Showing 129001 words to 132000 words out of 325075 words

Chapter 44 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29153

amma sun?i fassaruwa. Dubanta ta kai ga Umm dake lalla?a Adawiya taje sashensu amma ta?i, hakan ya sake tabbatar mata da lallai ba lafiya ba kuwa. Baba malam daya shigo gidan yanzunne ya dakama Adawiya tsawa. Jiki na rawa ta mi?e tsaye.
"Wane irin rashin hankaline wannan tun daga wajen gate anajin muryarki, tona mana asiri zakiyi da shirme ko mi?. To wlhy bara kuji bama ita ba duk wanda na sakejin bakinsa a wannan maganar saina ?ata masa rai, naga dai Abdallahn a ?ar?ashin ikonmu yake shima, dolene kuma yabi abinda mukeso inhar yana bu?atar gamawa da rayuwarsa lafiya. Kowa ya shige ciki".
Jan ?afa kowa ya shigayi zuwa sashensa. Kubrah ta kama hannun Adawiya suka shige tare. Inda suka bar Addah da bata fitaba nan suka isketa zaune. Babu wanda taima magana a cikinsu har suka zazzauna kowa na ?annun magana. Batace musu komaiba dai har lokacin, saima jingina da tai da kujera ta lumshe idanu.

Nu'aymah suna shiga sashensu ta shiga tambayar Umm abinda ke faruwa. Dan ita harga ALLAH bata fahimci komaiba dai har yanzun. A ta?aice Umm ta fa?a mata, sai ko ta zabura a matu?ar razane. "Ya salam. Umm Yah Ab kuwa yana da hankali?! Wannan ai gogama mutane sharri ne da zai ce saboda ni ya aikata saki ga matansa".
"Wannan sakaki a cikin da yayi shine ya sake tada mana hankali muma Nu'aymah. Dan zai iya zama wata fitina daban wadda ba'asan iyakar inda zata tsaya ba a gidan nan. Yanzu dai Abbanku ya gano inda yake, ya kuma bashi daga nan zuwa kwana uku idan bai dawo gida ba zai ha?u da ?acin rai mai tsanani daga garesu".
"Ai gara yazo ya kwance wannan ?ullin da yay min nikam, a dalilin mi zai sakani tsakkiya, a barni da abinda ya damenima nikam ya isheni Umm". Tai maganar tana fashewa da kuka.
Tausayinta ne ya kama Umm sosai, ta ru?o hannunta ta sakata jikinta tana lallashi............?


?? Yah Ab ya zaka mana haka ne??????¡â??????¡â?
_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________


Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????

Mamu gee??
MIN ?ALB!!????

Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????

Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????

Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????

?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu??????..*_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.


Ina fatan ansha weekend lafiya? ????????


No. 35

.............Kamar da wasa sai ga Abdallah ya shanye kwanaki ukun da baba malam ya bashi babu shi babu mai kama da shi. Ran baba malam da sauran ?an uwansa ya sake ?aci matu?a, amma duk sunta ?o?arin dannewa. Dan hatta Hajjo ranta a ?ololuwar ?ace yake.
Hankalin Nu'aymah ne ya sake ta shi. Dan koba komai har yanzu tana son Yah Ab, bazata so bari ya cigaba da munana a idon iyayensu ba akan shima son da yake mata. Tunda duk abinda yake aikatawa na laifi a garesu a kanta ne.
Kuka sosai Nu'aymah tasha akan wannan al'amari. Musamman ma da itama tai kiransa da wayar Umm amma ya?i ya ?aga tun a ranar.
Yau ma wayar ta sake ?akkowa ta Umm ta kirasa, sai dai bai ?aga ?in ba. Ha?ura tayi da kiran, sai dai kuma bayan kamar awa guda kamar an tsikareta ta sake zuwa ta aro wayar again. Test massege ta tura masa, bakinta cike da addu'ar ALLAH yasa ya duba.
Bayan kamar mintuna biyar kuwa sai ga reply ?insa. Jikinta har rawa yake wajen ?auka ta duba.

