Showing 207001 words to 210000 words out of 325075 words
da iska yana lumshe idanu da sake bu?ewa akan fuskartata. Hannunsa ?aya ya ?aga ya ?aura akan lallausan fatan kumatunta yana share mata hawayen. Kafin ya ?ara ran?wafowa kanta sosai fuskarsa gab da tata yay magana a hankali kamar mai ra?a.
"Please banason kuka Zeeynab. Idan zaki iya bu?e idanunki ka?an-ka?an na gani".
Uwaliya dai na tsaye a gefe tana kallonsu a wani yanayi.
Duk maganar da Yoohan keyi Aymah na jinsa, dan haka ta?an shiga motsa idanun nata ka?an-ka?an. Tana bu?esu a sannu-sannu harta bu?e kusan rabi a kansa. Murmushin ?arfin hali ya sakar mata yana lumshe nasa idanun da a kallo ?aya zaka fahimci shima lafiyar ba isasrsa tayi ba.
"Alhmdllh" ya sake fa?a a hankali yana kamo hannunta cikin nashi. Sake maida idanunta tai ta lumshe itama. Daga haka ?akin ya ?auki shiru. Yaja wasu mintuna uku haka kafin ya juya ya kalli Uwaliya. Saurin yin ?asa tai da kanta tamkar dama ba kallonsu take ba. Bai wani damuba duk da ya fahimci yanzu ne ta du?ar da kan. Shi gulmar ?an aiki ba irin wadda bai haddace ba.
"Ha?omin ruwa mai ?umi a roba, tare da towel".
"Okay sir". Uwaliya ta fa?a da girmamawa tana nufar toilet ?in Nu'aymah.
Kansa ya?an dafe yana yamutsa fuska, dan dauriya ce kawai ya keyi iya jarumta. Cikin mintuna ?alilan Uwaliya ta dawo da abinda ya bu?ata. Tana ajiyewa tace, "Sir ko za'a ha?a mata wani abinci haka?". Towel ?in data ajiye ?in ya ?auka. Batare daya kalleta ba yace, "Ki duba abu mai?an ruwa-ruwa haka da kika fahimci tana so sai ki ha?a muga ko zata sha".
"Okay sir".
Mi?ewa yay yabi bayan Uwaliya data fita. Ya murza key ?in ?ofar sannan ya dawo yana zame ba?ar jacket ?in jikinsa mai ?yalli kamar leda daya ?ora akan ?ananun kayan jikinsa. Inda ya tashi ya sake komawa ya zauna. Sake ran?wafowa yay kan Nu'aymah ya?an juyata ka?an ya fara jan zip ?in rigar jikinta ?asa.............?
??Tab?i, har words 3600. Kai yau gaskiya kun samu gara?asa. To harda na gobe????????.
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????
Mamu gee??
MIN ?ALB!!????
Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????
Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????
Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????
?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.
[6/17, 3:52 PM] +234 901 860 0202: *_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.
