Showing 144001 words to 147000 words out of 325075 words

Chapter 49 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29186

?insa na ?asa da masifar ?arfi. Da turanci yace, "Tayaya kake tunanin hankalina zai kwanta Godwin? Ko nauyin fa?amin Yoohan baijiba wai zai auri ?ar arewa, ?iyar hausawa masu sallah?".
Da sauri Uncle Mike yace, "Ah!Goshpower wani lokacin kana abu kamar ?wa?walwarka baya aiki da kyau. kai nefa ka sanar min yaron nan ya sanar maka yana da manufa akan duk abinda ya keyi. Mizai hana ka amince masa ya aureta ?in. Muma wata damace tazo hannunmu akan mahaifinta....."
A fusace papa yace, "Sai kuma akace muku da ?ana kawai zamu iya samun wannan damar? Salon suje su maidashi mai salla, to ni......"
Saurin ?aga masa hannu wani da suke kira Chief yayi da sauri. Ya juya maganarsa zuwa yarensu da ayanzuma bilynku bataji ba??. Magana ya farayi kamar zai ha?iye harshenshi cikin maida gaba ?aya hankalinsa ga papa. A mamakina kuwa sai naga gaba ?aya papa ya nutsu yana saurarensa tamkar ?an uwansa. A hankali na ga fushin papa ya fara sauka daga fuskarsa. Saima ya koma sakin wani mugun murmushi yana gya?a kai. Kafin ya mi?e cike da wani irin farin ciki ya rungume Chief ?in. Suma sauran duk tsantsar farin cikinne ya bayyana a fuskokinsu. Da alama dai shawarar Chief ta zauna da ?yau a zukatansu.
Tashi papa yay ya shiga neman Number Yoohan. Sai dai kusan kira goma bata shigaba. Canja akalar kiran yay ga Solomon.
Yoohan na kwance har yanzu a gadon Solomon yay knocking. Bai motsaba balle ya amsa masa. Shikuma Solo jin yayi har kusan sau hu?u babu amsa sai kawai ya tura ?ofar ya shigo. ?arasawa yay inda Yoohan ?in ke kwance cike da tsoro da girmamawa yace, "Am sorry sir. Boss ne yace na baka waya". Kamar Yoohan bazai tankaba ya watsar da shi. sai kuma zuwa can ya mi?a masa hannu alamar ya basa wayar. Yana bashi ya fice abinsa. Yoohan ya ?ora wayar a kunne batare da yayi magana ba.
Cikin sanyin murya papa daga can yace, "I am so sorry my son. Raina ne kawai ya ?aci dan ina tsoron su canja min kai su cuceni. Amma kuma sai nayi tunani da sake tuna bayanin da kaimin kwanaki sai na fahimci kaima ba ?aramin abune mai muhimmanci zai saka yin hakan ba. yanzu yaya kaso ayi to?".
A karon farko Yoohan yayi wani munafukin murmushi ya kai hannu ya shafi sumar kansa har zuwa sajensa. Idanunsa ya bu?e a hankali ya sauke bisa frame ?in da akai adon ?akin hotel ?in da shi. Magana ya farama papan nasa da yare cikin taushin murya.

To su din?in dinkum balkisu saina koma gehe kawai ina zare idanu dan anzo dai-dai wajen. Turancinma da yaya nake ha?osa nake masa fassara????????.

Papa da Yoohan sun ?auki lokaci mai tsaho suna waya. Dan har sai da na ?osa kafin su kammala. Yanda naga Yoohan ?in ya ?an rage buyagin nasa ne ya sakani fahimtar maybe har sun gama tsara wani abune.

¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï


Kusan ?arfe tara na dare Nu'aymah ta farfa?o. Dr Sa'ad dake tare da ita dan duty ?in dare ne da shi yay azamar kiran Dr Yoohan da har yanzu yana a hotel ?in bai kuma waiwayar asibitin ba.
Cikin kuwa mintuna ?alilan ya shigo asibitin. Tsabar yanda ransa ke a jagule sai ya toshe idanu da ba?in Glasses da yay masifar sake fiddo masa ?yawun fuskarsa da kwarjinin hasken musilinci dake mamaye da shi. Tunda ya shigo asibitin baiyi magana da kowa ba. Ko gaidashi da Nurses suke da sauran ma'aikatan hannu kawai ya dinga ?aga musu kansa a ?asa ya rufe rabin fuskar da p-cap bayan glasess ?in. Shi dai Solomon na biye da shi kamar jela.
?akin da Nu'aymah ke a kwance ya tura a hankali ya shiga da sallama ?asa-?asa. Dr Sa'ad da Nurses guda biyu dake a tare da shi suka amsa suna ?agowa. Da girmamawa Nurses ?in suka risina suna gaishesa. Batare da ya amsa musu ba suma ?in ya ?aga musu hannu kawai. Kafin ya mi?ama Dr Sa'ad hannun sukayi musabaha shi kuma.
A hankali ya juya kansa zuwa ga sashen da kan Nu'aymah ya ke. Ya ?an ran?wafa kanta ?a?an ya janye wani igiyan na'uran dake a gefen kanta gab da kunne.
Yanda ?amshin turarensa ya buga mata hancine ya saka ?irjinta harbawa. Bu?e idanun nata tayi da ?yar saboda bala'in nauyin ciwo da sukai mata. Dai-dai Dr Yoohan ya dubeta shima yana ?o?arin zare glasess ?in idonsa. Kallon ido cikin ido sukaima juna, duk da ita ?in dishi-dishi take ganinsa hakan baisa ta gagara ganesa ba.
Wani irin juyawa kanta ke mata, daga ciki tanaji kamar ana karta mata ?arfe, zabura tayi, ta yun?ura zata tashi Sai kuma tai saurin dafe kan nata tace, 'Aushhh kaina!'.
Yoohan da shima zuciyar tasa ke wani irin harbawa, da sauri ya wani ?auke idanunsa daga kanta cike da basarwa, tamkar bai fahimci halin da take a ciki ba.
Yanda jikinta ke wani irin ?an karkarwa ga kanta data ri?e da duka hannayenta tana jujjuyawa ya saka Nurses ?in nufarta da sauri tare da Dr Sa'ad. Yoohan dai na tsaye baiko motsaba. Sai dai yana kallonsu ne ta ?asan ido. Yanda duk sukaso Nu'aymah ta nutsu hakan ya gagara, dan ganin Yoohan ?in ya sake dawo mata da komai cikin memory ?inta, wanda hakan ke mata barazana cikin kanta tamjar ?wanyarta zata tarwatse.
"Ku barta" ya fa?a a hankali tamkar ba shine yay maganar ba. Baya Nurses ?in suka ja domin cika umarninsa, amma tausayin Nu'aymah fal ransu. Dr Sa'ad kam sai ?o?arin son ri?o hannun Nu'aymah data ri?e kanta da shi gam ya keyi. A bazata yaji an ri?e masa hannun lokacin da yake gab da ?orasa saman nata..............?



Ni dai nace 'Hummm'.?? inji mai tsoron gulma.


__________________________
ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????

Mamu gee??
MIN ?ALB!!????

Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????

Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????

Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????

?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.*_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.


