Showing 183001 words to 186000 words out of 325075 words
daka musu tsawa. Dan ciwon kai suke neman ?ara mata bayan wanda take ciki. Saboda akan idonta Aymah ta sakama Miracle ?afa. Amma tai shiru saboda wani dalilinta. Tsaki Joy taja da yima Gebrail alamar zasu ha?une da yatsunta. Shima sai ya ?age kafa?a da ta?e baki irin na I don't care ?in nan.
Wani irin tafasa zuciyar mira ta ringayi, ga abin fa?a a bakinta amma babu damar cewa. Ita kanta yanzu maganar Joy ta sakata ?ara tariyo a yanda ta fa?in. Tunda tasan lafiyar ALLAH take tafiya babu kuma komai a gabanta. Aiko tabbas saita damalmala kan yarinyar nan bisa tiles ?in gidan nan bara ta warke dai.
Su mama debora nata cancana maganar da Joy ta fa?a akan tunanin Aymah ce ta kada Mira. Yayin da su Maman Favour keta ?o?arin kare Nu'aymah ?in akan Joy ?in ta fa?i dai son zuciyarta ne kawai.
Oho, Nu'aymah batasan sunayi ba, tana can sunata zagaya lungu da sa?o na gidan ita da su Victoria. A ?arshe suka yada zango cikin garden ?in gidan da yay mugun tafiya da tunanin Aymah. Musamman ma swimming pool ?in da ruwan cikinsa sky Blue da keta ?aukar idanun mai kallo. Sun ?ata lokaci sosai a garden ?in, dan har sai da duhun magriba ya fara rufa sannan suka fito.
Yanzun kam babu kowa a falon kowa ya shige, sai masu aiki biyu maza dake gyarawa. Sashenta tai wucewarta suma su Favour suka nufi ?akinsu.
___________¡ï¡ï¡ï__________
A kano kam shiru kakeji babu wani abu daya sake faruwa bayan jin labarin inda su Abdallah suke. Ashe Abdallah saudia yay komawarsa, Naseer kuwa yana anan cikin garin kano sai a yau yazo gidan. Kowa yayi mamakin ganinsa hankali kwance sa?anin yanda sukayi tunanin samunsa.
Dominma ya ?ara tabbatar musu da hankalin nasa a kwance yake sai da ya shiga kowanne sashe yay musu bangajiyar biki. Da yamma su Abba Musbahu zasu koma Lagos harda shi cikin ?an rakkiya airport.
Bayan ya dawo ne shi da malam ?arami da suka kaisu ya samu gaisawa da baba malam daya shigo. Yanda babu wanda ya tambayesa ina yaje cikin su hajjo haka baba malam ma baice masa komaiba. Sai dai a ?asan ransa mamakin yanda babu wata damuwa tattare da Naseer ?in yakeyi. 'To mi hakan ke nufi?' ya tambayi kansa acan ?asan zuciya. babu mai basa amsa, dan haka yaja bakinsa ya tsuke ko Umm baima wannan maganaba. Bai san itama abinda Naseer ?in yayi yana cikin ranta ba, tayi shiru ne kamar yanda kowa yayi ne kawai itama.
___________¡ï¡ï¡ï¡ï__________
Lafiya lau Nu'aymah tai barcinta a sashen ita ka?ai batare dajin ko ?ar ba na tsoro. Dan haka sam dama ba ?abi'arta bace ba kowa ya sani. Abinda kawai yayta cimata rai shine ka?aici da kewar ahalinta. Gashi bata da ko ?ar waya balle ta kirasu taji koda muryarsu. Sai damuwa akan wa?an nan mutanen gidan data fahimci sam babu mai ?aunarta a cikinsu. Sai dai kowa da nasa salon kallon data lura yana mata. Yaran nan su Victoria ne kawai babu ruwansu, sai su maman Destiny. Amma har masu aikin gidan tana fahimtar kallon ?yama da suke binta da shi duk da kuwa duk suna mata gaisuwa da girmamawa. Lallai kuwa dolene ta ?aura ?ammarar zama mara jin magana, inba hakaba wahala zata sha tunda ta fahimci shi daya ajiyeta bamai zama bane. Yazama lallai kenan itace zataima kanta ya?i da kanta basai ta jira daga wurinsa ba. Da wa?an nan tunane-tunanen tai barci a wannan daren, hakan yasa washe gari bata fita a sashen nata ba sai bayan sallar zuhur.
