Showing 228001 words to 231000 words out of 325075 words

Chapter 77 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29093

duk akan abinda zai amfani rayuwarsa ne suke tattaunawar. Daga bisani suka dawo da firar tasu akan Aymah. Hannu Yoohan ya kai ya janye bargon data rufe har fuskarta a hankali, dan ya gama fahimtar wannan ?abi'artace na lullu?a da bargo har kanta. Lumshe idanu ya ?anyi ya sake bu?ewa a kanta, dai-dai yana amsama baba malam da cewar, "Uncle babu wani damuwa yanzun kam. Gata nanma tasha magani tana barci. Sai nan da kamar awa uku zata tashi insha ALLAH". Murmushi yayi mai ?ayatarwa saboda jin abinda baba malam ?in yace daga can. Ya sake kai hannu akan girar idon Aymah ya shafa yana sakin murmushin da har ha?oransa suka bayyana. "Uncle ai zata daina watarana. Yanzunma ?uruciya ce kawai, kowa dama da irin tasa. A dalilin aikin ma gashi yanzu tayi sanyi sosai. Duk ta zama shiru-shiru". Fa?a?a murmushinsa ya sakeyi sosai saboda amsar da baba malam ya sake bashi. Daga haka suka gaisa da Umm sannan yay musu sallama ya kashe.
Ran?wafawa yay akan Aymah ya sumbaci kuncinta da saman ido. Bargon ya sake gyara mata yanda bazata rufe fuskarba sannan ya mi?e ya karasa kimtsawa ya?an mata short note ya ajiye mata da wayar ya fice.

X¡ïx*x¡ïX

Sosai Nu'aymah tasha barcinta. Bata farka ba sai bayan a wanni uku da fitar Yoohan kamar yanda ya ambata. Taji da?in barcin sosai. ta mi?e tanata faman ?ata fuska irin ta wanda ya tashi a barci. Wanka tayo da ruwa mai ?umi. Ta bu?e Wadrobe zata ciri kaya tajita gam. mamaki ya kamata da takaici ganin rufewa yayi. ?un?uni ta fara tana fa?in, 'Gaskiya wannan mai jajayen kunnuwan yama rainani. Nasan maganinsa ai ALLAH kuwa. Sai yasan yayi da ?ar Umm da baba malam'. Ta ?are maganar tana huci kai kace wani uban laifi akai mata. Har ta nufi gado da fushi sai kuma ta dawo da baya. ?ayan murfin Wadrobe ?in ta bu?e. A mamakinta sai taci karo da akwatin nasu anan. Shi ta bu?e tana ?wafa da fa?in, 'Na rantse akan kayanka zan huce takaicina. Dan sakasu zanyi naita birgima a ?asan ?akin nan har sai sunsan ni?in Zainabu ce jikar Zainabu Abu hajjaju Hajjo matar malam Hashim ?an jibiy.......' ta kasa ?arasawa sabida cin karo da wata leda da tayi a gefen akwatin. ?auka tayi ta bu?e ledar tare da zazzago kayan ciki. 'Ikon ALLAH sai kallo. shiko wannan bawa mi yake nufi dani dazai ajiyemin wa?annan kayan kamar ?iyar tsuntsuwar sama jannati? Shin wai nufinsa ni jikar ?an jibiya ce zansa wannan a tsokani shari'ar komi?, dama shiyyasa ya?i ?akkomin kaya sai wani jallabiya guda biyu dan tsabar ya maidani doll'. Tai maganar tana ?aga wandon da bazai wuce rabin cinyarta ba. Ajiyesa tai ta cigaba da ?aga sauran ma. Duk da bawani na fidda tsiraici bane sun bata haushi. Dan ba saba saka irin wa?anan ?ananun kayan tayiba a gida. Wani lokacin ko wando da riga ta saka sai Umm ta korata ta ?ora after dress a sama inhar zata fita daga sashensu. Mansa ta ?auka ta shafa tanata cika baki da iska. Sosai takema man shafawar matsar mugunta. Wai shima sai yaji a jikinsa tunda ya saya mata wa?anan fingalallun kayan kamar wata ?ar tsana. To wlhy tunda ya raina mata jiki saita ta narkar abinci ta zama ?atuwa kafin subar ?asar nan. Sai tama aljihunsa ?ibar karan mahaukaciya (Dan?ari. To kaji Yoohan talautaka za'ai a ?asar Austria??).
