Showing 225001 words to 228000 words out of 325075 words
ALLAH tana bu?atar aron kayan kuma da gaske. Dan bazata iya kwana da rigar wanka ba. Juyowa tayi a hankali idanunta a ?asa ta kasa kallonsa. Yanda ta koma kamar wata munafuka ne ya bashi dariya. amma sai ya gimtse kayarsa baiyiba. Takowa yay gabanta ya tsaya gab. Yasa hannu a kar?i kayansu dake a hannunta tare da ?ora na damar a ha?arta ya ?ago fuskarta. Tsaf ta runtse idanunta kuwa. Baiyi magana ba, sai kallonta kawai da ya keyi musamman bakinta da arayuwa yake bala'i-bala'in ?aukar masa hankali. Kodan shine yafi masa tsiwa oho. "Je gasu can a Wadrobe ki ?auka badan halinkiba dai".
Batare data bu?e idanunba ta motsa la??anta ka?an tace, "Thanks you".
Sakar mata fuska yayi ya matsa. Da sauri tabar wajen dan gaba ?aya idan ya tsaya kusa da ita koya zauna jinta take a matu?ar takure, duk sai yay mata kwarjini. Tana bu?e akwatinsa dake a Wadrobe ?in yana isowa wajen. A bayanta ya tsaya gab tare da zura hannunsa duk biyu ya ?ora akan nata dake ?aga murfin trolly ?in data bu?e. Jitai numfashinta na fita da ?yar lokacin da ?irjinsa ya mannu da bayanta duk da akwai kaya a jikin nasu. Ta?an rintse ido zuciyarta na harbawa. Kansa ya ?ora gefen kafa?arta ya ajiye kayansu daya amsa a wajenta yana magana a hankali. "Ashe kin iya wanki?". Kasa bashi amsa tayi, dan harga ALLAH ta matu?ar takuruwa. Shima fahimtar hakan da yayine sanadin numfashinta da yaji yana seizing ya sakashi sakar mata kiss a wuya yaja baya. Ka?an ya hana fitsari zuboma Aymah. Ta sauke ajiyar zuciya da ?yar sannan ta bu?e idanunta dake tara ?walla. ?aga kayan ta farayi ko zataga wanda zai ?an mata, sai taga kayanta har kala hu?u ashema a ciki. juyowa tai ta?an kallesa da masa ?aramar harara. Baisan tanayi ba, dan ya juya mata baya ne zai zauna a inda ya taso a bakin gado. ?un?uni taitayi tana ciro kayan. Gaba ?ayansu ma kala hu?u ne. Na barci biyu, dogayen riguna biyu, sauran duk nasane suma dai basufi guda biyar ba, Sai kayan ciki datai fatan ALLAH dai yasa bashine da kansa ya ?akko mata su ba. Dan wlhy daya gama da rayuwarta kam. ?aukar wa?anda zata saka tayi ta maida sauran. Ta ha?o harda wayarta data gani a ciki da Charger. Ta gabansa tazo ta wuce bayi, acan ta canjo kayan ta yafo mayafin jallabiyar data wanke dan dashi ta koma. Kayan bama wani kamata sukayiba, kuma basu fidda mata jikiba. Sai dai wandon iyakarsa gwiwar ta. Sannan hannun rigarma bawani babba bane can sosai. Amma bai mata yanda zataji kunya ba. A kwance ta samesa yanzun, idanunsa a lumshe suke amma batasan duk yana kallonta ba. Wajen Wadrobe ?in ta koma, ta ?auki turarensa data gani har biyu saman akwatin ta hau fesawa. Daga haka ta dawo wajen gadon tana kallonsa fuska a tsuke.
"Wai bazaka tafi ?akinka ba ne?". Tai maganar a hankali kamar maijin tsoro. Sarai ya jita, amma sai yay shiru abunsa kamar yayi barci. Idanuntane suka cika da ?walla. Dan gaskiya ita dai bazata iya kwana da shi a ?aki ?aya ba. Ta ?an ?aga murya fiye da ?azun tace, "Kaji! Dan ALLAH kaje ?akinka. Kokuma ni naje can sai na kwana".
