Showing 255001 words to 258000 words out of 325075 words
Sosai ta tur?une fuska tana zuba masa harara. Tace, "To na rantse kuwa zakaja kafin mu dawo gidannan a fara wucewa damu police station ?in garin nan, saboda ?alla ?a?an jama'a zanyi na zubar a banza. Dama gasu ba ?wariba girman ?an?ara da Ice-creem da biscuits".
Ransa fes da fahimtar soyayyarsa dake tattare da matarsa ya rungumota ta baya dan tana gama maganar ta juya tana ajiye turaren data fesa masa. A cikin kunnenta yace, "I love you irin trillions ?in nan My Cutie".
Hannu tasa zata ture masa fuska danfa taji haushin zancen ?ammata da yayi mata. Harda Miracle da tuni ta manceta a babin rayuwarta. tunda ita dai tasan itace ta ta?a ?allama ?ashi da fasama baki.
Da sauri ya ri?o hannunta yana dariya. "Na tuba wasa nake. Ai wannan Zenabu ?in har abadan a bada, insha ALLAHU ita ka?aice da Dr Yahya goshpower har ?arshen numfashi. My angel kece ka?ai uwar ?a?ana da yardar UBANGIJI. Ke ka?aice sirrin Yoohan in ALLAH ya yarda. Daga ke babu wata mace data isa sanin koda sirrin murmushin Yoohan ne balle ma ta ra?u miki miji My Noorunnisa".
Cike da jin da?in jin kalamansa da suka sanyaya mata jiki ta juyo a hankali ta jingina da mirror ?in, shi kuma tana fuskantarsa. ?wallar da suka taru mata a ido suka ?arama idanun ?yau ta zuba masa. A hankali ta motsa la??anta wajen fa?in, "Idan nace kai na dabbane, ina nufin na dabban har ?asan zuciya da bugun numfashina My boo. Tabbas bani ka?ai bace haske a gareka. Kaima haske ne a rayuwata. Dan ka cetoni daga wahalhalun jarabawar rayuwa da ?addara ta tilasta zamansu a tafin hannuna. I love you so very much Yah Yoohan". Ta ?are maganar da fa?awa jikinsa ta rungumesa.
Idanu ya lumshe a hankali yana mai ?ar?arta da hannu biyu. harga ALLAH yanama yarinyarnan soyayya da ?auna mai tsanani. Wanda ?ata lokacine wajen zama yayta fa?a da fatar baki. Tana ri?e da wasu darajoji da martabobi da mace tagari ce kawai ke iya samunsu a wajen ?a namiji.
"I love you more.... More.... More and more Zeeynab ". Ya fa?a shima cike da shau?i da sar?ewar harshe a cikin kunnenta. A tare suka sauke ajiyar zuciya sannan ta ?aggo daga jikinsa. Sumbatar la??anta yayi yana lumshe idanu da sake bu?ewa a kanta. Kafin ya juyata suka kalli mirror ?in yay musu hoto. Sosai sukayi ?yau kuwa. Tamkar ka sacesu ka gudu dan tsabar dacewa da sukai da juna. Daga haka yaja hannunta suka fice a gidan gaba ?aya. Cab suka samu zuwa wani ha?a??en shopping mail da Amerikawan ke ji da shi. Dan yasan zasu samo duk abinda zasu iya bu?ata a can.
Aiko sosai wajen ya birge Nu'aymah. Babu kunya balle damuwa tattare da ita ta shiga kashe kwarkwatan idanunta tana jinjina jin da?in duniya da turawan nan keyi. tare da ?unbin jin tausayin Africans da wahalar Yunwa da kashe-kashe ta gama jigatawa da fiddamu a hayyacinmu gaba ?aya.
Yana ri?e da hannunta suke duba duk abinda zasu iya bu?ata. Kasancewar kowa harkar gabansa ya keyi babu ruwan wani da wani sai suke komai kansu tsaye. Bayan sun kammala shopping ?in suka fito ta ?an wajen mail ?in kafin a gama musu packaging ?in kayan zasusha coffee.
Sosai Nu'aymah yanzu take bala'in son coffee. Ta rasa dalilin hakan. Dan dacan har haushi takeji yanda Yoohan ya ?auki amanar kansa ya bama coffee ?in. Amma tunda suka dira U.S ta koma tamkar mayya akan coffee.
Shi dai Yoohan yakanyi dariyane idan yaga yanda take bankarma cikinta. Cike da shakiyanci yake fa?in, *_Bugun daga kai sai mai tsaron gida kenan_* duk yanda Aymah taso fassara kalmar nan tasa ta kasa. Da taga ma wahala kawai take bama kanta sai ta daina damuwa da sanin. Daya fa?a sai ta zuba masa harara kawai ta cigaba da hidimarta.
Sunsha coffee suna ?ar hirarsu cike da farin ciki. Dan kayansu tuni an tura musu gidansu. Kusan zaman awa guda sukayi a wajen sannan suka mi?e. Gaba sukai wani shagon sai da tsuntsaye dake tsallaken mail ?in. Aymah ta zabi wasu kyawawan tsuntsaye mata da miji dake cikin keji. Yoohan ya biya yana tausayama ?an ku?a?ensa da yau Nu'aymah kema ?ibar karan mahaukaciya????. Zata ?ara nuna wasu yay saurin ri?o mata hannu yana magana da ?ar hausar daya fara iyawa a wajenta.
