Showing 66001 words to 69000 words out of 325075 words

Chapter 23 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29130

ya biye mata harda binta kitchen sukai aikinma tare.
Bayan sun gama kuma ya jata ?akinsa sukai wanka tare, dukda babu abinda yay mata irin na nuna soyayya ga ma'aurata ?innan hakan baisa ta damuba. acewarta ai yanzun aka fara wasan. Dan haka ta ?ara ?aimi wajen saka masa sunan Nu'aymah akan duk abinda zasuyi.

Zuwa dare bayan tayi barci a ?akinta shima yana nasa sai ya shiga dogon nazari akan shawarar Adawiyan. A yanda ya ?iyasta zaiyi amfani da yarinyar wajen dawo da martabarsa ga Nu'aymah kamar yanda ta fa?a masa. Duk da yayi saurin ?ago dabararta nayin hakan game da sakko Nu'aymah a lamarinsu, sai yaga ai shima wata damace a hannunsa da zai dama ya yadda ?wallon mangwaro kuma ya huta da ?uda.
Dan haka ya kammala shirinsa tsaf game da yanda zai bida Adawiya akan Nu'aymah har ha?arsa ta cimma ruwa ya mallaki abar sonsa su gina rayuwar da yagama tsara musu tun asalin fara mallakar hankalinsa.
Da wannan ?warin gwiwar yay barci ranar. Washe gari kuwa tunkan ya tashi Adawiya harta shirya masa breakfast wai acewarta irin abincin da Nu'aymah tafi ?auna kenan. Yakoyi farin ciki, a ?asan ransa kuma yana mai mata kallon ?uruciya da wauta. Zama yay yaci sosai ya ?oshi, ya kuma taimaka mata suka gyara gidan sannan suka fita tare ya kaita makaranta kafin shima ya wuce tasa.

Ba ?aramin farin ciki Maman Aaida tayi da labarin da Adawiya ta bataba. da kuma abinda ta gani da idonta na kawo Adawiya da Abdallah yayi school, rabonda hakan ta faru tun randa ta fara zuwa da kwanaki ukun da suka biyo baya. Daga haka yace ta cigaba da zuwa ai zata gane hanya. Sai gashi yau ya kawota da kansa cike da farin cikinsa.
Haka taita walwala a majaranta har lokacin tashi yayi. Abin mamaki kuma sai gashi ya sake dawowa ya ?auketa. Suna isa gida kuma ya mi?a mata kwalin waya sabuwa fil harda sim card a ciki. Wani uban tsalle ta buga ta ?aresa tana masa tagwayen kiss a wuyansa da fuska. Daga haka ya biye mata ya kwashi gara sanan ya sake wanka ya fice gidan ya barta da murnar waya.

Wani irin ji Adawiya tayi kanta na yawo a sama. Ta tsaya gaban mirror tana kallon kanta cike da nisha?i da yabama tunaninta da shirinta. 'Yo ashe nice na zauna shashanci akanka Yah Ab, ashe kawai wata ?ar gajeriyar hanyar da zan bi da kai na samu nasarori a kanka bama nasara gudaba, amma na zauna ?ata hawayena da lokacina wajen tunani da ba?in rai. To yanzu kam saika shirya, dan Adawiya tayi al?awari da alwashin sai kayi nadamar cin kashin dakai mata akan wata shasha Nu'aymah. Kaida Nu'aymah kuwa sai dai gani a hoto, dan lokaci zaizo da ko gaisuwar waya sai kun tsani kanku wajen dinga yinta balle ta zahiri. Ni Adawiya Mustapha Hashim Jibiya, ni ka?aice matar da zata mallakeka a duniya da komai naka. Kuma Nu'aymah bazata ta?a samun wanda ko ya kama ?afar matsayin Slippers ?in wankan kaba Yah Ab. Dan saina sakata kuka da ba?in ciki kwatankwacin wanda ta sakani a baya saboda zazzafar ?aunarka da begenka inhar ni?in jinin Fauza ce (Addah).

Tofa Adawiya anya baki ?ebo da zafiba kuwa???????.