Idanunsa ya bu?e a kanta. Yace, "Ohooo! Silly girl. Nan gidanki ne ma ashe ko? Dahar sai kin za?i ?akin barci?".
"To amma ai kasan mu biyu ne sai ka kama ?aki biyu". Tai maganar da iya gaskiyarta. Fahimtar da yay yarintar tatace ta motsa ya sakashi gyara kwanciyarsa yana fa?in, "Wasa nake miki ga key ?in ?akinki anan zoki ?auka". Ya nuna mata bedside ?in. Da iya yarda ta nufo wajen kuwa ita zata ?auki key. Tana ?ora hannunta saman handle ?in drawer ?in kuwa ya ri?esa caraf.
Bata ankaraba sai jinta tai a jikinsa ya fisgota ta fa?o. Duk da yaji zafi bai damuba, sai ma juyi da yay da ita suka koma tsakkiyar gadon sosai. Mutsu-mutsu take nason ?wacewa ya matseta da ?yau. Ga bakin ya kasa magana. Bargo ya jawo da hannu ?aya ya lullu?esu, kafin ya kai hannu ga makunnar fitulin ?akin duk ya kashe na barci suka kawo da kansu.
Cikin kunneta yace, "Silly girl, ai kecema kike kama da ?an damben. Garama ki nutsu muyi barci dan zaki gajiyar da kankine. A wancan karonma dana ?yaleki akwai dalili. Yanzu kam ki fiddama ranki zamu cigaba da raba wajen kwanciya yarinya".
"Ni dai gaskiya bazan iya kwanciya da Namiji a ?aki ?aya ba". Tai maganar tana kuka.
Cikin kwaikwayon maganarta yace, "Nima gaskiya bazan iya kwanciya da mace ?aki ?aya ba".
?agowa Aymah tayi tana kallonsa fuska sha?e-sha?e da hawaye. Ya ?aga mata gira da kansa yana fa?in, "Kin zata kece ka?ai kika iya drama ?in? Nima actor ne a film ?in ai Trouble maker".
"Kaima Trouble maker ?inne ai, Kuma sai na fa?aka da Abbana".
"Nima sai in fa?aki da Papa na. Kinga saisu ha?u su mana fa?a muyi-muyi mu kawo musu jikokinsu, dan ni nama ?agara na ganki da ciki".
Da sauri Aymah ta maida kanta a ?irjinsa saboda kunya. Ta dun?ule hannunta dake a bayansa tai masa ?aramin dundu.
Dariyar da bata ta?a ganin yayiba taji ya sanya mata yana ri?o hannun nata. Da ?ayan ta ?ara dukansa a ?irji itama tana dariyar ka?an-ka?an. Matseta yayi gaba ?ayanta a cikin jikinsa yana ?ora ha?arsa bisa gashin kanta da hular ta zame duk ya mimmi?e. Sumbatar kan yayi yana lumshe idanu har sannan da murmushi a fuskar tasa.
"Yanzu fa idan nace zan rama sai ki kamamin raki ko? Kuma naji zafin dukanmin baya da kikayi".
Da sauri tai ?o?arin ja da baya yay azamar ri?ota cikin jikinsa yana mata magana a hankali. "Matsoraciya kawai, wasa nakeyi. Tashi kisha maganinki sai ki kwanta".
Itama luf tayi tana sha?ar ?amshinsa, kusan mintuna biyu suna a haka kafin ya saketa dan yanayinsa neman fara sauyawa yakeyi. Jin ya saketa ta tashi zaune. Shima kunna fitilar ?akin ya sakeyi ya tashi da kansa ya ?akko mata maganin da ruwa ya kawo mata. Amsa tai tasha tana ?an matse ido. Ta mi?a masa sauran ruwan batare data bari sun ha?a ido ba. Shima baice mata komaiba ya amsa ya juya. Da wannan damar ta tattaro filos ?in gadon ta hau jerawa a tsakkiyarsu tana fa?in, "Kowa ya kwanta sashensa to gaskiya".
