Showing 153001 words to 156000 words out of 325075 words
la'asar ?in ya shigo suna magana dasu hajjo a falo.
Ana idar da sallar la'asar mafi yawan mutanen dake cikin gidan suka fice wajen walimar. Anguwar tayi tsit bakajin komai sai karatun alkur'ani Muhammad ?aninta ke rairawa cikin zazza?ar muryarsa mai da?i. Lamo tai a kan gadon hajjo dan bata da sha'awar fita wajen walimar. Fitar tata zai iya fama mata ciwuka masu yawa da suka zame mata gyambo a zuciyarta. Hakan yasa ta za?i cigaba da zamanta tunda daga nanma tana iya jiyo komai da ake fa?a tamkar tana a wajen.
A wajen walima kam bayan Muhammad ya gama karatu baba malam ya bu?e taro da addu'a ga amare da angwayensu dama al'umar musulmai gaba ?aya. Daga nan aka fara abinda ya tara mutane.
Duk yanda akaita ragargaza wa'azi mai ratsa jiki a kunnen Nu'aymah ne, duk ba itace amaryarba sai da ta taya su Aunty Hajarah hawaye. Lokacin sallar magrib nayi akaje akai salla aka sake dawowa. Sake ?orawa da wasu nasihohin sauram manyan malamai abokan su baba malam sukayi. Daga haka akaci aka sha kowa yay hani?an, aka kuma raba abubuwa kamar yanda suka saba duk lokacin aurar da yaransu ko yaran gidan marayunsu.
Lokacin da aka tashi tuni Nu'aymah data koma sashensu tai barci a falon baba malam. Umm bata sani ba, dan tana can wajen taimakawa ba?in da zasu kwana a sashenta samun wajen kwana. Sai da baba malam ya shigo wajen sha biyu sannan ya ganta kwance a doguwar kujerar falonsa ta na?e waje guda alamar sanyi takeji. Zama yay a kujerar gefen da kanta yake yana kallon ?ya?y?yawar fuskar ?iyar tasa mai tsananin kama da mahaifiyarta abar sonsa da ?aunarsa. ?an murmushi yayi tare da shafa kumatunta sannan ya mi?e. Batare daya tadata ba ya cire babbar rigarsa ya lullu?a mata. Yana jinta ta sauke ajiyar zuciya, tare da gyara kwanciya. Shima ajiyar zuciyar ya sauke ya ?auka remote ?in ac ya rage mata shi sosai sannan ya wuce bedroom ?insa cike da tausayinta.
*_JUMA'A_*
Da asuba baba malam bai wuce massallaci ba sai da ya tada Nu'aymah. Bayan an idar da salla bai jimaba ya dawo dan yau basuyi zaman karatu ba daman. A falo ya iske Nu'aymah inda tai salla tana karatun Al-qur'ani. Zama yay kallonta da sauraren zazza?ar muryarta da a yau take fita da sanyi matu?a. Yayi kusan mintuna arba'in sannan Umm ta shigo falon da sallama. Tray ?in hannunta ta ajiye a gabansa tana kallon Nu'aymahn da mamaki. dan ita dai bataga wucewarta ba. Kallon baba malam tai, ya sakar mata lallausan murmushi tare da maida idanun nasa shima kan Nu'aymah da batasan sunayi ba.
Zama Umm tai a kusa da shi. Cikin magana ?asa-?asa tace, "Yaushe tazo nan?". Murmushin ya sakeyi kamar bazaice komaiba, sai kuma ya ?an sauke numfashi yana ri?o hanun Umm cikin nasa. Cikin wani irin yanayi yace, "Anan ta kwana. Nima na dawo wajen walima na sameta anan da alama bama taje wajen walimar ba".
Guntun numfashi Umm ta furzar, batare da tace komaiba ta zare hannunta cikin nasa. Shayin daya saba sha duk irin wannan lokacin ta shiga ha?a masa. Yayinda Nu'aymah keta karatunta batare da tasan mi sukeyi ba. Sai dai tana ?an jin motsinsu ka?an-ka?an, dayake hankalinta baya a tare da sune yasa batajin mi suke fa?a.
