Showing 270001 words to 273000 words out of 325075 words
ce shifa tabar masa godiya dan akwaima lefenta a kansa wanda baiyiba. Aymah dake dariya tace, "Ai gashi anan kayi my boo".
Hancinta ya lakace da fa?in, "No. Wancan special ne hausa girl. taso muje kiga sa?on Umm".
Tunda Aymah taga duk abinda tacema Umm an ha?o mata shi saita haukace da murna har Yoohan na mata dariya. Ta tasa fara gaba ta hau ci harta bashi tausayi. Dan yayi-yayi taci abinci ta?i, tace sai dai suje shagon shan coffee. Haka dole bayan ta gama cin farar da shan su alawar madara ya ?auketa sukaje shan coffee ?in. Tako shawosa bana wasaba harda guzirin na anjima. Shi dai gaba ?aya sai take bashi tausayi, dan yasan da bata shan coffee.
Haka su Nu'aymah suka cigaba da kasancewa suna rainon ?an tayin cikinsu ita da mijinta abin sonta. Duk da ya?i fa?a mata gaskiyar zancen cikin, a yanzu bata da abinci sai kayan da Umm ta aiko mata da su. Randa tayi tuwon dawa miyar kuka ta tsare Yoohan wai sai yaci. Dan itama ai taci abincin yarensa lokacin da aka kaita gidansu. Shiru kawai yayi yana kallonta idanu na farfar dan shikam dai harga ALLAH miyar kukar har saka masa tsigar jiki tashi take. Garama tuwon yana masa kallon amalan yoroba. Dan yana ?anci a dalilin joseph data zama abincin yarensane. Ganin yanda yakeyine ya saka Aymah yin fushi. Marairaice mata yayi akan tayi ha?uri shi wlhy bai iya ci ba. Batama nuna taji miya fa?a ba.
Ganin da gaske fa fushin ta ?auka ya tilasta masa daurewa ya rintse ido ya matsa kusa da ita. Muryarsa har sar?ewa take wajen fa?in, "To kawo zanci Sweet girl. Shiru ta kuma masa tana cin abinta cike dajin da?i harda lumshe ido, gashi ya sha yajin daddawa da man shanu kuwa sai ?amshi yake. Sake marairaice mata yayi cike da lallashi.
"Nace zanci ai ko. Tunda Unborn ?ina yanaci nima a bani zanci, yi ha?uri".
"Sai dai na baka da hannuna, dan karma kaita zubashi a riga ban saniba daga baya kaje ka zubar".
Ta bashi dariya, amma sai ya gimtse dan ya kula itafa da iya gaskiyarta take maganarta. Yace, "To na yarda".
Laumar farko dai Yoohan sai da ya ri?e numfashin sa sannan ya korata da ruwa batare da ya tauna ba. Lauma ta biyuma haka. Ana uku ?ar rigimarsa ta tubure bata yarda ba. Yoohan dai kam yaga takansa. dan rigimar Nu'aymah dabance a rayuwa. Dole-dole kuwa sai da ya tauna lauma ta ukun nan. Daga haka yace. Dan ALLAH tayi ha?uri ta barsa haka tunda koya yakeyi. Dariyar mugunta taita masa kuwa.
Tun daga ranar daya fahimci zatayi tuwo sai ya gudu. Idan kuma ya fita asibiti sai ya bigi cikinta yaji mitaci ko zataci. da yaji batun tuwo sai yaki dawowa da wuri. Tun Aymah bata fahimtaba harta ganosa. Aiko saita daina sanar masa idan zatayi. Haka ta dinga ritsashi akan cin tuwon nan dole. Tun yana gudu bayaso har ya fara masa da?i. Sai gashi cikin ?an?anin lokaci ya iya ci kuwa. Shima kuma komawar da yay Nigeria sau kusan uku duk xuwan da zai dawo sai yazo da wani abinda yasan na yaransune. Sai dai cikin ikon ALLAH kuma ita Aymah ciki ya sakata ci take hankali kwance. Dan yanzu kuma komai ci take anbar coffee. kayan wajen Umm ma duk zuwa sai yazo mata dasu.
