Showing 42001 words to 45000 words out of 325075 words
za?i tahowa a mota duk da Mom bataso hakanba. Sake rumtse idanunsa yay da shegen ?arfi da cije lip ?insa na ?asa sosai tamkar zai hudashi da ha?ori.
Duk abinda ya keyi drivernsa na kula ta cikin mirror, hakanne ya saka zuciyarsa sake zafafa da abinda yarinyar tai musu shima, ya kai hannu ya shafa inda Nu'aymah tai masa rotse da dutse aka saka masa bandage, wlhy yau badan oga ya hanasu ba da yarinyarnan saidai uwarta ta haifa wata. Shiyyasa shifa a rayuwarsa yay mugun tsanar ?an Arewa ?in nan musamman hausawa, ?auyawa dasu ko karatu basayi sai rashin mutunci. (Humm malam driver naka tunanin kenan, amma ?an Arewa sun wuce da sanin duk wani gur?ataccen tunaninka ai????). Shi yanzu babban tashin hankalinsa ma mi zasuce da Madam ?insu akan wannan al'amarin daya faru?, dan kowa yasan yanda family ?in gaba ?aya ke masifar so da ?aunar ogan nasu tamkar wani tsoka ?aya a miya.
Haka dai suka cigaba da tafiya kowa da abinda yake sa?awa a cikin rai. Gashi mahaukacin gudu sukeyi kai kace Lagos suka nufa ba Abuja ba.
Tunda 6pm tayi kiran Mom ya fara shigowa a wayarsa, sai dai ko sau ?aya bai amsa mataba ya share, sai ma kwanciya daya gyara cikin lallausar kujerar motar ya cigaba da latse-latsen laptop ?insa har yanzu da takaicin Nu'aymah a ransa.
*_ABUJA_*
*_09:30pm_* Dai-dai suka shiga garin Abuja saboda holdup daya ri?esu a madalla zuwa Kubwa expres, da ?yar suka fita a jigace, dan kafin su iso Asokoro ji yay tamjar ya fasa ihu dan gajiya, shi dama can mutum ne da baida jimirin tafiya mai nisa a mota, duk da tafiye-tafiye sun kasance cikin ginshi?in aikinsa kuwa.
Anguwace da bata da maraba da a cikin turai saboda rashin hayaniya da ha?uwarta. Ko ina ?wanyar yake da wutar nepa tamkar rana, duk da dare baiyi nisaba babu abinda kakeji sai haushin karnuka. Motocin uku suka tsaya dai-dai saitin wani ?aton ba?in gate da zaka iya hango cikin gidan daga waje kasancewarsa tamkar net. Horn sukai, da gudu sai ga wani dake cikin Blue Uniform ya iso da sauri ya bu?e musu.
Tunkan su gama dai-daita parking idanunsu suka sauka akan Madam Chioma dake ta faman kai kawo ta barandar saman bene. Sai dai ganin shigowar motocin tuni tabar wajen da alama zata fitone.
Tuni Securitys ?in gidan kusan su goma sha biyar suma sukayoma motar caaa. Bu?e masa akai da sauri, sai dai kafin ya fito Madam Chioma harta iso. Da kanta tasa hannu ta fiddosa a motar, tai saurin rungumesa tana magana cikin yarensu. "Yarona miya sameka? Ina kuka tsaya? Miyasa kaki ?aga kiranmu?". tashiga jero masa tambayoyin batare data bashi damar amsa ko guda ?aya ba daga ciki.
"Relax Maa! i'm okay". "Ka tabbatar?". Ta fa?a tana ?agosa daga jikinta hannayenta duka biyu akan kwantaccen sajensa tana shafawa, sai kuma tabi jikinsa da kallo daga sama har ?asa. Ganinsa dai lafiya lau saita sake rungumesa tana fa?in, "Thanks God".
"?an uwa sannu da zuwa". Wata murya ta fa?a daga bayansu cikin harshen nasara. Sakinsa Madam Chioma tai suka juya suna kallon mai maganar. Matashin saurayine da bazai wuce 22years ba, sai kuma wasu dake bayansa su kusan bakwai. Kallonsu yay ?aya bayan ?aya kafin ya bu?e masu hannayensa sukazo duk suka rungumesa suma suna masa sannu da zuwan. Sai da duk suka gama sannan ya amsa musu da "Thanks you". a jimlace.
Har sun nufi babbar ?ofar shiga ainahin cikin gidan ?aya daga cikin yaran cikin harshen turanci tace, "Jesus!! Miya faru da motarka Brother?!".
A tare duk suka juya suna kallon motar, amma banda shi dama yay gaba abinsa tamkar baiji mi Joy ?in ta fa?a ba.