"Ai garama haka, ni karkimata ball da ni da wa?anan ?afafun naki da basa zama waje ?aya". Yanda yay maganar yana kwanciya da juya mata baya kamar bashine yayiba ya sakata gallama bayan nasa harara. Itama bata tankaba ta kwanta ta juya masa bayan. Murmushi yayi dan yasan abin cewarne ya ?are mata shiyyasa tayi shiru. Ba'afi mintuna biyar ba sai jin saukar numfashinta ya farayi a hankali alamar maganar ya fara aikinta har tayi barci. Juyowa yay a hankali yana kallon bayanta, musamman sumar kanta dake kwance luf a ?eyarta har zuwa dokin wuya da ?ananu sukaima wajen ado mai ?ayatarwa bisa farar fatarta mai she?i da bawai ?al-?al takeba irin ta turawa. Dan shi kansa ma ya ?an ?arata haske duk da farin fatar tasu ba iri ?aya baneba sam.
Hannu ya kai a hankali yana ciccire filos ?in data jera musu a tsakkiya, sai da ya ciresu duka sannan ya matsa sosai jikinta ya sakata a nasa jikin yaja musu bargo. Ajiyar zuciya ya shiga saukewa a hankali, a ransa yana raya 'Sarkin rikici' tare da tura hannunsa cikin rigarta ya shafa cikinta dake lafe a jikinta kamar babu hanji a ciki. Lumshe nasa idanun yayi shima yana karanto musu addu'ar barci da ayanzu Alhmdllh ya haddace duka..
_________¡ï¡ï
Alarm ?in daya saka musu ne ya tadasu sallar asuba. Shine ya fara farkawa, sai da yayo alwala sannan yazo ya tada Nu'aymah da ?yar. Ganin yanda take ha?a hanya alamar barcin bai saketa ba ya sakashi taimaka mata har ?ofar toilet ?in. Bayan ta shiga ya canja kayan barcinsa zuwa jallabiya yasa abin salla ya kabbara raka'a-tainul fajir kafin ta fito.
Itama koda ta fito doguwar riga ta cira a kayanta ta saka. sannan ta hau sallayan daya saka mata a bayansa tai tata nafilan raka'a biyu. suna zaune kowa na lazimi har lokacin sallan ya ?arasa. itace ta bashi shawaran yay musu jam'i. Da farko ya nuna mata shi ina iliminsa ya kai da har zai musu jan salla. Ta masa ta?aitaccen bayanin da zai iya fahimtarta kafin ya jasu sallar asubahi.
A mamakin Nu'aymah sai gani tai ya ?akko Al-qur'ani ya dawo gabanta ya zauna. Kallonsa take kamar yanda shima nasa idanun ke a kanta.
"Daga yanzu matata ce zata zama malamata kamar yanda Uncle ya bani shawara (baba malam)". Sosai Aymah ta waro idanu waje, da fa?in, "Ni kuma Yaya Yoohan?".
"Insha ALLAH kuwa. Dan duk abinda zanje nema a wajen wani malami na tabbata kinada kaso hamsin a cikinsa insha ALLAH. Karkiyi min wasa da damata Please Zeeynab, dan na yarda tun a farko UBANGIJI ya sakoki rayuwatane dan ki zamarmin fitila mai haska min hanya. So ni koda shekarunki basu kai hakaba zan zauna a gabanki na koyi abinda ban saniba. Cire duk wani kokwanto da shiriritanki nan wannan ba ga?ar wasa bane. Akwai manyan ?alubale a gabana da dole sai da wannan ilimin zan tunkaresu".
Kan Aymah a ?asa tana wasa da yatsun hannunta ta jinjina masa kan. Cikin nutsatstsiyar murya tace, "Insha ALLAH zaka sameni yanda kake bu?ata. Sai dai ka sani har yanzu ni ?alibar ilimice, nima banje ko inaba a neman ilimin. Ko a gidanmu ?aramin ajin yara nake koyarwa bawai manya ba".
