Showing 318001 words to 321000 words out of 325075 words

Chapter 107 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29145

uwanta kuwa sai da suka bar ?asar saudia. Tsakanin rasuwar Abban Anum da Ummu kuwa baifi watanni bakwai ba. Kuma hakan nada ala?a itama da kasa goguwar tabon da aka ringa jifan Anum da mijinta da shi na safarar ?wayoyi. Duk da su sunsan ba haka baneba, amma tayaya zasu fahimtarma duniya ba haka ?in bane?. wannan ciwon shine ya tarwatsasu zaman cikin saudiya ya gagaresu duk da kasancewarsu manyan mutane.
A hankali Yoohan ya mi?e yabi bayan Jay kansa na juya masa, da ?yar yake iya ganin wajen taka ?afarsa. Jay na tsaye jikin mota ya kifa kansa kawai yana hawaye yaji an rungumesa ta baya. Kamar dama wannan damar Yoohan ya ke jira sai kawai ya fashe da kuka. Duk mai imani ya gansu a wannan yanayin sai yaji rauni ya ?ara riskarsa. Juyowa Jawaad yayi ya rungume Yoohan ?in, hakanne ya sakashi sake fashewa da sabon kuka dan yama manta shi namijine a yau.
Jay dake murmushi yana bubbuga bayansa yasa hannu ya ?auke nasa sabbin hawayen da suke sake zubowa yana kallon su Aliyu dake fitowa da Goshpower da yaransa daga cikin gidan. Basu Jabeer ba, hatta da papa kansa sai da zuciyarsa tai masa nauyi. Sai da aka gama tasa ?eyarsu cikin motocin sannan Aliyu yazo inda Jay da Yoohan suke. Cikin lallashi yayma abokin nasu kuma ?an uwan nasu magana akan ya kamata su wuce lokaci na tafiya.
Kai kawai Jay ya jinjina masa. Sannan ya ?ago Yoohan daga jikinsa, hannu yasa yana share masa hawayen daketa zuba babu ?a??autawa. Ya ?anyi murmushi da fa?in, "Yarona bazai kasance rago mai kuka a gaban matarsa da jikana ba ai na sani". Murmushi ya su?ucema Yoohan da sabbin hawaye a lokaci ?aya, sai yay saurin sake fa?awa jikin Jay ?in kuma.
Suma su Naser dake sharar hawaye duk ?ar dariya sukayi saboda yanda Yoohan ?in yayi. Jay ya yafito Nu'aymah dake goye da Deen tana ta faman kuka itama. "Zo nan my daughter ki lallashi mijin nan naki naga da gaske ?an shagwa?a ne". ?arasowa Nu'aymah tayi tana murmushi da hawaye. Jay ya sake ?ago Yoohan yana fa?in, "Kai dama ashe likitoci ragwagene ban saniba ni Muhammadu?".
Cikin dariyar ?arfin hali Jabeer yace, "Boss da alama kam, dan gashi Son ya tabbatar mana". Duk sukai ?ar dariyar ?arfin hali data rage musu nauyin zukata. Daga haka suka shiga motoci, dan an bincike gidan babu komai a cikinsa. Sabone ma da alama suma su papan jiya suka shigesa. Su Yoohan mota ?aya suka shiga da Jay. Umar yaja motar, Jay na gefensa, Nu'aymah da Yoohan a baya. Su Abdallah kuma suka koma a motar da sukazo suma. Waya Jay ya ?auka ya turama Baba malam text message dan hankalinsu ya kwanta, kafin ya juyo ya kalli su Yoohan dake taimakama Nu'aymah ta sakko da Deen daya sake farkawa daga barci.
"Abuja zan wuce da ku, zanyi magana da malam insha ALLAH".
Sun amsa masa da girmamawa, dan shi kansa Yoohan baya bu?atar yin nesa da Uncle ?in nasa sam.
Su Abdallah sun wuce gida kamar yanda Jay ya basu umarni, su kuma suka wuce airport domin komawa abuja, fatansu suyi sallar asubahi acan insha ALLAHU.

