Showing 162001 words to 165000 words out of 325075 words
da shara?in duk randa na kama wani da laifin mata koda maganar banza a cikinku ko cikin yaranku sai mutum yabar gidan nan koda ace kuwa cikin su Gebrail ne. Itama kuma na muku al?awarin bazata shiga rayuwarku ba bayan mutuntawa da girmamaku".
Cike da wani mamakin suke kallonsa. Zasuyi magana papa yay saurin fa?in, "Wannan tsarin na John yayi dai-dai. Dan shine zai kawo mana masalaha da kwanciyar hankali a zuri'ar mu. Mukuma sake tabbatar da kowannenmu nada ?ancin aikata abinda bai sa?amana ba".
Babu wanda ya iya sake cewa komai. Sai singing ?in da Yoohan ya fara yi ya basu suma duk sukayi. ?aya ya ?auka ya basu ?aya. ?ayan copy ?in kuma da aka saka cikin frame ya nufi bangon falon daga kusurwar d/table ya kafesa jikin ginshi?in wajen daya zama kwalliya.
Wannan abu da Yoohan ?in yayi ya kuma girgiza su matu?a. Gashi babu damar magana dan ya tsuke fuskar fiye da ?azun.
Wannan takardar Agreement itace ta zama makullun rufe bakin duk wanda keda ?arfin fa?a a ji a family ?in su Yoohan. Sai ma zaman shirya biki sukai dan nuna bajintarsu ga gudan jininsu tamkar yanda akema kowa.
Shi dai Yoohan bai tanka kowa a cikinsu ba akan shirin bikin, ranarma yini yayi a asibiti shi da Richard. Basu dawo ba sai dare. Gajiyar da sukayi ce ta sakasu ko zaman hira basuyi ba Yoohan ya shige sashensa. yau ma tsabar wula?anci hana su Rich shiga yayi. da sukai magana yace shi yanzu yayi aure baya bu?atar su a sashensa. Suje can su ?arata a sashen ba?i suyita loda kwalaben barasarsu.
Aiko sun hayayya?o masa tamkar zasu cinyesa. Ya fice yana murmushi bayan ya musu gwalo.
______¡ï¡ï¡ï_______
*_KANO_*
A kano kam tunda garin ALLAH ya waye yau da shirye-shiryen tahowar su Nu'aymah aka tashi. Dan zasu taho abuja gidan su Abdallah. washe gari sai a mi?ata ?akin mijinta daga nan gidan. Saboda ma baba malam baya bu?atar ayi wata gayya jirgi zasu biyo.
Jin abuja zasu wuto yasa Nu'aymah fara tunanin ko dai yah Ab aka ?aura mata aure da shi? Ko burinsu na mallakar juna ya tabbata ne? To amma idan har hakane mizaisa a ringa ?oye mata?. Har yanzu babu wanda ya sanar mata wanene mijinta. sai dai kowa na zaunar da ita yay mata nasiha dai-dai gwargwadon saninsa. Haka ne yasa yau taci kuka harta godema UBANGIJI. Mai ?unshi ma da Addah tasa aka kawo da ?yar Aymah ta yarda akai mata. Hakama da za'a kaita gyaran jiki sai da baba malan ya saka baki wajen lallashinta sannan ta amince. Ai ko sai gata tayi ?as tamkar ka saceta ga gudu. ?ar ramar da tayi saita sake ?ara fiddo mata da ?yawunta da haskenta. Sai dai a kallo ?aya ka?ai ya isa ka tausaya mata duk tayo laushi kamar ba Nu'aymah tsiwa ba. Duk ta zama shiru-shiru, ta kuma nanema Umm ta?i barinta sukuni.
Lokacin da aka idar da sallar la'asar Ananah tazo har sashensu tajata dan taje a kimtsata tunda jirgin 5:30pm zasu bi saita saka musu sabon rikici. Babu wanda bai lallasheta ba amma ta?i tai shiru. Sai da baba malam ya fito yay mata jan ido da nuna mata ?acin ransa sannan. Aiko tana kuka tana shar?ar hawaye. Koda ta fito ma sai Aunty Kulu yayar Naser ce tai mata kwalliya ka ?an dukda kuwa ba wai gidan su Yoohan ?in zata sauka kai tsaye ba.
Tsaf ta sakata ta shirya cikin atamfa lass ?ar ubansu, ?inkin zani da riga. Kasancewar atamfar ba?a ce da kwalliyar golden sai tai bala'in zama mata a jiki tamkar ka saceta ka gudu.
