Showing 210001 words to 213000 words out of 325075 words

Chapter 71 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29173

Baki Rich ya bu?e zai ?ara yin magana Yoohan yay azamar ?aga masa hannu.
"Please Rich, kana ?aramin headache. Ka bani lokaci zamuyi magana".
Zama kawai Richard yayi batare da ya sake magana ba. Dan yasan Yoohan ?in ya kai ma?ura kenan. Idan ya cigaba da jan maganar komai zai iya faruwa a tsakaninsu. A ganinsa kuma yanzu na lokacin samun matsala bane. Kamata yay ya taimakama Yoohan ?in ya dawo cikin hankalinsa dan ya fahimci an gusar masa da hankaline kawai ta hanyar asiri. Shiru ?akin ya ?auka har zuwa wasu mintuna kusan ashirin. Kafin Yoohan ?in ya fara mi?ewa ya ?auka jacket ya ?ora saman ?ananun kayansa. Batare da yayi magana ba ya nufi ?ofar fita. Shima Richard ?in mi?ewa yay yabi bayansa suka fice daga hotel ?in. a waje suka tari taxi dan komawa asibitin.

__________¡ï¡ï¡ï¡ï___________

*_WASHE GARI_*

A yau data kama ranar da za'aima Nu'aymah aiki su baba malam sukaso tahowa shi da Abban Abdallah. Sai dai a bisa dalilin wani ?an tsaiko hakan ya gagara. Tafiyar tasu ma ta tabbata sai zuwa jibi idan ALLAH ya kaimu.
Hakan baisa sun sare zaman jigum-jigum ba. Sai sukai zaman yin addu'oin samun nasara a aiki dan yanda Yoohan keta maimaita a tayasu da addu'a yana ?ara saka tsoro a zukatansu. Shi kansa sun fahimci a tsoratan yake. Saboda bai ?oye musu ba game da ha?arin da aikin da za'ai mata ke da shi tun farko. Sai dai idan ALLAH ya amince sai ayi kaga kamarma bata ta?a shiga makamancin matsalar ba.
Hajjo har abincin sadaka tasa akayi, aka kuma sayi abubuwan wasan yara da makamantansu aka rabama yaran gidan marayunsu don suyi farin ciki suma. Maybe darajar hakan ALLAH ya saka musu hannu a lamarinsu suma.

*_?ASAR AUSTRIA*

A nan kuwa Yoohan cike yake da fargaba. Sai dai yanata ?o?arin dannewa saboda kwarin gwiwa da Dr Liam Ke basa akan aikin. Dan shi da Rich sai a hankali. Ya ?auki fushi dashi babu gaira babu sabar. Shi kuma sai hakan yay masa zafi ya tattarashi ya watsar. Ko game da harkar asibitin ya daina tuntu?arsa da komai. Idan abu yake bu?ata zaisa Solomon ne kawai yayi masa. Kai a yau ma gaba ?aya baisa Richard ?in cikin idanunsa ba har yanzun da suke shirin shiga da Nu'aymah ?akin da za'ayi aikin.
Baya bu?atar ha?ama kansa damuwa da yawa. Shiyyasa ya ?auki lamarin Rich ya ajiyesa gefe. Dan shi dai abinda ya sani bazai ta?a komawa abinda Richard ?in ke bu?ataba dan ALLAH ya nuna masa ?ya?y?yawar hanya a yanzu mai cike da ?umbin haske. Ai ko papa dake matsayin mahaifinsa bai isa sashi komawa kafiri ba balle Richard duk da kuwa yana sonsa har cikin ranshi.