No. 55
_________________
_*HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION._*
_Ina mata masu son ingattun kayan kamshi: Na kece raini? Kayan mata masu sa kishiya k'wafa? Bikin dangin miji ba za'a baki yankan albasa ba da wankin tumatir? To matso kusa domin HAJARA COLLECTION ta kawo muku kayayyaki na gyara ciki da wajen mace, Wanda suka kunshi:_
_Khumrahs: Sudaniyya, Chadian, Dufr, Fara da brown, Kai harda masu flavours... _
_Akwai turaren wuta irin su sandal, Hawi, Alut, Gab gab da sauran su.._
_Akwai turaren tsugunno dana jiki original gangariya tafiyayye dan gaske_
_Hajara collection ta kawo muku air fresheners, Mopping sprays da turaren wanki..._
_Akwai herbal organic soap wato sabulun gyaran jiki na maida tsohuwa yarinya.._
_Sannan Hajia hajara collection tana gyaran jiki.. Tana kuma siyarwa da kayan gyaran jiki na dilke set, Fata tai luwai luwai kamar ta jarirai.._
_Akwai special bridal spa wato gyaran jikin Amarya... Duk Amarya mai son tadinga kamshi har bayan shudewar bikinta to ta nemi hajara collection.._
_Akwai duk wasu nau'in kayayyakin turare masu kamsasa unguwa baki d'aya, Ki mopping tiles suyi sati suna kamshi, Kayan Haj hajara collection akwai inganci sosai._
_Akwai page dinta a favebook mai suna *GIDAN KAMSHI* ga mai son zuwa ya duba hajarta, Ko kuma ya tuntubeta a number wayarta kamar haka: 09032069304_
_Adireshi: KANO NIGERIA, MARIRI dake Kan titin MAIDUGURI RD. KANO STATE.._
_TANA BADA KAYANTA AKAN FARASHIN SARI KO SAYA DAYA DAYA, SANNAN TANA TURA KAYANTA A KOINA AFADIN NIGERIA_
_AVAILABLE IN WHOLESALE/RETAILS. Nationwide deliveries. 100% tested and trusted...!!!_
_Kyau, inganci, Rahusa... Sai kayan HAJARA COLLECTION....!_
_idan anje siya ace daga zafafa biyar.. Akwai special package da Za'a hada maka masu kamshi?????????¡á?_
_________________
No. 55
.............Sai da ya dire zip ?in har ?asa sannan ya maidata ya kwantar, hannun rigar ya kama ya cire, ?ayanma haka. Sannan ya cire rigar gaba ?aya ya ajiye gefe. Idanu Aymah ta rumtse da ?arfi jin zai zame skirt ?inma. Bata da ?arfin iya koda magana balle tace zata hanashi yin abinda taji yana ?o?arin aikata mata. Tanaji tana gani ya barta daga ita sai B&P. Ji take inama ?asa ta tsage kawai ta zurma ciki. Sai dai tasan hakan bamai yuwuwa bane. Ta na sauraren ya idasa abinda ya fara sai taji baiyinba. Saima towel ?in daya ji?o da ruwan ?umin nan ya fara goge mata jiki da shi a hakan batare daya cire sauran suturar tata ba. Taji da?in hakan har cikin ranta. Sai kuma ya ?ara mata girma a zuciya. Ta tabbata shi ?in ba mutum banza bane. Dan inda wanine duk da bata da lafiyarnan hakan wata damace a garesa. Amma shi tana kallonsa ta ?asan ido aikin gabansa kawai yakeyi ko kallon ?urilla bai tsaya mata ba.......
Ajiyar zuciya ta saki a hankali lokacin daya ?agota ya saka a jikinsa. Bayanta ya goge tsaf sannan ya ?alle bra ?inta. Batare daya ?agota ba ya zare ya ajiye, a haka ya goge mata ?irjinta tana a kife. ?agota yay zai kwantar ta ?ara narke masa alamar batason ?agowar. Yoohan ya fahimci inda ta dosa. Dan haka ya?an murmusa ka?an cike da ?arfin hali. "I'm sorry bazan kallaba na miki al?awari". Duk da tana jinsa ta?i yarda ya ?agotan. Dole ya barta a yanda take son. Ya jawo bargo a haka ya lullu?a mata sannan ta yarda ya kwantar da ita. Ta cikin bargon ya zare mata sauran kayan ya goge wajajen. Ya tattare kayan da kansa ya maida toilet. A washing machine ya saka ya wankesu. Ya shanya mata su bra ?inta, kayan kuma ya barsu a boket idan Uwaliya ta shigo sai taje waje ta shanyo su.
Sake dawowa ?akin yayi ya ?auka mata kaya. Rigace mara nauyi da kayan ciki wa?anda dai bazasu takura mata ba. Bai damu da yanda ta?i sake bu?e idanunba. Ya bita a yanda takeso ya saka mata kayan. Sannan ya yaye bargon daga jikinta yana sauke numfashi a hankali. gyara mata abinda baiyiba yayi ya ?auketa cak zuwa bayi yana fa?in, "Muje kiyi fitsari nasan kinaji ko?".
