Showing 75001 words to 78000 words out of 325075 words
yasa Mom saurin tashi tsaye har tana neman fa?uwa, da yarensu tace, "Ina zaka kuma yaro na? Kaga zo na shafa maka man ma da kaina idan bazaka iya b....."
Kafin takai ?arshen maganarta harya maida ?ifar bayin ya rufe, jingina yay a jikinta ya lumshe idanu zuciyarsa na ?ara ?arfin bugu. Duk da yanda take buga ?ofar a hankali tana kiran sunansa bai motsa ba, sai ma wani haushi dake sake ziyartarsa. Sam bayason wannan halin da Mom take masa, a ganinsa bai daceba, yakamata tasan da ba yanzu bane, yanzu fa ya girma, shekararsa talatin har da biyu a duniya, miyasa bazata daina masa kallo kamar ?an shekara goma ko ?asa da hakaba?. bawai yana saka abinda take masan a wani mizani daban bane, dan yasan soyayyar da suke masa mai yawa ita da papa ne ya jawo hakan, amma ya kamata ta fahimci yanzu ya wuce ta dinga masa wasu abubuwan kanta tsaye ai......
A hankali ya bu?e kumburarrun idanunsa dake cike da barcin da baisan ranar yinsaba, ya sake lumshesu yana sauraren yanda Papa ke lalla?a Mom akan su fita su bashi waje ya shirya, idan yaso saisu dawo daga baya.
Badan madam Chioma taso hakanba ta yarda suka fita ?in ranta na mata ?una.
Yoohan najin sun fita shima ya fito, dan dama a gajiye yake da tsayuwar saboda ?afarsa wani bala'in zogi take masa. Sai da ya le?o ya tabbatar babu kowa sannan ya fito. Bai kalli ko inda Mirror ?insa yake ba balle ai tunanin shafa mai ya nufi wajen kayansa kawai. Dogon wando ash mai taushi da farar t-shirt data kama jikinsa ya saka. Ya taka zuwa gaban gadon yana cije baki, zama yay yana mai kallon ?afarsa data ?an kumbura dai-dai idon sawu. Hannu yasa ya ta?a wajen yana yamutsa fuska, duk da zafin da yaji haka ya daure ya kama ?afar yaja da ?arfi. Siririyar ?arar azaba ya saki tare da sakin ?afar itama.
Har rige-rigen shigowa ake tsakanin papa da Mom da Richard da yazo gidan yanzu babu jimawa. Sai Solomon da Miracle dake ?o?arin shigowa falon suma Joy biye dasu tare da masu aiki dake ?auke da abincin Yoohan ?in.
Yanda sukagansa a kan gadon ya saka hankalinsu sake tashi, suka zagayesa da tambayoyin yaya akai?. Duk da surutun nasu haushi yake sake bashi sai ya tashi zaune, ganin Rich tare da su ya sakashi mi?a masa ?afarsa. Kallon ?afar Richard yayi da ?yau, kafin ya jawo stool ?in mirror ya zauna yana tambayarsa garin yaya yaji ciwon?.
Bai tanka masa ba, dan haka Rich ?in ya kama ?afar kawai ya hau ja masa. "Jesus!!!" ya fa?a da muryar nan tasa mai amo data ha?u da damuwa a yanzun. Saurin zama Momy tai a kusa da shi ta amshe filon daya dam?e ta maye gurbin filon. Caraf kuwa ya kama hannunta ya dam?e cikin nasa da masifar ?arfi, dan har sai da ta saki ?ara itama.
Yanda jikinsa ke rawa zufa na fito masa sai duk tausayinsa ya sake kamasu, Miracle tai saurin zama ?aya gefensa tare da kwanciya a jikinsa tana hawaye. Sai da Rich ya tabbatar ?afar tayi yanda ya kamata sannan ya barsa. Sai faman jera masa sorry sukeyi.
Duk da yaji mutum kwance a jikinsa bai motsaba sai da zafin ?afar ya daina sosai, a lokacin ?amshin turaren Miracle dana Momy suka tabbatar masa sune nanu?e da shi. A hankali yasa hannu ya ?aga Miracle dake lafe a jikin nasa, kafin itama Mom da tunda ta farga da Mira take zuba mata wani kallon ?asan ido na garga?i, shi dai ya zare hannunsa daga cikin nata, jan jikinsa yay baya ya haye gadon sosai batare da yace uffanba duk da sannun da suketa faman yimasa har yanzun.