Sai da ya kammala shiryawa tsaf cikin kayan da zasuyi aikin. Ya gabatar da salla raka'a biyu sannan ya fito ya ?arasa kimtsawa. Kasa shiga yay ?akin da Aymah take domin fiddota zuwa ?akin theatre ?in.
Sai su Dr Sophia suka fiddota yana tsaye a ?ofar ?akin. Cike da rauni ya bita da kallo sam?al akan gadon da aka turota tamkar gawa. Dan sun mata wata allura ne tun awa biyu da suka wuce. Wannan allura kuwa itace wasu da yawa masu irin matsalarta daga an musu ita suka tafi doguwar sumarnan shikenan har abadan. Ko an kammala aikin basa farfa?owa. Wasu kuma koda sun farfa?o sukan kasance komai sun manta na rayuwarsu ta baya. Sai an sake koya musu komai tamkar jinjiraye. Wasu kuma akan dace su tashi cikin rahamar UBANGIJI.
Wannan shine fatan su Yoohan akan Nu'aymah. Har aka shigar da ita hankalinsa yayi nisan kiwo wajen tafiya a dogon tunani. Sai da Dr Liam Yazo ya kama hannunsa ne ya kawo nannauyan numfashi. Lumshe idanunsa yayi ya bu?e a hankali akan ?akin, Dole ne ya dawo da jarumtarsa jikinsa inhar yana son samun nutsuwa akan aikin nan duk da bashi ka?aine zai gudanarba.
Ya cija lip ?insa na ?asa. Cike da ?arfin hali da ?arfafa kai ya nufi ?akin zuciyarsa na wani irin bugu dai-dai da takunsa.
"ALLAH ya bada nasara".
Yaji an fa?a a bayansa. Cak ya tsaya tare da lumahe idanunsa ya bu?esu kafin ya juyo dan yasan Richard ne. Kallonsa yay kusan na sakon biyar cike da rauni. Sai kuma ya tako inda yake ya zo ya rungumesa idanunsa cike da ?walla.
Bayansa Rich ya shafa cike da kulawa. "Zakayi nasara X-man, Please ka yarda da kanka".
?agowa Yoohan yayi suna kallon juna. Rich ya jinjina masa kai yana murmushi. "Ka yarda da ni, inaji a raina matarka zata tashi da yarda ALLAH, kodan taimakon mutane da yawa da kayi a rayuwarka a dalilin wannan aikin. Kaima ALLAH zai baka farin ciki akan matarka yau".
Yoohan yaji da?in maganar Richard, dan haka ya sake rungumesa yana fa?in, "Thanks you Rich, I proud of you".
Sake shafa bayansa Richard yayi shima yana murmushi, dan har cikin ransa yana ?aunar Yoohan, ba kuma zai iya dogon fushi da shiba komi ya zama, kai koda kuwa criminal ne shi zai iya cigaba da sonsa da taimakonsa. Yasan wanene Yoohan tun ?uruciya. Ya tabbatar kuma bazaiyi abu kansa tsaye ba sai da dalili. shiyyasa yaga ya dace ya ajiye fushin da yake yi da shi ya bashi ?warin gwiwa akan abinda ya kawosu har komai ya dai-daita. Ya tabbatar zai masa bayanin dalilinsa na komawa mai salla. Wannan shine dalilin dawowarsa. amma da har masauki ya canja tun a daren jiya. Proud of you too". Ya fa?a shima sunama juna murmushi.

Koda Yoohan yazo shiga ?akinma sai da yayi addu'a sannan ya shiga. Duk Doctors ?in da zasu gudanar da aikin sun hallara, da alama ma shine kawai bai shigoba. Handglove ya cira ya sakama hannunsa. Ya zari Norse mask ma ya saka, duk abinda yakeyi idanunsa na akan ?ya?y?yawar fuskar Aymah ne. Tayi wani irin ?yawu fiye da wanda ya santa dashi. Fuskarta tayi fayau ?an bakin tsiwarnan yana a tsuke. ?o?arin maida ?wallar data cika masa idanu yayi yana Murmushin tuno tsiwa-tsiwar data ringa masa tun daga ha?uwarsu har zuwa rayuwar aurensu ta ?an kwanaki. Bai ta?a jin haushiba dan tana masa tsiwa. Hasalima wani lokacin yana takalarta ne dan kawai tayi masan. Saboda tsiwarta dake burgesa ko son ganinta shiru-shiru bayayi sam. Ya ?arasa gaban gadon ya dur?usa a saitin fuskarta. Hannunta ya kamo cikin nashi ya ri?e, ?ayan kuma ya aza bisa kucinta na dama. Ya kafeta da kallo idanunsa na sake bayyana jan damuwa. Baice komaiba har tsahon mintuna biyu kafin ya mi?e yana ha?iyar zuciya da murmushin da baisan dalilinsaba shima.