Cike da firgici Madam Chioma ta shiga ?wala kiran sunan guards ?insa ?aya bayan ?aya. Aiko jikinsu har rawa yake suka nufota ransu cike da tsoron amsar da zasu bata akan abinda sukasan dole su amsa tambayoyinsa dama.
Aiko a jajjere ta shiga jero musu tambayoyin ko bari su bada amsa batayi. Sai da ?aya a cikin yaran da zatama iya kai sa'ansa tace, "Mom ki shiru haka mana su bamu amsar miya faru?". Zata sake magana budurwar tai saurin sake fa?in, "Please Mom". Shiru tayi badan taso hakanba. Ta maida hankali ga guards ?in da saima yanzune ta kula da masu fasashshen goshi biyu a cikinsu. Babban ne ya shiga mata bayanin duk abinda ya faru tsakanunsu dasu Nu'aymah daga farko har ?arshe. A take takaici da ba?in ciki suka sake rufeta ta shiga zagin Hausawa da kiransu da sunaye marasa da?in ji. Sai da tayi iya iyawarta kafin ta bar wajen tabi bayansa. Suma sauran yaran bayan nata sukabi suna zagi.
Shikam yana shiga ?aton babban falon gidan dake ?auke da set ?in kujeru biyu mabanbanta kala baiko tsaya ba yay saurin hayewa sama inda sashensa yake. Baya bu?atar kowa ya biyosa, dan haka yay saurin maida ?ofar corridor ?in sashen nasa ya rufe, sannan ya ?arasa nasa madaidaicin falon daya gama ha?uwa, yanata wani tattausan ?amshi mai da?in sha?a da kwantar da zuciya. murza ma ?ifar falon key yayi sau biyu sannan ya shige. dispencer dake acan gefen dining mai ?auke da madaidaicin d/table ya nufa, ya ?auki glass cup dake cikin wani showglass mai ?yau da ?aukar hankali ya matsi ruwa. Tas ya shanye wanda ya ?iban, ya ajiye kofin saman d/table ?in ya baro wajen zuwa wata ?ofa dake a cikin falon. Nan ?inma dai corridor ne, sai dai ?ofa biyu ce kawai a cikinsa, ?ofar ?arshe ya nufa yana zame ba?ar jacket ?in jinsa tunkan ya bu?e. Ya ri?eta a hannu ?aya sannan ya ?arasa ya murda handle ?in ?ofar ya tura ya shiga.
Fes ?akin yake shima, yanata tashin ?amshin fresheners data ha?e da turaren da yake amfani da shi. Jefa jacket ?in yay saman gadon ya ?arasa gaban mirror yana ?o?arin cire sar?ar cross ?in wuyansa. Ya ratayeta jikin wani ?an hangar ?arami mai ?yau dake cike da sar?o?in kala-kala a ajiye saman mirrorn. Zama yay a stool ?in gaban madubin yanata faman yamutse fuska dan yunwa yakeji, sai da ya cire takalman ?afarsa da safar, farar ?afarsa dake fes ta bayyana kafin ya mi?e kansa tsaye ya nufi wata ?ofar da ko ba'a fa?aba kasan toilet ne.
Yana shiga aka fara knocking ?ofar falonsa, amma sai ya share ya cigaba da abinda yake a ciki. Anyi kusan sau uku sannan aka bari. Ya ?auki tsahon lokaci a bayin kafin ya fito sanye da bathrobe Milk color. Hannunsa ri?e da ?aramin towel yana tsane sumar kansa da kallo ?aya zakai mata ka fahimci tana masifar lasar ku?a?e kodan ?yawun da take dashi ga mai kallo a ido balle kuma wanda ya ta?a.
"Yoohan! Bu?e min ?ofa". Ya tsinkayo muryar Mom tana fa?a cikin yarensu da ?an buga ?ofar yanda tasan bazai takurasa ba. Gefe ya karyar da wuyansa yana yamutsa fuska da yarfar da hannayensa duka alamar shifa an takura masa. Fuskarsa cike da takaici yaje ya bu?e mata tare da juyowa a binsa batare da ya tsaya saurarenta ba.
?ar dariya tayi abinta, dan ko ka?an hakan bai dametaba, tasan ya gajine matu?a, shikuma idan ya gaji to lallai sannan ba?in ransa ke ?ara hauhawa, kowa kuma yimawa yakeyi har ita da Papa. ?arasawa tai inda yake tsaye a gaban mirror yana cigaba da tsane kansa. Kama hannunsa tai ta zaunar, ta amshi towel ?in ta cigaba da goge masa kan tana kallonsa ta cikin mirror fuskarta washe da murmushi.