_____¡ï

Idan nace muku wani babba mai hankali a gidan su Nu'aymah ya rintsa a wannan dare nayi ?arya. Kamar yanda su Ahmad suka kwana zaune tare dasu Papa haka suma su baba malam suka kwana zaune cike da tashin hankali. Duk da ma Abdallah yayi ?o?arin kiran wani a gidan ya sanar masa anga su Yoohan ?in amma network yayta basa wahala. Dole ya ha?ura kawai musamman da labarin da papa ke basu ya ?auke masa hankali da tunani.
Motar su na shiga cikin gidan duk su baba malam suka firfito da yakema asuba tayi. Ganin babu su Aymah tare da su ya saka jikinsu ?arayin sanyi kuma. Sai dai kuma Murmushin kwantar da hankali da Naseer yayi ya saka zuciyarsu samun sassaucin bugawar da takeyi. Su Abdallah suka ?arasa garesu jikkunansu duk a sanyaye, dan gaskiya ba ?aramin tausayin Yoohan zukatansu suke a ciki ba.
Kafinma wani a cikin su baba malam yay magana malam ?arami yace, "Abba ku kwantar da hankulanku duk an gansu, sai dai sun wuce abuja yanzu haka tare da Uncle Jay, harma da masu laifin".
Kusan a tare suka shiga sauke ajiyar zukata, dan baba malam baiga text message ?in Jawaad ?inba dama. Jin haka yasa baba malam cewa, "Alhamdulillahi ala'kullihalin, inaga sai muje kowa yay haramar salla dan lokaci yayi".

Ina idar da salla kuwa kowa dole ya nema gado ramuwar barcin daya gagaresu. Musamman ma Umm da jininta ya hau ita da Hajjo.

¡ï¡ï¡ï

?an Abuja ma dai suna sauka wucewa akai da su Papa station, madam Chioma natama mutane kukan iskanci wai Yoohan ya taimaketa kar sonshi ya kasheta. Wannan kalma ta daki zuciyar papa. Ya bita da kallon tsoro da firgici sai dai babu bakin magana dan shi koma tafiya baya iyayi saboda duka ?afafun sunsha harbi.

Ganin yanda Deen ke numfashi da ?yarne yasa Yoohan bayan sunje gida sun sauke Nu'aymah su kuma suka koma massallaci. Suna idar da salla yace zaije ya samowa Deen magani dan an ?ibar masa sanyi. Jikin yaronma zazza?ine.

Nu'aymah na shiga Miemaa ta fito ta shiga da ita ciki dan Jay ya kirata dama. Ganin yanda Deen keta kuka yasa ta amshesa ranta duk a jagule da ?aukar alhakin yaron da akayi. Bata wani zauna jan zance ba tai ciki da shi, tare da cewa itama Nu'aymah ta biyota tazo tai wanka dan duk a galabaice take. Ruwa mai zafi ta ha?a mata, shima Deen tai masa wankan da ruwa mai ?umi sosai. ta kuma gasa masa jikin da towel dan tasan mugayen can ba ?aukar tausayi zasuma yaron ba. Aiko anayi yana uban kuka. ana kammalawa tunkan ta tsamesa a ruwan har yayi barci. Tausayin yaron ya kuma kamata. Goyashi tayi domin yin salla. bayan an idar ta nufi ?akinta da Nu'aymah ke can. Har tayi wanka tama shirya cikin doguwar rigar data bata. kasancewar ba salla zatai ba tana zaune tana matsa ?afarta da tun ciwon dataita mata da cikin Deen har yanzu data haihu bata gama saki da ?yau ba. "Yauwa ?iyata kin idar?".
Kan Aymah a ?asa tace, "Eh Miemaa ina kwana?".
"Lafiya lau, ya gajiyar gwagwarmaya?".
Murmushi Nu'aymah tayi dan kuwa da gaske jiya sunsha gwagwarmaya mai wahalar mancewa a tarihin rayuwa. Miemaa ta bata Deen daketa ajiyar zuciya yana barci. "Kinga bashi abinci, kema bara na ha?o miki ko tea ne kisha ku kwanta ku huta".
Babu musu Aymah ta amshesa. Miemaa kuma ta fita ha?o mata tea. Yanda Deen ke amsar abincinsa har tausayi ya bata. Dan ita dai acan bawani samun nutsuwar ?warai tayi wajan basa ?inba. Ta shafa kansa tare da kissing goshinsa, daga shi har mahaifin nasa ?unbin tausayinsu da ?aunarsu ya mamaye mata zuciya. Babu jimawa itama Miemaa ta kawo mata tea da bread da soyayyan ?wai. Amsarsa tayi da cewa. "Zauna kema ki karya, bara naje da shi babansa zai dubasa, idan kin kammala ki kwanta kema ki huta".
Godiya Aymah tai mata. Miemaa kuma ta fita.