Tunda suka fara aikin kuma sai jarumta ta baibaye Yoohan. Duk wani rauninsa da fargaba suka gudu. Ya maida hankali sosai akan abinda sukeyi da ya?ini da fatan samun nasara. Ko sau ?aya baiyi saken addu'a ta ?u?ucema zuciyarsa da harshensaba. Ambaton ALLAH yake tayi gwargwadon abinda ALLAH ya bashi ikon sani.
Sun shafe tsahon awanni a cikin ?akin. Solomon da Richard na zaune a waje idanunsa nakan ?wan lantarkin dake a waje. Fatansu kawai suga ja ya koma green. Sai dai tun suna saran hakan a kusa har suka fara sarewa. Dan ba ?aramin da?ewa su Yoohan sukai ba basu fito ba..

(Ya rabbi ka bamu ikon cinye jarabawa??????).

¡ï¡ï¡ï¡ï

Kamar yanda su Rich ke cike da fargaba acan Austria, anan gida Nigeria mas baba malam cike suke da fargaban. Sai dai sun mi?a lamuransu ga UBANGIJI akan koda rasa Nu'aymah sukayi haka ALLAH ya ?addara. Kuma sun tabbatar hakan shine mafi alkairi a gareta. Sai dai fatan ALLAH ya basu ha?urin hakan.
Idan kuma ALLAH ya ?ara ?addara mata cigaba da wata rayuwar a gaba suna fatan nasara akan wannan aiki. ALLAH kuma ya hana samuwar loosing memory a gareta darajar Al-qur'ani izifi sittin dake haddace a cikin kanta da ?irjinta.

Duk bayan wasu awa guda baba malam kan kira wayar Yoohan yaji ko sun fito. sai dai ba'a ?agawa. Hakan ke sakashi fahimtar basu fito ?inba kenan. Ko yace ya ha?ura bazai sake kira ba har sai Yoohan ya kirashi sai ya kasa ha?urin bayan shu?ewar lokaci sai ya ?auka wayar ya sake kira ?in. Tunfa yana saka ran ganin kiran Yoohan a kusa-kusa har lokaci mai tsayi ya shu?e. Yana son shiga gida amma ya kasa dan bayason zuwa yaga halin da Umm take a ciki itama. Yasan suna tsananin son Nu'aymah, da wannan damarma ma?iyansu keyin amfani wajen azabtar da su, saboda sun gama fahimtar itace tarkonsu. Sai dai hakan bashi ke nufin bazasu iya ha?uri ba idan ALLAH ya amsheta. Dan dama ai shine ya basu batare da yayi shawara da su ba.

****
A tare Richard da Solomon suka mi?e tsaye ganin jar wuta ta mutu blue ta kawo. Suka kafe ?wayeyen uku da ido cike da tashin hankali. Rich likitane, yasan mi blue ?in wuta ke nufi sa?anin green da sukai fatan gani. Shi kansa Solomon kasancewarsa tare da Yoohan a koda yaushe yasan ma'anar hakan. Cike da rauni suka kalli juna sai dai babu wanda ya iya furta komai.
A hankali ?ofar ta zuge, wani irin mummunan fa?uwar gaba ta riski Solomon da Richard a lokaci ?aya saboda ganin an fito da Yoohan a gadon da aka shiga da Aymah alamar dai suma yayi. Da?ar Richard ya koma ya zauna kansa na juya masa. dan fito da Yoohan a wannan halin kawai shine amsar dukan tambayoyinsu akan rasa Nu'aymah...............?