BARKA DA JUMA'A


No. 39

.............Ba Dr Sa'ad ba hatta Nurses ?in da Dr Aysha dake ?o?arin shigowa da drip a hannu sai da suka kalli Dr Yoohan ?in. Amma a mamakinsu ya fiske abinsa tare da sake tsuke fuska tamkar ba shine ya aikata ba. Sai tura tattausan nasa hannun yay ?ar?ashin kan Nu'aymah da dogon gashinta ke a tsefe duk ya baje a saman filon.
Da sauri ta sake bu?e idanunta, dan kusancin da suka samu gaba ?ayansu neman haifar da barazana yake a bugun Zucikatan su, cikin rawar jikinta daya ?aru ta sake bu?e baki zatai magana, sai dai kuma hakan kamar da wuya a gareta. Dan sa?anin yin maganar sai hawaye sharrrr!! Suka fara bin kumatunta. Yanda damshin ruwan hawayen nata suka sauka bisa fatar hannunsa ne ya sakashi lumshe idanu yana wani jan numfashi da sassarfa. Sai kuma a hankali ya janye hannun nasa daga cikin kanta dama jikinta gaba ?aya ya ?an matsa baya kozaiji sau?in yamutsawar da dukan ga??an jikinsa ke masa.
Da sauri Dr Aysha tace, "Doctor akwai matsala ne?".
Shiru mai amsa mata ba. Sai idanu da ya zubama Nu'aymah da jikinta ke vibration a hankali, har zuwa yanzun kuma ri?e take da kan nata da duka hannayenta tana ?an mirginashi bisa filon. Kusan mintuna biyu yana kallon nata, kamar yanda su Doctor Aysha ke kallonsa a tsorace, kafin ya ?auka file ?in Nu'aymah yaja da baya daga gaban gadon. jikin Window ya koma tamkar halin da take ciki bai damesaba. Ya shiga bu?e shafukan takardun dake a ciki file ?in yana bin rubutun ciki daki-daki da nazari a nutse.
Su Dr Sa'ad kam duk sun rikice, sai dai sun kasa fahimtar wane taimako ya dace su bata ne. Dawowar da yay gaban gadon ri?e da file ?inne ya sakasu zuba masa idanu su duka. Ya ajiye file ?in a saman drawer'n gefen gadon da take sannan yay magana a ?an kausashe yana kallon Aymah. "Malama ki nutsu".
Ai maganar tasa tamkar zuga Aymah ma ma tayi, dan gani kawai sukai tayi wani irin masifar zabura zata mi?e. Cikin sassarfa Dr Aysha ta ?araso ta tareta. Da ?yar ta iya dannata saman gadon ta kwantar, duk da hakan kuma fisge-fisge takeyi har yanzun. Batare da Yoohan ya ?ara magana ba ya matsa jikin makunnar wutar ?akin ya kashe. a take duhu ya mamaye ko ina. Wata razananniyar ?ara da ta amsa duka Word ?in Nu'aymah ta ?walla. Duk firgita su Dr Aysha sukayi, dan haka suka shiga lalube a cikin duhu kowa na neman wajen ?uya. Shiko yana tsaye ko gezau, duk da kuwa ?arar tata jiyay tamkar zata tarwatse masa kayan cikin kansa. Lumshe idanu yayi ya bu?e a hankali sannan ya kunna wutar. Baiko kalli inda su Dr Sa'ad suka ma?al?ale ba ya taka zuwa ga Nu'aymah dake yashe a ?asa alamar fa?owa tayi ?asa.
Du?awa yay yasa hannu biyu ya ?auketa cak ya maida saman gadon, a kallo ?aya zaka fahimci batama yin numfashi. Sai da yaja bargo ya lullu?a mata sannan ya maida mata duka na'urorin da ke manne da kanta ?azun. Juyawa yay yayima su Dr Aysha alamar su fita. Suna gaba yana biye dasu ri?e da file ?in Nu'aymah.

¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï

Tun barin Yoohan gidan su Nu'aymah babu wanda ya sake samun nutsuwa. Musamman ma Naseer da Abdallah. Dan furicin Yoohan akan Aymah ba ?aramin girgiza musu zukata yayi ba.
A yanzu hakama Naser ne zaune can bayan sashen samarin gidan. Waya ce mane a kunnesa alamar magana yake da wani. Muryarsa cike da rauni yace, "Ananah wlhy ina sonta, dan ALLAH karku bari wannan karon na rasata. A wancan karonma na ha?ura ne saboda duk kun goyama Abdallah baya. Ni kuma banason abinda zai kawo rikici a cikin zuminci ta dalilina. Amma a yanzu wlhy babu abinda zai sakani na janye, dan ALLAH kizo kano, nasan Hajjo duk abinda kikace zatayi, dan kece ke sakata tayi abu koda bataso matsayinki na babbar yayarta".
Shiru ya ?anyi yana sauraren abinda take cewa daga can. Sai kuma naga ya saki lallausan murmushin daya sake ?awata ?yawun fuskarsa ta jinin katsinawa, ya kai hannu ya shafi kwantaccen sajensa da fa?in, "Na gode sosai Ananah, furucinki ya koremin dukkan damuwata da tashin hankali, wlhy ba cikiba ko ?a?a goma Zainab ta haifa ina sonta a hakanta, kema kuma shaida ce akan hakan Ananah". Ya sake jim na saurare sannan yace, "To nagode sosai, sai kun iso". Daga haka ya yanke wayar yana sake fa?a?a fuskarsa da murmushi. Yanaji a ransa insha ALLAHU a wannan karon ya gama mallakar farin cikin rayuwarsa Nu'aymah ya gama, musalta irin son da yakema yarinyar ?ata bakine, amma wlhy ko rantsuwa yay babu kaffara a cikinta yafi Abdallah son Nu'aymah.

(To masu karatu kun yarda?????).

A can sashen su Abdallah kuwa Abdallah ne zaune a gaban Momy a karo na farko tun dawowarsa gidan, dan daya gaisheta baya ?ara ko minti ?aya yake barin wajen. Tun tana damuwa da hakan harta zuba masa ido kawai da kaima UBANGIJI kukanta. A yau kan tun bayan watsewar kowa daga falon hajjo bai zame ko inaba sai sashen iyayen nasa. Momy na zaune a bedroom ya sameta. Ganinsa kawai tai a gabanta ya ?ora kansa bisa cinyarta yana hawaye.
Cikin tsoro da mamaki tace, "Abdallah lafiya kuwa?". Da muryar kuka yace, "Momy wannna karonma zasu rabani da ita. Wlhy ina sonta, dan ALLAH karki bari su rabamu, itama tana sona Momy". "Ikon ALLAH Nu'aymahr dai?". Da sauri ya gya?a mata kansa, kafin ya shiga bata labarin duk abinda ya faru yanzu a falon hajjo.
Cike da al'ajabi Momy tace, "Nikam wannan lamari da ?aure kai, har raina zuciyata ta kasa aminta da zancen likitocin nan akan Nu'aymah. To amma yanda duk bakin nasu yake zuwa ?aya ne zai sakama kowa ru?ani, sannan shi kuma yaron yanzun yazo da batun cewa zai aureta. Kodai....? Kai ina ba haka bane, hakanma bazata ta?a faruwa ba". Ta ?arasa fa?a tana girgiza kanta.
Abdallah yace, "Momy wlhy koma hakan gaskiyane ni inasonta a hakanta, ?ilama fya?e yay mata". Murmushi Momy tayi a karon farko, tace, "Humm Abdallah zuciyata na hasashen abubuwa da yawa a gidan nan, sai dai bazan furtaba har sai zargina da zatona sun zama gaskiya a idanun kowa".
"Momy kamar ya?". Abdallah ya fa?a da sauri yana kallonta. Kanta ta girgiza masa. "No, bazaka ganeba share kawai. Yanzu kai da kake batun auren Nu'aymah su Adawiya daka yima aika-aika fa? Kasan kowa a gidan nan ciki yake da kai harni wlhy. Abinda ya hana ace maka komai wannan tashin hankalinne kawai. Abdallah kodai ka fara shaye-shaye ne bamu sani ba?".
"Momy shaye-shaye kuma? Ni ban fara shaye-shaye ba wlhy. Kawai dai na rushe katangar da sukace itace zata hanani mallakar burina ne, kema kin sani momy Nu'aymah farin ciki nace, da sonta na fara sanin kaina, tayaya lokaci ?aya za'ace za'a ruguzashi. Itama tana sona. Batason a rabamu".
"Nasan duk haka Abdallah, shawarar da zan baka kawai kabi komai a hankali, ka kuma saka a ranka wani ramin rijiyar yafi gaban tsallakawa saboda fa?in baki, a kuskure ka?an zaka iya afkawa ciki ka halaka. Zan tayaka da Addu'a, insha ALLAH kai da Nu'aymah sai kunyi farin ciki. Daga ni har mahaifinka kuma sai inda ?arfinmu ya ?are wajen ganin ka mallaki Nu'aymah a wannan karon kodan samun farin cikinku kai da ita".
Sosai yaji da?in kalaman mahaifiyar tasa. Yay mata godiya sannna ya fice daga sashen cike da ?warin gwiwa.

