Showing 288001 words to 291000 words out of 325075 words

Chapter 97 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29135

ta girgiza ta koma ciki, inda ta iske Aymah ta fito daga toilet da alama fitsari tayo. Cike da kulawa tace, "Kinji mijin naki ya tafi wai zai dawo da safe. Dama kunyi dashi hakan?".
"A'a wlhy Umm, ni kawai yace na shigo zaije massallaci ne". Tai maganar cikin ?ata fuska. Murmushi kawai Umm tayi ita dai, tace, "To kiyi wanka kawai sai na samo miki abinda zakici ke tunda shi ya gudu. Cike da kunyar Umm ?in data aro ta yafama kanta ta amsa da to. Daga haka ta koma toilet ?in danyin wanka.

Babu wanda Umm ta sanarma da zuwan Nu'aymah a gidan sai hajjo. Sai ko Muhammad daya dawo massalaci ya ganta a bazata. Baba malam ma sai da ya sallami ?alibansa ya shigo yaci karo da ita a falo zaune ita da Hajjo da Umm da Muhammad dake li?e da ita.
Tuni Nu'aymah ta manta da kunya, ta mi?e da sassarfa ta nufi Abbanta dake kallonta cike da kewa da so da ?aunarta. Gabanta tai niyyar dur?usawa ya ri?ota yana fa?in, "A'a mamana keda ke fama da kanki. Irin wannan zuwa haka na bazata".
Hannunta yaja ya maida a kujera sannan shima ya zauna. Kanta a ?asa ta shiga gaisheshi cike da kewa. Shiko yana amsawa da kulawa. Abakin Umm yaji cewar Yoohan ya gudu. Dariya kawai yayi dan ya fahimci kunya Yoohan ?in keji da alama.
Haka sukayi murnarsu su hu?u kawai. Ganin dare ya farayi Hajjo taje sashenta danta kwanta. Aymah kuwa a ?akin Umm zata kwana tare da Umm ?inta data bar baba malam shi ka?ai.
Aiko maimakon barci sai suka bu?e sabon babin hira ita da Umm ?in, sai da suka kusan kai asuba sannan barcin ya kwashi Aymah, daga nan itama Umm tayi.

__________¡ï

Washe gari kam a bazata kowa yaga Nu'aymah a gidan. Kafin kace mi sun rikice da murna da hayaniya. Tun Aymah na ?unshe-?unshen ciki harta saki jikinta ta shige cikin ?an uwanta anashan shafta. Zuwa tashin hantsi kuwa sai ga Hajarah tazo gidan, dan ita dama tasan da zuwan nata. Rungume juna sukai cike da farin ciki. Yanda suka nuna ?in har mamaki ya bama kowa. Dan gaba ?aya salon sha?uwar Adawiya da Nu'aymah ne ya koma kan Hajarah a yanzu.

A ranar da yamma suma ?an Abuja suka iso. Ganin Nu'aymah kuma ya matu?ar basu mamaki dansu da suke Abujan ko a labari basusan da zuwan nataba. Har Momy ma sai da ta kasa ha?uri tai complain ?in cewar Yoohan bai ?yautaba. Suna matsayin iyayen Nu'aymah amma yazo da ita har Abuja bai fara kaita canba sai dai suzo su ganta anan tsulum.
Daga karshe dai Yoohan ?inne da yazo gidan ya kare kansa akan wannan tuhuma. Dan Aymah bata iya cewa komaiba tunda itama tunanin zuwa can ?in baizo mataba. Zumu?inta kawai azo kano.
Ya bama su baba malam ha?uri akan rashin tsayawarsa jiya. Acewarsa aikin gaggawa ne ya samesa shiyyasa bai tsayaba. Duk sun masa uziri akan haka. Sannan suka ?ora da godiya akan hidimarsa ga gidan marayunsu daketa ?ara nunkuwa a koda yaushe. Akan bikin nanma kawai da za'ai ba ?aramin hidima yayiba.

Washe gari ba?i suka fara cika gidan, ?an katsina, ?an lagos da sauransu, kowa kuwa yana sake yaba yanda Aymah ta ?ara girma da canjawa a cikin shekara ?aya kacal. Gashi daga gani ansan ta samu lafiya yanzu. Sai dai fatan ALLAH ya sa ta sauka lafiya kuma.
Da yamma sukaje can orphanage akai walima, anan ta ha?u da sauran yayunta su Kubrah. Tayi mamakin ganin yanda Aunty Kubrah ?in dukta lalace. Harta kasa ha?uri ta tambayi aunty Hajarah.
Cike da damuwa Hajarah tace, "Humm Aymah ke dai ALLAH ya ?yauta, zaman natane babu da?i daga ita har mijin da kishiyar. Kwanaki ai kusan watanta biyu a Lagos wajen Abbah Musbahu. Sunyi fa?a ya daketa shine taje can".
Kasa magana aymah tayi saboda damuwa. Kodai babu komai Kubrah ?ar uwartace duk da a yauma ta nuna har yanzu ba sonta takeba.
Duk wannan hidima da akeyi kuwa su Aymah zagaye suke da yaran Jay ta ko ina. Motsin kowa akan idonsu yake faruwa. Tun daga orphanage har cikin gidansu.