*_Inason naja hankalin masu karatu anan. Wlhy kasancewar Nu'aymah matsayin jarumar littafin SARAN ?OYE bashi ke tabbatar da bazata iya rasa ranta ba. Dan haka kar mu saduda akan wai dole labarin bazai tafi yanda ake bu?ata ba sai tana raye. Wannan gur?ataccen tunani ne. Mutane nawane masu muhimmanci a rayuwarmu suka fita kuma gamu namu LABARAN basu daina tafiya bisa ?addararmu ba??. Rayuwar Nu'aymah ba itace tabbacin fiddo da aynahin sa?on da SARAN ?OYE keson isarwa ba. Dan haka Please karku saka rai, kar kuma ku sare, dan SARAN ?OYE yazo muku ne da sabon salo da gasken gaske, dan haka mu daure wajen amsar salon da yazo mana da shi dan ALLAH?????????????¡â?._*

ALLAH ka gafarta mana??????.


ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????

Mamu gee??
MIN ?ALB!!????

Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????

Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????

Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????

?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.
[6/18, 1:14 PM] +234 901 860 0202: *_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.


No. 56

.............A hankali Yoohan ya ringa bu?e idanunsa da ke ganin wanda ke zaune a gefensa dishi-dishi. Hannunsa ya ?aga da ?yar ya kamo na Richard wasu zafafa hawaye na silalo masa daga cikin idanu. Cikin rawar murya yace, "Da gaske ta na rasata ko Rich?".
?asa Richard yay da kansa shima hawaye na ciko masa idanunsa. Ya zare hannunsa da ga cikin na Yoohan zai mi?e. Saurin ri?osa Yoohan yay yana girgiza masa kai. "Please Richard fa?amin gaskiya".
Kai Rich ya girgiza masa. "Basu ce mana komai ba har yanzun Yoohan. Tun da aka kawoka nan suka sake komawa ?akin har yanzu basu fitoba kuma".
Da sauri Yoohan ya yun?ura zai tashi. Sai dai ya dafe kansa da hannunsa saboda tsananin sara masan da yayi. Saurin ri?osa Rich yayi yana fa?in, "Please cool down.
"Bazan iya ba Richard, Karka damu dani, ina bukatar ganinta".
Duk yanda Rich yaso Yoohan ya ha?ura ya?i sauratensa sam. Dole ya taimaka masa suka fito a ?akin yana dafe da kansa. Sai dai dole a ?ofar ?akin suka tsaya dan dokace bazaiyi knocking ba ba kuma zai shigar musu kai tsaye ba. Yadai danna wani ?an abu dake a jikin Computer ?in dake ma?ale a bangon ?akin. Bayan kamar mintuna biyar ?ofar ta zuge ya shige.
Da ?yar ya iya ringa ?aga ?afarsa ya shiga saboda tsabar fargaba. A tare duk Doctors ?in suka juyo suna kallonsa, fuskokinsu ya dinga bi da kallo ?irjinsa na bugawa da sauri-sauri. Yama gama yarda ya rasata kawai. Dan haka ya juya zai sake fita hawaye na gangaro masa a saman fuska. a hankali Dr Sophia Tace, "Dr Yoohan!". Cak ya tsaya da ga yun?urin fitar tasa. Sai dai ya kasa juyowa. Sai da yaja kusan mintuna biyu sannan ya juyo a hankali yana kallon fuskokinsu da a yanzu suke ?auke da murmushi.
Kafin ya nema ba'asi Dr Liam Yace, "Smiles". Yay maganar da ?ora yatsunsa biyu a gefen bakinsa alamar Yoohan yayi murmushin. Da gaske kuwa sai ga murmushin ya su?uce masa ga hawaye. Ya tako da hanzari inda aka saka Aymah cikin wata na'uwar glass.
Su kansu yanda yayi ?in sai da ya basu tausayi da dariya, ta cikin Computers ?in ya tabbatar da gaske Nu'aymahn sa nada ranta. Sai dai tana a halin suma haryanzu. Zuciyarta dai tana harbawa. ?afafuntane kawai a waje zuwa gwiwa, sauran jikin duk yana a cikin glass ?in. Ya koma wajen ?afafun ya ri?esu duka cikin hannunsa ya sumbaci tafinsu sau kusan uku-uku. Ga hawayen da?i yanzu na sakko masa.
Kamashi Dr Liam yazo yayi ya mi?ar. Ya rungumesa yana masa Congratulations, aiki yayi kyau, sai kuma fatan farfa?owarts da addu'ar kartai loosing memory ?inta. Suma sauran duk sun masa Congratulations shima yayi musu, sannan suka tattaro suka fito dan sai zuwa nanda awanni goma sha biyu za'a fiddota daga ?akin a maidata wani inda nanma zata share wasu awanni goma sha biyu daga nan ake fatan farfa?owarta gaba ?aya kuma.