Haka tasa kayan tana mita. ta ringa zazzagama jikinta turarensa wai shine target ?in farko da zata fara. A gaban ?aton mirror ?akin taje ta tsaya tana kallon kanta. Ta wani ri?e ?ugu tana fa?in, 'Woow na kumafa ha?u' tai maganar tana jujjuyawa. 'Yauwa nama tuna. Bara nayi yanda naga matar jiya tayi' ta fa?a tana tattare ?asan farar top ?in tata ta ?aure a gefe. Hakanne ya bama ?ingilis ?in wandon nata kalar blue na jeans damar fitowa sosai. 'Tab, wlhy su Umm an haifo baturiya ba'a saniba. Hummm inama zan ha?u da hajjo yanzun. Nunawafa zanyi bamma santa ba, dan saina gama folata irin nifa bamma san African ?innanba sannan'. Ita kanta abun sai ya bata da dariya. Ta ?yal?yale kuwa da ita kamar dai har yanzun kan da motsi??.
Haka taita shirmenta ita ka?ai harta gaji ta bari taje ta gyara gadon da kanta. A wajen gyaranne taci karo da note ?insa. Koda ta gama karantawa saita murmusa. Wayar daya ajiye ?in ta ?auka ta nufi ?ofar da taga sun fita jiya ta danna yanda taga yayi da zai rufe. a take kuwa labulen ya zuge. Ta sake dannawa ?ofar glass ?in itana ta bu?e. Farar ?afarta dake a cikin blue Slippers ta zira waje tana wani zu?ar dadda?ar iskan wajen. Barandan ta ?akinne kawai, hakan yasa taji ta ta sake dan babu ruwan wani da wani. Sannan anyi iyakar da wa?anda ke ma?waftaka da ?akin bazasu gantaba, kamar yanda itama bata ganinsu sai ainahin birnin Vienna da kuma harabar hotel ?in da ?aton swimming pool yake. Shima sai idan ta mi?ene a jikin ?arfen barandar zata iya ganin masu hutawa na wanka, wasu kuma suna zaune a kujeru ana zu?ar drinks.
A ?aya daga cikin kujerar wajen ta zauna, ta ciro buk ?aya dage cikin ?an kantan wajen ta ajiye sannan ta hau ?o?arin kiran su Baba malam cike da ?oki. Kamar kuwa jira sukeyi, tana kira ring baifi uku ba Umm ta ?aga. Dan baba malam yana wanka a lokacin. Cike da ihun murna ta farama Umm magana. Itako daga can sai dariya take da jinjina wauta irin ta ?iyar tata. Dan ita ta tabbatar ba kuruciyace kawai ke ?awainiya da Aymah ba. Akwai tsantsar wauta tattare da ita. A dai ?asar hausa mai shekaru irin nata ai budrwace cikkakkiya kowa ya sani. Biye mata tai ko tanata faman bata labarin haduwar hotel ?in da suke, da gine-ginen garin Vienna. Harda cewa Umm bara ta katse ta kira video call wai dan ta gani. da sauri Umn tace, "A'a shugabar rawan kai na gode. Nima ai nazo na gani da idona".
"Yo Umm ai dai bakiyi yawoba" tai maganar cike da shagwa?a. Dariya Umm tayi da fa?in, "ALLAH ya shiryeki Nu'aymah. Ga Abbanki nidai barni na hutama raina. Ga autana can kwance yana fama da zazza?i bara naje naji da shi".
A take kuma sai mood ?in Aymah ya canja jin abokin fa?a babu lafiya. Duk sai ta marairaice kuma har ma abin ya bama Umm da baba malam dariya. Haka dai ya amsa shima ta zuba masa shiriritarta. Sai da yace ta kashe wayar haka karsu ?ararma Yoohan da ku?i sannan sukai sallama bayan anbama Muhammad shima sun gaisa, duk da a kwance yake bayajin dadi. Daga haka Hajjo ta kira. Itama suka gaisa. Badan tasoba ta ha?ura ta ajiye wayan ta ?auki buk ?in data ?auka ta fara dubawa.