Cike da kulawa Rich ya basu shawarar ya kamata su fita abar Yoohan ?in ya huta, dan ya kula da yanda Yoohan ya sake cika tamkar zai fashe, hakan kuma yanada nasaba da zamansu a ?akin, dan shi ?in shaidane akan yanda Yoohan yay mugun tsanar jin kowanne kalar motsi a kusa da shi idan har yana cikin wannan yanayin.
Papa da ya gamsu da shawarar Rich ?in sai ya tarkatasu suka fice duk da uwar gayyar Mom bataso hakanba ita. Bin bayansu Richard yay shima dan yana bu?atar ?akko wani abun da yake son gwadawa Yoohan ?in ko zai aminta wannan karon yasha.
Yoohan na zaune yanda suka barshi idanu a lumshe Richard ya dawo ?auke da ?aramin tray mai ?yau. Duk da Yoohan na jinsa bai bu?e idanu ba balle ya motsa, Rich ya jawo ?aramin table glass dake gaban sofa zuwa gaba gadon. Trayn dake ?auke da kwalbar barasa da kofuna biyu, sai ?an?ara a wani bowl ya ?aura a kai yana kallon Yoohan ?in. "Mr-x!". Ya fa?a yana ?o?arin bu?e kwalbar barasan.
Bu?e idanu Yoohan yayi a hankali batare da ya amsama Rich ?inba. Rich ya ?an murmusa, dan bai damu da rashin amsawarba, barasan ya zuba rabin kofi, ya ?iba ?an?ara ya zuba a ciki yana murmushi. ?agowa yay ya mi?ama Yoohan dake kallonsa ta ?asan ido kofin.
?auke kai Yoohan yayi fuskarsa na nuna ?arin ?acin rai, dan yasan Rich ?in yafi kowa sanin shi baya shan giya...........
"X-Man! inhar bazaka yarda na maka allurar da zata taimakeka kayi barci ba to ka daure kasha wannan, na tabbatar ita zata saka ka barcin koda na awa ?aya ne. Kai fa likitane, kasan illar wannan matsalar da yanda take maida rayuwar mai fuskantarta a ?arshe. Idan kana tunanin ?in shan giya ne dan karta shiga maka rayuwar aiki yanzu ai ba'akan aikin kake ba, sannan don neman lafiyarka ne".
Shiru kamar Yoohan bazai kulasa ba, dan har Rich ?in ya fidda tsammanin samun kulawarma. Sai ya tsinkayi sautin tsakin Yoohan ?in a hankali. Kallonsa Yoohan ?in yake cikin ido da jajayen idanunsa dake a kumbure, murya a da?ile yace, "Rich! a wajenka ya kamata mutane su ?ara sanin halina akan idan nace bazanyi abuba bazan ta?a yinsa ?inba, dan haka karka sake tunanin zansha barasa koda ba yau ba".
Yanda yay maganar cikin kaushin murya ya saka Rich saurin cemasa "I'm very sorry". Batare da Yoohan ?in ya sake cewa komai ba ya maida idanunsa ya lumshe duk da yasan barcin ba ?aukarsa zaiyi ba.
Haka suka cigaba da zama a cikin ?akin shiru, Richard da ya sha barasar da Yoohan ya?i sha har ya fara barci a gefen sa, shiko idanunsa biyu amma suna a lumshe. Lokaci-lokaci hawaye kan ziraro masa ta gefen ido. Yana sauraren yanda Momy da Papa keta faman zaryar le?owa ?akin, sai dai ?auka suke ko Rich ?in yaci nasara yasha giyar barci ya ?aukesa, shiyyasa hankakinsu ya?an kwanta suketa faman jin da?in yanda duk shigowar da sukeyi suna samun Yoohan ?inne a kwance.
Wajen misalin goma na dare Yoohan ya gaji da kwanciyar, tashi yay ya sauka daga gadon yana bin Rich dake barcinsa hankali kwance da kallo, bayi ya shiga ya watso ruwa. Bai jimaba ya fito sanye da bathrobe. a bakin gadon ya zauna tare da jingina da fuskar gadon. Ya kai hannu zai kashe fitilar gefen gadon idanunsa suka sauka akan farar envelope, cak ya tsaya yana kallon rubutun jiki, janyewa yay kamar zai share, sai kuma yasa hannu ya ?auka tare da bu?ewa ya zaro takardar dake a ciki.
Rubutun bashi da wani yawa sosai, amma a tsare yake gwanin sha'awa, sannan yanda aka tsara kalaman cikin rubutun da harshen turanci sunyi matu?ar jan hankalinsa har yana ?an lumshe ido. Sai da ya maimaita takardar sau biyu sannan ya ninketa ya maida cikin envelope ?in ya jawo drawer ya ajiyeta yana juya abinda ta ?unsa a cikin ransa.......