Su Yoohan na fitowa Rich ya nufosu, rungume juna sukayi yana tambayar tana da rai ne? Saboda ganin farin ciki tattare da Yoohan. Fuskar Yoohan washe da irin dariyar da shi kansa Rich ?in bai ta?a gani ba yake tabbatar masa aiki yayi ?yau. A take farin cikinsu ya ?aru har Solomon. Dan shima Yoohan ?in rungumesa yay.
Baba malam Yoohan ya fara kira ya sanarmawa. sai kuma Papa dake tare da Momy dan ya koma Nigeria yau da safe. A wayar dai kam ya nuna murnarsa. amma yana katsewa yaja wani shegen tsaki mai nuna tsantsar takaici. ba haka ya soba sam. Dan game da aikin nan da za'aima Aymah a mutuwar da sukai fatan zatayi harsun gama tsara komai game da aikinsu akan baba malam.
Ransa a ?ace ya ?auki waya ya kira Dr Mateo. Domin kuwa sunyi da shi lallai Nu'aymah bazata tashi ba. Dan zaiyi duk abinda zaiyi su kasheta tun a wajen aikin. Sai dai har wayar katse Dr Mateo bai ?aga masa kira ba. Maida kiransa yay ga Solomon. Shi kuma a lokacin suna tare da Yoohan da Richard shiyyasa ya kasa ?agawa dan yasan dalilin kiran papan tunda a gabansu Yoohan ya kira ya sanar masa anyi aiki kuma an dace.

Ba ?aramin sake haukacewa Papa yayi ba kuwa. Ya ringa zazzaga bala'i Momy na tayasa itama duk da ba komai ta sani game da shirin papa ?inba. To amma itama wannan ranar itace fatanta tun a daren auren Yoohan da Aymah da papa ya sanar mata matsalar Aymah da aikin da Yoohan zai fita da ita bayan auren. Wanda yana ?aya daga dalilan yin auren da gaggawa. Shine dalilin sakankancewarta tabar Aymah mi?e ?afa a gidanta tana zuba iskancin data gadama. To yanzu kuwa inhar Aymah bata mutu a wajen aiki ba lallai game ?in zai canja salo kenan. Dan babu wata mace a duniya data isa ra?ar Yoohan inhar tana a raye tana numfashi. Shiyyasa ma ta ?auki mataki a kansa tun shekaru da dama ta kashe masa mazantakar tasa. Wannan yana ?aya daga abinda ya sake assasa rashin damuwa da mata ga Yoohan, dan akan Nu'aymah ya farajin feeling makamancin hakan bayan shekarun farkon balaga da suka shu?e masa lokacin yana farkon shiga University. Dan yanayinsa ya fara masa yanada ?arfin sha'awa, amma ko a wancan lokacin yayi ?o?arin ri?e kansa dan shekararsa sha tara kacal, sai dai abin mamaki kafin suje level 2 sai yaji sam matanma basa burgesa. Kizo ki gama ta?ararki a gabansa da nuna masa jiki ko a kwalar rigarsa bayajin komai ko a ?anyatsan ?afa kuwa. Rashin kula ta hanashi fahimtar akwai damuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login