Showing 165001 words to 168000 words out of 325075 words

Chapter 56 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29191

dai bai kulataba ya ?akko kofin shayin ya mi?a mata.
"Ban sha" ta fa?a tana kuma matse jikinta a cikin bargon. Sake tsuke fuskarsa yayi da ?yau sannan ya kalleta, dan duk da da hausa tayi maganar sarai ya jita. Sake mika mata kofin yay tare da matso da fuskarsa gab da tata. Yace, "Silly girl! Koki kar?a ko ki sha allurai a bom-bom ?inki yanzun nan".
Duk da tsoratar da tayi sai da tace masa ?an iska a zuciya, saboda kalmarsa ta ?arshe-?arshe. kofin ta amsa tana hawaye da tunzura baki gaba. Shi dai bai kulata ba, sai hararar Rich da kema su Osin gulmar ha?uwar matar Yoohan ta waya da yare yayi. Richard yi yay kamar bai gansa ba ya cigaba da rattafa bayani dalla-dalla.
Nu'aymah bata son shan shayin amma tana tsoron allura, hakan yasa ta daure ta shanye duka tana hawaye. Amsar kofin yayi yana sakin wani shegen Murmushin gefen baki. Aymah kanta sai da Murmushin ya daki zuciyarta, dan tunda ta sanshi a rayuwarta bata ta?a ganin yayi murmushi ba sai yanzun. Saurin ri?e bargon da take neman rufama har kanta yayi.
"Ban gama da ke ba". Yay maganar a hankali tamkar mai yin ra?a. Cikowa idanunta sukai da sabbin hawaye. Ta ture hannunsa dake ri?e da bargon tana fa?in, "Bana shanye ba, nifa ka takuramin da yawa, yanzu ba da bace inada aure ka daina ta?ani banaso".
Da ?an wani salo yace, "Oh really? Smalley! Waye mijin to?".
Sosai rawar sanyin nata ya fara raguwa, sai ma wata zufa dake taruwa mata a goshi, hakanne ya saka bakin tsiwar tata sake fitowa fiye da sanda suka shigo. Tai masa wata irin harar da ta saka tsigar jikinsa tashi tana murgu?a baki, "To ina ruwanka shugaban masu shishshigi. Idan ka gama abinda ya kawoka zaka iya tafiya".
Bakinsa ya ta?e ya ?auke kai tamkar bai ji mita fa?a ba. Sai ma aljihun jeans ?in jikinsa daya laluba ya zaro ledar daya ?akko daga mota. Wani ?an kwalin magani ne ?arami ya zaro. Ya fiddo maganin ciki ?an kanana, a gaban idonta ya ?alli ?aya, sai taga ya rabashi biyu ya maida rabin a ramin daya ciro ya li?e tare da sakawa a kwalin. Mi?ewa yay zuwa inda Rich ke zaune har yanzu yana waya, ya halbi ?afarsa sannan ya ?auki gorar ruwa ?aya cikin wa?anda aka ajiye musu ya bar wajen batare da ya kula Rich daya ri?e ?afarsa da yaji zafin halbin da yay masa ba.
Duk abinda suke Aymah kallonsu, har addu'a tayi a ranta ALLAH yasa Richard yace sai ya rama koda sun fita ne. Cikin katse mata tunanin muguntarta ya mi?a mata maganin dake cikin hanun nasa. Baki ta bu?e zatai magana yay saurin ?aura yatsansa kan baki yace, "Shiiii!! bana son musu malama, ki kar?a inada abinyi jirana akeyi". Da mugunta tasa yatsu biyu zata ?auki rabin maganin dake cikin lallausan tafin hannunsa da jini keta kai kawo tamkar zai tsillo waje. Saita ha?o da fatar hannun ta mintsina da ?arfi. Duk da yaji zafi sai baiko motsa ba balle ya nuna yasan mi tayi. Tai masa harar gefen ido tare da jefa maganin a bakinta tana fa?in, 'Sai shegen dauriya wai shi jarumi, ai ko baka nunaba nasan wlhy kaji zafi' ta ?are zancen zucin nata da jefa maganin cikin baki.
Shi dai yana kallonta ne ?asa-?asa. Ya mi?a mata ruwan hannun nasa, babu musu ta amsa ta tuttula cikin baki tana yamutsa fuska tamkar zata fasa ihu. Dan shima maganin bawai tana ?aunarsa bane ba. amma dai yafi mata sau?i-sau?i akan allura.
Goran ta mi?a masa, ya amsa tare da ran?wafowa ya kama bargon ya rufa mata a jikinta yana magana kamar baya so. "Kwanta". Bata musaba ta zame ta kwanta tare da lumshe idanunta masu cikar gashin gira dana ido.
Tasowa richard daya gama gulma a waya yayi yana gaisheta da jiki. Batare data bu?e idanunba ta amsa masa sama-sama alamar barcine mai nauyi ke fisgar idanunta.