Duk hidimar da ake a gidan da sake cika da yake yi da ba?i Nu'aymah tana sashen baba malam ta?i fitowa. Yau tare da shi ma sukai breakfast. Sashen nasa ma itace ta gyara masa yau. Bayan yayi wanka ya fito ta shiga ta gyara masa bedroom ?insa tsaf, ta dawo falo inda yake zaune shida ?annensa da huhunan goro dana alawa da aka shigo da su, magana suke ?asa-?asa alamar tattauna wani abu mai muhimanci a garesu. Cike da girmamawa ta gaidasu, duk suka amsa mata da kulawa tare da tambayarta yaya ?arfin jikinta.
Har zata fice baba malam yace ta koma tai wankan a bathroom ?insa tunda mutane sunyi yawa a gidan. Da?i taji sosai, dan haka ta juya cike da ?oki ta koma bedroom ?in baba malam ?in.
Tsaf Nu'aymah tai shiri da kayan da Umm ta kawo mata ?akin baba malam ?in. Lass ne ?an ubansu sky blue da akaima ?inkin riga da zani. Ya zauna mata ?as a jiki tare da haskaka farar fatarta daketa ?yalli. ?ar ramar da tayi sai ta sake fiddo ainahin dogon hancinta da manyan idanunta masu matu?ar haske da cikar gashi. Turaren baba malam dana Umm dake a bedroom ?in babu wanda bata fesa ba. Hakan yasa take zuba uban ?amshi tamkar tayi wanka da turare. Gashi caku?asun da tayi sai ya bada wani irin shu'umin ?amshi mai narkar da zuciyar mai sha?a. ?an kwalin ta ?aura bisa gyararren gashinta da hajjo ta matsa jiya Yah Omar ya kaita wajen wankewa tare da su Amal. Ta saka sar?a da sauran kayan adon sannan ta ?auki blue gyalen da aka ha?o mata da shi ta ?ora a kafa?arta. ta zira flat shoes ?inta suma blue. Tayi ?yau sosai tamkar ka saceta ka gudu. Kamar yanda Umm ta garga?eta akan idan ta shirya ta fito ta gaisa da ba?i batayi musu ba ta nufi sashen Umm ?in bayan ta kulle falon baba malam ta taho da key ?in a hannunta.
Tunda ta fito jama'ar dake zazzaune a falon Umm keta ambatar masha ALLAH. Ita dai cikin ?an jin nauyin wasu daga cikinsu ta shiga risinawa tana gaishesu. Masu tsokanarta kuwa ta kasa maida murtani. Sa?anin da da kowa yasan Nu'aymah bata barin saita kwana ga abokin wasa. da kace kule take cewa cas. Amma yau sai ga bakin ya mutu murus sai ?an sassanyan murmushi kawai take musu a ta?aice.
Har bedroom ?in Umm ta shiga inda ?anen Umm da yayunta ke cike da shi. Nanma gaidasu ta shigayi. Sukam sunata amsawa cike da ?aunar ?iyar ?ar uwar tasu. Aunty Hibba dake cin abinci ta jawo hanunta ta zaunar kusa da ita tana fa?in, "Zauna kici abinci. Ni wannan ramar taki sam banason ganinta dota". A ?an shagwa?e Nu'aymah tace, "ALLAH na ?oshi Umma, munyi breakfast tare da Abba, kuma naci sosai ki tambayi Umm ma kiji".
"Eh breakfast ai tun ?azunne, kusan awa uku kenan, wannan abincin rana ne. Ke dama nasani da masifar son masa". Duk yanda Nu'aymah taso zamewa sai da Aunty Hibba ta dinga bata masar a baki tare da naman. Sai gashi kuwa ta?anci babu laifi ta kuma shanye ?aramar roban zo?o data ?auka.
¡ï¡ï¡ï¡ï
A ?angaren su baba malam kuwa duk sun ?unguma massallacin juma'a inda za'a gudanar da ?aurin aure bayan sallar juma'a insha ALLAHU.