Watan su Aymah ?aya da sati biyu a U.S Juliet ?in Omar ta haihu mace mai kama da ita. Su Aymah ansha murna. Sai taji itama tanason ta haihu. Tako dage harda addu'a a cikin salla (??bar wahal da kanki baby Aymah).
Shi Yoohan baisan tana addu'ar ba shiyyasa bai sanar mataba. Dan a lokacinma baya ?asar shi. Sai da ya dawone yaga baby. Omar ?inma yana 9ja bayan haihuwar da kwana ?aya yazo. Dan dama yaso Juliet ?in taje Nigeria ta haihu ta?i. Yarinya dai taci suna biyu. Aysha & Lisa, Dan shi dai Omar duk abinda ya dace uba musulmi yayi akan ?a?ansa shi yayi akan baby Aysha. Itako Juliet da yake dama bawani bidi'oin suna sukeba suna kawai ta sakama yarinyarta bayan wanda Omar ?in ya saka mata. Saima yazam itama yanda Nu'aymah ke kiran sunan Aysha ?in yana mata da?i. Sai gashi tafi kiran yarinyar da Ayisha ?in. Saboda da?in da Omar yaji har ?yauta yayma Nu'aymah da godiya. Tare da ro?onta dan ALLAH taita jan Juliet ?in a jiki ko itama za'a dace ta gane gsky. Aymah ta amsa masa. duk da tasan hakan abune mai wahala ga baturen ba'amuruke irin Juliet. To amma komai ai na ALLAH ne.
_________________¡ï
*_KANO NIGERIA_*
Anan kano ta dabo kam Umm najin da?in zama da Afrah data ta fara aiwatar da aikinta cike da ?warewa da nutsuwa. Gaba ?aya ta ?auke musu kewar Aymah. Koda yaushe Muhammad inhar ba makaranta ya wuce ba yana nane da ita. Itama tana matu?ar son yaron, dan yana ?auke mata kewar ?an ?annenta.
Haka ma tana matu?ar jin da?in zama da baba malam da Umm. Dan mutanene masu dattako matu?a. Ita da hajjo kam ai ba'a magana. Daka gansu tamkar jika da kaka. Kai gaba ?ayama al'ummar gidan Afrah nada ?ya?y?yawar ala?a da kowa. Dan malam ?arami harya ?yasa. Ita kuma ta?i sanar masa tanada mijin aurenta a hannu. Dan gab ma ake da saka musu ranar aure tunda iyaye duk sun shaida tuni.
A cikin dabarun da ALLAH yay mata a sashe su Nu'aymah ta manna cctv ?in nan mai kama da stones. Hakama sashen hajjo da duk wasu gurare na cikin gidan batare da kowa ya farga da itaba. Bata da wata ?awa mai shekarunta a gidan, dan haka taita jan yaran gidan jikinta sosai. Dan su Adawiya ma har yanzu suna Abuja. Admission ma za'a nemar musu su fara karatu tunda na Adawiya yasha kashi. Su baba malam sunso ta koma saudia ?in ta cigaba hajjo ta hana hakan. Acewarta su jira dai suga iya gudun ruwan Abdallah ?in.
A cikin kwanaki goma da Afrah tayi a gidan ta kammala aikinta na manna camaras a duk inda ya dace. Sosai Jay yaji da?in ?wazon ?ar tasa. Hakama Bily.
Sai kuma ta koma bama Dawood da little, Yoohan, Omar bayanai akan duk motsin ?an gidan. Da wanna suka fara aywatar da aikinsu batareda jama'ar gidan sunsan sirrin ba. Hatta da Nu'aymah batasan hidimar da akeyiba. Dan koda Yoohan ya koma U.S bai sanar mataba. Takan dai gansa yayi serious a lap-top duk dare. kuma baya zama latse-latsen sai tayi barci. Inko har yazam ta farka to yabar aikin kenan. Dan duk dabarar da zaiyi ya ajiye abinda yake ya sani.