*_"Zan iya amsar gayyatarki akan dalili guda ?aya, idan kin amince da shi ko yanzu zan iya dawowa gida na fuskanci iyayenmu"._*
_Dalilin kawai ki amince a ?aura mana aure ranar bikin su Kubrah._

Wani irin mugun bugawa ?irjin Nu'aymah yayi, tai mugun waro manyan idanunta waje hawaye masu zafi na rige-rigen fitowa. A fili cike da karyewar zuciya ta furta, 'Anya kuwa Yah Ab bai fara shaye-shaye ba jama'a? Na shiga uku ni Zainab, wane irin tsaka mai wuya bawon ALLAHn nan yake ?o?arin jefani a gidan nan?'.
Kuka sosai ta kuma sha fiyema dana ?azun, dan sai da taji kanta ya fara sara mata sannan ta ha?ura. Har bayan anyi sallar isha'i bata fitaba ta cigaba da zama a ?aki. Wayar Umm ma da Muhammad ya shigo aran littafinta na *Ahdhari* ta bashi ya kai mata. Yunwa ce ta fara takura mata, dole ta mi?e ta shiga bayi, wanka tayo ta fito, tai shirin cikin wando da riga na barci masu taushi. Tanajin yunwa amma bata jin cin abincin kuma, sha'awar shan lipton ne yazo mata a rai. Dan haka ta mi?e ta ?auka hula ta saka a kanta sannan ta fito.
A falo sukaci karo da Rabi ?auke da ?aramin jug da alama ma ?akinta zata. Baki Rabin ta washe ta na fa?in, "A'a uwar ?akina kin tashi ashe? Kamar kinsan kuwa zo?on nan zan kai miki dama ko zaki ?ansha dan na sanki da son zo?o".
?an lumshe idanu Nu'aymah tayi ta bu?e akan rabin tana ?ata fuska ka?an. "No bar zo?on nan ma dai baba Rabi. Idan ban takura miki ba dan ALLAH ha?amin lipton kaina ciwo yake min".
Da sauri Rabi tace, "Ah wlhy babu wani takura uwar masu gida. Kinga zauna bani mintuna biyar kacal, barama nai miki amfani da ganyen shayin baba malam, ina dai kina so ko?".
Kai kawai Nu'aymah ta gya?a mata dan surutunta ya isheta. A ?asan ranta kuma tana mamakin yanda Rabin ta amsa dafa mata shayin ?in babu ko musu balle sukai ga fa?an da suka sabayi kullum.

?akin Umm Nu'aymah ta nufa kafin Rabi ta kammala, sai dai ta iske tana wanka dan haka ta fito akan idan ta gama zata koma. Fitowarta dai-dai da fitowar Rabi da ga kitchen ?auke da kofin shayi dake ta turiri. Sai da tai mata godiya sannan take tambayarta ko baba malam ya shigo?.
"A'a bai shigoba, dan naji Muhammad na fa?in kamar yayi ba?i ne ma".
"Okay".
Kawai Nu'aymah ta fa?a tare da ?aukar kofin ruwan zafin ta kai bakinta tana ?o?arin kunna television da hannunta na haggu.
Sosai shayi yayma Nu'aymah da?i, harta shanye wanda Rabi ta zuba mata itama ta sake zuba sauran wanda ya rage a butar shayin. Tana cikin shan wanda ta zuba ?inne Umm ta fito...
"Oh dama kin tashi?".
"Eh, nama shiga ?akin na tarar kina wanka. Umm kaina ke min ciwo ALLAH".
Cike da kulawa Umm dake dubanta tace, "Ba dole kanki yay ciwoba Nu'aymah, kukan da kikayine ai. Halan ma da kika tafi ?akin ba barcin kikayi ba?".
"Umm barcin nefa bai zoba. Amma yanzu na?an fara ji, sai dai zan jira Abba ya shigo sannan naje na kwanta".
"Wayasan sanda zai shigo, ki tashi kije ki kwanta banason sakarci. Miyasa ke wai sam ba?ya tattalin lafiyarkine? Kin fison kullum ki ganmu hankali a tashe".
"Kiyi ha?uri Umm ba haka baneba wlhy, dama dan yau duk bamu ha?u da Abba bane shiyyasa. Amma bara nasan insha ALLAHU da safe zamu ha?u. Sai da safe".
"Ki tabbatar kinyi addu'a kafin ki kwanta".
"To Umm".
Nu'aymah ta fa?a tana nufar ?akinta badan taso hakanba. Kamar jira tana kwanciya sai barci mai nauyi ya kwasheta batare da ko addu'ar da Umm ta garga?eta yi ba tayi ?in.

¡ï¡ï

Sai wajen sha ?aya baba malam ya shigo gidan. Koda ya tambayi Nu'aymah Umm ta sanar masa ta kwanta sai ya nufi ?akinta. Yayi sallama kusan sau uku babu amsa, dan haka ya juyo falo yana fa?in, "Nayi magana shiru, inaga tayi barci ma".
"Dama tace barci takeji, amma tsabar fitina wai zata zauna jiranka dan yau duk bata gankaba".
Murmushi kawai baba malam yayi, amma baice komaiba.