Kanta ta?an girgiza masa alamar a'a. Bai saurareta ba ya kaita, da taimakonsa tayi fitsarin da brush. Yana dawo da ita Uwaliya nayin knocking. Bu?e mata ?ofar yay ta shigo. Tana ajiye kunun gya?a data damo da soyayyan ?wai dan a?an zaman da tai da Aymah ta fahimci tana san soyayyen ?wai.
Zama yay da kansa ya bata cikin lallashi kamar ba shi ba. Da farko taso ?insha amma lalla?atan da yake yine ya sakata daurewa tasha. Dan yanda takejin muryarsa duk sai taji babu da?i..
Idanun nata ta bu?e a hankali tana kallonsa. Yanda yaketa yawan kai hannunsa yana murza goshinsa ne yasata tunanin shima kamar baida lafiyan. Ga jijiyar kansa tayi ru?u-ru?u. A bazata yaji hannunta bisa goshinsa.
Saurin ?ago idanunsa yay yana kallonta. Da?i yaji a ransa ganin ta ?ara bu?e idon harma yafi na ?azun. Ya ?ora hannunsa shima akan nata data aza bisa goshinsa. "Kina bu?atar wani abu ne?". Yay maganar a hankali yana kwantar da kanta a jikinsa.
Kai ta girgiza masa. sai kuma ta sake ?agowa tana kallonsa ?asa-?asa sosai, da alama batason bu?e idanun saboda ciwon kai da ke addabarta. Cikin magana ?asa-?asa sosai da shi ka?ai ke iya jinta tace, "Kaima kanka na ciwo ko?".
A bazata murmushi ya subuce masa. Ya sumbaci goshinta tare da sake maida kanta ya kwantar a ?irjinsa yana shafa damtsen hannunta a hankali batare da ya bata amsar tambayar tata ba.
?are lafewa tai bata sake magana ba itama. Sai ma barci daya sake ?aukarta a haka saboda allurar bata gama sakinta yanda ya kamata ba.
Idanu ya tsura mata na kusan mintuna goma, a zahiri kallonta ya keyi. a ba?ini kuwa ya tafi duniyar tunani mai zurfi. Ganin ta koma barcinne ya sakashi sauke ajiyar zuciya da sake maidata ya kwantar ya lullu?eta. Fita yay dan yana son shirya abinda ya dace, ya kumayi sallama da jama'ar gidan. Dama ya kira Papa tun ?azun sunyi magana. Papan ma yace zai samesu acan ?asar Austria ?in shima a randa za'aymata aikin.
________¡ï¡ï¡ï_______
Dukkan abinda ya dace Yoohan ya kimtsa akan tafiayarsu ya tattara. Yayi sallama da kowa na gidan. Momy dai nata ba?in rai dan tace zata bisu yace a'a. Ta bari idan papa ya dawo sai suzo tare.
Bayan la'asar ?an gidan su Abba suka iso, har dasu Adawiya. Duk ?iyayyar da Adawiya kema Aymah yau sai da tai hawayen tausayinta kamar yanda su Yusrah keyi suma. ?arfe biyar dai-dai Ambulance da zata ?auki Aymah ta shigo gidan tare da Dr Shikurah.
Yoohan ya ?ara duba komai na sashen nasu, ya tabbatar ya kashe duk wani kayan wuta, an kuma fidda duk abincin da zai iya lalacewa. Da kansa ya kulle ko'ina ya saka keys ?in a jikkarsa. Duk ?an gidan sun fito compound, babu dai wanda ke nuna jin da?insa da halin da Nu'aymahn ke ciki a zahiri. Sai dai a zuciya ALLAH ka?ai yasan karatun kurma.