Washe gari juma'a aka ?aura auren amare ashirin da takwas maza da mata. Kowa ya kalli su baba malam yasan suna cikin farin ciki. Sai dai ai fatan ALLAH ya basu ladan hidimarsu ga marayun ALLAH babu gajiyawa.
An mi?a amare ?akunansu, daga haka ba?i suka fara raguwa sai na jiki kawai aka bari. Kamar yanda Jay ya samu tattaunawa da baba malam a ranar ?aurin aure a yau suka yanke hukunci bisa shirinsu. Duk da kuwa da ?yar baba malam ?in ya yarda da bu?atar Yoohan, Jay, Omar ?in. Dan basu ?oye masa komaiba game da shirin nasu gudun kar a samu matsala.
Tun a yammacin ranar baba malam ya fara takalar Umm da batun mallakama Nu'aymah wasu kaddarorinsa dan yasan lallai mai musu la?e na tare da su saboda tuna Nu'aymah tazo garin ya fahimci mai la?en ya ?ara ?aimi wajen yimusu. Ta riga tasan shirinsu, itama sai ta biye masa. Sai dai zancen bai tsahoba suka barshi akan zasu ?arasa da safe dan lokaci baba malam nada uziri..........?


ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????

Mamu gee??
MIN ?ALB!!????

Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????

Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????

Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????

?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.
[7/6, 6:56 AM] +234 901 860 0202: *_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.


No. 73

.............A yau kam su Nu'aymah da duk wanda yasan da wannan shirin sun tashi a shirye tsaf bisa ya?inin tarkon da suka ?ana ya ?anu. Kasancewar sanyi da akeyi duk sauran jama'ar gidan da ?an biki suna can a sassan gidan a ma?ale, duk da madai ?an bikin da suka rage duk na jikine babu bare. Babu kowa a tsakar gidan sai yaran Jay dake ?o??oye.
Yau kam Jay ya shiga har falon baba malam tare da lauyan malam mahaifin su baba malam a zuwan zasu tattauna akan kaddaririn baba malam ?in. Acan kuma ta waje little bee ce da wasu jami'a a harabar gidan a mabanbanta wajaje duk da Jay yasan akwai camaras ?in da Afrah ta saka masa a wancan zaman. Yafi bu?atar gani ga ido ga kowa kafin ya banka?a sirrikan dake a cctv ?in. An kira Aymah da Yoohan falon, sai su Abban Abdallah da hajjo data san komai itama. Sai Omar da yazo matsayin lauyan Nu'aymah shima.
Bayan bu?e taro da addu'a baba malam ya fara da nasiha a garesu duk dai a cikin salon tarkonsu, dan a zahiri fa babu wani maganar mallakama Nu'aymah kaddarorinsa da yakeyi. Shirine kawai irin nasu Jay.
A gefe kuwa idanun su Yoohan gaba ?aya na'a Windows ?in falon a kaikaice. Baba malam kuwa na cikin nasiha sai ga abinda suke jira ya bayyana. Kallon juna sukai shi da Jay dasu Yoohan sukayi murmushi. Daga haka ya cigaba da bayaninsa hankali kwance.