___________________________________

Nu'aymah da batasanma Adawiya nayiba tana can dur?ushe gaban Umm da Baba malam tana mai basu ha?uri akan ?acin ran data assasa musu a safiyar jiya game da abinda ya faru. Dan jiya gaba ?aya ?in kulata Umm tayi. Baba malam kuma basu shigo gidaba sai gab da magriba. Yana zuwa yay alwala ya wuce massalaci ko Hajjo bai le?aba. Bai kuma shigo gidanba sai goma saura kamar yanda ya saba. Zuwa lokacin kuma Nu'aymahr ta gama jigata da aman da taita kwarawa na ?a'idar zuwan jininta hartasha magani tai barci.

?inyin magana Baba malam yayi har sai da Umn ta gama yima Nu'aymah fa?a sosai akan shegen tsiwarta kamar zata daketa kafin ta koma nasiha kuma.
Bata bartaba har sai da taga tana sharar ?walla, dan Nu'aymah fa batason fa?a a rayuwarta, sai dai kuma babu yanda ta iya dan iyaye nagari suke saurin tsawatawa yaransu idan sun gansu akan dokin kuskure. Bayan Umm ta gama nata shima bana malam ya murje nasa idanun yay mata tas fiye da wanda Umm ?in tai matama. Kafin shima daga baya ya koma nasihar da nuna mata illar rashin kunya ga ?iya mace.
Tasha kuka da neman gafararsu sosai, dan har saida Muhammad ya sulale sashin hajjo ya sanar mata tazo ta ?waci Nu'aymah a hannunsu sannan suka barta. Duk da dai itama Hajjo ba ?yaleta taiba sai da ta mata nasihar itama.

Haka Nu'aymah ta wuni ranar cikin halin ciwo da takaicin Yoohan da Guards ?insa da duk ta tattara laifin a kansu saboda fa?an da akai mata. Bata da riko sam idan akai mata abu. amma sai gashi yau Yoohan ?in da tarkacensa sun kasa barin ranta harma washe gari da shima dai haka ta yini babu walwala saboda jinin nata.

Da haka kwanaki suka cigaba da ?ara shurawa, baba malam yana cigaba da ?o?ari neman hanyar ha?uwar Doctor da Nu'aymah batare da kowa ya saniba. Sai dai kuma har yanzu dai ba'a dace ba kam. Har gasu Yusrah sunyi nisa a zana jarabawarsu, wadda a dalilinta baba malm ya dakata da nemawa Nu'aymah makaranta. A cewarsu idan sun kammala sai a nema mata ita da Amal, tunda ita Yusrah zatabi Abdallah ne taje itama tayi nata karatun kamar adawiya.
Cikin wannan tsukun takardun da bawan ALLAH nan da har yanzu basusan ko wanene ba suka gama kammala. Daga na neman aiki harna karatun yaran daya bu?ata. Haka suka tattarasu aka aika masa ta hanyar daya fa?a.
Kamar wasa kuwa sai ga sa?on ?aukar aikin nata zuwa ?aya bayan ?aya. Hakama na masu shiga makaranta ba'a ?ulla sati uku ba ya turo da kammaluwar komai da makarantun da duk zasuje ?in.
Wannan al'amari yayi masifar yima baba malam da duk ahalinsa da?i. har takai ya shirya family meeting na musamman ya ro?a duk yaran da iyayensu akan su ware dare guda wajen mikama UBANGIJI addu'aoinsu na alkairi akan wannan bawan ALLAH da basusan wanene ba ?an kuma wane yankine. Kowa ya aminta da wannan tukuyci, sunkuma ?auki alwashi da ?amnarar gudanarwa insha ALLAH.
Yanda Nu'aymah taga mahaifinta yana farin ciki da al'amarin ita bayanma ?iyamullaili da tayi harda azumi ta tashi washe gari, dan a duniya babu abinda ke sakata nutsuwa da ma?aukakin farin ciki irin ganin iyayenta a farin ciki.