Duk wa?anda zasu musu rakkiya airport sun shiga mota, harda Uwaliya da zata koma da zama gidan Abba sai su Aymah sun dawo. Haka motocin suka fita a jere wa?anda aka bari na binsu da addu'ar ALLAH yasa a dace.
Tafiyar mintuna ka?an ce ta kaisu airport. kasancewar jirgin nasu na gab da tashi aka shiga da Aymah cikin jirgin, kafin suma su Yoohan da sauran passengers su shishshiga. su Abbah na binsu da addu'a kafin suma su taho. Basu bar airport ?inba sai da jirgin ya ?aga a samaniya ?arfe biyar da rabi dai-dai.
Sun sauka a Dubai, daga can suka shiga jirgin kaisu Austria.
________¡ï¡ï¡ï_______
Tun jiya Nu'aymah keta zuwama Umm a rai. Ta kira wayarta kusan sau uku kuma a kashe. Gudun karta saka abin yay mata tasiri a rai sai ta barshi akan Aymah bata da cajine maybe. Ko kuma ta kashe wayar a wajen shiriritan ta.
Haka taita juriya har washe gari da baba malam ya dawo daga tafiya. Shine ya lura da yanayinta. Cike da kulawa ya shiga tambayarta ko lafiya?. Duk yanda taso dannewa kartace komai saita gaza. Muryanta a sanyaye tace, "Haka kawai taketa zuwamin a zuciya tun jiya. Na kirata kuma wayan nata a kashe. Na nema Uwaliya mun gaisa nace ta bata tace min wai barci takeyi. dana sake kira daga baya kuma itama wayan tata a kashe. sai nakeji a raina kamar ba lafiya ba".
?an jimm baba malam yay yana kallonta. Dan Abbah ya kirashi bayan sallar magriba ya masa bayanin cewar jikin Nu'aymah ya motsa sosai harma sun wuce Austria yau da yamma. Murmushin ?arfin hali yayi dason kwantar mata da hankali. Yace, "Babu komai insha ALLAH sai alkairi. Kimata addu'a kawai nasan zata kiraki idan ta kunna wayar. Nima tun jiya da safe bamu sake waya da itaba ma. Karki damu Jannat, ALLAH na tare da Zainab a duk inda take".
Yanda ya ambaci ainahin sunan Nu'aymah ya sake sakata jin wani iri. Amma sai ta danne dan karta sake ?aga masa hankali shima.
Daga haka suka bar maganar, sai dai daren ranar daga farkonsa har ?arshe akan sallaya Umm da Baba malam suka kwana suna mikama UBANGIJI kukansu akan lafiyar yarinyarsu. Duk da ita dai Umm batasan ainahin abinda ke faruwarba.
____________********___________
Jirgin su ya sauka lafiya a babban birinin ?asar Austria, Vienna International airport. ananma dai Ambulance ce tazo ta ?auki Nu'aymah, Yoohan da Richard & Solomon kuma suka shiga taxi. Tafiyar mintuna kalilan ta kaisu katafaren babban asibitin Vienna daya ha?u harya gaji. Babu ta yanda za'ai ka ?auka asibiti ne na gwamnati inba fa?a maka akaiba. Sannan abun zai matu?ar birgeka a yanda suka samu tarba. Ko hakan yanada nasaba ne da sanin Yoohan ?in oho.
?aki na musamman inda sam babu hayaniya aka kai Nu'aymah. Da alama ma an tanajesane domin irin masu matsalarta. Wajen koda takalmi mai ?ara ba'a shiga. Kai ko key ?aramin alhaki ba'a bu?ata. Duk wani abinda ke'a sashen na amfani zaka samu na robane saboda tsabar sanin makamar aiki. (a raina nace hummm ya kaga irin haka a 9ja??).
Gaba ?aya Aymah batasan a inda kanta yake ba, dan tun daga 9ja aka yo mata allurar data sakata doguwar suma saboda ba'a bu?atar duk wani motse-motse a kusa da ita.