Shiko ya ciskule tasa kamar zai fasa ihu. Sai da ta tsane masa kan tas kafin tajawo hand dryer ta jona a jikin soket ta fara busar masa da shi. Ajiye dryer ?in tayi da jan hancinsa tana fa?in, "Nasan wannan fushin bana komai bane sai yunwa da gajiya my boy. Taso kaje kaci abinci ka kwanta ka huta". Tai maganar da turanci
Yana shirin mi?ewa danya shirya akai knocking ?ofar, jiyay tamkar ya fasa ihu dan takaici, shiyyasa sam bayason zaman gidan nan wani lokacin, dan ana hanama rayuwarsa sha?atawa da hutawa. A hakanma gwara nan, abinda yafi tsana shine zuwa ?auyensu, dan anfi cika masa ciki da takaici acan fiyema da nan Abuja. Mom ce tai magana, shiko tuni ya mi?e ya koma wajen kayansa. ?aya daga cikin ?annensa ce mai suna Victoria. Tarkacen kayansa ne daya bari a mota cikin guards nasa ya kawo tun ?azun, shine yayta masa knocking lokacin daya shiga bayi, da yaji ba'a bu?eba ya koma dasu ya bama yaran akan idan ya fito saisu kawo masa.
Zubesu tai akan table ?in gaban gadon, ta juya garesa zatai magana ya ?aga mata hannu da sauri tare da nuna mata ?ofar fita. Baki ta kumbura ta juya ta kalli Mom nasu dake murmushi sannan ta fice tana buga ?afafu da ?ananun kukan ta?ara.
Mi?ewa Madam Chioma tayi itama tana fa?in, "Ina jiranka kai maza ka fito". Kansa kawai ya ?aga mata ya cigaba da abinda yakeyi...........?
Read more har bakwai yau?.??????????.
_____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________
Wani kaya sai amale ka ?auka??.
SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.
Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ?an gaske.
*_Ina mata masu ?an bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ?ar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ?an ?walisa masu son sabunta gida da kayan ado ?an waje masu sau?in farashi da nagarta!._*
_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ?aya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ?yau da nagarta a farashi mai sau?i kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ?an gayu suma akwaisu babu ?ayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba'a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ?aki basu da tsara_.
Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.
Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ?arin bayani ?ar uwa.
*_Siyen nagari??, maida ku?i gida?? sai SAHFAT PREORDER??????????_*
_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????
Mamu gee??
MIN ?ALB!!????
Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????
Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????
Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????
?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.
[3/18, 7:07 PM] +234 901 860 0202: *_Typing??_*
No. 12
________________________
*ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE*
*_KAJI shahararrun kuma mandiyoyin ?an ?walisar kawo kayan kitchen masu tafiya dai-dai da zamani. Idan nace nadaban ina nufin su?in nadabanne wajen kaya ?an gaske dake ?awata kitchen ?in amarya harma dana uwargida ?ar ?walisa. Ka siya ka tabbatar ka saya ?in ko a gaban tsaranka sai ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. sunan kayansu sa kishiya cin bashi??, dan tana ?yalla ido taga kitchen ?inki tsarin amerikawa tuni zata fara ?wafa da tunanin zuwa gidan delu dillaliliya mai saida kwanika. Sai dai kuma kama da wane akace bata wane, dan haka ku maza ku garzaya ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. domin samun naku kuma. Suna kawo kaya daga ?asashen ?etare akan farashi mai sau?i da rahusa. Suna order ?in products kamarsu, dukan kayan kitchen na zamani, bedsheets, shoes dade sauransu, products ?insu pre-order ne dake zuwa akan lokaci batare da mai kaya ya ?osa da jira ba ko samun matsala. Zaku iya samunsu a Number waya kamar haka ko Location nasu. Phone number: 08102393622. Location Gombe. Amma Zasu iya turawa kowani gari dake a lungu da sa?o na ?asarnan. Sayen nagari maida ku?i gida. Ku garzaya kar ayi babu ku. Da ?yar nasha yafi da ?yar aka kamani inji masu iya magana??????????._*
___________________
................Sai da ya kammala ?alular shirinsa cikin kayan barci wando 3quarter da riga Armless sannan ya zura slippers masu taushi ya fita. Kusan su shidda ya iske a falon kowa da hidimar da yakeyi. Wasu kallo wasu danna waya wasu surutu.
Da sauri Miracle ta ?auki remote ta rage ?arar television ?in dan tasan ya tsani hakan. Shikam baimabi takan kowaba ya nufi d/table. Kafin ya ?arasa Miracle ta rigashi isa, yana ?aura hannunsa saman kujera zai jata baya ta ?ora nata akan nashi. A take fuskarsa ta sake tsukewa, ya ?ago fararen idanunsa ya zuba mata wani banzan kallo. Maimakon ta janye hannun saita kashe masa ido ?aya tana murzawa a hankali. Kallon hannun yayi cike da tsantsar fushi. Duk da tsoronsa dana yanayinsa a yanzu ke ratsata bata fasaba, saima karta za?o-za?on faratan ta ta farayi tana matsawa da hannunta gaba akan nashin cike da salon iskanci.
