Showing 309001 words to 312000 words out of 325075 words
nan. "Kaga mahaifiyarka nan Yah Yoohan, wlhy ba wannan shai?aniyar bace. Bana tantama akan har mijinta ba shine ya haifeka ba, akwai abinda suke ?oye maka. Iyayenka na gaskiya bazasu sace maka ?anka ba. Mahaifiya ta ?warai bazata so tarayya da ?anta ba koda kuwa bata da addini, sai dai idan dabbace ita mai juyayyen tunani.........."
"Hhhh da ?yau tsagera". Madam Chioma ta fa?a tana dariya har yanzu bindigarta na akan Yoohan da zantukan Nu'aymah sukema kai kawo a rai. Ta cigaba da dariya da fa?in, "Ashe tsaurin idon naki ya kai haka? Ko da yake ashefa kinsan zafin haihuwa ko? Hhhhhhh. Ashe kuwa za'a kwashi gawa da yawa a hotel ?in nan yau". Tai maganar da ha?e fuska ta nuno Nu'aymah da bindigar.
Cikin kaushin murya Umar yace, "Kibar wannan haukar da kikeyi ki ajiye bindigar hannunki kawai madam".
Kallonta ta maida garesa. Cikin yatsina fuska tace, "Richard kake kowama? Kai kuma a suwa shiga family issue?. Maza kama kanka wannan ba shigarka baceba....."
Kafin ta rufe baki taji an hanka?ata, sai ga ta ita da bindigar ?asa wanwar. Da sauri ?aya a cikin ?an sandamln ya ?auke bindigar, wani kuma yazo ya danna mata ankwa ta baya. Yaran nata ma duk an kamesu. Nu'ayma kuwa da gudu ta ?arasa jikin Yoohan dake a ?aure ta rungumesa tana fashewa da kuka. Biyota Umar yayi ya fara warware igiyar da suka ?aure Yoohan ?in da ita, itama Aymah sai ta mi?e tana taimaka masa. Suna gama kwancesa ya rungume abarsa yana shafa bayanta. Sai dai bakinsa ya kasa furta komai saboda irin tafasar da zuciyarsa ke masa. Hoton hannun nata ya zare ya kafe balarabiyar jiki da kallo tare da papa dake gefenta. Jiyay wani abu na tsarga masa tun daga zuciya har zuwa tafin ?afa. Ya kafe fuskar papa yana nazari sosai akansa batare da su Nu'aymah sun fahimci abinda yake nazartarba. A hankali ya janye Aymah a jikinsa yana mi?a mata hoton, gaban madam Chioma ya karasa. Babu wani kace nace yasa ?afa ya ta?e ?afafunta sai gata a ?asa ta zube. Kasancewar hannayenta ?aure suke ta baya da ankwa sai ta fa?i a rubda ciki. A take goshinta da hancinta da baki suka fashe, ha?oran gaba guda biyu sai gasu a ?asa.
Wata wahalalliyar ?ara ta saki. Yoohan yasa hannu ya birkitota ta dawo rigingine. Gaba ?aya fuskarta ta gama damewa da jinin raunukan data samu, "Ina ?ana?". Wannan itace kawai tambayar daya jefa mata batare da ya damu da yanda jini yayma fuskarta jage-jage ba.
Kanta ta shiga girgiza masa, cikin rawar murya da la??a tace, "Nima ban saniba John, Please ka yarda da ni".
Uffan Yoohan baice da itaba, sai bindigar hannun ?an sanda ?aya ya fisge ya ?ora mata a goshi. "Humm ke ?aramar ?ar iskace ashe. Idan kika cigaba da min gardama ba shakka zan tarwatsa ?aramar ?wa?walwarki da harsashin cikin bindigar nan. Idan kinada taurin kai tun kan haihuwata, ni ki ?auka bayan haihuwar tawa na damaki na shanye. Da kika ganina anan tsageran kainane nima wlhy. Fa?amin ina Yarona yake?".
Wutar bala'in da madam Chioma ke hangowa cikin idanun Yoohan ya sata saurin fa?in, "Zan gaya maka, amma ka taimakeni ka cikamin burina nima, kayi tarayya dani koda sau ?aya ne naji sanyi a raina John. Ka tausayama wahalar danasha a kanka ta tsahon shekaru".