A haka kwanaki suka cigaba da shu?awa har aka shiga watan azumin Ramadan. Wanda ya kasance na farko ga Yoohan da Omar. Sosai Aymah ta yabama ?o?arin Yoohan randa aka kai azumin farko. Dan ko irin nuna yau ya fara ?in nan bai nunaba. Itacema sai da ta karya nata saboda jiri data dinga gani, daga ?arshe kuma taita amai.
Omar U.S ya koma domin yin azumi. Hakan yasa kullum anan wajen Nu'aymah yake zuwa shan ruwa. Wani lokacin ma harda Juliet suke zuwa da Baby Ayisha.
Azumi nada kwanaki goma sha biyu hutun Afrah ya ?are. Ta tattara ta koma Abuja cike da kewar su Umm. Dan ita dai taji masifar da?in zama da wa?anan bayin ALLAH musamman cikin azumin nan. Su kansu duk sai da sukaji babu da?i akan komawar tata. Sai dai babu yanda suka iya tunda zata koma kan aikintane.
An kammala azumin watan Ramadhan lafiya. Ansha kuma bikin salla a ?asashen musulmai. Yayinda su dai su Aymah sai ?an yawo sukai anan U.S, da ?anyin nasu bikin sallar anan cikin gida.
Tsakanin Yoohan dasu papa har yanzu basu ta?a masa magana akan dukan Gebrail da yayiba. Dan komawar da yayi 9ja can gidan ma ya sauka abinsa. Sun kuma tarbesa kamar yanda suka saba. Ya iske su momy Destiny sun koma. Hakama maman Madam Chioma. Mama debora kawai ya iske da sauran ?annensa sai guards ?in gidan su Solomon daya koma gadin nadam Chioma yanzun. Gebrail kam tunda yaji Yoohan ?in yazo gidan ya gudu. Har yabar ?asar kuwa basu ha?uba. Daya sake komawama yay wajen kwana goma shima wasan ?uya suka dingayi da Gebrail ?in.
Wannan shiru da sukai ya bama Yoohan mamaki matu?a. Badan dukan da yayama Gebrail ba. Sai dai maganar Solomon da baiji sun sake tayar masaba. Sai dai kuma shima baiyi magana ba ya bar Solomon ?in cigaba da kasancewa da shi da sauran guards ?insa duk sanda ya shigo Nigeria. Duk inda ya shiga suna tare anan kam.
_____________________
A kwana a tashi babu wahala sai ga cikin Nu'aymah ya shiga watanni shidda. Tun cikin azumi kuwa ta fahimci ciki gareta. Murna taitayi zasu samu baby suma. sa?anin yanda Yoohan yay tunanin zata tayar da hankalinta. Aiki shima yaji da?in yanda ta nuna murnarta akan Unborn ?in nasu. Wata ?aunarta mai girma na sake fa?a?a masa a rai.
Ganin laulayin ya rage mata a lokacin sai kawai ya shiga ?o?arin nema mata admission. Wannan abu ya saka Aymah murna harda kuka. Dan tanason karatu sosai a rayuwarta. Addu'a ta dage ta dingayi babu dare babu rana akkan samun gurbin karatun nan. Su Umm ma sunsha addaba akan su tayata da addu'ar. Har Muhammad tasa ya fa?a a islamiyya wajen ?an ajinta su mata addu'a.
To Addu'a dama takobin muminine ai. Balle gashi result ?in Ayman da Yoohan ya amso a gida wani zuwa da yayi dama yayi ?yau masha ALLAH. Sai gashi kuwa an dace. Ranar kowa yasan Aymah ta samu cikar burinta. Yoohan kam ai yafi kowa shan kallo dacin dariya a wannan rana, sannan kuma yasha tukuyci mai tsoka da ba'a bama yaro mai ?iwa.