A falo Yoohan ya amshi Deen ya dubashi da bashi maganin daya siyo sannan Miemaa ta sake amsarsa ta goya. Sashen Awwab da baya ?asar yana Spain aka kaisu. Jay yace suyi wanka su sha tea ga shi nan da Miemaa ta ha?a musu suyi barcin gajiya. Sun masa godiya. Su dukansu barcine a idonsu, hakan yasa basu wani zauna zaman maida yanda akayi ba. Dan Yoohan ma sai da yasha magani saboda ciwon kai. da taimakon maganinne ya samu barci mai nauyi yay gaba da shi.

__________¡ï

Su Aymah sunsha barci sosai. Bayan tashinsu duk suka sakeyin wanka. Zuwa lokacin gida ya cika da su Little bee. Sunsha kuka labarin da Jay ya basu game da ainahin gaskiyar rasuwar Gwaggosu Anum da mijinta. Da kuma tabbatar Yoohan ?an uwansu. Lamarin ya ta?a musu zukata sosai duk da bama sanin Anum ?in sukai ba su. Sanda ta rasu Little ka?ai aka haifa, bakuma wanda ya ta?a fa?a musu gaskiyar magana akan rasuwar tata sai yau. Deen yana hannunsu kowa ji yake da shi, hakama da su Yoohan suka tashi sai murnar kowa ta ?aru. Anuwar ya rungumesa yana kuka. Shima Yoohan ?in sai da ya koka. Ransa kuwa cike yake da ?umbin farin cikin tsintar kansa a cikin dangin mahaifiyarsa. Ya ?auki komai matsayin ?addara kamar yanda Uncle Jay ya fa?a.
Sunci sunsha tare, kafin su zauna kuma aka gabatar da juna. Sannan aka tsaida ranar da zasuje Oman wajen sauran dangin Anum da ke can a yanzu suna rayuwa. Anan kuma Nigeria za'a zagaya dasu cikin danginsu suma insha ALLAH.
Kiran Jay da aketayine ya sakashi fita dole. Dan yau daga shi har Miemaa da little basu fita aiki ba. Duk da kuwa gari ya ?auki ?umi akan kama Papa da yaransa da akayi. Musamman daya kasance an saki video ?in labarin da papa ya bayar akan saka twin Brother ?insa a tarko domin shi ya ku?utar da kansa. Wannan al'amari ya girgiza zukatan jama'a sosai. Masana nata sharhi akan hukunci daya dace ace ya fuskanta. Wasuma gani suke a kashesan kawai shine babbar mafita ga ?asar gaba ?aya. Dan barinsa koda a prison ne wataran wani zai iya fiddosa a ?oye tunda ?asar tamu sai a hankali. Hakama jama'ar gari ba'a barsu a bayaba wajen maida yanda akayi dayin sharhi akan wannan al'amari.
Lokacin da labarin ya isa gidan su Aymah har cikin kunnen Mama debora sai ta yanke jiki da fa?i. Dan su su Abdallah ne sukai zaman fa?a musu yanda komai ya faru ma. Kwasarta akai zuwa asibiti a rikice, su Victoria nata faman kuka dan suna ?aunar kakar tasu. Musamman daya kasance yau sun wayi gari da wannan tashin hankali na halayen iyayensu da ya ?ara fitowa duniya taji. Basu da kamarta a yanzu, dan sun tabbatar ko ?auyensu kam yanzu sai ya gagaresu zuwa, dan maimakon tarba da zasu samu daga jama'ar garin kamar da, yanzu idan sunje duka zasuci.
Ganin ta farfa?o baba malam ya hana a fa?ama Yoohan. Yace a barsa shima ya hutama ransa, idan ta warware zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu sai suma a maidasu Abuja ?in.