Yau kam babu kowa a falon sai Abraham kawai yana kallon cartoon, yanda yaron bai tanka mata ba haka itama bata kulashi ba tai ficewarta. Kai tsaye garden ta nufa abinta. Shiru wajen babu komai sai kukan tsuntsaye da iska mai da?i dake ka?awa. Ta zauna a bakin pool ?in tare da zira ?afafunta ciki tana lumshe idanu saboda sanyin ruwan. Haka ta zauna tsahon lokaci a wajen rabin hankalinta duk yana ga tunani, kamar ance ta waiga sai idanunta caraf akan Gebrail da ita kanta batasan adadin lokacin daya ?auka a wajenba. Kanta ta ?auke daga dubansa tana sake tsuke fuska. Yayinda shi kuma ya shiga takowa inda take yana wani rangaji irin na gayu marasa jin magana. A mamakinta sai kawai ganinsa tai ya zauna daf da ita shima ya zura ?afafunsa cikin ruwan.
Kallonsa tai da wani irin takaici, shiko ya saki murmushi. Kafin ya furta maganar dake bashinsa taja baya ta fidda ?afafunta tana jan wani shegen tsaki........ Da sauri yace, "Ayya sorry my aunty, i......"
Wani shegen kallon da tai masa ne ya sakashi ha?iye abinda ke bakinsa. Ta zira takalmanta ta fice daga garden ?in gaba ?aya. Ta kula yaron nan yana son shigar mata hanci, to lallai zata fyatoshi kuwa da gaggawa tunda shi ?an bunsuru ne.
Gebrail kam da kallo ya bita a wani irin yanayi yana lashe la??ansa, harga ALLAH tun ganin Aymah a wajen dinner ya rikice, dan yarinyar da shekarunsa ta dace bawai yayansa ba.
Takaicin da take ciki na Gebrail yasata ko ganin hanya batayi take tafiya kawai ta bayan garden ?in. Dan jitai sam batama bu?atar shiga cikin gidan balle ta sake karo da wani takaicin kuma. Cak ta tsaya saboda jin ana magana ?asa-?asa kamar cikin tashin hankali. Tai saurin komawa baya ka?an ta ma?e jikin rassan flowers ?in da suka sar?e wayar garden ?in. ?afafunsu kawai take gani banda fuska saboda karewa da bishiyan ayaba tayi, saboda da turanci suke ha?awa a maganar ya bata damar jin wani abu a ciki.
Wanda ke maganar yace, "Boss! Nima ganin hoton nan ya matu?ar tadamin hankali, dan bamu saniba koma bashi ka?ai baneba, tunda wannan ma a tsakkiyar file ?in nan na companyn na samesa". Cikin tsananin tashin hankali taji wanda aka kira boss ?in ya fara magana da yare, kafin ya kuma dawo yi da turanci kamar zai ha?iye harshensa. "Tabbas akwai damuwa idan hoton nan ya shiga idon wani, dan zai iya zama silar bu?ewar ?oyayyen sirrina da babu wani mahaluki daya sanshi bayan mutum hu?u, suma ?in ba komai suka saniba akai sai abinda na sanar musu. SB kayi gaggawar ?atar da hoton nan, sannan dolene a cikin watannan mubi kaf takardun nan mu bincikesu dama gidan gaba ?aya, sai mun tabbatar da babu wani makamancin irin wannan hoton sannan hankalina zai kwanta, zan shigo Lagos ?in nima amma bari sai tafiya mai tsaho ta sam....". Sai kuma ya sake komawa yin maganar da yare wancan na amsa masa.
Gani tai ?aya na takowa alamar zai fito. Tai azamar sake ma?ewa a wajen dan ta?au alwashin sai taga kosu ?in su wanene?.
Har yayo nisa taji wancan ya tsaidashi, da turanci yace, "Kaga bani hoton nan kar a sami kuskure, zan ?onashi ni da kaina kawai". Batare da wancan ?in yayi musu ba ya mi?a masa yana fa?in, "Okay sir". Daga haka ya juyo zai fita.
Da kallo Aymah ta bisa harya ?acema idanunta, bata sanshiba, dan babushi a cikin duk wa?anda aka nuna mata a cikin gidan. Jin ana takowa za'a fito ya sata sake komawa da sauri ta ma?e. Wani irin waro idanu tayi ganin Papa ne ya fito. Ta bisa da kallo zuciyarta na wani irin motsi a ?irjinta. Sai da ta hangi ya shige cikin falon gidan sannan ta sauke ajiyar zuciya ta fito a wajen zuciyarta na mamakin wane sirrine yake i?irarin babu wani mahalukin daya sani sai mutane hu?u?. Miyasa yace sanin zai iya zama sanadin bu?ewar sirrinsa? 'Sirrin mi to?' ta ayyana a fili cikin jimami.
Wata zuciyace tace, 'Ke ko Aymah ina ruwanki, ko shishshigi da son asani. Hakane fa'. ta sakke ayyanawa a ranta tana barin wajen. Daga nan ma sai ta koma cikin gidan itama.