Acan waje kuwa su Little bee na mamma?ale a ma?oyarsu sai ga mutum sanye cikin dogon hijjab har ?asa da ni?ab ya fito daga tacan bayan gidan yanda babu mai iya fahimtar daga ainahin sashen da aka fito. Basu da tabbacin mace ce ko namiji, dan komai an rufe ba'a gani.
A yanda mai la?e ke tafiya da dabaru zaka san cewar lallai an ?ware, sannan aikine da akeyi tunba yanzuba. Cikin salon iya aiki Little bee taima abokan aikinta wani salo da yatsun hannunsa suka bada ?ass!! Sau ?aya. A take duk suka ?ara shiryawa dan suma dai suna biye da mai la?e akan idanunsu.
Sai da suka tabbatar mai la?e ya isa dai-dai sashen Malam marigayi alamar dai ?an gidanne, tunda har ansan a ina su baba malam zasuyu taron nasu aiko sai wanda yasan gidan. Kamar yanda mai la?e ya saba a koda yaushe ya isa jikin Window. Wani siririn abu ya sa?a a tsakanin glasess ?in Window ?in da alama na ?aukar magana ne. Dan yana gama turashi ya kai hannu ya ta?a kunnensa alamar tabbatar da daidaitar komai. ?aramin tsaki akaja jin Nasihar da baba malam ya fara dan ba ita ake bu?ataba a yanzu. Jin baba malam zai fara jawabinsa mai la?e ya ?ara nutsuwa da maida hankalinsa ga window ?in domin saurare..
Da wannan damar su Little bee sukasamu isowa wajen cike da ?warewar aiki suka toshe gaba da baya na ?an siririn lungun bayan ?akin malam marigayi. ?arar sa?on daya shigo wayar Little bee daga Jay ne ya fargar da mai la?e ya juyo da sauri. Sai kawai ganinsa yayi zagaye da mutanen da baisan ta ina suka ?ullo ba.
Tashin hankali ba'a saka maka rana. Wannan shine ?oyayyar kalma a zuciya da bakin mai la?e duk da bai fito ya furta manaba a zahiri. Dan kuwa dai gabas da yamma kudu da arewa babu wajen guduwa. Katanga a bangon gabas. Ginin sashen malam a bangon yamma. Little bee da jami'ai uku a bangon kudu duk sun nunasa/ta da bindiga. Dawood da jami'ai uku shima a bangon arewa duk sun nunata/sa da bindiga nanma.
Wannan itace kwana casa'in da tara ta barawo ?aya tak ta mai kaya. Little bee ta ciwo wayarta da hannu ?aya a aljihu ?ayan kuma ri?e da bindigar data nuna mai la?e. Kiran Jay tayi a waya. Yana ?agawa tace, "Sir! Aikinmu ya kammala zaku iya fitowa".
"Woow!" Jay ya fa?a yana mi?ewa idonsa akan su baba Malam. Takawa yay jikin windown da yake hango inuwoyinsu ya zuge gilas ?in tare da net. Abinda mai la?e ya sa?ala ya fa?o. du?awa yay ya ?auka yana jujjuya shi a hannunsa kafin ya kalli su baba malam da suma duk shi suke kallo.
"Malam zama ya ?are ai, suspect ?inmu yazo hannu zamu iya zagayawa".
Harga ALLAH sai da gaban baba malam da Umm ya fa?i. Hakama Aymah duk sai taji tsoro kuma. Su Abba Musbahu da basusan mi akeyiba suka shiga kallonsu da tuhuma. Ko a jikin Yoohan da Umar. Dan sunema farkon ficewa a falon.
Baba malam dake kallon su Abban Abdallah yace, "Kuyi ha?uri wannan itace kawai mafita a garemu gudun kar wataran a kai ga rasa rai bisa makircin da bamusan wake ?ullasa ba". Daga haka yay gaba ya barsu da kallon kallo ma juna sai dai ganin kowa ya fice suma sukabi bayansu jiki a sabule.
Ganin duk sun iso Little bee ta dakama mai la?e tsawa da fa?in, "Cire Ni?af". Ko motsi ba'ayiba. Sai dai yanayin tsayuwar ya tabbatar da koma wanene a tsorace yake kuma cikin ?ololuwar tashin hankali da firgici.
"Inada cikaken dama nayin harbi, hakan na nufin bullet ?in zasu iya fita a cikin bindigarnan zuwa jikinki/jikinka a koda yaushe. Zan irga iku kawai bisa lasisin dama a gareki ko a gareka. *_?aya! Biyu! Uku!!"_* ta fita daga bakin Little bee tare da bullet ?inta zuwa ?afar mai la?e da ko motsi baiyiba balle ya nuna kota nuna zata cire nikab din da aka bada umarni.
A take ?arar muryar mace ta kara?e gidan saboda azaba shigar bullet. ?asa ta dur?ushe jiki na rawa. Da wannan damar Little bee ta ?arasa gareta tasa hannu ta fisge ni?ab ?in ta jefar gefe. Baba malam da Umm da sauri suka kauda kawunansu gefe da tsananin fargabar tsoron ganin koma wanene. Sai da Nu'aymah ta furta,
"Illalillahi wa'inna ilaihirraji'un Addah!! Kece dama?!!!".
Sannan su Umm suka juyo a firgice. A take wajen gaba ?aya ya ?auki salati. Dan duk jama'ar gidan kururuwar ihun Addah da Little bee ta harba dama duk ya fito dasu a hautsine.
Cikin girgiza kai hawaye na sakkoma Umm a guje tace, "Inaa bazai yuwuba. Addah ki sanar musu ba abinda suke zargi bane ya kawoki nan. Dan ALLAH ki tabbatar musu domin bamu kariya kema kika zo nan. Ki tabbatar musu bake bace kike la?en nan dama can dan ALLAH, kicemin yau kika farayi......"
"Bata da bakin baki wa?an nan amsoshin domin wanke kanta Umm-Muhammad. Domin kuwa duk sa?aninsu da baki eson ji daga bakinta sune gaskiyar amsoshin naki da ma kowa dake anan wajen".
Bily dake kusa da Jay tsaye ta bama Umm amsa kanta tsaye.
"Karkice dani haka Maman Awwab. Dan ALLAH karkice haka. Wannanfa Fauza ce, wadda muka tashi tare tun ?uruciya tamkar uwa ?aya uba ?aya ta haifomu. Ban ta?a ?oye mata sirrinaba, itama bata ta?a ?oyemin nata ba. Tare muke raba farin ciki, sannan mu raba kuka tare idan ya samemu....."
Murmushi Bily tayi da takawa a hankali zuwa gaban Addah daketa faman magowar azabar ?afarta dake zubda jini. Ta nunata tana mai kallon Umm ?in, "Tabbas a zahiri haka take a gareki Umm-Muhammad. Amma a ba?ini itace babbar ma?iyyarku. Idan kuna bu?atar tabbatarwa mu a shirye muke wajen nuna shaidar gani da ido a gareku dan duk mun tanajesu dama". Ta ?are maganar tana duban su baba malam da alamu ya nuna tamkar duk sunyi sumar tsaye ne har yaran Addah da duk suma suna a wajen.
Daga haka Jay ya bama Yoohan da Omar damar cire bullet ?in jikin Addah. Cike da ?acin murya Yoohan ya dubi Jay ?in idanunsa jazur. "Uncle ka gafarceni, hannuna bazai ta?a iya aikata jin?ai ga maci amana ba". Daga haka ya kama hannun Nu'aymah da jikinta ke karkarwa suka bar wajen.
Murmushi kawai Jay yayi. Baba malam zaiyi magana Jay yace, "Karka takura masa Malam. Umar Please ka cire mata sai mu wuce da ita. Malam sai ku samemu a statlon ?inmu nan kano mu ?arasa maganar".
Da sauri baba malam yace, "A'a Jawaad ina neman alfarma komi zai faru muyisa anan cikin gidan domin rufin asirinmu, wannan itace alfarmar da zan nema a gareku".
?an jimm Jay yayi, sai kuma ya ka?a kansa alamar kar?awar alfarmar baba malam ?in.
Badan Umar yaso ba ya amince zai cire. Dan haka aka ?akko Adda daga lungun zuwa sashen Malam. Gaba ?aya yaran sa'an su Muhammad zuwa kansu Adawiya ba'a barsu sun shigaba. Duk da kuka da Adawiya keyi iyakar ?arfinta wanda babu wanda yasan dalilinsa. Su Hajarah da sauran yayunta na ma'auri duk suna gidajensu basusan abinda akeyiba. Sai malam ?arami kawai da sauran ?annensu. Shiko gaba ?aya da alama ma jinsa da ganinsa sun gushe dan bai iya motsawa a lungunba har kowa ya fice. Hakama Abba Mustapha saida Hajjo ta kama hannunsa da kanta saboda tsabar firgici.