"Lallai k! a tumakin ma balama ce". Yoohan ya fa?a yana cije baki da ?ana kunamar bindigar ya maida bisa tsakkiyar kanta.
Jikinta karkarwa ya farayi, tana kuka tace, "Kayi ha?uri karka kasheni zan fa?a maka Jonh. Na rantse zan fa?a maka. Yaronka na a hannun Papanku acan wani gida dake cikin G.r.a, nima ya sakanine na kai masa kai, shine nai amfani da wannan damar domin fara cikama kaina burina a kanka na tsahon shekaru. Na biyo da kai tanan kafin na mi?aka wajensa. Miracle ita aka saka ta sace maka yaro a wajen bikin da kukeyi, dan dama muna biye da duk wani motsinku......."
Duka ya kai mata a fuska ?an sanda yay saurin ri?esa. "Cool down Mr Yoohan. Karka damu dolene ta kaimu har inda suke ai. Kwantar da hankalinka kaji".
Huci kawai Yoohan ya keyi, tsabar zuciyar dake cinsa sai ga hawaye sharrrr suna sakkowa. Matsowa Nu'aymah tayi ta ri?e masa hannu batare da tayi magana ba. Da sauri ya jawota jikinsa ya rungume ko zaiji sassaucin zuciyarsa.
An tattara yaran madam Chioma zuwa police station da su. Su kuma su Yoohan da sauran jami'an suka shiga motar da aka sato Yoohan tare da madam Chioma bayan an sakata kiran papa ta sanar masa cewar gata ta samo Yoohan harda Nu'aymah ma. Wani ihun gigitacciyar dariya papa ya saki har su Yoohan na jiyosa. Umar da Jami'an sun rufe fuskokinsu tamkar su ?inne yaran madam Chioma. Itace ta dinga nuna musu hanya har suka isa anguwar. A daidai ?ofar gate ?in gidan suka tsaya. Maigadi na le?owa yaga motar sai ya bu?e da tunanin su madam Chioma sun ciyo nasara suma.
Yoohan da Nu'aymah aka sakama ankwa a hannu suka fara shiga, jami'an tsaron da fuskokinsu ke a rufe na biye da su a baya. Umar ne ?arshe da madam Chioma a gabansa. Acan waje dama tuni ?an sanda sun gama zagaye gidan dan dama babban burinsu shine kama papa da sauran mutanensa. Abinda suka share watanni biyu suna nema ga dama ta samu a lokacin ?an?ani.
Da sauri Papa dake zaune cikin kujera su Joshua zagaye da shi duk suka mi?e sabida ganin Yoohan da Nu'aymah. Deen na kwance akan centre table ?in falon cikin showal ?insa. Yayi kukan wahala har ya gaji yayi barci. Gefensa an ajiye shar?e?iyar wu?a.
Cike da wata irin mahaukaciyar dariya papa ya shiga tafa hannayensa yana kallon su Yoohan.
Ya tako gabansu a hankali batare da tunaninsa ya haska masa cewar wa?anda ke bayansu ba yaransu bane ba. Da dariyarsa ya shiga fa?in, "Oh my Son & Darling daughter in-low ?ina. Welcome to my new land. Nice meeting you my guys".
Da ga Ayma har Yoohan dai kallonsa kawai suke. Papa ya kalli jami'an da yake tunanin yaransa ne yana fa fa?in, "Ku cire musu ankwa amfaninta ya ?are ai. Dan game zamu buga da su mai zafi".