"Bani da banbanci da wa?annan yaran nima ai Nu'aymah, domin abinda kike koya musu nima shi nake bu?ata a yanzu ki koyar dani. Dukkan littatafan da zamu iya bu?ata gasu Uncle yazo mani dasu. dan dama muna karatu da shi ta video call a kullum bayan sallar la'ar a duk inda nake. Da wannan ne na ?an samu abin salla da addu'oin da kikeji a bakina".
Sosai tausayinsa ya kama Aymah har idanunta suka cika da ?walla. Ya kuma birgeta matu?a, dan ?aukakarsa da girmarta da yayi, da matsayinsa na miji a gareta bata sakashi girman kai ba........
"Please ki ceto rayuwata Zeeynab ". Furicinsa ya katse mata tunani. Saurin ?ora hannunta tayi akan bakinsa saboda jin yanda yay maganar da rauni. Ta shiga girgiza masa kanta ?walla na sake taruwa mata a ido. "Ka daina ro?ona, umarni kawai zaka bani a matsayinka na babba gareni kuma mij......"
Sai kuma tai shiru ta kasa karasawa. Murmushi yayi da ?aga mata gira. janye hannunta tai daga kan bakinsa ta hararesa. Yay karamar dariya da fa?in, "Hy karasa mana. Wai dama kinada kunya ashe?".
Harara ta kuma zuba masa tana kumbura baki, tace, "Silly boy".
A tare suka fashe da dariya babu zato, dan ita kanta kalmar Silly boy ?in datai saurin kiransa da shi kafin shi ya kirata ta bata dariya.. Sai da sukayi mai isarsu sannan suka nutsu. Ya gyara zamansa yana fa?in, "Silly girl kin rainani wlhy". Batace komaiba sai murmushi.
Shima dai murmushi ne ?auke a fuskarsa. Ya kara gyara zamansa. "Gashi Al-qur'anin ?aya ne yaya zamuyi kenan?".
Murmushi ta kumayi mai kayatarwa tana lumshe idanu. Batare data kallesa ba tace, "Karka damu, ko babu Al-Qur'ani a hannuna zan iya ai".
"Woow masha ALLAH" ya fa?a yanajin wata ?aunarta da girmanta a cikin zuciyarsa da bargo. Daga haka suka nutsu ya fara karanto mata iya inda ya tsaya da harshensa da baya fita sosai. Hakan yasa karatun nasa yay mata da?i. Sai da ya tsaya ta dubesa da kulawa. "Zamu cigaba da yin Al-qur'ani. Amma ina ganin ya kamata ka fara koyan larabci hakan na taimakama mai karatun Al-qur'ani sosai wajen furta abinda ake bu?ata".
Idanu ya lumshe a hankali ya bu?e a kanta. cikin muryarnan tasa mai amo yace, "Okay maa. Duk yanda kikace haka za'ayi". Duk da ya bata dariya batayi ba, sai dai ta murmusa kawai. Cikin baiwar da ALLAH ya azurtata da ita na wadatuwa da ilimin addini ta fara ?orama Yoohan karatun. Ba ?aramin nutsuwa da shagala yayi a kallonta ba. Dan yaune karan farko da yaji yanda take raira karatun Al-qur'ani mai girma a fili. Wata irin nutsuwace ta ringa saukar masa. har ?ananun ?walla suka taru masa a cikin ido bai saniba. Sai da suka sakko a fatar idonsa ka?an idanunsa sukai masa gizo sannan ya lura. ?an yatsa yasa ya ?aukesu yana cigaba da saurarenta.
Tabbas Yoohan ya saka a ransa zai nema ilimin addini babu wasa a ciki. Hakanne yasa UBANGIJI riko da hannunsa. Gashi kuma ya bashi Aymah a kusa da shi da har cikin ransa ya yarda itace zata zame masa malama kuma sirrin rayuwarsa. Dan haka basu tashiba a wajen sai da ta tabbatat ya fahimci abinda ta koyar da shi.