Haka Nu'aymah ta kasance ita ka?ai a wannan yini. Duk da garga?in karta zauna da yunwa da Yoohan yayta mata bataji ba, sau kusan uku ma'aikatan hotel ?in na kawo mata abinci amma sau ?aya taci. Da lokacin shan maganinta yayi kuma tasha kamar yanda ya rubuta mata a note ?insa. Novel ?in data samu ne ya ?auke duka hankalinta. Dan shi taita karantawa. Salla kawai ke sakata ajiyewa. Bata damu ba da rashin dawowar tasa. Tunda ya rubuta mata uzirinsa zaije ya ?araso yau gaba ?aya shiyyasa. Kuma ya bata ha?uri akan barintan da zaiyi ita ka?ai ?in.
Lokacin shan maganin darenta nayi taci abincin da aka sake kawo mata ka?an tasha duk magungunanta tai wanka. Kwanciya tai tana cigaba da karatun buk ?in har barci yay awon gaba da ita.

A haka Yoohan ya shigo a matu?ar gajiye ya isketa. Ya zauna a bakin gadon yana kallonta. Hannu ya kai ya zare buk ?in data rungume a ?irji a hankali. Motsawa tai, tare da bu?e idanunta da ?yar ta kallesa. Batare datayi maganaba tai luu dasu ta maida tarufe kayanta tare da gyara kwanciya.
Idanu kawai ya lumshe shima ya bu?e akan buk ?in. Batare da yace komaiba ya ajiye ya mi?e domin yin wanka.
Har ya kammala dukan hidimarsa Aymah nata barcinta. Bai tadataba kuwa yay shirin barci shima tare da sallolinsa da suka rage ya hawo gadon ya kwanta dan a matu?ar gajiye yake. Addu'ar barci yay musu ya rungume matarsa suka lula duniyar barci mai da?i.

*_WASHE GARI_*

Yau ma kamar jiya bayan sallar asuba sunyi zaman karatu. Koda suka idan tasha magani shi kuma ya fita motsa jiki. Da ya dawo ma ya sameta tana barcin. Wanka kawai yayi ya fiddo lap-top ya fita ?ar barandar Aymah ta jiya bayan yayi order ?in abinda zaici. Acan ya shafe tsahon lokaci har Aymah ta tashi a barcinta. Ganin baya ?akin tai tunanin ko ya fita. Wanka tayo tazo ta shirya cikin sauran kayan jiya. Yau dai wando ne ta saka yellow da black t-shirt. Tayi ?yau yauma sosai, ta gyara gashinta tana ?an yatsina fuska ganin yana bukatar wanki. Badai tayi maganaba dan bason a ta?a mata kai takeba daman. Kobi takan abincin data gani batayiba. Ta ?auki buk ?in jiya dake a durowar gefen gadon ajiye ta nufi wajen zamanta na jiya. Kasancewar ya rufe yasa bata fahimci yana a wajenba sai da ta fito.
Yoohan dake zaune a kujerar ya ?ora ?afafunsa bisa table ?in, lap-top a saman filo daya sa kan cinyarsa yanata aikinsa ya ?ago idanunsa jin sabon ?amshin turarensa data bunku?a a jiki. Suna ha?a ido ta turo baki gaba tana kauda fuskarta.
Baiyi maganaba shi dai. Bai kuma daina mata kallon ?urilla ba, dan kayan sun matu?ar mata ?yau, kodan yau ne ya fara ganinta a cikin irinsu oho. duk da kuwa yana bala'in son yaga tayi shigar Hausawa dan tana masa ?yau. Amma yauma dai tayi irin ?yawun da yake bu?atar ganinta a ciki.