Jin motsi a bayansu yasa duk suka juya. Momy ce ta fito akan ko zasu bu?aci wani abu. Kai Yoohan ya risinar, cike da girmamawa yace, "Aunty mu bara muje, insha ALLAH barcin da zatayi yanzu zai taimaka mata zazza?in kuma zai sauka, shima sanyin zata bar ji".
Fuskar Momy da fara'a tace, "To Alhmdllh Son, mun gode sosai".
Kansa kawai ya jinjina mata sukai mata sallama suka fice tare da Omar dake zaune a ?ofar corridor ?in Abban yana jiransu dama. Su aunty Hibbah duk sun shige kwanciya saboda gajiya. Hakan yasa suka fice abinsu babu wata gargada

Tunda suka bar gidan bakin Richard ya kasa yin shiru wajen yaba ?yawun Aymah, da tambayar Yoohan ya akai ya samota? Bayan yasan hausawan nan basa son bama kowa ?a?ansu sai yarensu kawai. Tun Yoohan na sharesa harya gaji ya ?auki Bluetooth ya ma?ala a duka kunnensa alamar baya bukatar cigaba da jin surutun na Rich. Kai tsaye Hotel ?in suka koma. Inda a canma Rich yay zaman bama su Joseph labarin matar ta Yoohan, sai dai a cewarsa ?ar karamar yarinya ce.
Ko sau ?aya Yoohan bai saka musu baki ba, gefe ma ya koma yasa aka kawo masa coffee dan su Godwin sun cika wajen da warin giyar da suka sha harda sigari. Dan dai ita sigarin ana mata shan gayune kara ?aya ko biyu shikenan. Giyar ce dai aka maida ruwa??.

WASHE GARI

Washe gari da safe company ?in da aka bama kwangilar kayan Nu'aymah suka isa gidansu Yoohan bisa address ?in da aka basu. Wannan al'amari ya bama dangin Yoohan mamaki, dan su dai basu saba ganin hakaba. A saninsu miji shike kayan gida. Amma sai gashi su an kawo musu. Da alama kuma babban company ne.
Kiran baba malam. Yoohan yayi yana ro?onsa akan basai sun saka komai ba, shi zaiyi komai insha ALLAH. Amma sai baba malan ya nuna masa sam bazai yuwuba. Mu hausa fulani hakan al'adarmu ce, yayi ha?uri ya barmu muyi. Yanajin nauyin baba malam da kimarsa. Shiyyasa dole ya bari aka kwashe kujerun falonsa da kayan gadon dake a ?ayan ?akin, harma dana karamin falonsa na hutawa da sai ya bushi iska yake shigarsa duk suka fidda. A wani sashe na cikin gidan aka maida kayan, su kuma suka shiga aikinsu cike da ?warewa. Kayane ?an ubansu masu shegen tsada. Dan sai dama suka bama Yoohan ?in za?in wa?anda yake so ta hanyar pictures sannan suka koma company suka ?akko akazo aka shiga hadawa.
Zuwa lokacin kuma gidan nasu ya fara ?aukar ba?i na nesa. Dan sosai Papa da su Gebrail sukai gayya, hakama su Richard sun bala'i-bala'in gayyato abokansu kamar hauka. Harda na ?asashen ?etare. Shi angonma baisani ba, iya wa?anda kawai ya gayyata ne yasan da zuwansu.