¡ï¡ï¡ï

Bayan azabar cire bullet da Addah ta gama sha Omar yay mata allurar rage ra?a?i. Umm dake kuka har yanzu ta sake duban Addah. "Fauza dan ALLAH ina ro?onki a karo na ?arshe ki ?aryata tuhumar da ake miki. Ki tabbatar musu da kawai yau ?addara ta kawoki amma ba ke bace. Har abada bana fatan kunnuwana da zuciyata suji sa?anin tunaninsu a kanki Fauza......."
Shiru Addah batai ko motsiba, kanta a ?asa kuma ta?i kallon kowa. Gyaran murya Jawaad yayi da gyara zama. "Hajiya karki wahal damu anan, dan alfarma ki ke ci, badan darajar malam ba da zamu wuce dake station ne ki mana bayani ta duk hanyar da mukaso bi da ke. Kar kiyi tunanin ?oye mana komai dan a tafin hanunmu kike, duk wanda ke cikin labarinki sai da na gurfanar da shi a gabana kafin ki ganni anan, na za?i bin komai mataki-mataki ne saboda sau?a?a firgici a zuciyar wa?anda kikema cin dunduniya. Nasan kinsan Hamisu ai gashi a gabanki tsaye".
Da sauri Addah ta ?ago ta kalli inda Jay ke nuna mata. Kallon ido cikin ido sukaima juna kuwa ita da Hamisu. ya ko zuba mata mummunan kallo. Da sauri maida kallonta ga Jay. Kai shima ya jinjina mata fuska a ?aure. "Bayan Hamisu akwai ?arki Kubrah ko, sannan akwai......"
Da sauri ta ?aga masa hannu, sai kuma ta fara tari, gefen ?an kwalinta tasa ta tare bakinta sai ga jini na zuba. Babu wanda bai mata kallon tsoro da firgici ba a


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login