Ha?iye abinda ya tsaya masa yay a ma?oshi yana furzar da nannauyan numfashi. Yanda yayi ?inne ya saka Aymah dake tsaye kamar an dasata kallonsa. da alama kunyace ta hanata motsi kokuma ganin da tai masa a wajen a bazata. Saurin janye idanunta tai ganin har yanzun kallonta yakeyi. Harga ALLAH ita tanajin nauyin ganinsa da kaya irin wa?anan. Rigace armless fara tas a jikinsa, sai wando dako cinyarsa bai gama rufewaba oxblood. Duk da lap-top ?in daya ?aura bai hanata ganin farare cinyoyinsa da gargasa suka kwanta ba.. Cikin sanyin muryar da baisanta da ita ba tace, "Good afternoon".
Idanunsa ya?an lumshe ya bu?e a kanta. Sai kuma ya maida ga lap-top ?insa yana fa?in, "Same, How are you?". Hararsa tai ta gefen ido saboda jin yanda ya amsa gaisuwar. Da tamayi niyyar komawa ciki, amma yanda ya amsa matanne ya sakata takowa ta ?araso inda yake. Kujerar taja itama ta zauna tanata wani faman ha?e fuska irin batason wargi din nan.
Duk abinda takeyi Yoohan na kule da ita. Sai faman ?o?arin danne dariyar dake taso masa a rai kawai ya keyi. Aikinsa ya cigaba da yi ita kuma ta karatun novel. duk da kuwa bama karatun takeba satar kallonsa kawai takeyi tana gulmarsa a zuciya. Tunda ya fahimci kallonsa takeyi shima sai ya kasa ci gaba da yin aikin. Saboda tsabar neman magana ya tura ?afarsa ya tan?wa?e littafin nata ya fa?i. Ya kuma fiske abinsa ya?i kallonta tamkar bashi ne ya aikata ?in ba.
?ara tsuke fuska tayi tanabin buk ?in dake yashe a ?asa da kallo, ?an bakin kuwa sai motsawa yake amma ta kasa magana. Cike da takaicin daya kumeta ta ?auki filo ta maka masa a ?afa harda cije baki.
"Ouch!" ya fa?a yana saurin janye ?afarsa. "Silly girl!. Wane mugunta ne haka? Mina miki?".
Harara ta balla masa. batare da tace komaiba ta du?e zata ?auki buk ?inta. Sai dai kuma hannunta bazai kaiba dole sai tazo ta gabansa. Fitowa tai tazo har inda littafin yake. ta ?auko harma ta mi?e zata koma inda take ya saka mata ?afa. Sai ko gata a kan cinyarsa ?are-?are.
Mutsu-mutsun ?wace jikinta ta fara ya saka hannayensa yay mata zobe. Duk yanda taso ta motsa kuwa sai ta kasa. Sake kumbura baki tayi da ?yau, dan haka kawai ta tuno randa ya ta?a rungumeta a gidansu har Aunty Kubrah ta gansu.
Kansa ya ?ora bisa kafa?arta yana busa mata numfashinsa. Cikin magana ra?a-ra?a yace, Silly girl, K ba'a zama lafiya da ke sai kinja fa?a ko?". Wani shegen mintsini ta bashi a cinya wanda ya sakashi sakinta babu shiri. Mi?ewa tsaye tai daga jikinsa tana masa gwalo. Yanda ya ?ata fuska kamar zaiyi kuka ya sakata ?yal?yalewa da dariya tana nufa hanyar ?ofa. Yatsu biyu ta ?aga masa, ?ayan hannunta ri?e da ?ugunta tace, "Wannan na yadda buk ne na maka. Saura na......"
Ganin ya mi?e ya sata kwasa da gudu tai ciki batare data ?arasa fa?aba. Baya ya rufa mata har cikin ?akin. Nanfa suka shiga zagaye ?akin. Duk yanda yaso kamata ta?i tsayawa, duk da dai da alama ya barta ne kawai. Ganin yanda yake hakki da nuna matu?ar gajiya ya saka taketa ?yal?yala masa dariya tana masa gwalo. Harda yin yanda yara keyi na tsokana. Tana saka yatsunta a kunne da jujjuyasu tana masa gwalo.
Shiko ?ara narkewa yake irin shifa ya gaza kamata. daga ?arshe ma ya fa?a saman gado yana hakki da fa?in, "Silly girl".