________________________
*_SAUDIA_*
Duk da fushi da zuciyarsa keyi ga duk zuri'ar gidan tasu hakan bai hanashin jin ?okin zuwan hajjo da Ahmad ba, dan baisan harda Nu'aymah a tafiyarba. shiri yay tsaf ya wuce airport domin tarbosu batare da ya saurari Adawiya da tace zata bishi ba, dan tana wanka ma ya si?a?e ya fice daga gidan.
Cikin sa'a kuwa yana isa airport ?in jirginsu Nu'aymah na ta?a ?asa. Lumshe idanu tayi tana karanto addu'oi da fatan cika al?awarin da taima iyayenta akan kama kanta batare da wata fitina ta ?ullo ba. Hajjo na lura da duk motsinta, amma sai batace da ita komaiba har sukabi ayarin masu fita. Sanye take cikin wando blue na jeans da farar rigar fakistan da tsahonta yake har gwiwar ta, an ma rigar ado da blue ?in duwatsu manya da ?anana, sai farin veil da ta na?a a kanta wanda ya sake fidda ?uruciyarta da ?yawun da ALLAH ya bata. Farar ?afarta da kalar wandon ya haska tana sanye cikin blue ?in takalmi da yay masifar mata ?yau dan bata da babbar ?afa sam. Sai ?aramar jakarta itama dai blue ?ince.
Kallon agogon dake ?aure a tsintsiyar hannunta tai lokacin da suke ?o?arin sakkowa daga jirgin, ta ?an yamutse fuska tana sauke hannun a hankali da kai dubanta can ?an nesa dasu. Wani irin bugawa ?irjinta yayi saboda hango Abdallah dake tsaye jikin motarsa sanye cikin ?ananun kaya da sukai masa ?yau, ya ?ara ?iba da ?warjini a idanun mai kallo kamar ba azumi ake ba. A take wata kasala ta saukar mata, tafiyarta ta sake raunana fiye da farko. Dan sai da Hajjo ta kama hannunta ta ida sauka da ita ma.
Abdallah da ya yun?uro saboda hango Ahmad dake a gabansu da yay yaja ya tsaya cak lokacin da idanunsa suka sauka akan Nu'aymah da bai zato ko tsammaanin gani ba.. Wata irin hajijiya-hajijiya ya faraji tana neman ?ibarsa a wajen, ya kasa motsi balle ?auke ido daga kallonta har suka ?araso inda yake.
Hajjo datai tamkar bataga halin da suka shiga ba ta mangare masa ?eya tana fa?in, "Kurwata kur dan gidanku". Firgigit yay da sauke nannauyan ajiyar zuciya, sai dai ya kasa ?auke idanun nasa daga kan Nu'aymah da ta ?auke kanta gefe tamkarma batasan da zamansa ba a wajen. Hannu yakai ya shafa inda Hajjo ta tallaresa kafin ya janye idanunsa da ?yar ya maida kan hajjon data wani ?ya?e fusaka tana zuba masa harara.
"Yanzu dan ALLAH daga zuwanki mina miki zaki tallemin kai?". Ya fa?a yana ?ata fuska da kallon Hajjon. Watsar dashi tai ta?i magana, saima hannun Nu'aymah data kamo suna shirin barin wajen.
Dariya Ahmad yayi, ya matsa ya rungume Abdallah, "Oh Yaya kaifa kai da Hajjo sai a slow, manta da batunta kayi tani da ?anwarmu kawai". Murmushi Abdallah yay tare da rungume Ahmad ?in shima. Kafin su saki juna kowanne fuskarsa da murmushi jin da?i. Abdallah ya sake kai dubansa ga Nu'aymah sannan ya kalli Ahmad.
Kai Ahmad ya ?an jinjina yana murmushi, amma baice komaiba sai ?yafta idanu da yayma Abdallahn. Ab ya ka?a kansa kawai da nunama Ahmad hanya alamar suje to.
Nu'aymah da Hajjo na baya, yayinda Ab da Ahmad ke gaba. Hajjo ce kawai ke magana a motar Ahmad na tayata, dan mafi yawan maganar tata duk tsiya takema Abdallah, shi kuma Ahmad ?in na karesa.
Abdallah kam rabin hankalin na'a tu?i ne rabi akan Nu'aymah da a yanzuma ta ?auke kanta tamkar bata gansa ba. A haka suka iso madaidaicin gidan nasa mai ?yau da tsari. Sai da ya faka motar inda ta dace kafin su fita shi da Ahmad, Ahmad ya bu?e na Hajjo, ya taimaka mata ta fito, Nu'aymah kuma ta bu?e da kanta ta fito tana kallon gidan dama anguwar gaba ?aya, a ba?ini kuwa zuciyarta har wani zallo take saboda ganin Yah Ab ?inta, duk yanda tai tunanin zata daure sai ganinsa ya canja dukan ?udirin nata lokaci guda. Sai dai kamar yanda ya fiske itama haka tai ?o?arin fiskewar.