Babu musu ?an sandan nan suka cirema su Yoohan ankwa. Komawa papa yay ya zauna a kujerar daya taso. Ya ?an ta?e bakinsa da dora ?afa ?aya kan ?aya ya ?auki kofin giyarsa ya kur?a yana kallon su Yoohan. "John badan inada ?arancin lokaci ba dana baka wani labari mai ban mamaki da al'ajabi. Amma share kawai muje ga game ?inmu. Idan lokaci ya rage mana a cikinsa sai na baka labarin. Daughter in-low karki tada hankalinki kinji, ?anki yana lafiya, kingama barci yake abinsa". Yay maganar da tasowa daga kwanciyar da yayi jikin kujera ya yaye showal ?in da deen yake ciki yana lakatar hancin yaron da ?an yatsa. "Daughter kin iya haihuwar ?a fa". Ya fa?a yana kecewa da dariya su Mike na tayasa. Giyarsa ya kwankwa?a ya ajiye kofin yana ha?e hannayensa waje guda. "Oh Sorry my son karka fusata na sanka da zuciya". Takardun dake a gefen Deen ya jawo ya tura ?arshen tebirin ta sashen da su Yoohan suke. "Wannan takardun sune game ?inmu tare da ?an jinjirinku ?ya?y?yawa. John kanada za?i biyu. Ku?utar da yaronka ta hanyar yimin signing a duk takar dunnan, ko kummaaaaa nai masa yannnnnkan rago da wannan wu?ar tawa a wannan lallausar fatar tashi". Ya ?yal?yale da dariya yana ?ora wu?ar bisa cikin Deen dake barci a binsa yanata sakin ajiyar zuciyar kukan da yasha.
Ko motsi Yoohan baiyiba, haka ma Nu'aymah duk da hankalinta a tashe yake kallon papa kawai take zuciyarta na tunanin anya kuwa wannan mutumin ma mahaifin Yoohan ne?
Hannunta taga Yoohan ya saki tare da takawa a hankali zuwa gaban papa yana wani ?ya?y?yawan murmushi, dan cikin ?an sandan nan ?aya yay masa alamar yaje. Zuwa yanzu sunsan sauran ?an uwansu sun gama tattare yaran papa gaba ?aya dake cikin gidan. Sannan sun gama nazarin su papa kaf babu wani makami tare da su anan sai wu?ar dake akan Deen. Babu wani alamar damuwa a fuskar Yoohan balle tambayar papa ba'asin yin hakan. Yazo gaban tebirin ya zauna akan ?aton tum-tum dake kusa da shi yana murmushi. Cikin kwanciyar hankali ya ?auki pen ?in dake saman takardun ya rike a hannu. Shafin farko na takardun ya karanta cike da nazari. Ya?an ?ago ido ya kalli papa da shima ke kallonsa. Murmushi Yoohan ya sakar masa da taune lip ?insa na ?asa ya ?age gira ?aya da lumshe idanunsa ya sake bu?ewa akan takardun. Har cikin jini Murmushin Yoohan ya daki zuciyar papa da su Mike. Amma sai basuyi magana ba. ?aya bayan ?aya Yoohan ya fara signing takardun. Yana gab da gamawa Mike da ya farga babu Madam Chioma. yace, "Brother wai nikam ina madam ma ne? Ta kawo mana su amma banga ta shigoba ita".
Da sauri Papa ya kalli Mike, sai kuma ya kalli Yoohan dake signing yana murmushi da taunar lip dinsa na ?asa. "John mikake kullawa? Ina matata?".
Ko motsi Yoohan baiyiba balle ya kalli papa. Sai da ya gama signing ?in duk takardun sannan ya kalli papa da tsoro ya fara bayyana masa a fuska. Wu?ar kan Deen ya dauka yana fa?in, "Ashe kuwa inhar wani abu ya samu matata saina halaka wannan yaron".
Murmushi Yoohan ya sakeyi har ha?oransa na bayyana. Ya mi?e tsaye hannunsa ?auke da takardun da yay Signing. Ya?an sosa pen din a gefen wuyansa yana duban papan. "Oh my sweet papa ya da karaya haka da wuri?". Yay maganar da wani shegen murmushin ya?e. Sai sukaga ya girgiza kansa yana ?an bu?a hannayensa. "Karfa ka damu papa. taya zan cutar da mahaifiyata. Guys Please ku kawo masa matarsa". Ya juya yana kallon ?an sandan nan. Umar dake can ?ofar falon bai shigoba ya turo madam Chioma ta fara shigowa bakinta a ?aure. Bindiga a bisa kanta.