Kamar wasa sai ga tattaunawar papa da ba?onsa ta kasa barin ranta. Duk yanda taso yakicewa abin sai sake tisa kansa yake a zuciyarta. Haka kawai takejin ?wa?ayin son ganin hoton nan. Sai dai idan tacema zata gani a ina zata gansan? Tunda yace ?onawa zaiyi. Koma bai ?onaba tayaya zata iya shiga ?akinsa binciken hoto?.
Wa?an nan tambayoyi sunta mata kaikawo a zuciya har lokacin Yoohan ya shigo gidan bata sani ba.
Yoohan da ?arfe takwas na dare da wasu mintuna jirginsu ya sauka sun iske guards ?insa na jiransu a airport, basu wani ?ata lokaci ba suka nufo gidan. Lokacin da suka shigo basu iske kowa ba a falon sai Blessing dake shirya dinner. Itace ke sanar musu ai su Momy duk sunje church. Baice komaiba yay gaba Solomon na biye da shi har ?ofar sashensa. Cikin in-ina da rawar harshe Solomon yace, "Sir! Ga kayan inaga ni basai na shiga ba?". Da ?an mamaki Yoohan ?in yay masa kallo ?aya ya ?auke fuska a tsuke, kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru yana mi?a masa hannu alamar ya bashi kayansa dake a hannunsa. Saurin mi?a masa yay da fa?in, "Am sorry sir ba laifina bane dokar madam ce hakan". Shi dai Yoohan baice masa komaiba ya amsa ya rufe ?ofar. Harga ALLAH shi Solomon ma dariya yaso bashi. jin ko ina shiru yayi tunanin kota kwanta ne? Ya ?an kalli ?akin sai ya wuce nasa kawai. Wanka kawai yayi ya fito dan sai da yayi salla tunkan su taho. Abincin dake kan dining ?in ya nufa ya bu?e, shinkafa ce dafa duka da taji ha?in kayan lanbu tanata ?amshi, sai gasashshen nama kaza da ha?in salad a gefenta. Zama yay ya zuba abincin ka?an yasa salad ?in da yanka ?aya na naman dan yunwa yakeji, rabonsa da abinci tun breakfast saboda aikin daya sha masa kai.
Baifi lauma uku ba aka turo ?ofar aka shigo babu ko knocking. Yasan Momy ce kawai ke masa wannan halin a gidan, ilai kuwa itace sanye cikin skirt da riga na lass, taci uban gashin Attachment da kallo ?aya zai baka tabbacin mai tsadane dan sai wal?iya yake da ?yalli. Bible ?in hannunta ta ajiye saman tebirin taja kujerar kusa da shi ta zauna tana shafa masa kai. "My Boy duk yunwarce tasa ko kallon mutane ba'ayi?". Tun shigowarta sai yanzu ya ?ago ya dubeta yana wani sake ?ata fuska. "Momy ai ke ?ince sam ba?yama mutane knocking sai dai ki...." Da sauri ta katsesa da fa?in, "To naji sarkin ?an ?orafi, kai kullum magana ?aya baka gajiya zan gyara".
Haka kullum take fa?a masa idan yayi magana, kuma bazata gyara ?inba. Hannunta data ?ora saman sajensa tana shafawa da fa?in, "To kayi murmushi mana" ya janye da cewa "Niba fushi nayi ba yunwa nakeji". Jin yace yunwa yakeji duk sai ta rikice kamar ba abincin ta samu yana ci ba. Amsar spoon ?in tayi daga hannunsa ta ?iba takai bakinsa. Zaiyi magana tai saurin fa?in, "Hahh! Kona maka ?ura na rantse". Yasan idan baiyi yanda take so ?inba ba barinsa zatai ba. Dan haka kawai ya shiga bu?e bakin tana bashi. Data kai hannu saman jikinsa kuma zai ture.
Nu'aymah da tun shigowar madam Chioma surutunta yaja hankalinta ta fito ta kuma ?ya?e baki a karo na babu adadi. Barin jikin ?ofar tayi ta fito tsakkiyar falon sosai tana wani ?an munafikin tari data ?ir?iro.
Da sauri duk suka juyo suna kallonta, ganin ta cigaba da tarin Yoohan ya zare hannunsa dake cikin na Momy ya ?auki glass cup ?in dake cike da ruwa ya nufota. Yanda madam Chioma ta tsuke fuskane murmushi yaso su?ucema Aymah, sai ko yawu ya sar?eta ta shiga yin tari na gaskiya. Tuni Yoohan ya manta da Momynsa dake a falon, ya ri?ota da sauri ya zaunar bisa centre table da ke kusa da su. A gabanta ya dur?usa ya saka mata kofin a baki. Da sauri ta ?ora hannayenta duka biyu a saman nasa da ke ri?e da ruwan suka karasa da kofin bakinta a tare. jikinta sai rawa yake hawaye na zirara dan taji sar?ewar sosai. ?ayan hannunsa ya ?ora a gadon bayanta yana shafawa. Kusan rabin ruwan tasha sannan ta janye, ta maida hannayen nata ta ri?e kumatunta tana ?an murzawa da sauke wahalallen numfashi irin na wanda ya sar?e. Cigaba yay da shafa mata bayan yana jera mata sannu.