________¡ï¡ï¡ï________

Baba malam na zaune a falonsa hannunsa ri?e da Littafin gawurtaccen barubucin malamin addinin nan Sheikh: Salihu bn Fauzan bin Abdallahil Fauzan yana dubawa, sai dai sam hankalinsa bama ya tare da fahimtar abinda littafin ya ?unsa. Karantawa kawai ya keyi. Kiran da akaima wayarsa ne a karo na biyu ya saka Umm dake kwance cikin kujera idanunta a rufe an cire mata drip ?in da aka saka mata kallonsa. Ganin sam bama yajin kiran wayar ya sakata mi?ewa a hankali zaune. Hannu ta mi?a ta ta?ashi.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke da juyowa ya kalleta da sauri, sai kuma ya maida ga wayarsa data nuna masa da hannu. Sake sauke numfashin yayi, ya gyarama Muhammad dake kwance jikinsa yayi barci kwanciya, sannan ya ?auka wayar dai-dai ta tsinke. Ganin wanda yay kiranne ya sakashi kiransa babu jinkiri. Sai dai kuma bai ?aga ba harta tsinke shima, tana tsinkewa kiransa ya sake shigowa wayar baba malam ?in. A karon farko baba malam yay ?an murmushi, wannan ?abi'ar Yoohan ce, baya ta?a yarda baba malam ya kirashi sai dai shi ya kira. Koda kuwa baba malam ne ya fara kiransa zai bari har sai ta katse sannan shi ya kirasa.
Kamar yanda ya saba cike da ladabi yayma baba malam cikkakkiyar sallama da harshensa da baya fita da kyau. Baba malam ya amsa masa da kulawa tamkar yanda ya saba, bazaka ta?a cewa wani abu ya faru tsakaninsu ba. Gyara zama sosai Yoohan ya sakeyi a kujerar office ?insa kafin ya farama baba malam ?in bayani a nutse.
"Uncle Alhmdllh patient ?in ta farfa?o, sai dai kuma......." Sai yay shiru kuma. Cike da dauriya da kawaici irin na baba malam yace, "Yahya! Sai dai me? Karkaji komai kai min bayani akan duk halin da Nu'aymah take, domin UBANGIJIN daya jarabceta a wannan yanayin ya fimu sanin dalilin hakan, ita rayuwa da ?addara duk suna cikin kundin jarabawa ne, mai ?arfin imani da ?wa?ayin rahama ne kuma kawai ke iya juriyar cinyesu komai tsanani da zafin da sukazo masa da shi. UBANGIJI ya fimu sonta ai, bai kumayi shawara damu ba sanda ya bamu, idan ya ?ar?eta a yanzu sai dai mu gode masa da ni'imar da yay mana na samunta tsawon shekaru sha bakwai a gabanmu. Dan haka fa?amin kawai".
Baki Yoohan ya cika da iska ya fesar, zuciyarsa da ruhinsa na ?arajin ?auna da son baba malam har cikin jini. A komai nasa yana fatan yin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login