Wani irin zabura papa yayi jikinsa na rawa. Kafin yay magana Yoohan yay ?ar dariya yana fa?in, "Oh my sweet papa relaxxxxx!!. Idan ban mantaba kace zamuyi game ko? So karka damu bazan canja ba zamu buga ai. Nasan kana son matarka, ba kuma zakaso rasata ba, gata ?ar ?ya?y?yawa kuwa". Yay maganar da wata shegiyar dariya. Sai kuma ya gimtse fuska da ha?e hannayensa waje guda yace, "Oh sorry papa bazan sakeba. Ga takardu na maka signing kamar yanda ka bu?ata. Sai dai kana da za?i. Matarka ko wa?anan takardun. Idan su kafi bu?ata, zan baka, amma zan tarwatsa kwanyar matarka a gabanka. Idan kuma matarka kafi bukata, zaka bani ?ana, na kuma wuce da takardun nan a gabanka. Wannan shine game ?in Yahyaaaaaa! Much??! much??!!, I love you my papa!!". Suka kwashe da dariya a ?arshen maganar shi da Nu'aymah tare da tafawa.
Wani irin huci papa ya fara fitarwa kamar zai shi?e. Ya kai hannu zai fisgi wu?ar nan Yoohan yay saurin fa?in, "No! no! no no no no!!!! Pastor goshpower. Karka fusata da yawa fa, kasan ?an naka mai fa?a da cikawa ne. Ai yanzun game ya tashi daga tsakanin takardu da yarona, ya koma tsakanin takardu da matarka ok?".
Kafin papa yace wani abu Yoohan ya fisge handkerchief ?in da suka ?aure bakin Chioma da shi. Wani wahallalen ?ara ta saki da fashewa da kuka. Cikin ro?o tace, "Please Darling ka basu yaronsu, ka taimakeni, na rantse john zai iya kasheni, kagafa yanda ya ciremin ha?wara, karkai jayayya dasu nan duk jami'an tsarone ba yaranmu ba".
"What!!!".
Papa da su Mike suka ambata a firgice. A take duk jami'an tsaron da Omar suka janye abinda suka rufe fuska. Sai ga wasu na shigowa suma akai ma su papa zobe. takawa Yoohan yayi gaban papa yana dariya ya ?auki Deen ya rungume a jikinsa tare da sumbatar goshin yaron. Da sauri Nu'aymah ma ta matso garesa ta ha?ashi shi da yaron ta rungume. Umar kuwa ya damkama ?an sanda Madam Chioma ya matso ya ?auki takardun da Yoohan yayma Signing yana dubawa.
"Kai!! Dude!, anya kuwa mutumin nan ma shine mahaifinka kuwa?"..
?agowa Yoohan yayi daga sumbatar kumatun Deeen, yasa hannu ya share hawayen da suka cika masa ido yana mi?ama Nu'aymah yaron. Yace, "Goyashi akwai sanyi". Babu musu Aymah ta juya ya ?ora mata Deen a baya ta goyashi, ya gyara mata hijjab ?in jikinta sannan ya dubi Umar da yay tambayar da furzar da zazzafan huci.
"Bana zaton haka Umar, dan abubuwa da yawa sun banbanta tsakaninsa da wanda ke a hoton nan. Sannan wa?anan takardun mallakin kaddarorine a cikinsu wanda alamu suke nuna ba nasa bane sam. Dan signing ?in cikinsu ba irin nashi baneba. Akwai sirrin da yake ?oyema duniya a kaina........"
"Sirri mai girma kuwa".
Muryar da basuyi zato ba ta kara?e kunnuwansu a bazata. kusan gaba ?ayansu suka dubi bakin ?ofar inda maganar ta fito. *Jawaad Abdul-aziz Yusuf* ne tsaye cikin ?ananun kayan da suka rage masa shekaru, sai dai duk wanda yasan shekarun girma ya kallesa yasan shi?in bana wasan yara bane, (Duk ya girmi masu karatu yanzu, duk da a gabansu aka haihesa????????).
Bayansa jami'ai ne biye da shi. Cikin falon ya karasa shigowa ya zauna a kujerar da ke kallon papa dake a dur?ushe bisa gwiwoyinsa yanzu shi da su Anthony saboda zagayesu da akai da bindugu.