Iyayenta sun sake taruwa a kanta sun mata nasiha da garga?i mai fa?i akan rayuwar da zata fuskanta ta aure mai cike da ?alubale. Dan aure ibadane. Ita kuma ibada a koda yaushe tana a cike ne da jarabawa kala-kala. Daga haka aka mi?ata wajen Umm tai mata sallama. Ba Umm da Nu'aymah kawaiba, hatta duk wanda ke a wajen sai da ya matse hawayen tausayinsu. Da ?yar aka ?anbare Aymah jikin Umm. Hakama Muhammad dake taya yayar tasa kuka abin tausayi. Daga haka aka kaita kowane sashe tai musu sallama sannan aka shiga da ita ?aya daga cikin motocin da zasu musu takkiya zuwa airport. Abban Abdallah da duka yaransa duk sun fito dansu daga haka zasu koma kenan sai kuma anyi hutun makaranta. Sai matan Abba Musbahu duka biyu da zasu mata rakkiya. Sai Ananah da Aunty Kulu. Aunty Aysha, Sai ?anen Umm biyu da yayarta ?aya. Sai Yusrah da Adawiya da taso tirjewa bazataje ba. Sai da Hajjo ta zageta tas sama da ?asa sannan ta yarda da binsu badan taso ba. Sai Nanah, da Rufaidah autar su Naser.
Tunda motocin suka ?auki hanyar airport Aymah ta kwantar da kanta jikin Aunty Hibbah ta cigaba da raira kukanta a hankali. Aunty Hibbah dai nata shafa bayanta cike da lallashi amma batace uffanba.
Basu wani ?ata lokaci ba a airport ?in jirginsu ya ?aga zuwa Abuja. Tafiyar mintuna ?alilan kuwa ta kaisu. Anan ?inma dai tarbarsu akazo akayi, daga gani dai daga company ?insu ne masu tarbar. Zuwa yanzun jikin Nu'aymah yayi zafi zau da zazza?i, hakan yasa suna isa Momy ta kama hanunta zuwa ?akinta, sai da ta sakata tai sallar magriba da aketayi lokacin da suke shigowa gida, tana idarwa ta haye gado ta kwanta Momy ta lullu?a mata bargo saboda rawar sanyin da taketa faman yi.
Ganin yanda rawar sanyin nata ke ?aruwa Momy taje ta sanarma Abban su Abdallah dake shirin fita massallaci sallar isha'i. Biyota yay suka dawo ?akin tare. Shima sai hankalinsa ya tashi jin yanda jikin Aymah yay masifar zafi. Ga rawar sanyin na ?aruwa harma tana ro?on a ?ara mata wani bargon.
"Khadijah inaga bara na dawo masallaci sai a kira Yahya zaifi, dan yayi garga?in bata magani kai tsaye. Nasan yanzu kuma a duk inda yake yana ?o?arin yin sallar isha'i ne tunda kiji gashi can za'a tayar".
"Eh gaskiya, hakan zaifi Abbansu. Bara nayi sallar nima kafin ku shigo".
Bayan an idar da sallar isha'i Abba ya shigo gida. Kai tsaye waya ya ?auka yay kiran Yoohan. Sai dai harta katse bai ?aga ba. Ya sake kira nanma bai ?aga ba. Ajiye wayar yayi yana fa?in, "Maybe baya kusa. Amma idan ya gani nasan zai kira". Kai Momy ta jinjina masa kawai.
A lokacin da Abbah ke kiran wayar Yoohan yana massallaci, wayar kuma na mota, dan suna wani hotel tun kafin magriba shi da su Joseph akan dinner ?in da za'a gudanar gobe idan ALLAH ya kaimu bayan kawo amarya. koda ya fito kuma wajen nasu ya koma dan dama yace musu ne kawai yana zuwa, sukuma tsare-tsaren da sukeyi ya ?auke hankalinsu basubi ta kansa ba akan inda zaije ?in.
Kujerar daya tashi ya ja ya zauna yana harar Osin da aka ajiyema kwalbar giya da yayi oda. Bai dai ce komaiba, sai Osin ?inne yay murmushi yana fa?in, "Duk iya hararka dai ba ?insha zan ba. Kaima koda ?ura gobe sai ka shata domin farin ciki, koba komai kaji da?in cin soyayyarka da amryarka". Dariya suka kwashe da ita gaba ?aya. Richard yace, "No, bazai shaba a wajen dinner sai ya koma gida, so kake y......" bammm kakeji Yoohan ya dokema Rich baki da bayan hannu kafin ya karasa fa?a. Aiko mizasuyi inba dariya ba. Tsabar mugunta Godwin har fa?uwa yake ?asan korayen ciyayin da akaima wajen shimfi?a da su. Richard daya ?ata fuska yace, "Mr X da zafi fa". "So.." Yoohan ya fa?a a wani salo yana ?age kafa?a.
