya kawo matsala sai tai ?anyi murmushi da ran?wafawa saitin kunnensa tai magana. "Bara naje, su Zuhrah na jirana zamu wuce. Ga takardun nan duka na ha?o maka na case ?in matar nan mai safarar ?wayoyi".
Kansa ya jinjina mata kawai yana murmushi. Yana son ?an sumbatar matarsa babu dama. Dan haka ya kashe mata ido ?aya cike da salon ?warewar manyan masoya????.
Itama murtani ta maida masa da nata salon taima su Yoohan sallama ta fice. Numfashi Jay ya furzar a ?oye. sannan ya maida duka hankalinsa gasu Yoohan da kansu ke a ?asa. Dan gaba ?aya zuciyar Yoohan ta gaza samun nutsuwar zama a waje ?aya. Yadai dage yanata ambaton sunayen ALLAH kozai samu sassauci daga abinda yakeji cikin jininsa.
"Tom Doctors ina saurarenku. Dawood ya sanarmin kuna son ganina cike da magiya a garesa. Ina fatan dai lafiya ko?".
Omar yace, "A lafiya lau sir. Wani taimako mukazo nema ne a wajenka da alfarma akan wani case".
"Okay. Babu damuwa. Dawood zoka ?auka dukkan bayanansu dan kar a samu kuskure ko".
Da tsantsar girmamawa Dawood yace. "Okay sir". Yay maganar da ?ame jikinsa waje guda yana buga kafarsa ?asa. Hannu Jay ya?an mi?ar alamar amsawa. Daga haka ya ciro takarda da pen ya zauna ya fara sauraren bayanin da Omar ya farayi kasancewar Yoohan ya sanar masa komai dangane da gidan su Aymah akan abinda yaji daga gareta da wanda ya sani.
Sai da ya kai aya Jay ya sauke numfashi yana janye pen ?in da yake gogawa saman la??ansa. Ya ?an murmusa da fa?in, "Babbar magana. ?an jibiya family kam ba ?oyayyan gida bane. dan ahaline na masu daraja saboda ilimin addini da harkokin kasuwancinsu. So dama akan samu irin wa?anan rikice-rikicen da ZAGON ?ASA a irin mafi yawan wa?an nan gidajen. Shi kuma zagon ?asa Kamar wani SARAN ?OYE ne mai cin rai da ru?a tunanin wanda akemawa. So na tayaku murna tare da shigowarku cikin hasken musulinci. Na kumayi al?awarin taimaka muku wajen ban ka?o abinda kuke bu?ata bisa son ?yautatawarku ga Sheikh Soorajidden Hashim. Saboda nima malamina ne ai. Kuna ambata masa sunana zai baku labari. Har ?aurin aurenku naje ma. tabbas kwanaki dana bu?aci zuwa wajensa muyi magana ya sanarmin zaiyi tafiya za'aima yarinyarsa aikin ?wa?walwa a ?asar ?etare".
Da jinda?i a fuskokinsu suke dubansa.
Shima murmushi yayi yana zare glasess ?insa. ya cigaba da cewa, "Ina ?aunarsa sosai dan yayima rayuwata hidima mai yawa. Insha ALLAH nima bazan gajiya ba wajen banka?o azzalumai masu cin dunduniyarsa. Sai dai wannan aikin dolene ya kasance na sirri". Yakai ?arshen maganar da duban Dawood.
"Dawood! Ina bu?atar ganin Bilkisu Jawaad".
Da sauri Dawood ya mi?e yana fa?in, "Okay sir".