?afa ya ?ora ?aya kan ?aya yana wani shegen murmushi, yace, "Hii Goshpower, sai kuma gaka. Hhhh ALLAH sarki. Haka rayuwa take ai, duk iya gudun mai tsere bai isa zarta ?addararsa ba. Dama naji a jikina dole ka dawo, dan yanzu da dukiyar da wannan takardun kawai kake tunanin ka tsira. Kafa birgeni, dan da gaske ka iya wasa. Kana da basira ?warai da gaske. Sai dai kuma kanada da?i?anci a wajen kuskuren lissafi. Da ace bakabar Yoohan a raye ba da lissafinka bazai ta?a ?ata ba. Sai dai kash a dalilin ?wa?ayin abinda baka taraba ka saka kanka a tarko tsahon shekara talatin da biyu. Tsem! Tsemm tsemmm!!! Gaskiya ka bani tausayi. A farkon labarin dai cike yake da birgewa da ?ayatarwa ga marubucinsa. Sai dai a ?arshe an samu dagulewar ?wa?walwa ga marubucin. Mai makon yanda aka fara da nasara a ?are da nasarori sai aka ?ige da fa?uwa ?asa wanwar. Kash matsalar tunani ko Mr goshpower".
Jay yay maganar ?arshe yana ?age gira da sakin dariya. Ya cigaba da fa?in, "Oh sorry bara na ta?aita, dan ka sani tafiyar da ban shiryaba a daren nan daga Abuja zuwa kano ga uban sanyi. Maganar gaskiya ma ban yafe ba. ?an jarida ku shirya kayan aiki". Ya fa?a yana shafar girarsa da nuna hanyar ?ofa.
A take kuwa suka shigo kusan su shida. Duban Yoohan da Nu'aymah da Umar yay ya nuna musu kujerun alamar su zauna suma.
Zama sukai a sanyaye kamar an doke gwiyawunsu da ?arfuna.
Jay ya kalli agogon hannunsa sannan ya dubi papa. "Mr Goshpower bamu da isashen lokaci, dan awoyi uku da mintuna ashirin da ?aya suka rage alfijir ya keto. Bana son wasana da kai yay tsamari a wannan ga?ar dan daga ni har kai mun jigatu, inason sanin wanene Yahya? Su wanene kuma wa?anan na jikin hoton?".
Shiru papa yayi ya ?i magana, hakan yasa Jay ?inma bai sake magana ba, sai kawai ?arar bibdiga su Aymah sukaji da ?arar papa. Ru?ewa Aymah tayi ta ?wa?ume Yoohan jikinta na rawa. Ga Deen dake bayanta ma ya farka da wani irin firgitaccen kuka. Taimaka mata Yoohan yayi ta sakko da shi, ya rungumesa a jikinsa yana jijjiga shi. Da kallon papa da Jay yayma harbi biyu a duka ?afafunsa saboda tsabar ?warewa a iya harbi.
Jay ya girgiza kansa da dafesa. Yace, "Oh kana neman fusatanine Mr Goshpower. Gashi ni kuma hannayena ?ai?ayi sukeyi. Na fa?a maka a jigace nake matu?a, karka jani da nisa ana idar da sallar asuba nake son komawa Abuja".
Cikin magautar ra?a?i papa ya fara magana. Ga wata irin zufa ta ji?esa a take duk da uban sanyin da ake zubawa a garin. Yace, "Shima sunansa Goshpower, shi ?in twin brother ?inane. Wannan kuma matarsa ce".
"Yayi ?an gari, haka nake bu?atar jinka. Omar a cire masa bullets ?in nan".
Da sauri Omar yace, "Okay Uncle ".
Tsabar son azabartarwa Umar sai ya ?auki giyar da papa yasha ya rage ya zuba masa akan harbin. A take kuwa ya saki wata wahalliyar ?ara ya suma. Ko a jikin Omar. Ya amshi First aid box a hannun wani jami'i da sukazo da shi ya cire bullets ?in cike da rashin tausayi. Sai da ya kammala komai sannan aka zubama papa ruwa ya farfa?o.