Kamar yanda Baba malam ya ro?ama wannan bawan ALLAH addu'a ga iyalansa haka ya ro?ama masa a massallaci, ya kuma ro?a masa a gidan marayun da alkairin yazam duk a kansune. Dan bayan wancan aiken duk ?arshen wata sai an kawo mota guda ta kayan abinci gidan daga wannan mutumi da basusan ko waneneba. Wani abin mamakima harda yankakkun kaji lafiyayyu ake hado musu yanzun ko ?anyen kifi ko jan nama.

______________
*_SAUDIA_*

Tunda Adawiya ta samu waya shikenanfa harka ta bu?e mata. Kullum cikin kiran ?an uwanta takeyi suna shargallensu. duk da Nu'aymah bata da waya a hannu yanzu haka Adawiya ke addabama Umm kira akan ta bata. Kokuma wayar Amal ko Yusrah, kai harta hajjo kira take a ha?asu.
Duk hakan tanayinsane danta birge Yah Abdallah ya yarda da gaske tanason cika masa al?awarinsa na maido Nu'aymah rayuwarsa. Shi kuma duk da yasan dalilin yin hakan bai ta?a nuna mata ya fahimta ?inba. Haka ya cigaba da biye mata akan ?uruciyarta da wauta. Sai dai yanajin farin cikin yanda yakejin muryar sahibarsa kullum sama da sau biyar a rana. Duk da har yanzu bai ta?a amsar wayar sunyi maganaba koda kuwa a gabansa ne Adawiya zatai fira da Nu'aymah.

A gefe kuma abinda Abdallah bai ta?a fahimtaba shine Adawiya ta daina shan maganin da yake bata. Duk sanda zai batan bata musawa wajen amsa, sai dai fa cikin dabara da wayon da ALLAH yay mata zata zirar dashi cikin riga tayi kamar tasha. Sai ta faki idanunsa ta watsa cikin wani abun da tasan idonsa bazai kaiba. A haka suka cigaba da shurawa ?ar sha?uwar dake tsakaninsu kafin aure tana dawowa a dalilin saka Nu'aymah da sukayi a tsakkiyar lamarinsu.

¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï

A ranar da Adawiya ta fara kiransu a waya suka gaisa Nu'aymah tasha kuka a ?oye, dan har Umm sai da ta gane tayi kuka. Dan haka ta jata a jikinta sosai cikin hikima taita lallashinta harta ware. Daga nan kullum Adawiya ta kirata bayan sun gama hirar da ?yar take iya danne zuciyarta. Dan tunkan ai nisa ta fara fahimtar kamar da biyu Adawiya ke kiranta tana gasa mata magana a fakaice kan Abdallah.
Duk da ?uruciya da yarinta dake tattare da ita hakan bai hanata zama ta harha?a wasu abubuwan cikin rantaba gameda abinda ya shu?e na rayuwarta da Abdallah harma lalacewar aurensu da har yanzu an gaza gano musabbabin sa a gidan. Kuma har yanzu wasu basubar kallonta da tabon guduwaba a ranar auren nata. Yayinda sukeji a ransu rashin dawowar Ameer gareta butulcine da alhakin Abdallah.

A wayar da Adawiya takeyi da ita kowa yana kallonta a matsayin shakuwar da sukayice da ?unbin soyayyar dake a tsakaninsu. Amma kuma a ba?ini Nu'aymah ita ka?ai tasan mike faruwa tsakaninta da Adawiyar. Ta kuma shanye a ranta duk da yana damunta bata ta?a nunama kowa a fuskaba koda kuwa su Yusrah ne balle Umm.