Anan gidansu Abdallah ma ragal Aymah ta tashi, sai dai rashin ?warin jiki da ?ar fargabar tunanin wanda ya kasance mijin nata. duk da ranta yafi bata Yah Ab, ganin an kawota gidansu ne na nan abuja.
Gari na fara haske Aunty hibbah ta fara mata gyaran jiki na musamman, hakan yasa bataga idanun su Adawiya ba. Koma nace Adawiya kawai dan su Yusrah da Amal suna nane da ita.
Ji tai duk kewar su Umm ta gallabeta, ta amshi wayar Yusrah tai kiran baba malam, ALLAH yasa lokacin yana gida bai fita ba. Shima yaji da?in jin muryarta, dan Abba ya sanar masa jiya tayi zazza?i sai da Yoohan yazo ya dubata. Sai dai kuka data saka masa ne ya sashi fara mata fa?a, daga ?arshe kuma yay mata nasiha mai ha?e da lallashi. Yace bazai bama Umm wayarba sai idan ya kirata anjima yaji bata kukan. daga haka ya yanke kiran itama ta ajiye tana sharar ?wallan da har yanzu sun ?i tsayawa. Sosai Yusrah da Amal ke tausayinta. Shiyyasa duk sai suka zama shiru-shiru suma.

________¡ï¡ï¡ï¡ï________

Kasancewar su dai basusan da zaman dinner ?in da gidansu Yoohan ke shiryawaba ?arfe hu?u suka shirin mi?a amarya ?akinta. Dan jirgin 8pm zasubi ya maidasu kano. Anayin sallar la'asar kuwa aunty Aysha ta tsaya akan Aymah sai da taga ta shirya tsaf cikin lifaya fara da kwalliyar golden. Tai mata ?ar kwalliya duk da ta nuna bataso. Kowa ya ganta sai ya ambaci masha ALLAH, ga uban ?amshi da take zubawa kamar gidan turaren (miss xoxo??lol).
Kamar yanda tsarin yake ga duk amaryar da za'a mi?a gidan miji a gidansu haka itama akai mata. Dan kuwa Abba ne yay mata rakkiya gidan aurenta sai su Momy dasu Aunty Hibbah. Su Adawiya ma Abba cayay bazasu je ba sai gobe idan ALLAH ya kaimu dan bandasu za'a koma kano dama. Zasu ?anyi kwana biyu a nan.