Sai da Yoohan ya tabbatar an ?orata akan matakin farko sannan suka bar asibitin. Hotel ?in da Yoohan yafi sauka idan ya shigo ?asar suka nufa. Acan suka kama masauki. A kallo ?aya zaka fahimci shima yana bu?atar kulawar, dan haka Rich ya matsa masa akan yay wanka ya?an kwanta koda bazaiyi barcinba zai huta.
Bai musaba yabi shawararsa. Shi kuma Rich ya fita zuwa nasa ?akin. Bayan ya fito a wankan gorar ruwan addu'oin da Abba ya bashi ya fiddo, yay bismilla ya sha tare da shafe fuskarsa zuwa kansa sannan ya kwanta yana ambaton sunayen ALLAH da tuni ya gama haddacesu a kansa. Tun yanayi la??ansa na motsawa har ya komayi a zuciya. Cikin amincin UBANGIJI gagara misali sai gashi nannauyan barci yayi gaba da shi cikin lokaci ?an?ani. Sai dai yayisa ne cike da mafarkin Nu'aymah. Hakan yasa bai wuce awanni uku ba ya farka. Alhmdllh ko yaya dai yaji sassauci ba kamar ?azun ba. Ganinma lokacin salla yayi sai kawai yayo alwala yazo ya kabbara salla. Ko raka'ar farko bai ?ulla ba Richard ya shigo ?akin domin son dubashi.
A wani irin mugun shock yace, "Jesus!! Yoohan!! Salla ka komayi?".
Bai samu amsa daga Yoohan ba dan shi gaba ?aya ma hankalinsa baya a nan kusa. ya nutsu sosai wajen bautar ALLAH.
Ru?ani iya ru?ani Rich ya shiga. Dan a take gumi ya ji?esa sharaf ya nata kaikawo da surutai kamar wani zararre.
Shi dai Yoohan bai katse sallarsa ba, sai da ya idar a tsanake yay addu'oin fatan samun lafiya ga matarsa sannan ya dubi Richard da ya kasa zaune ya kasa tsaye. A da?ile yace, "Lafiyarka kuwa?".
"Kai zan tambaya kana lafiya kuwa Yoohan?!. Salla fa naga kanayi?!".
Idanu kawai Yoohan ya tsurama Rich dake maganar da yare tamkar zai ha?iye harshensa.
Ganin kallon da yake masa ne ya sake harzu?a Richard ?in, ya hayayya?o ma Yoohan da iya masifarsa, "Yanzu wannan ?ar yarinyar har takai ta canja ka ka bar addininka na gaskiya ka koma nata. John What's wrong with you? Are you mad? Are you............?".
Saurin katsesa Yoohan yayi ta hanyar ?aga masa hannu.
"please Richard!!. Ni ?aramin yaro ne da zaka zauna kana min ihu a kai? Karka manta shekarata ?ai-?ai har talatin da biyu. Kasan kuwa inada right ?in za?ama kaina abinda nasan ya dace dani ko?......."
"Yes! Kanada za?i, kuma shekarunka sun kai. Amma tabbas alamu sun nuna baka a cikin hankalinka ne. Shin ?yawunta ne ya ru?eka kokuwa ku?in da mahaifinta ya mallaka? Sunan da yay? Kokuwa asiri sukai maka?".
A kanran farko Yoohan yay wani malalacin murmushi, sai kuma ya tsuke fuska tare da jan tsa?i yana bin Rich da wani irin shegen kallon ?acin rai da fusata. "Richard! Mubar wannan maganar dan ni ta shafa......."
"Nima ta shafeni Yoohan. Dan ka wucemin aboki kai ?an uwana ne jinina da zan iya bama kariya a kowanne irin yanayi a kuma kowanne irin hali".
"Tunda kasan hakane sai ka bani lokaci dan ka fahimceni".