"Aiko na rantse sai kaji a jikinka yau" Rich ya fa?a yana rarumo kwalbar giyar da Osin bai kai ga bu?ewa ba. Da gudu Yoohan ya tashi yana dariya shima saboda yasan mi Richard ke shirin aikata masa. (a karan farko dana ta?a ganin dariyarsa mai fa?i irin haka). Suma gaba ?aya dariyar sukeyi, dan Rich bin Yoohan ?in yayi shima da gudu. Mota Yoohan ya bu?e ya shige ya saka lock yana yima Rich dake ?o?arin ganin ?ofar ta bu?e da??uwa. Da ?an ?arfi yace, "Stupid boy". "Same to you". Shima Rich ya fa?a yana masa da??uwar.
Gwalo Yoohan ya sake masa yana ?o?arin ?aukar wayarsa dake haske. Da mamaki yake kallon sunan wanda yay kiransa har 3missed call. Bai kula Rich dake masa knocking glass ba ya shiga ?o?arin dailing Number Abban Abdallah.
Bugu biyu kuwa ya ?aga. Kamar yanda yake gaida baba malam da girmamawa haka ya gaida Abbah. Shima Abba sai ya amsa da kulawa, sannan yayma Yoohan ?in bayanin abinda ke faruwa. ?an lumshe idanunsa yayi ya bu?e a hankali tare da kwanciya jikin kujera. "Uncle bara nazo na dubata kawai".
Cikin jin da?i Abba yace, "To shikenan ALLAH ya kawoka lafiya. Ai kana da address ?in gidan ko?".
"Eh Uncle inada".
Daga haka suka yanke wayar. Glass ?in motar ya sauke yana kallon Rich da ke jiransa ya kammala wayar. Da ?ar damuwa yace, "Sorry Rich ina zuwa, bazan jimaba insha ALLAH ku cigaba kawai".
Richard yace, "Lafiya dai ko?".
"No, babu damuwa dear, wani ?an uzirine idan na dawo zan maka bayani".
"Ban yardaba gaskiya muje tare kawai". Richard ya fa?a yana bu?e motar ya shigo shima.
Yoohan ?in baice da shi komaiba, sai waya daya ?auka yay kiran Godwin, yana ?agawa yace, "G-boy muna zuwa Please, just 30minutes". "Okay no prob.." ya amsa masa da salon iya shege na gayu.
Motar ya tada suka fice daga hotel ?in. Yanda yake driving ?in a hankaline ya sa Rich fa?in, "X-man are you ok?". ?an murmushi Yoohan yayi kawai bai ce komaiba.
Tafiyar mintuna ?alilance ta kawosu gidan. Sun iske Omar tsaye a bakin gate da alama zuwan nasu yake jira. har ciki Yoohan ya shiga da motar. Da ga shi har Rich bin gidan suke da kallo dan kuwa ya ha?u. A ransa kuwa ayyanawa yake lallai su baba malam sunada ?u?i. Sai dai sun iya takunsu dan basu da fariyya akan ni'imar da ALLAH ya basu.
?ofar da zata sadasu da cikin gidan suka nufa. Omar na gaba suna biye da shi, shi dai Rich ransa fal mamaki dan baisan ina suka zo ba. Su Aunty Hibbah na baje a falo zasuci abincin da Omar ?in ya fita yayo musu takeaway suka shiga da sallama. Cikin girmamawa Yoohan da yay musu kallo ?aya yay ?asa da kansa ya shiga gaishesu. Hakan yasa shima Richard da ke binsu da kallon tsaf ya gaida su. Daga haka suka wuce falon Abba dake zaman jiransu.
Aunty Aysha ce tai ?ar dariya bayan shigewar su Yoohan. Duk kallonta sukai na alamar tambaya. Tace, "Wannan angon namu dai akwai kunya, abokinsa yay mana ?uri da idanu, amma shi ya kasa kallon ko sashen da muke". Aunty hibbah ta kar?e da cewa. "Sai kace jinin hausawa, inma ba fa?a maka akaiba bazaka ta?a cewa ba bahaushe bane wlhy. Musamman wanda yasan yanda ?abilun nan suke da shegen tsaurin ido".
Haka suka cigaba da hirarsu ?asa-?asa akan Yoohan. Har Umm tazo ta wuce ta fito da Aymah zuwa falon Abbah basu lura ba. Adawiya ce kawai da Amal babu a falon. Adawiya dai ?in fitowa tai, tunda suka iso gidan ta shige ?akin Amal bata sake le?o waje ba. Amal kuwa kanta ke ciwo shiyyasa tasha magani ta kwanta tana idar da sallar isha'i.