An tarbesu yanda basuyi zato da tsammani ba, ba kuma komai ya jawo hakanba sai dogon garga?in da papa da Yoohan ?in sukayi, sai kuma sauran matan su Uncle Mike suma sunsha garga?i wajen mazajen nasu. Shiyyasa suka zama gaba-gaba wajen ?an amsar amarya basu bari su mama debora sun kwafsa ba. Koba komai dangin Nu'aymah sunji ?ar nutsuwa, sai dai har cikin ransu sunji tausayinta na zama cikin wa?an nan gurguzin kahiran da idanunsu ke bu?e da wayewar karatu dana ku?i. Amma sun rigada sunyi imani da cewar UBANGIJIN daya ?addara shigowarta cikinsu, yafisu sanin alkairi da hikimar yin hakan. Sun sake mata nasiha sosai, tanata kuka dai duk da bata fahimci ina aka kawota ba.
Duk da tarin abinci da kayan sha da aka kawo musu basu ta?a komaiba, sai ma mi?ewa da sukayi da zummar tafiya bayan sun le?a ko ina na sashen nata sukaga yanda company ya tsarashi gwanin birgewa. ?an gyare-gyaren da suka ?ara mata ba wasu masu yawa baneba, shiyyasa basu jasu lokaci ba.
Ganin suna shirin tafiya kamar yanda Abba daya fita tuni suna tare da papa a harabar gidan papa yace ya zasu tafi bayan ana shirin yin taro suma anan.
Murmushi Abba yayi, yace, "Ai su anjima ka?anma zasu koma kano, muna musu fatan alkairi dai". Yoohan da duk ke saurarensu yay saurin cewa, "Uncle Please ka barsu, na maka al?awarin insha ALLAH zasu sami jirgin safe saisu wuce. Itama zata damu idan taga babu family nata a wajen".
?an jimmm Abbah yayi yana nazari, yasan gaskiya Yoohan ?in ya fa?a, duk da dai su ba ?abi'arsu bace yin wannan bidi'oin, to amma a yanzu basu da iko akan Aymah tunda sun kawota gidan mijinta. Basu da ikon kuma cewa su Yoohan bazasuyi nasu shagalinba tunda shi aure rahama ne, yin shagali a cikinsa kuma ba aibu bane. Abinda kawai ba'a bukata wuce gona da iri da yin almabazaranci da dukiya. (Wadda a yanzu hakan ne yafi yawa a bukukuwanmu. shiyyasa tun a filin bidi'oin ake zazzage daraja da albarkar auren atafi da gayyar she?anu??????).
Kansa ya ?an jinjina da fa?in, "Tom shikenan. Amma bara na fara kiran Yaya (baba malam) na sanar masa tukunna". Wannan ?abi'ar tasu na birge Yoohan matu?a.
Bayan Abbah daya koma gefe ya gama waya da Baba malam ya dawo yana fa?in, "Shikenan zasu zauna ?in, amma yanzu su fito muje idan lokacin yayi sai a kaisu can. Idan mun koma sai ?an uwanta suzo su tayata zama su yanzun".
"Muna godiya Uncle, ALLAH ya ?ara girma".
Murmushi kawai Abbah yayi, hakama Papa fuskarsa kamar gonar auduga.

¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï

Tun bayan magriba mai kwalliya tazo yima Aymah. Amma saita tubure akan sai tayi sallar isha'i. Dole aka ha?ura akan hakan, duk da su ?an bikima harsun fara wucewa inda za'a gudanar da shagalin. Duk yanda taso su Amal su sanar mata wanene mijin sun?i. Dan Amal da Yusrah da wasu ?awayen Amal ?in biyu ma?waftansu suna nan tare da ita. Adawiya kam batazo ba wai kanta ke ciwo tasha magani sai anjima zata biyo su Aunty hibbah. Hakan bai wani damu Aymah ba, dan ita mantawa take ma da babin wata Adawiya yanzun.
Bayan an idar da sallar isha'i aka ranga?ama amarya Nu'aymah kwalliyar garari. Dan ko makaho ya ta?a saiya jinjina. Hakama su Amal an musu tasu. Momy daketa danne zuciyarta bisa shawarar ?awartace da kanta ta kawoma Aymah rigar da zata saka wadda garariya garara har ?asan amuruka akaje sayota daga aljihun papa da umarninsa.
Nu'aymah taso yin gaddamar sakawa. Amma yanda Momyn ke mata da lallashi ita da ?awarta ya sakata amsa ta saka ganin rigar akwai hannu a jiki. Ammafa ta bala'i-bala'in ha?uwa sai ?aukar ido takeyi. Farace tas sai kwalliyar furanni pitch color data ?awata rigar. Hakan yasa dogon takalminta da shi kansa abin kallone ya kasance pitch. Sar?a ?ankwali duk pitch. Humm lamarinfa ba'a cewa komai. Ita da kanta Aymah tasan ta ha?u, sai dai zuciyarta a raunane take, dan ta tabbatar ba Yah Ab ?inta bane angonta. Musamman data san danginta basa irin wannan shirmen bidi'ar, kuma tasan ba Yah Naser bane shima, dan da ace shine katsina za'a kaita. 'Ni Zainab wanene iyayena suka bama ni' ta fa?a cikin zuciyarta tana kukan zuci, a fili kuwa idanunta sun cika da ?walla. Tayi jarumta sosai wajen ganin basu zubo ba.