Kanta a du?e ta tokare gwiwar hannunta da cinyoyinta ufan bata iya cemasa har tsahon mintuna kusan biyu. Sai a sannan ne madam Chioma ta taso inda suke. Hannunta ta ?ora akan nasa dake shafa bayan Aymah ta ?an bubbuga ta wuce batare da tacema Nu'aymah sannu ba. Binta yay da kallo harta fice. Haka kawai ya samu kansa dajin haushin abinda tayin. A ganinsa ya dace ace tama matarsa sannu tunda a gabanta komai ya faru ai. Wannan halin na Momynsa ya fara damunsa shi kam. Ya kula batason kowace mace ta ra?esa a rayuwa daga ita sai ?annensa. Kai su kansu ?annen nasa wani lokacin fuskarta nuna ?acin rai takeyi........
Hannunsa da Nu'aymah ta janye a bayanta ne ya maidosa hankalinsa, saurin ri?ota yay ganin zata tashi. "Ina kuma zakije?".
Cikin ?an sanyin muryar da sar?ewar taja mata tace, "Zanje in kwanta barci nakeji".
"Da miya fito dake nan ?in?".
Baki ta tunzira masa da fa?in, "To bahar na kwanta ba surutunku kai da Momynka ya tasheni".
"K ba momynki bace?".
"Bayan bata sona". Ta fa?a da iya gaskiyarta.
Tsatstsare ta yayi kawai da idanu ya kasa cewa komai. Ganin zata mi?e ya sake ru?ota, "Kinga muje kici abinci kafin kije ki kwanta ?in".
"A'a ni na ?oshi".
"Mi kika ci?".
"Babu komai, kawai dai na ?oshi".
"Silly girl, kodai sauran kayana kika tattare kika cinye?".
A yanda yay maganar sai yaso bata dariya, amma saita gimtse abinta batayi ba, ta zare hannunta kawai daga cikin nasa tana mi?ewa, "ALLAH ni barci nakeji ka barni na kwanta".
Bai sake ce mata komai ba ta ra?a ta gefensa ta wuce. Kallo ya bita da shi harta shige ta maida ?ofar ta rufe. Idanunsa ya?an lumshe da sauke ajiyar zuciya sannan ya mi?e. Shima jiyay baya bu?atar cigaba dacin abincin, dan haka yay kiran Blessing ta telephone ya sanar mata tazo ta kwashe. Yana cikin ha?a tea a kofi Blessing ?in ta shigo, ta tattare komai ta fice da shi, shi kuma ya nufi ?akin Aymah da kofin shayin da biscuit guda ?aya. Zaune ya sameta a gaban mirror tana ?aure gashinta, ta canja kaya zuwa wando da riga na barci. Wandon ?an fit ko cinya bai gama rufe mata ba, sai rigar itama dai babu wani girma da siririn hannu. Rikicewa tayi sosai dan batayi zaton shigowar tasa ba. Yanda taketa budum-budum ?in neman hijjab ne ya bashi damar kallon abinda take ?o?arin son rufewar.
Sosai ?irjinsa ya harba. Ya ajiye shayin a kan mirror da biscuit ?in yana fa?in "Gashi nan kisha kafin ki kwanta". Daga haka yay ficewarsa dai-dai da ita kuma taja hijjab ?in sallarta data samu nasarar gani a yanzu ta ?udundune jikinta.
Koda Yoohan ya fita da sassarfa ya rufe ?ofar falon ya kashe komai ya nufi nasa ?akin shima. ?ofar ya maida ya rufe ya jingina a jikinta da rumtse ido da ?arfi. Tsaf Nu'aymah ta shiga dawo masa cikin idanu. '?ar 17years ce da wannan surar?, ko ina ya kai yanda ya kamata?'. Ya ayyana a ransa tsigar jikinsa na wani yamutsawa................?
???ar yarinyace fa Dafta, ka bari sai ta girma kawai????.
_______________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????
Mamu gee??
MIN ?ALB!!????
Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????
Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????
Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????
?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.[6/11, 11:54 AM] +234 901 860 0202: *_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.
No. 50
____________
_Ina ma'abota karance karance littafin hausa? Wanda ke nishadantar wa ya fadakar? Kana ya tsunduma ku a kogin lobayyar kauna..?_
_*REAL FEEDO* hazikar marubuciyar nan ta zo muku da wani gangariyar littafi mai suna: *BA AMO...!* *BA AMO* wani nazartaccen littafi ne daya zo da wani