Massallacin ya cika dan?am da manyan mutane daga kowacce kusurwa ta Najeriya harma da wasu ?asashen ?etare. Tun daga kan malamai, ?an kasuwa, harma da masu mulki. Sai abokan arzu?a da ?an uwa na kusa dana nesa. gayyar anguna dana jama'ar gari da girma da kimar su baba malam ?ince ta tarasu a wajen.
Bayan kammala sallar juma'a akai ?aure-?auren aure ciki harda na ?a?an su baba mala su Aunty Kubrah. Ana kammalawa manyan ba?i suka ?unguma babban hall ?in da aka kama domin gudanar da ?warya-?waryar walimar cin abinci.
Walimar ce ta jasu har sai bayan la'asar sannan suka koma gida da wasu tawagar ba?in da ba'a ranar zasu wuce gida ba.
Zuwa yanzun kam gidan su Nu'aymah ya sake cika dan?am da mata, dan yau ne Addah ke nata yinin bikin. Hayaniya akeyi sosai babu maijin wani. Dan tun bayan ?aurin aure su Omar sukaje gidan da labarin yanda komai ya kama.
Nu'aymah na tsakkiyar dangin Umm har yanzu. Sun sakata a tsakkiya anata hirar zuminci cike da farin ciki. Wata Gwaggon su Umm ce, data kasance kaka ga Nu'aymah ta shigo ?akin tana gu?a. Da mamaki duk suke kallonta har suna rige-rigen fa?in, "Gwaggo an ?aura ne?".
"?warai da gaske an ?aura. Yanzun ma haka ?an ?aurin aure sun dawo, kuma harda sabon albishir na ?arin amarya".
Aunty Fareeda tace, "?arin amarya kuma Gwaggo? A cikin yaran gidan dai?".
"?arku ma kuwa" ta sake basu amsa tana cillara wata sabuwar gu?ar. Kafin su gama fita daga ru?ani su Nanah suka shigo suna ?wala kiran "Nu'aymah amarya".
Dakatar dasu Aunty Hibba tayi. "Kai mufa kuna sake ?atar damu, Gwaggo wai mike faruwa?".
Da sauri "Raudah tace, "Momy baku san Nu'aymah ma an ?aura mata aure ba yanzu tare da su Aunty Hajarah. Yanzun ?an ?aurin aure da suka dawo suke fa?a ai".
A take ?akin ha harmutse da murna da taraddadin wanene angon? Miyasa kuma aka ?oye musu, dan su dai basusan da auren ?iyar ?ar uwar tasu za'ayi ba. Duk sunzone yima Addah baici kasancewar zumincine mai ?arfi da kowa ya sani a tsakanin Umm da ita.
Tunda aka fara wanan kace nace Nu'aymah ta ?ora hanunta saman kai ta ri?e. Cusashi tai a tsakanin cinyoyinta jikinta na wani irin tsuma. Ga kanta ya fara sara mata sama-sama. Duk yanda taso ta daure ta kasa. Dan haka cikin ?arfin hali ta shiga laluben wanda ke a kusa da ita. Cikin sa'a ta dam?o hanun Aunty Magajiya yayar Umm. Hankali tashe Aunty Magajiya ta dubeta, sai kuma yanda taga jikin Nu'aymahr na karkarwane ya sakata ambaton 'Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un' da ?arfi.
Kusan mafi yawan ?an ?akin sai hankalinsu ya dawo wajen. A take kuma sai duk sukai tsitt tare da zabura kan Nu'aymah......
Gwaggo Ramma ce ta hana ?aga maganar mawuyacin halin da Nu'aymah ke a ciki a gidan har lokacin da su baba malam suka dawo. Dan Umm ma bata fasa kai da kawowar da takeyi tsakanin sashen Addah da sashentaba saboda son ganin ba?i kowa ya samu abinci. Yin komai takeyi cike da ?arfin hali. Sai ta fakaici idon mutane take share hawayen dake cika mata idanu. Duk da kuwa ita tasan da maganar auren. Kuma tana cikin masu goyen bayan ?aurashi a yau ?in saboda wasu dalilainsu ita da baba malam da hajjo.