Zuwa tai har inda yake kwance ta shuri ?afarsa zata gudu. Dama tarko ya mata. Yako har?ota da ?afar sai gata a jijinsa. Da dai taga da gaske an kamatan saita fara kukan ?arya tana kai masa ?ananun duka a ?irji. Dariya ya farayi ya ha?a duka hannayen ya ri?e tare da juyata akan gadon ya koma kanta. "Wana kama to yanzun?". Ya fa?a yana busa mata iskar bakinsa a kan idonta dake hawayen ?arya.
Baki ta sake kumburawa tana matso hawaye. "To bakai ka fara tsokanata ba. Ni dai dana fita ai banma kulaka ba amma ka takaleni".
?an?ance idanunsa yay da ?age gira sama. Yace, "Yarinyar nan kin iya sharri. A yaushe na tsokanekin?".
"Na rantse da ALLAH kai ne ka fara tsokanata, kuma bazan ?yaleka ba sai na rama".
"Da gaske?". Ya fa?a a hankali yana sake matsar da fuskarsa dab da tata har hancinsa na gogar nata. Cikin sar?e idanunsa cikin nata ya sake fa?in, "Yaushe zaki daina rashin ji ne?".
Duk yanda taso bashi amsa ta kasa. Saboda goga mata lips ?insa da ya farayi akan nata. Tai ?o?arin kauda kanta gefe, yay saurin tarewa da nashi yana fa?in, "Uhmyim?. Fa?amin yaushe zaki san kin girma?".
Ba ?aramin harbawa zuciyar Aymah tayiba saboda jin a yanda yay maganar, kafin tai wani yun?uri ya ha?e bakinsu waje ?aya. Tabbas yau kam tamafi ranar shan chocolate, dan Yoohan ya tabbatarma Aymah a matu?ar zalame yake dason kasancewa da ita. Duk yanda yaso sassauta mata ya gagara, sai da ya ?ora mata sabon salon karatunsa mai wahalar haddacewa.
Gaba ?aya kukan da taso masama sai ta nemesa ta rasa, sai wani irin tsoro da matsananciyar kunyace da bata ta?a karo da itaba a rayuwarta ta lullu?e ta. Tunda ta samu ya barta ta tura kanta cikin filos bata sake yarda sun ha?a idanu ba. Sun kwashe mintuna talatin a kwance kafin taji ya sake matsota. Ba ?aramin bugawa ?irjinta yayi ba jin ya kwanto a bayanta. Amma sai ta daure tana ambaton sunan ALLAH.
"Akwai matsala fa".
Ya fa?a a cikin kunnenta yana tura hannunsa a rigarta. Saurin ri?e masa hannu tayi ta zabura zata matsa ya?i bata space. Dole ta ha?ura sai daifa mutuniyar taku tsorone fal cikinta.
"Kin jamin sai nayi wanka, kuma ni ban iya ba".
"Hu'um. wankan ne baka iyaba? Babu dai ?yau manya na ?arya". Tai maganar da son jan jikinta. Saurin sake ru?ota yayi ya matse. A kunnen nata Yace, "Bafa normal wanka bane, Uncle ya sanarmin a addinin musilinci wanka ya kasu kashi da yawa. *_Fitar maniyyi kai tsaye, ta hanyar jin dadi daga mace ko namiji. 2. ?oyewar kan azzkari a cikin farji. 3. Idan mutum ya mutu ya wajaba ayi masa wanka, sai dai in shahi?i ne. 4. Musuluntar kafiri ko wanda ya yi ridda. 5. Jinin al'ada. 6. Jinin biki (wato jinin haihuwa). 7. Wankan jumu'ah. 8. Wankan shiga harami (da hajji ko da umarah). 9. Wanka ga wanda ya yi wa mamaci wanka, Wankan idi biyu (na zuwa karamar sallah da babbar sallah). 10. Idan mutum ya farfado daga hauka ko
farfadiya. 11. Wankan shiga Makkah.
12. Wanka domin sallar kisfewar wata ko kuma rokon ruwa. 13. Wanka na mai istiha a kowacce sallah. 14. Ga kowanne jima'i an so a yi wanka._* �kinga kenan yanzunma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login