Bayan sun kammala abinci mara nauyi yaymata, order dan taci tasha magani kar lokaci ya wuce. Tunda shan maganin nata akwai ?a'ida. Hatta da barcinta yanzu yanada lokacin yi da tashi har sai komai ya ?arasa dai-daita yanda ya kamata. Tea kawai ta iya sha da cake ka?an, dan ita dai wannan abinci na Austrian baya mata da?i. Wanima ?yan?yami yake bata. Musamman da harshenta har yanzu ba komai yake masa ?an?ano ba. A hakama cake ?in sai da Yoohan ya tayata ci sannan. Tana kammalawa ya bata magani tasha ta shiga wanka. Shi kuma fita yay dan motsa jiki a gym ?in hotel ?in. Da kuma son ?arasa magana da Rich.
Aymah na fitowa kaya kawai ta canja sai kwanciya. Ko mintuna biyar bata rufaba kuwa barci yay gaba da ita.............?
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????
Mamu gee??
MIN ?ALB!!????
Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????
Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????
Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????
?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.
[6/23, 1:15 PM] +234 901 860 0202: *_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.
*_FEJI SATTIN??_*
______________
*Sunana Nafisa k Abdullahi am a singer, actress.. wakokina are based on siyasa da kuma na sarakuna *
https://youtu.be/1VyZ6f1GTWg
*(YouTube link)????*
*This is my YouTube channel IN SHAA ALLH! I will be bringing to you my latest films, And musical videos*
*NafisaKabdullahi* *Sabuwar ficacciyar jaruma ce data shahara wajen fina finai da kuma wakoki na siyasa, Masarautu da sauran su*
*Ina masoya makaranta littafan zafafa? Ku fito ga dama ta samu, Munason a nuna mana k'auna ta hanyar subscribing a sabuwar channel dinnan ta Nafisa mai suna a sama. ????A kalla a kuma danna kararrawa domin sauraron shirye shiryen ta a duk sanda ta dora..*
*Danna kararrawa domin kasancewa da ita da zarar ta dora sabbin shirye shrye.*
*DAN ALLAH! Ayi subscribing, Akuma dinga viewing, Inda hali ma ayi comment da sharing zuwa ga wanda basu sani ba...*
*Akwai Facebook page dinta mai suna: https://www.facebook.com/preetyfeenat.abdullahi*
*Domin karin bayani sai a tuntub'i Nafisa kai tsaye ta number ta: *
*08071172003*
*kada ku mance ko minene daya danganci wakokin al'adun hausa, Da ire-iren fina-finan mu na hausa, Nafisa zata dinga kawo muku shi a wannan sabuwar channel din nata, Saboda haka MASOYA a temaka aje ayi mata subscribing a kuma dinga kallan abubuwan data dora.*.
____________
No. 60
..........Koda Yoohan ya dawo ?akin bayan awanni kusan biyu da fitarsa bai tada Aymah dake kudundune cikin bargo tana barci ba. Wanka yayi, yay shirinsa tsaf na fita asibiti. Turaren hannunsa ya ajiye dai da ring ?in wayarsa. guntun tsaki yayi tare da ?aukar brush ya nufo inda take yana kwantar da sajensa. Sai dai kuma ganin wanda yay kiranne ya sakashi ?an waro idanu waje ya dafe goshinsa. Zama yay a bakin gadon dai-dai da katsewar kiran. Shine ya kirashi zuciyarsa fal takaicin tsakin da yayi. Koda baba malam yaga shigowar kiran da ga can murmushi yayi kawai ya ?aga suna kallon juna da Umm dake a kusa da shi. Cike da girmamawa Yoohan ya shiga gaishesa. Shiko yana amsa masa da kulawa. Sun?an ta?a hira da duk Yoohan ke ?arajin ?aunar Baba malam. Dan