Key da baba malam bai gani bane a inda suke ajiyewa ya sakashi kiran wayarta. Cikin sa'a kuwa wayar tana a tare da ita. Dan haka ta ?aga ya sanar mata gashi ya shigo amma baiga key ba. Ta kira masa Nu'aymah ko ta canja masa waje.
"To" kawai tace masa ta yanke wayar.
?akinta ta fara shiga inda danginta ke zaune jigum-jigum da Nu'aymah shimfi?e bisa gado tana fidda wahalallen numfashi tamkar mai Asthma. Aunty Juwairiyya sai shafa mata ruwa take a fuska wasu kuma na tofa mata addu'oi. Wani Key ?in ta ?auka a drawer ta fita batare da tace musu komaiba ta fice.
A kallo ?aya baba malam ya fahimci akwai matsala. Tunkanma ta bu?e ya shiga jero mata tambayoyi akan mike damunta?. Sai da ta bu?e ?ofar suka shiga sannan tai masa bayani. Shima hankalinsa ne ya tashi, dan haka yace taje su maido Aymah sashensa, karsu bari kowa kuma ya fahimci halin da ake ciki. Bara ya kira Doctor.
Tunda aka dawo da Nu'aymah sashen baba malam ALLAH ya bata ikon ganinsa saita dam?e hannunsa tana cigaba da jujjuya kanta da fisgar numfashi a wahalce. A hankali take magana wadda idan ba'a kusa da ita kakeba ma bazakajita da ?yau ba.
"Abbah kaina, kaina zai fashe Abbah. Kamin addu'a kaina zai fashe, Abba kamar ana kartamin ?arfuna a ciki. Innalillahi... Abbana zan mutu.."
Cikin rawar harshe baba malam yake girgiza mata kansa da ha?iye abinda ke cinkushe masa ma?oshi da ?yar. "Bazaki mutuba Mamana kinji, daina magana kiyita addu'a a ranki insha ALLAH ga Doctor nan zuwa kinji". Ya ?are maganar da saka ?an yatsa ya ?auke hawayen da suka tsatstsafo masa saman fatar ido. Hajjo da Ananah ma hawaye sukeyi. Haka su Abban Abdallah ma duk zukatansu suya suke da tausayinta.
Sallamar da akayi a bakin ?ofarne ya sakasu duk kallon ?ofar tare da amsawa. Ahmad ne ya fara shigowa, yana sanye cikin tattausan farar shadda harda babbar riga. Har yazo tsakkiyar falon sai kuma ya ?an juya ganin wanda suke tare bai biyosa ba. "A'a Doctor shigo mana".
Kusan seconds biyar kafin a ?aga labulen ya shigo bakinsa ?auke da tausasa kalaman sallama. Sanye yake cikin wata shegiyar bugaggiyar shadda getzner kalar royal blue. Wando da riga harda babbar riga. Sai hular zanna daya murza itama royal blue data samu nutsatstsiyar sa?a. Hatta da agogon dake a tsintsiyar hannunsa kalar blue ne. Wanda bai saniba sai ya ?auka wannan ?in itace shigarsa dama can tun fil azal. yayi ?yau harya gaji a cikin kayan. sun sake fidda masa kwarjini da cikar haiba da kamala. Farar fatarsa ta sake haskawa tamkar wata ?an daren sha biyar. Yanda sajen fuskarsa da kwantaccen gashin kansa dake ba?i si?ik kwance a ?eyarsa suke ?aukar ido babu tababa zaka iya sakashi a jinsin larabawa. Idanba fa?a maka akaiba bazaka ta?a yarda Dr Yoohan ?an gidan Papa da Madam Chioma ne ba wanda ko hausar bai gama fahimtar inda ta dosa ba balle akai ga larabci.
A hankali ya cigaba da tako ?afarsa dake sanye cikin ba?ar safa cikin falon, dan ya cire takalman a ?ofa.