Ita da kujerar ya ha?a ya wancakalar gefe, kafin takai ?asa ya bita da halbi, sai gata ?asa wanwar. ?arar data firgita kowa a gidan ta ?walla tana faman ihu kamar wadda aka yanka. Dukansu kanta sukayo, yayinda Yoohan ya sake ?aga hannu zai ?wa?a mata mari Gebrail ?aninsa yay saurin ri?esa, fisgewa yay yayi ?wallo da kujerar kusa da shi ta dining ?in ya juya fuuu kamar wani kumurci ya nufi sama. Da sauri Mom data fito daga wani ?ofa yanzu saboda jiyo ihun Mira ta shiga ?wala masa kira da turanci. "Yoohan! Yoohan!! Yi hakuri zo kaci abinci".
Baiko waiwayeba balle tai tunanin samun amsa. Da gudu ta bisa tana ha?a steps ?in da bibbiyu. Kafin ta ?arasa har ya tura ?ofar ya maida ya rufe. Bugawa Mom ta shigayi tana kiransa cike da lallashi "Yoohan! yi ha?uri kaji, kar kayi fushi zo kaci abinci Please". Duk da yaransu take maganar, amma ya?i bu?e mata. Shi tunima yabar jikin ?ofar harya shige bedroom ?insa.
Zuciyarsa cike da matsanancin ?unci ya fa?a saman gadonsa ya kwanta a rufda ciki. Ji yake gaba ?aya duniyar ta masa masifar ?aci, yaja filo ya danne kansa da shi da ?arfi.
A falo kam Mom data sakko a ranta a ?untace ta ?arasa inda Mira ke faman kuka har yanzu, cikin fa?a tace, "Miracle bance ki fita hanyar Yoohan bane? Kin riga da kinsan halinsa baya son wannan banzan halayar amma ke kam bazaki kama kankiba. Ki cigaba, wataran idan ya karyaki ko ya miki mugun dukan da za'a gaza ganeki zaki kiyayesa ai". Batare da ta saurari amsa daga Mira ba ta wuce ?akinta cikin fushi itama, dan a rayuwarta ta mugun tsanar ganin an ?atama Yoohan rai a gidan. Tana masifar son yaronta fiye da sauran ?a?anta.
Kuka Mira ta sake ?arkewa da shi iya ?arfinta su Joy na lallashinta, da ?yar suka iya ?agata dan tanada jiki sosai bawai siririya bace, sannan a shekaru sai dai suyi sa'anni ma da Gebrail ?anin Yoohan ?in.
Da taimakon su Joy Miracle taje ?akinta, sai da suka kwantar da ita a gado Gebrail ya kalleta shima cike da takaicinta. "Mira idan baki fita hanyar Brother ba na tabbatar shine zai maidaki gurguwa kafin ki koma gidanku, nasha fa?a miki shifa a rayuwarsa yanda ya tsani shan giya haka ya tsani harka da mata. Wanda yay kashi biyu cikin ukun rayuwarsa a turai matan can basu sakashi ya iskance ba ta yaya kike tunanin ke ?aramar ?waruwar Najeriya zata iya sakashi aikatawa? ?ilama dakin kama kankine zai soki kamar yanda kikai fata, amma a haka ina tabbatar miki tsanarki yake ?arayi dan baya ?aukar lamarin ta fuskar soyayya, idan kinji shawarata sai ki kiyaye". Yana gama fa?a ya juya yay ficewarsa, kafin duk suma sauran su fito a barta daga ita sai Joy da take kusan sa'arta itama. Dan twins ne ita da Gebrail ?in. Hawayenta ta share tana danna ?afarta data buge, da yarensu tace, "Joy wai miyasa Brother ?inku bashi da kirki?, gashi duk iskancin da wula?ancin da yakema mutane su Mom sai sudinga goya masa baya basa son ?acin ransa, kamar sunajin tsoronsa ma......" da sauri Joy ta rufema Miracle baki da hannu tana girgiza mata kai, sai da ta tabbatar tayi shiru kafin ta saketa, ?ofa ta nufa da sauri ta le?a, ganin babu kowa saita maida ta rufe sannan ta dawo wajen Miracle ?in. Daf da ita ta zauna cikin magana ra?a-ra?a tace, "Ni kaina na da?e inason yin maganarnan da Wani Mira, kinga dai su Mom duk su suka haifemu, amma idan kika lura sunfi son Brother Yoohan, ko yaya suka gansa a damuwa sai kiga sun rikice, sannan duk abinda yakeso shi ake masa. Kiga dai yanda kike sonsa yana wula?antaki a gidan nan amma basu ta?a nuna masa rashin dai-dai akan hakan ba. Kowafa tsoronsa yakeji anan gidan har