Su Nu'aymah basu san hidimar da akeba. suna nan cikin zuri'ar data kasance ta Yoohan hankalinsu kwance, kowa zallar ?auna da kulawa yake ?o?arin nuna musu. Tare da bama Yoohan labarin dangi kala-kala dana mahaifiyarsa, tare da hotunanta. Ranar dai haka suka kasance cikin ?umbin farin ciki, dan ma fitar Uncle Jay ta rage armashin hirar.

A ?angaren Jay kuwa ashe kirane na sirri ya samu daga manyan ?asa. Inda sukai zaman tattaunawa dangane da shari'ar papa. Sun yanke shawarar a mi?asa hannun ?uliya manta sabo da wuri. Wasuko sunce ai masa allurar poison tun kafin shiga kotun, dan suna tsoron abinda zai iya zuwa ya dawo musamman da Goshpower ya kasace yaron manyan shegun duniya ne. Babu hanyar da bazasu iya biba domin ganin sun ku?utar dashi. Barin irin su papa a duniya kam ai tashin hankaline. Dan babu makawa a yini guda suna iya tada jama'ar ?asa da ?asar baki ?ayanta.
Shi dai Jay bai yarda ya tofa wata maganaba, dan suma ?in ai baisan yaya nasu zukatan sukeba, balle ayyukansu na ?ar?ashin ?asa. Sannan baima saniba ko suma ?in wani abu sukesan binnewa ta wannan hanyar tunda kowa yasan yanda papa ke mu'amula da manyan mutanen ?asar ai. Sai da duk suka gama surutansu yace shidai a nashi shawaran kawai su bari a mi?asa kotun, yanke hukunci aikin al?aline ba nashi shi jami'in tsaroba. Idan kaga mai laifi ya rasa ransa a hannun jami'in tsaro sai dai akan kuskure ko kare kansa ga mai laifi idan yanada makami. Amma haka ?akatatan basu da damar yima goshpower allurar poison. Duk da wasu sun nuna jin haushinsa shidai bai damuba. Yay musu sallama ya wuce office. Gudun zuwan abinda zaije ya dawo ya sakashi tattara duk wasu bayanai dake a hannunsa a yammacin ranar ya tura ?ara kotu sannan ya koma gida.
Miemaa ka?ai ya sanarma halin da ake ciki, amma su Yoohan baice musu komaiba, saima sakawa yay aka kawo masa Deen da bai gajiya da barci saboda kasancewarsa jariri har yanzu. Kwata-kwata yau kwanansa tara kenan ma a duniyar. Amma ya fara cin karo da gwagwarmayar cikinta.
Kasancewar Aymah jego take yasa Miemaa tsayuwar daka a kanta ta ?arasa jegon anan, dan summa gama magana dasu baba malam idan su mama debora zasu wuto Abuja gobe idan ALLAH ya kaimu zasu taho mata da kayanta dana Deen kawai. Koba komai hankalin Nu'aymah ya?an nutsu waje ?aya yanzu, hakan yasata ?agara ma a kawo mata kayanta ta koma sauraren lectures kota online ?inne kafin suga abinda ALLAH zaiyi akan maganar komawarsu. Danshi kansa Yoohan harma ya ?auki hutun ?arshen shekara mai nisan zango sosai.
Washe gari su Jay suka tattare al'amarin papa suka mi?a kotu, yayinda dangi keta tururuwar zuwa gidan Jay ganin Yoohan. Dan su Afrah duk sun baza labari ta waya. Khairiyya kanta da ba'a garin take aure ba sai gata a wannan ranar ganin yayansu. Duk da dai bama wani girmanta yayi sosaiba, amma dai little ta girmesa. shiyyasa abu ka?an ke sakasu fara fa?a. Shi son girma ita son girma. Daya motsa tace shi?infa ?anintane. Shi kuma yace ALLAH ya kiyaye ya zama ?aninta. Abun nasu na bama kowa dariya. Musamman ma Nu'aymah.