Tunda yay sallama Ananah da Hajjo suka zuba masa idanu cike da jin da?in isowarsa a kan lokacin da ya dace. Umm kam kallo ?aya tai masa ta maida idanunta ?asa tana sauke ajiyar zuciya a hankali. Cikin girmamawa ya gaida su Hajjo. Suma sun amsa masa da kulawa harda ?ar tsokana. Ka?an gefen bakinsa ya motsa alamar murmushi. Dan bayan gaisuwar baiji mi suka fa?a ba sam tunda da hausa sukai magana.
Baba malam da ya tashi daga inda yake zaune ne ya nuna masa alamar ya zauna anan. Bai musaba ya zauna idanunsa akan Nu'aymah da har yanzu take ri?e da kanta. Sai da yay mata kusan kallon minti ?aya da wasu sakanni sannan ya ?ago. ?an kallonsu yayi sai kuma ya sake maida idanun nasa kan Aymah.
Da sauri Ananah tace, "?an nan ko akwai matsala ne?". Ya ?anji wani abu daga zancen nata. Sai dai bai iya ha?asu a jimlace yanda zai fahimta ba. Hakanne ya sakashi kallon Ahmad dake ?an murmushi. Fa?a masa abinda tace yayi, hakan yasa Yoohan cewa, "No babu damuwa Mama. Sai dai a ringa kula, indai zata ringa shiga irin wannan yanayin akwai matsala. Aikinmu zai dinga komawa baya".
"Yoni yaro bafa jin wannan yaren naku na masu jajayen kunne nake ba, kai Amadu fassara mana mi yake cewa". Ananah ta fa?a da iya gaskiyarta.
Gaba ?aya su baba malam murmushi sukayi dajin zancen Ananah. Umm ma saita nufi ?ofar fita ita dai tana nata murmushin. Cike da ?ar tsokana Ahmad yace, "Gaskiya Abba kubani kwangilar maida Hajjo da Ananah makaranta, dolene su fara jin turanci kwanan nan".
Da?uwa Abban Adawiya yay masa. Yayinda Hajjo ta talle masa ?eya tana fa?in, "Kaci gidanku Ahmadu. Yo turancin banza turanci wofi. tunda munajin yaren da ALLAH yayimu a cikinsa muna kumajin yaren dayafi kowanne daraja, yaran MANZON ALLAH larabci ai mungama nasara. Kune kuka ?auki amanar kanku kuka mi?ama masu jan kunne shiyyasa gashinan kullum sai hanyoyin wajiga rayuwarmu suke ?ara ?ir?irowa. Shima Yahaya ?in kwanan nan dan gidansu sai ya fara iya hausar".
Duk da Yoohan bajin abinda ta fa?a yay ba, baisan sanda murmushi ya kufce masa ba ganin yanda take masifa akan Ahmad tana duddungure masa kai hularsa har tana matsawa baya. Su Baba malan kuwa sai zuba murmushi sukeyi. Sosai abin nasu sai ya birgesa, musamman daya tuna nasa kakannin da kullum babu abinda sukafi ?warewa sai masifa da fa?a kamar kajinaye.......
Hannunsa da Nu'aymah ta ri?o ne ya sakashi saurin juyawa gareta. Cikin yanayin ciwo ta sake matse lallausan tafin hanun nasa cikin nata tare da ?orasa bisa kanta, "Abbah ka ri?emin zai fashe".
A hankali Yoohan ya lumshe idanunsa ya sake bu?ewa a kanta. Baiyi magana ba, bai kuma janye hannunsa data ?ora akanta ba ta danne da hannunta kuma.
"Inaga mu bara mu barka kayi aikinka". Ya tsinkayi maganar Abban Abdallah a cikin kunnensa. Janye idanunsa yay daga kallon da yakema Aymah, sai dai kafin ma ya ?ago su duk sun fice. Hajjo da Ananah da Ahmad kawai aka bari.
Baice komaiba sai hannunsa da yay ?o?arin janyewa daga kanta. Amma sai ta sake ri?esa da ?yau tana fa?in, "Abbah Please karka tafi ka barni, kaimin addu'a kaji Abbana".
Sosai tausayinta ya sake lullu?e su Hajjo. Yoohan ya