Da taimakon Juliet yay mata komai daya dace, dan itama tanayin wani course ma a cikin makarantar yanzu haka. Sai dai a online take ?aukar lecture. Da wannan damar Yoohan ma yay amfani akan Aymah. Zata dinga ?aukar lectures ta online. Idan kuma taso shiga school bai hanata ba bayan ta haihu. Yayi hakane saboda yanayin jikinta.
To da yake itama yanzu lalla?a cikin take sai ta amince (wa yaga ba sabanba su Aymah za'ayi ?a?a??).
Umm, baba malam, hajjo ne ka?ai sukasan da zaman cikin Nu'aymah a kaf jama'ar gidansu. Dan ko Addah Umm bata fa?amawa ba sam. Tabar abinta a zuciya wai randa Nu'aymah tazo kowa ya gani. To kuma anyi sa'a duk wautar Aymah da surutu ita bamai irin sakin zance ?in nan bace ako ina. Dan ko su Umm ?in ai ba fitowa fili tai tace musu tanada ciki ba. Sune suka fahimta ita da hajjo. Baba malam ma a wajensu ya sani.
Cikin ya mata ?yau sosai a jiki, sai dai yasata ta ?ara ?iba, kumatun sun fito masha ALLAH. Idan Yoohan najin neman magana yakan tasata gaba yayta dariya. Ita kuma taita hawaye dan yanzun dai kam bakin tsiwarnan duk ya mutu. ta kanta takeyi duk tazama wata shiru-shiru.
¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï
Akwai aikin da Yoohan zaizo yi ?asar ghana, daga nan kuma zai shigo Nigeria akan case ?in gidan su Aymah. Dan zuwa yanzu sun tattara abubuwa da yawa ta dalilin Afrah. Sai bayanan sirrin da jay ya tattara ta hanyar camaras ?in nan wanda shi da bily kawai suka san dasu. Amma suma ?in basu duba komai ba a yanzu, dan sunbar komai ne ya tattaru, So suna son fara bu?e abubuwa a bayyane insha ALLAH a hankali. Sun san kuwa a wata uku kenan da zaman camaras ?in a gidan sun na?i abubuwa iri-iri, musamman daya kasance ansha shagalin bikin ?aramar salla da babba, duk kuma ahalin gidan sunzo, idan ka cire Abdallah da yay hijira.
Shirinsu na farko dai yanzu shine fara kama Rabi. Daga haka sauran abubuwa zasu cigaba da tafiya a bu?e. Nu'aymah taso biyo Yoohan a wannan karon. Sai dai kuma ya lalla?ata akan ta bari sai hutun ?arshen shekara idan ALLAH ya kaimu. Tunda baifi saura wata ?aya da sati biyu ba. Batai masa musu ba, dan yanzu duk ta ?ara yin laushi, danma wahalar cikin ta mata sau?i sosai zuwa yanzu Alhmdllh. Gashi kuma dama cikin fari. Ga kuma karatunta da ke mata matu?ar da?i. Dan harya kaita da mantawa da wasu su madam Chioma. Lamarin papa ne dai kam sun tattauna da Omar sosai a wani zuwa da yayi U.S ?in. Annan take fa?a masa gaskiyar lamari game da hoton data ?akko a ?akin papa ?in, harma da wa?anda ta gani. Abin shima ya bashi mamaki sosai. Nan shima yake sanar mata abinda ya ta?a faruwa tsakaninsu da Jay kwanaki. Itama sai abin ya tsaya mata a rai. Har taji sha'awar son samun kusanci da zuri'ar Jay ?in. A take Omar ya bata Number Afrah. Dama Afra ?in ita tanada ta Aymah, kirantane dai bata ta?a yi ba. Dan sanda tana a gidansu sai dai su gaisa a wayar Umm ne. Tun daga sannan suke ?an kiran juna a hankali, suna kumayin chart lokaci-lokaci kasancewar duk sunyi busy.
To yanzu dai sun ajiye magana akan duk sanda taje 9ja zata bashi hoton ya gani, daga nan sai su san tudun dafawa akan wannan al'amari. Daga haka suka ajiye batun.