Abdallah ne a gaba lokacin da zasu shiga gidan, Ahmad da Hajjo biye da shi, sai Nu'aymah a ?arshe tana karanto duk addu'ar da tazo mata a baki domin samun sassauci daga abinda takeji akan ganin Abdallahn.
Falon tsaf yake ko ina a gyare, ga ?amshi mai da?i yana tashi da sanyin ac. Sallamar Abdallahn da kara?in Hajjo ya saka Adawiya data cika da haushin tafiyar Abdallah batare da ta saniba ta fito. Sam idanunta basu kai a kan Nu'aymah ba, dan haka ta daka tsalle cike da ihun murna ta ?ane Hajjo, saurin ri?ota Ahmad yayi yana fa?in, "Ke malama karki ?arasata ki jamin tsiya wajen su Baba malam". Sakin Hajjon tai tana dariya ta juyo ta rungume Ahmad ?in shima tana tsale.
"Wannan matar taka bata da man kai sam Yah Abdallah ". Ahmad ya fa?a yana janye Adawiya daga jikinsa. Murmushi ya?e Abdallah yayi yana kama hannun Hajjo ya zaunar a kujera. Hakan yay dai-dai da ?agowar Adawiya zataima hajjo magana idanunta suka fa?a akan Nu'aymah dake tsaye gefe tana kallonsu.
"What?!!!!" Adawiya ta fa?a da sauri tana waro idanu waje, a take ta sar?e da yawu kuwa ta hau tari.
Karan farko Nu'aymah ta saki wani lallausan murmushi da har ya bayyana fararen ha?oranta waje, ta taho da wani irin ?oki ta rungume Adawiya dake tari tamkar zata amayo harshenta.
Dakatawa Abdallah da Ahmad da suka mi?e saboda ?warewar Adawiyar sukai. Nu'aymah ta ?an?ame Adawiya jikinta tana matso ?wallar da suka taru mata a ido akan dalili biyu. Ganin Abdallah, da kuma kewar Adawiyan.
Da wani irin sauri Adawiya tasa hannu biyu ta tura Nu'aymah, jikinta na wani irin rawar tashin hankali............?
??Tofa, hajiya Adawiya yaya dai???????.
Barka da juma'a????????
_______________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????
Mamu gee??
MIN ?ALB!!????
Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????
Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????
Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????
?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.
[4/4, 12:38 PM] +234 901 860 0202: *_INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN:_*
*_HERBALS APHRODISIAC NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_*
*_TO KU SAURARA KUJI, DOMIN NESA TAZO KUSA.._*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!!_*
*_MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA CIKI DA WAJE_*
*_MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI! LUWAI! TAMKAR TA JARIRAI_*
*_AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._*
*_KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_*.
*_AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_*
*_KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_*
*_MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_*
_INSTAGRAM LINK DIN MU:_
www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac
_WHATSAPP LINK DIN MU:_
https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz
_NAMBAR TARHON MU_
08169380189
*_KARKA BARI A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA 'DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYANMU A KO'INA A FADIN NAJERIYA._*
__________________________________
No. 21
................."Adawiya!!" hajjo ta fa?a a ?an tsawace. Yayinda Ahmad da Abdallah ma sukai wani zallon mamakin abinda Adawiya tayi suma.
Kallonsu tai a firgice idanunta na tara ?wallar takaici da jin zafin ganin abinda batai zato ko tsammani ba. Ta bu?e baki zatai magana a zafafe sai kuma ta tuna abinda ta nema mantawa. Saurin sauke numfashi tayi tana fashewa da kuka, tare da juyawa ta kalli Nu'aymah dake tsaye dafe da kujerar data taimaketa ta hanata fa?uwa lokacin da Adawiyar ta turata.
"Nayi fushi wlhy Aymah, yanzu dama dake za'azo amma kika?i sanarmin saboda ke yanzu kinma daina sona?". Adawiya ta fa?a cike da makirci da waskewa.
Ajiyar zuciya Abdallah da Ahmad suka sauke, dan duk zatonsu Adawiya da gaske da fa?a tayi abinda tayi. Hajjo dai bata motsa ba, amma ta kafesu da kallo su duka hu?un tana nazarin kowa.
Jin abinda Adawiya tace ne ya saka Nu'aymah sakin murmushi, dan tsaf ta fahimci