¡ï¡ï¡ï¡ï

Rayuwa ta cigaba da shurawa, inda alkairin wannan bawan ALLAH keta sake fa?a?a ga gidan marayunnan. Ga azumi nata gabatowa gamai yawancin kwana kuma. Kowa nata shirye-shirye da abinda ALLAH ya hore masa dan farantama iyalansa da bayin ALLAHn da basu da shi.
A gefe kuma babban gida irin na malamai su baba malam sunata shirye-shiryen tafsir da hidimar da suka shiryama marasa ?arfi wanda suke jiran sakamakonsu a gurin UBANGIJI al'arshi.
Duk shekara su duka hu?un suna gudanar da wa'azi a mabanbanta garuruwan da suke rayuwa. Abba Mustapha dake tare da baba malam anan kano shine keyi anan masallacin ?ofar gidansu. Yayinda shi kuma baba malam keyi a massallacin gidan sarki duk shekarar duniya.
To a wannan shekararma sun kammala shirinsu tsaf daga gidajensu har gidan marayunsu. Ta wani ?angaren kuma taimakone keta ?ullowa ta hanyoyi daban-daban zuwa gidan marayunsu. Amma duk da haka baba malam bai gazaba wajen tsayuwar daka akan tantance daga ina komai ya fito da ingancinsa ga lafiyar yaran da mutuncinsu.

Alhmdllh an shiga watan azumin ramadan cikin rahamar UBANGIJI da yardarsa. Kowanne musulmi na ?warai yana cike da murnar shigar wannan wata mai tarin falala dake zuwa mana a cikin watanni goma sha biyu na shekara sau ?aya kacal ya wuce.
Randa aka kai azumi na goma Baba malam ya gama shirya maganar Umrah da Hajjo kanje a duk shekarar duniya idan wata ya raba. A ?a'ida kuma takanje da yara biyune cikin ?a?an gidan. Namiji babba sai mace budurwa guda ?aya. Sau ?aya a wata shekara dasu Nu'aymah suka tada billi ita da Adawiya aka tafi dasu su biyu. Aiko Hajjo ta shawo wahala da su, tun daga lokacin ta rantse bazasu sake bintaba sai sunyi hankali. Sai dai idan wani zaije cikin iyayensu mata su bishi.
To a wannan karon koda Baba malam yay mata magana a mamakin kowa sai tace da Nu'aymah zataje. Babu wanda hakan bai bashi mamaki ba. Amma sai babu wanda yace wani abu tunda dama itake za?ar abokin tafiyartata.
Amsar passport ?insu baba malam yay ya bama Ahmad yay musu komai su biyun, sai shi Ahmad ?in da zaije a wannan karon tare da hajjon.
Haka kawai sai Nu'aymah ta tsinta kanta da rashin jin ?okin zuwan, duk da kuwa tana matu?ar son rayuwa a ?asar saudia saboda dalilan data ginu dasu a cikin rai game da ?asar.
Ta samu hajjo a ?oye ta ro?eta akan ta canja ta da ko Amal ko Yusrah, ita batason zuwa batajin da?in jikinta. Harara Hajjo ta watsa mata tana ta?e baki. Batare da tace mata cikankiba a zancen ta ?auke kanta ta maida ga lissafin atamfofin salla da ?a?anta kan siya mata danta rabama ?an uwa da abokan arziki. To da yake bata dawowa sai a daren salla sai yazam take rabasu kafin ta wuce.
"Hajjo dan ALLAH mana". Nu'aymah ta fa?a cike da shagwa?ar data saba yima hajjon tana kwanciya mata a gefen kafa?a.
Ture mata kai hajjo tayi tana fa?in, "K da ALLAH jacan shashasha, yo ko shi uban naki wama yake da suna (ba fa?afa zatai ba burgace sabida ?an farine??) bai isa sakani ko hanani abinda nai niyyaba bareke haihuwar jiya jiya Zainabu. Dukfa take-takenku ina sane dasu. Yanzu bautar UBANGIJI ce ma ba?yason zuwa saboda Abdullahi nacan ko yaya? Ke koma ?okin ganin ?ar uwarki da duk ta addabi kanta da ?ulafucinki a watannin nan ba?yayi? Ni na tausaya mukune dan kuga juna ke da ita shiyyasama na za?i tafiya dake. duk da nasan wahalarku da rashin arzi?i zaku jazamin acan kamar yanda kuka saba".