Cikin mintuna ?alilan sai ga Dawood ya dawo tare da matashiyar mace da bazata gaza shekaru talatin da biyu zuwa da uku ba. Daka ganta babu tambaya kasan jinin Boss Jawaad Abdul-aziz ce. Sanye take cikin wando da riga na Uniform ?in hukumar. Da alama itama jami'ace a hukuma (dan ?ari. Bilkisu ?ar bilkisu jikar bilkisu kenan??. Ita ?ar sanda, mamanrta ?ar sanda. Babanta ?an sanda??. Wani aiki sai Jay??lol).
Fuskarta cike da miskilancin data gada wajen iyayenta ta ?ame tare da salute ?in mahaifinta kuma oganta a wajen aiki. tace, "Sir gani".
Daga Yoohan har Omar kallon mamaki suke mata. Dan basa bu?atar ?arin bayanin komai game da Biljay.
Takardar da Dawood ya rubuta ya mi?a mata cike da bada umarni a gareta matsayin oga ba mahaifiba. "Duba min wannan takardar".
"Okay sir" ta fa?a tana ?aukar takardar. Cike da haza?ar ?warewar aiki ta duba rubutun takardar tsaf, kafi. ta ?ago ta kallesa tana sunkuyar da kanta da ?amewa. "Na duba Sir".
"Me kika fahimta?".
"Report ne na case ?in ?oyayyun mutane masu laifi".
"Masha ALLAH. Little bee kece zakiyi wannan aikin. Wa?anan sune masu kawo Report ?in. Zakiyi joining ?insu kuyi aikin tare. Sai dai kece zakiyi kutse a cikin gidan ko mubi ta wata hanyar insha ALLAH. Kinsan banson wasa, bana son kuskuren ganganci akan aiki, so be careful".
"Insha ALLAH sir".
Kai ya jinjina mata da maida dubansa kan Dawood. "Dawood tare zakuyi wannan aiki da ita, so zata kasance ?ar?ashin control ?inka, dukanku kuma zaku kasance akan umarni".
Shima ya amsa da "Okay sir".
Daga haka Jay ya maida dubansa gasu Yoohan. "Doctors wa?anan nan sune zasu taimaka muku akan wannan case. Insha ALLAH daga nan zuwa kwana uku zamu san wadda zata shiga cikin gidan matsayin maiyin hutu a wajen Sheikh. Sauran aiki duk zasu yisa baku da damuwa. Sai dai dole kuma sai da hannunku a ciki dan kun fisu sanin sirrin gidan a yanzun. Zaka ha?ata ?awance da matarka ta waya. Dan wasu abubuwan ta hanyartane zasu sami haske sosai. Duk abinda ya dace zaku cigaba da ji ta hanyar Dawood, dan shine oganta".
Godiya sosai su Yoohan suka shiga yimasa. Dan sam basuyi tunanin samun mafita cikin sau?iba haka daga garesa oga kwatakwata da ganinsama ke da matu?ar wahala. Yanda bai musu bayani akan matsayin Bilkisu a garesaba suma basu tambayaba duk da sunada bu?atar ji.
A tare da shi suka fito office zuwa massalaci saboda kiran sallar zuhur. Bayan an idar da salla kuma sukai masa sallama da ?arin godiya suka wuce cike da farin cikin wannan karamci da samun sau?i. Sai dai ?asan ran Yoohan shi ka?ai yasan mi yakeji game da Jay ?in.
Koda suka ?auki hanya kasa ha?uri Omar yayi sai da yayima Yoohan maganar kallon da yaga Jay ?in na masa da matarsa. Harma hanata maganar da yayi. Tare da cewa nifa, "Wlhy fisgen kamannima kukaimin".
Da mamaki Yoohan yace, "Kamanni kuma?".
"Yes X-man. Wlhy a fisge kunyi kamanni like na jini haka".
Nannauyan numfashi kawai Yoohan yaja da ?arfi ya fesar batare da ya iya cewa komaiba har suka ?arasa wani gidan cin abinci. Anan sukai lunch da cigaba da tattaunawa akan abinda ya shafesu. Daga haka sukawuce General hospital wajen Dr Shikurah. Sai dai sunyi rashin sa'ar samunta wai batama ?asar.
Yoohan yayi gaisuwa da abokan arzi?i suka koma hotel ?in daya sauka. Omar ya jima a wajensa dan har dare suna a tare sannan ya koma gidan papa dan acan ya sauka shi. Amma sai bai fa?ama kowa Yoohan na ?asarba.
Washe gari Yoohan yaje kaduna yin wani aiki. Sai washe garin daya cika kwana uku a 9ja ya dawo. Dai-dai da ranar da Little bee zata shiga gidan baba malam kenan. Dan haka kai tsaye gidansu ya nufa. Sai dai kawai su Madam Chioma suka gansa tsilum tamkar daren Christmas inji su.

___________¡ï¡ï

Tun wucewar su Yoohan Jay ya kasa zaune ya kasa tsaye a office ?insa. Gaba ?aya man kan sa ya gama tsiyayewa tas akan wannan kamanni. Goshinsa ya murza da cewa, 'Kai anya kuwa. Dolene nasan wanene wannan yaron'. Ya ?are maganar da ?aukar telephone yay kiran Dawood.
Dandanan Dawood ya amsa kiran boss. Nuna masa kujera yayi alamar ya zauna. Bayan kusan mintuna uku ya ture files ?in gabansa yana kallon Dawood ?in.
"Dawood nikam a ina kasan yaron nan ne?".
Cike da girmamawa ya bashi amsa da fa?in, "Sir, tare mukai secondary school da su".
"Masha ALLAH, lallai kayi masa sani na sosai. Anan cikin abuja suke?".
"Yes sir. Ai yaron sanannen Pastor ?in nanne Goshpower mai ?aton catholic church ?in nan dake a wuse2".
?an jimm Jay yay yana kallon
Dawood. Sai kuma ya sauke numfashi ka?an yana wani guntun murmushi mai kama da an masa dole. "Okay thanks you, zaka iya tafiya".
Mi?ewa Dawood yayi tare da salute ?insa ya fice yana mamakin tambayoyin ogan nasu.

Dawood na fita Jay ya shiga Google. Bayanai ya nema akan dukkan handles ?in papa dake a social network. Cikin mintuna ?alilan kuwa suka watso


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login