*_WASHE GARI_*

Washe gari su Mama debora da taji sau?i duk da bata koma garau ba suka iso abuja saboda suna son halartar zaman kotu da za'ayi. Ba kowa ya matsa hakanba kuwa sai mama debora. Dan tasha kuka, acewarta tanason taga idon papa ko zaiji kunyar yaudarar da yay mata na saka ?anta mutumin kirki a tarkon da aka kashesa.
Da yake tafiyar mota sukayo, kuma sun taho da wuri sai gasu kusan sha biyu sun shigo garin Abuja. Yoohan na tsakkiyar dangi da keta cigaba da zuwa kiran Gebrail ya shugo wayarsa. ?agawa yay ya koma gefe. Cikin girmamawa Gebrail ya gaidashi da fa?a masa gasu sun shigo Abuja. Zasu wuce can gidanne kokuwa suzo nan gidan Uncle Jay ?in su samesa?.
Yoohan yay ?an jimmm kafin ya furzar da numfashi, yace, "Okay, inaga ku wuce can, nima gani nan zuwa gidan".
Da girmamawa Gebrail ya amsa masa da to. Yana yanke wayar ya sami Uncle Anuwar da maganar, dan Uncle Jay baya nan ya fita saboda sunata kai kawo akan lamarin papa da yaransa su Solomon.
Uncle Anuwar yace, "Yahya ai daka barsu sun wuto nan?in kawai, dan an riga da an zama ?aya yanzu. A gidan nan kuwa munada isassun masauki insha ALLAH. Sanann kusancin zama da zamu samu dasu yanzu zaisa suma idan sunada rabo sai kaga sun kar?a musulinci".
Cikin ?an sosa wuya da jin da?in wannan fata Yoohan yay murmushi idonsa nakan Nu'aymah da suke hira dasu Afrah acan gefensu. Yasan komi rayuwarsa ta zama a yanzu itace sila, dan ha?uwa da ita shine ya zama hasken da ya haska masa hanyar da yake taka ?afa, iska ya?an furzan da fa?in, "Okay Uncle bara naje zuwa anjima ai sai nazo dasu ?in, kagama sannan Uncle Jay ya dawo".

Kamar yanda Yoohan ya fa?a bayan sallar azhur ya nufi gidansu. Duk an janye ?an sandan da suke zagaye da gidan, ko maigadi yanzuma babu balle wa?annan guards da ke cike da gidansu a da. Rayuwa kenan, ka shuka alkairi sai ka girbe abinka. Horn yayi kusan sau uku sannan Gebrail yazo da ?an gudunsa ya bu?e masa gate ?in. Sai da ya gama ?arema harabar gidan kallo da duk motocin dake cikinsa kafin ya furzar da nannauyan numfashi ya fito, dan Gebrail ya bu?e masa tuni.
Cikin gidan suka nufa yanama Gebrail tambayoyi, shi kuma yana amsa masa cike da damuwa, dan har cikin ransa kunya da ?aunar Yoohan ce cike da ruhinsa. Bama shi ka?aiba, duk sauran ?an uwansama hakane. Suna shiga kuwa da gudu su Victoria sukazo suka rungumesa. hakama mama debora rungumesa tai tana kuka da rera addu'ar neman sakayya a garesa da yarensu. Ba itaba ko mai saurarenta yaji yanda take addu'an zaisan akwai tausayi a ciki.
Da ?yar Yoohan ya lallashesu sannan suka zauna suka ?an sake tattaunawa. Mama debora tace tunda har papa ya kashe ?an uwansa da matarsa itama ta yarda a kashesa. Yoohan dai kunyar su Gebrail ya hanashi cewa komai akan iyayen nasu, daga ?arshema yace su shirya zai wuce da su.

Zan iya cemuku a ?ar-?ar su mama debora suke da zuwa gidan Jay, kamar yanda sukaita ?ari-?arin zuwa kano gidansu Nu'aymah. Sai dai abinda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login