Kusan ?arfe sha biyu saura Nu'aymah ta farka da wani Masifaffen ciwon ciki. Juye-juye ta shigayi a kan gadon tana kiran sunan Umm. Tun abin na mata sama-sama harya fara fin ?arfin tunaninta. Yun?urawa tai da ?yar ta tashi zaune tana ambaton 'Innalillahi.....' da ?yar ta iya sakkowa da ga saman gadon. Sai dai yanda ?afafunta da mararta suka ri?e sam bazata iya takawa ba.
?asa ta dur?ushe hannunta ?aya ri?e da cikinta, ?ayan kuma ta dafe gado da shi tana matse idanu da cije baki. Cikin azabar data isheta ta fara ?walla kiran sunan Umm da baba malam tana ro?on suzo su taimaketa zata mutu. Yanda zufa ta ji?eta sai ka ?auka ruwa aka watsa mata. Wata gigitacciyar ?ara ta saki lokacin da idanunta ke sauka akan Windown ?akinta. Gilmawar mutum ta gani, wanda alama ta nuna ya jima a wajen tsaye koma waye. Ai sai kawai ta daddage ta fasa ?arar da tafi ta farko badan taji tsoro ba sai dan wani irin kartawa da mararta tayi tamkar numfashinta zai bar ganar jikinta a lokacin.......

A rikice baba malam da Umm da barci ya fara ?auka yanzun suka farka. Har rige-rigen fitowa sukeyi dan ?arar Nu'aymah sun jitane tamkar a tsakkiyar ?walwar kansu.
Kwance suka isketa a ?asa wanwar tana numfashi da ?yar. Baba malam yay saurin kunna fitilar ?akin mai haske, Umm kuma ta nufeta tana kiran sunanta. Sai dai ina Nu'aymahn ta suma. Sake rikicewa Umm tayi, ta fashe da kuka itama tana girgiza Nu'aymahn.
Baba malam daya nufosu shima a rikice yay sauri ja da baya jin ?afarsa cikin wani abu mai ?umi. Kallon inda ya taka ?in yayi. gabansa yay bala'in fa?uwa ganin jini. Cikin rawar jiki ya dur?usa da kai ?an yatsansa ?aya ya?an dangwalo. Tabbas jinine kuwa. Dan haka yace, "Jini kuma?".
Saurin kallonsa Umm tayi itama. Tace, "Jini kuma malam? A ina?".
Da hannu ya nuna mata, sosai zuciyarta tai masifar harbawa. Tabi jinin da kallo har jikin Nu'aymah da alamu suka nuna daga nan yake fita. Kafin ta iya cewa wani abu sai ga Hajjo da Addah da Momy sun shigo a rikice. dan duk wanda yake a gidan yaji ihun Nu'aymah saboda dare yayi. Sai kuma ga matan Abba Musbahu su maman Yusrah, suma Samarin gidan duk sun shigo sai dai sun dakata a a falo.
Hankalin kowa ya tashi da ganin wannan jini. Ga dare ya fara.
Hajjo tace, "Mafita ya kamata mu nema ba wai koke-koke ba. Ya kamata a tado su Ahmadu dan a tafi asibiti".
Addah data maida Nu'aymah jikinta ta share hawayen da ke ziraro mata itama da fa?in, "Hajjo inaga a kira Doctor Sale tunda nan kusa yake shi. amma yanzu ko asibiti akaje zaiyi wuya a samu likitan kirki. Gashi yarinyar nan tana ciki wani hali".
Dukansu sunyi na'am da zancenta. hakan ya saka Abban Abdallah fita dan ya kiran Doctor Sale a waya. A falo ya wuce samarin gidan tsaitsaye jigum-jigum. Kusan a tare suka shiga tambayarsa mike faruwa?.
A ta?aice ya basu amsa yana ?o?arin kai waya kunnensa.

Cikin mintunan da basu gaza talatin ba Doctor Sale ya iso. Malam ?arami ne yaje ya shigo da shi, yay masa iso har ?akin Nu'aymah. Zuwa lokacin su Momy nata ?o?arin saka abu ana kwashe jinin da har yanzu bai dai na zuba da ga jikin Nu'aymah ba. Su baba malam kuma sun koma da ga ?ofar ?aki.
Ko gaisuwa bai tsaya sunyi ba ya shiga. Su Umm duk suka fito aka barsa da Addah da Umman su Yusrah a ciki. ?o?arin tsaida jinin ya farayi, kafin ya fara bama Nu'aymah taimakon gaggawa.
Kamar wasa sai da ya kwashe awa guda domin ?o?arin ceto ta, Umman Yusrah nata gyara wajen, Addah kuma na ri?e da Nu'aymahn har yanzun. Jinin an samu ya tsaya, harma an saka mata ?arin ruwa bayan an samu ta farfa?o. Fita yay ya basu waje dan su ?arasa gyara mata jikinta.