Sai dai kuma abinda su Aymah basu saniba ita da Omar shine tun randa Jay yaga Yoohan bai hutar da kansa ba a bincike dabin diddigin papa. A hankali duk wani motsin papa ya kasance akan idon Jay batare da shi yasan hakan na faruwaba. Dan ya rigada yayi imani da cewar ya toshe duk wata hanya ta le?en asirinsa daga wasu mutane koda jami'an tsarone. Sai gashi shi Jay yama kansa hanyar da yake kallon papan tsirara.
Dirar safe Yoohan yayma 9ja wannan karon. ya kuma sauka a Lagos ne. Sai da ya kwana uku sannan ya ?araso Abuja. Kamar ko yaushe ahalin nasa sunyi murna da zuwan nasa. Musamman ma madam Chioma da duk zuwa saita banka masa kayan tsibbunta a abinci yaci. Sai dai duk da bataga wani canjiba daga garesa tana ?auka aikinta na tafiya dai-dai. Musamman da bata ta?a jin ya zauna yimata zancen Nu'aymah ba.
Tun isowarsa gidan Gebrail ya gudu kamar yanda yakeyi yanzun. Tun dukan da Yoohan yay masa bai sake yarda sun ha?u a inuwa ?aya ba. da zarar yaji labarin zuwansa yake barin gidan, bakuma zai sake shigowaba sai Yoohan ya koma kokuma yaje wani jahan aiki. Duk da Yoohan na lure da Gebrail ?in bai ta?a nuna yasan yanayi ba. Gaba ?aya yi yake tamkar ya manta da wani halitta Gebrail a cikin ?annensa.
Blessing da su Favour yasa suka gyara masa sashen nasa wannan karonma. Bayan ya watsa ruwa ya?an mi?e a gado yanason ya huta. Sai da ya fara kiran Aymah suka ?an ta?a hira sannan ya kwanta. A ?an?anin lokaci kuwa barci yay awan gaba da shi.
Madam Chioma da tun shigowar Yoohan gidan yau ta kasa zaune ta kasa tsaye ta fito wankan maganin da boka Bangaruta ya bata a gurguje. Zama tai gaban mirror ta shiga tsara kwalliya kai kace fita zatayi. Sai da ta tsuke cikin wando da riga da sukai mata matu?ar ?yau sannan ta feshe jikinta da kalolin turarruka masu tsada da ?amshi. Gashin Attachment ?in nan sai uban wal?iya yake da ?aukar ido kasancewar sa mai uban tsada. Cike da takun gayu da ?asaita ta fito daga sashenta dan papa baya nan yayi tafiya yau kwana biyu. Mama debora dasu Victoria kuwa tasa sunbar gidan a cikin shirinta. Ta aika Blessing kuma kasuwa. Amma abinda bata saniba Blessing ?in batakai da fitaba saboda toilet daya kamata. Kanta tsaye sashen Yoohan ta nufa, hakan yayi dai-dai da hawowar Miracle sama hannunta ?auke da five alive da kofi. Waya takeyi da wata ?awarta tana bata labarin zuwan Yoohan. Saurin ?oyewa Mira tayi dan kar madam Chioma ta ganta, tare da jan wani shegen wawan tsaki dayin kamar zatai jifa da kwalin lemon. Sai kuma ta fasa saboda uban ku?in data kashe wajen yima lemon ha?in magunguna saboda Yoohan. Itama kanta cikin gayun take na kece raini. da alama kuma sashen Yoohan ?in ta nufa. Sai dai gashi Maman Yoohan ta ruguza lamarin. Ranta cike da ?una taje ta zauna a kan wasu kujeru biyu dake a upstairs ?in tana huci da bama ?awar tata labarin abinda Momyn Yoohan ?in tai mata. Zugata ?awar tata take famanyi daga can akan ya kamata Miracle tazo suyi duk yanda zasuyi wajan raba Yoohan da uwar tasa.