Tunda Momy dake ri?e da Aymah data langa?e mata a jiki tai sallama duk suka ?ago kansu. A hankali Richard ya furta 'Woow kaga wata ?ya?y?yawar halitta'. Akan la??ansa ba tare da kowa ya jisa ba. Dan Yoohan ma dake kusa da shi zaune hankalinsa gaba ?aya akan Aymah data takure cikin kujerar da Momy ta ajiyeta ya ke. Cikin rawar sanyi tace, "Momy Please ki bani bargo sanyi".
Kafin Momy tai magana Abba dake kallonta da tausayawa ya duba Omar da shima duk yay wani iri da tausayin ?anwar tasa. "Omar kaga rage gudun ac nan". Da sauri yace, "To Abba" yana ?aukar remote ?in.
Murya ?asa-?asa Rich ya cema Yoohan, "X-man who is she?".
Fuska Yoohan ya ?an tsuke tare da ?auke kansa batare da ya bama Rich amsa ba, saima maida hankalinsa yayi ga Abba da ke fa?in ga Nu'aymah ?in nan. Yana gama fa?a ya bar falon Momy biye da shi. Har Omar ya juya zai fita shima Yoohan yace, "Excuse me Fharook". Dawowa Omar yayi fuska ?auke da murmushi yace, "Yayah kana bu?atar wani abu ne?".
?an murmushin ka?an shima Yoohan yayi, yace, "Ka?an samo mata tea tasha first".
Kai Omar ya gya?a ya fita.
Yana fita Rich ya bugi kafa?ar Yoohan da yare yace. "Kaifa banza ne! Ina tambayarka kana basar dani. Ina ka kawomu nan, gidan ?yawawan mutane wai?!".
Dariya yaba Yoohan, amma sai ya gimtse bai yiba. Da gatse yace, "Gidan kidnappers ne" tare da zuba masa harara. Hakan yayi dai-dai da dawowar Omar falon ?auke da ?aramin tire an ?oro mug dake ta turiri.............?
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????
Mamu gee??
MIN ?ALB!!????
Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????
Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????
Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????
?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p.
*_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.
No. 45
............Hararsa shima Richard ?in yayi, amma sai Yoohan ya watsar da shi ya mi?e yana nufar kujerar da Aymah ke kwance a kai. Omar dake murmushi ya ?arasa inda suke ya ajiye tiren a copy table ?in dake gefen kujerar. Hakanne ya saka Yoohan dake tsaye yana kallon yanda take rawar sanyi zama kan hannun kujerar ka?an shi kuma.
"Thanks you" ya fa?a a hankali yana kallon Omar. Murmushi kawai Omar yayi shi dai.
Da hannu Rich ya yafito Omar, hakanne ya sakashi nufarsa. Tambayarsa yay wacece Aymah? Dan shi harga ALLAH ya gama rikicewa. Cikin ?ar dariya Omar ya fa?a masa amaryarsu ce mana.
Sosai kuwa Rich ya waro idanu waje yana fa?in, "Are you serious?". kai Omar ya gya?a masa alamar sake tabbatarwa.
Shi dai Yoohan na jinsu, amma sai bai ko waiwaye ya dubesu ba, sai ma hannu da ya kai a hankali ya janye bargon Abba da Momy ta ?akko ta lullu?awa Aymah. Zabura tai da sauri ta cafke hannunsa tana ?wa?e fuska zatai kuka. Dan a tunaninta Momy ce ma ita. Tace, "Momy Please karki cire sanyi nakeji".
Hannunsa yay ?o?arin janyewa daga cikin nata amma ta ri?e gam, hakanne ya sakashi barin hannun kujerar ya dawo ta gabanta ya tsugunna. Sosai ?amshin turarensa ya daki hancinta yanzu. Tai azamar bu?e idanunta da sukai mata nauyi, sai ko a cikin nashi.
Zabura tai da sauri tana saki masa hannu tare da wancakalar da bargon har yana rufe masa fuska. Hannunsa yasa ya janye bargon a hankali tare da saurin ri?ota dan tana ?o?arin barin kujerar ne. Hannun taja zata fisge. Fuska a murtuke yace "ALLAH idan baki nutsu ba allura zan miki".
Ai babu shiri tai saurin komawa ta zauna hawaye na zubo mata saman fuska da uban gudu. Ta bashi dariya amma sai baiyiba ya gimtse abarsa. Sai dai hakan bai hana lips ?insa motsawa ba ka?an.
Duk da halin da take a ciki sai da ta zuba masa harara ga hawaye na zirara kuma. Dariya Richard dake kallonsu tamkar ya samu television yayi. Juyawa Yoohan yayi yay masa da??uwa yana danne tasa dariyar. Sai kuma ya mike daga tsugunnon da yay a gabanta ya koma kujerar da take zaunen daf da ita, dan tazarar dake tsakaninsu ka?ance. Harara Aymah ta kuma zuba masa tana ma?urewa gefe. Shi