Yana fitowa duk suka yo kansa suna tambayar yaya jikinta. Doctor Sale ya sauke ajiyar zuciya yana fa?in, "Alhmdllh malam ku kwantar da hankalinku. Komai ya dai-daita, sai dai kuma anyi asarar cikin da ke jikinta. Nayi iya ?o?arina na ganin cikin bai dalwantaba amma hakan ya gagara, sai dai ha?uri".
Ga ba ?ayansu wani irin kallon rashin fahimta suke masa. Cikin ?arfin hali Hajjo tace, "Kai ?an nan bamu fahimci zancenka ba. Miya ha?a Zainabu da ciki kuma? Ko kuwa kana nufin wani ciki dai bana haihuwa ba?".
Shima ?in dai kallon mamakin yake mata, kafin cike da son fahimtar da ita yace, "Mama ina nufin ciki na haihuwa mana, ko bakusan tana da shi ba ne?".
Kallon juna suka shiga yi ?irjin kowa na bugawa da sauri-sauri musamman ma Baba malam da Umm da Hajjo. Da rawar harshe Umm tace, "Ya zakace ciki a jikin Nu'aymah?".
"Ikon ALLAH! Hajiya wlhy ciki ne da ita ?an sati shida ma kuwa".
Umm zata sake magana baba malam da zufa ke karyo masa ta ko ina a sannan jikinsa yay saurin katseta da fa?in, "Doctor yanzu wane hali take ciki ita?".
"Ah Alhmdllh malam, yanzu haka tama farfa?o, na kuma saka mata ruwa da zai sakata barci, zuwa da safe idan ALLAH ya kaimu zan dawo na sake dubata sai na taho da magungunan da ya kamata tai amfani dasu. Zuwa da yamma idan taji ?arfin jikinta za'a kaita asibiti dan na sake dubata da ?yau, a kuma yi mata wankin ciki, dan gaskiya ?arin yazo mata da matsala kamar".
"To shikenan, mungode sosai Doctor, ALLAH ya saka da alkairi".
"Amen" Doctor Sale ya amsa saboda jin da?in addu'a daga babban malami irin baba malam. Daga haka yay musu sallama ya tafi ya barsu da ru?ani.

Tun fitar Doctor Sale kowa ya kasa yin ko motsi. Sai ma Umm da hajijiya ke ?auka ka?an-ka?an ce ta ?an zauna jin zata fa?i. Cikin ?arfin hali Hajjo ta shiga ?akin Nu'aymahr, ta iske su Addah sun kammala kimtsata harma sun lullu?a mata bargo, ga ?arin ruwan da aka saka mata yana tafiya dai-dai.
"Kunga kuje ku kwanta dare na ?ara nisa. Tunda ALLAH yasa ta samu barci. Suma sauran ku sanar musu suje su kwanta".
Babu musu sukai mata sallama suka fita. Su da basusan mike faruwa ba sai suka shiga sake kwantar musu da hankali akan jikin Nu'aymahn da sauki. Hajjo ma tace kowa yaje ya kwanta.
Su Abban Adawiya ne kawai sukace Alhmdllh, amma babu wanda yay yun?urin tafiyar sai da Baba malam yay magana. Har kowa ya gama ficewa da ga sashen baba malam da Umm basu iya motsawa ba. Sai bayan kusan mintuna goma sannan ya kama Umm ta mi?e da ?yar. ?akin Nu'aymah suka shiga. Hajjo dake zaune ta zubama Nu'aymah ido ta ?ago tana kallonsu.
Saurin yin ?asa da kai Umm tayi, dan sai yanzu me wasu zafafan hawaye suka sami damar ziraro mata. Har ga ALLAH zuciyarta ta shiga cikin matsanancin ru?anin bayanin Doctor Sale. Wani sashe yana gaskatawa wani sashe na ?aryatawa. Hakama baba malam a matu?ar ru?anin yake. Amma da yake shi namijin duniya ne sai ya shanyeshi tsaf dan a ganinsa yana bu?atar lokacin yin tunani akan hakan..........
Hajjo ce ta katsesu da fa?in, "Ban yarda da wannan maganar ta likitan nanba, duk da kuwa koni jinin ya matu?ar tsoratani tunkan bayaninsa. Sai dai hakan bashine ke nufin mu amince da cewa ciki a jikin Zainabu ba. To ta yayama hakan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login