Baki Nu'aymah ta sake kumburawa tana fa?in, "Ada kenan, sai akace miki kullum zama zamuyitayi jiya iyau Hajjo, yanzu fa munsan kanmu".
Baki Hajjon ta ri?e tana ?ya?ewa, "Oho to lallai sannu uwata ?aharatu, keni dalla tashimin a falo koma kizo na aikeki gidan marigayi malam Aminu kikai wa?annan zannuwan na marayun ?a?ansu".
"Ni wlhy hajjo bani da lafiya, ki aiki Amal kosu Muhammad ai basa azumi".
"To wlhy ko zakiyi mushe a gidannan kece zaki aikarnan, kuma Umrah babu fashi sai kinjeta. Dan ALLAH idan kunga juna ke da Abdullahin ku babbaka juna saboda takaicin kanku da kukeji. Tunda shima ya zama babban hotiho ya ?auki fushi da mutane shi mai zuciya. Toni namaga kuturu ?arewa zuciyar banzarku da kuka gada wajen malam".
Nu'aymah bata sake tankawaba, dan ita ?aya tasan damuwar da take ciki da matsin da take fuskanta daga Adawiya akan Yah Abdallah ta waya. A ganinta suna a nesa da juna kenan inaga sun ha?u, tunda ta tabbata babu fashi a gidan zasu sauka. Tayi imani da ALLAH harta mutu son Yah Abdallah bazai bartaba, ?ilama shine zai zama ajalinta. Kafin ta san matsayin Yusrah da Adawiya a garesa tana fatan ko bayan shekara nawane idan ya gama fushin ya dawo gareta. Amma kuma zuwa yanzun ta ha?ura koda sonsa zai halakata. Badan bazata iya zama dasu bane, sai dai kawai tanason tayi sadaukarwa a garesu dukda tasan ta fisu bu?atarsa.
Tanaji a jikinta inhar ta matsama kanta saita mallaki Yah Ab kamar yanda ta rayu da wannan burin a ranta to lallai zumincin gidansu da aka gina tunkan samuwarsu yana gab da tsinkewa ya tarwatse ta dalilinsu. Dan kuwa Adawiya da gaske take nuna mata zata iya ya?i da kowa akan Yah Abdallah a yanzun har ita kanta Nu'aymah. Tana ?aunar Adawiya har yanzu a ranta, duk da SARAN ?OYEN da take mata batare da kowa ya saniba daga ita sai ALLAH. Wannan dalilan guda biyu kawai zaisa ta sakama ranta salama da ha?uri. Sai dai kuma ha?ura da Abdallah yana nufin harta koma ga ALLAH bazatayi aureba. Shiyyasa ta du?ufa addu'ar ALLAH ma yasa kar a samu likitan da ake fatan ta silarsa ciwonta zai barta. Dan a yanzu bata bu?atar kowacce irin lafiya kuma, tafi bu?atar ta rayu a haka harmai kasancewa ta kasance a gareta. Idan da rabo zasu hadu da yah Ab ?inta a gida mafi tsada shine Aljannah.
Da wannna tunani ta ?auki aikan Hajjo ta fice bayan ta shiga bedroom ?inta ta ?akko hijjab dan akwai kayanta anan sashen hajjon.

*_ABUJA_*

"Wai nikam Khadijah mike damunkine haka kwanakin nan? Ina lura dake kullum walwalarki da farincikinki ?ara nisantar rayuwarki da mu'amularki sukeyi. Ko baki da lafiya ne?".
Idanun Momyn Ab cike da ?walla take kallon mijin nata. Ta matso hawayen nata suka gangaro saman kumatunta tana girgiza masa kai.
Tausayintane ya sake kamashi, dan tsaf ya fahimci damuwar tata akan Abdallah ne da a yanzu ko kiranta a waya baya sonyi sai idan shine ya kirashi ya balbalesa da fa?a. "Khadijah!" ya sake kiran sunanta cike da taushin murya.
Kanta ta sake ?agawa ta dubesa. Sai kuma ta du?ar tana fadin, "Na'am".
"Mike damunki? Ki fa?amin dan ALLAH?". Jin ya ambaci ALLAH ya sakata sake fashewa da kuka, cikin rawar harshe irin na mai kuka tace, "Abdallah ne, gaba ?aya Abdallah ya?i sauka daga fushin rashin Nu'aymah. Kuma nama lura yanzu fushin nasa duk a kaina ya tattarashi bansan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login