Tare suka tafi dasu madam Chioma a mota ?aya, dan shi ango yana acan hotel ?in da za'ayi dinner ?in, acan suke zaune da abokansa da ba?i da shi kansa wasu ma baisan da zuwan nasuba sai da sukazo ?in. Dan ba ?aramar gayya su Rich suka yo ba. Harda abokansu tunna secondary skull.
Lallai biki yayi biki kam, dan tun a ganin zu?a-zu?an motocin dake cike da harabar hotel ?in har waje zaka san eh lallai manya ne ke lokacinsu. Ga ?an jarida da ?an sanda a wajen harda soji.
Momy da ?awarta ne kawai suka fita. Aymah kam zata jira angonta. Su Yusrah ma dake motar bayansu duk sun fito suna tsaye. Ba'a rufa mintuna biyarba sai ga Doctor Yoohan mai zamani ya fito tare da gayyar abokansa. Tab, lallai kam ita ranar aure ta musamman ce ga kowa. Duk da shigar suit ?abi'arsa ce sai yau tafi ta kullum. A kallo ?aya zaka gane cewa ku?a?e masu nauyi aka zuba wajen sayen kayan. Fararene tas shima sai shirt ?in ciki ce ka?ai ta kasance pitch. Gashin kan nan nasa da saje sunsha gyara sai wal?iya da ?aukar idanu sukeyi. Duk da fuskar babu murmushi a sake take bai ?aure ta ba. Hakan ya saka ?yawunsa sake fita da ?yau, ga wani irin kwarjini na angwanci dana ruwan alwala daya fara bin ?ofofin gashinsa na ?awainiya da shi. Duk da ?yawun da abokansa sukayi suma duk sai ya damasu ya shanye saboda darajar hasken musilinci.
Solomon yay saurin bu?e masa motar da Aymah ke a ciki zaune tanata ha?iyar zuciya. Baice komai ba sai matsawa da yayi jikin motar. Ya ?an ran?wafa ka?an yanda zai iya ganinta da ?yau. A tare hancinansu suka sha?ar musu ?amshin turaren juna. Kowanne zuciyarsa ta harba ka?an, musamman ma Yoohan da ?yawun da Aymah tayi ya nema zarar da shi a tsaye. Amma a fili sai ya fuske abinsa ya mi?a mata tattausan tafin hannunsa, cikin harshensa da baya fita da ?yau yace, "Bismillah".
Wani irin harbawa da ?arfi ?irjin Nu'aymah yayi a karo na biyu, duk da kuwa dama ta tsargu tun jin ?amshin turarensa. Amma sai bata kawoma ranta shi?inne ba..... Kafin ta fahimci ru?anin da take neman afkawa taji ya sa?ala hannun nasa cikin nata.
Da sauri taja zata fisge jikinta na wani irin tsuma. Ri?esa yayi da ?yau tare da matso fuskarsa gab da tata. A cikin kunnenta yace, "Wlhy kina min tsiwankin nan sai wannan ya shiga jikinki, garama ki nutsu mubar wajen nan lafiya". Yay maganar yana nuna mata syringe da batasan daga ina ya cirosa ba.
'Innalillahi....' Aymah kawai ke iya maimaitawa a cikin zuciyarta. Kanta ya sake shigewa a ru?ani har batasan lokacin daya fiddota waje ba, ta dai ganta akan ?afafuntane kawai dake sanye da dogon takalmi. Sau?inta ma ta iya tafiya dasu dama can, amma da ansha kunya yau.
Gaba ?aya ta zame masa mutum-mutumi, binsa kawai take duk yanda ya juyata. ?an jarida da abokansa da duk suka rikice sai zuba musu hotuna suke tako ina. Hasken camaras kawai kake gani babu ?a??autawa.
Duk da a cikin abokansa wasu na ganin Nu'aymah tayi kan?anta hakan bai hanasu taya abokin nasu murna ba da mamakin inda ya samo wannan ?ar shilar. Yoohan dai ya fuske abinsa,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login