"Hy madam ki taimaka mani karki ?aremin ku?i anan. Bakiga munyi shopping ba, kalli wallet ?inafa". Yay maganar yana nuna mata cikin wallet ?insa kamar zaiyi kuka.
?ar dariya tayi ?asa-?asa da cewa, "Humm sarkin raki na ha?ura. ALLAH zai baka wasu masu albarka tunda ka farantama iyalinka rai ne. Kaima ALLAH ya faranta maka da ?ya?y?yawan sakamako My boo".
Murmushi yay cike da jin da?i. Dan duk wautarta ya shaideta da iya lafazi mai da?i a garesa. Ko tsiwa take masa zaka samu babu kalaman raini a ciki sam. Sumbatar la??anta yayi da kashe mata ido ?aya, yace, "ALLAH yay miki albarka my Sweet girl".
"Amin my Boo". Ta amsa masa cike dajin da?in addu'arsa. Daga haka suka fito yana ri?e da cage ?in ?yawawan tsuntsayen masu dadda?an kuka. A ?afa suka ?an ringa tafiya suna hira kamar yanda Aymah ta bukata. Ya fahimci tanason ganin kanta a inda bata saniba. Shiyyasa yake biye mata wajen ?an fita da ita dan tai farin ciki, ya kuma rage mata kewar ahalinta daya rabota a cikinsu ya kawo nan ya ajiye.
Saida suka gaji da tafiyar sannan ya tare musu abin hawa suka ?arasa gida. A barandar gidan suka iske shopping ?insu. dan haka ya bu?e gidan suka dinga kwasa suna shiga da kayan ciki har suka kammala.
Sallar la'asar data riskesu a hanya sukai ?o?arin gabatarwa. Bayan sun idar Aymah ta fara wucewa kitchen ?in. Kayan da duk suka siyo ta fara bu?ewa tana ajiye komai inda ya dace da zamansa. Tana kammalawa kenan ta ?akko tukunya zata ?auraye Yoohan ya shigo waya manne a kunnensa yana magana. Idonsa a kanta ya dafe kitchen cabinet ?in dayin ?an tsalle ya haye samansa ya zauna. Kallo ?aya tai masa ta ?auke idanunta ita dai, dan ta fahimci wayar tasa mai muhimmanci ce.
Sai da ta gama wanke duk abinda zatai aikin da shi sannan ta jawo rigan girki ta ?aura. Dai-dai kuwa da kammala wayar Yoohan. Sauka yay ya nufeta da ?an alamun gajiya tattare da shi. "Wlhy duk kin gajiyar da ni Sweet girl. Inata murna yau zan huta a gida bazanje asibiti ba. Amma sai da kika sakani yawo".
Hararsa ta ?anyi tana ri?e ?ugu da duk hannayenta. Cike da rigima tace, "Uhm uhum uhmyy. Wani aiki sai rago dai wlhy".
"Oh nine ma ragon?". Ya fa?a yana wani hangame baki.
Gira ta ?age masa tana wani juya idanunta manya masha ALLAH. Tace, "Na gaske ma".
Wata dariyar mugunta yayi yana matsota, da sauri ta manne jikinta da cabinet ?in tana marairaice fuska. Kafin ta samu damar magana yazo dab da ita. Matseta yay a wajen ya hanata ko guntun space yana wani ?age gira sama da ciskule fuska. Hannayensa na a gefe da gefenta ya kai fuskarsa gab da tata suna sha?a da busama juna numfashi. Ga idanunsu cikin na juna kowa kwarjini da sirrin na ?an uwansa na ratsa masa jiki da zuciya. Da wani irin karya harshe na ma'abota shau?in soyayya yace, "Yarinya kema kinsan ni ?in ba rago bane. Amma zan sake tabbatar miki kuwa a yau ?in nan da iznin ALLAH. Sai wannan bakin rakin naki ya kai titi saboda neman agaji". Ya ?are maganar da ?allar la?anta da yatsunsa biyu.
Da sauri ta dafe bakin hawaye na cika mata idanu. Ta kai hannu bisa damtsen hannunsa yay saurin kaucewa yana wata sha?iyyar dariya ?asa-?asa dan yasan muguntar da zatai masa.
Kumbura tayi tai fam. Cike da haushi ta kama rigar zata kunce ya ri?e hannunta. "Ai yarinya baki isa ba. Kin riga da kin yarda da game ?in nan dan haka girki dole ne".
Baki ta tura masa tana kwa?e fuska da fa?in, "Na fasa game ?in. Girkinma sai dai kay....."
"Hhh daga baya kenan hajjaju Zenaba ?ar farar bakanuwa ?ya?y?yawa".
Yay maganar da ri?ota hannunta ya maida ?aurin rigar yana mata wani dariyan iya shege a gefen wuya.
Gaba ?aya neman susuta mata jiki yake da salonsa. Saurin zame jikinta tai ta koma gefe tana fa?in, "Ai inba yau a kwai gobe indan ALLAH ya kaimu. Ka ?auka yau ?in kaine a sama ni a kwana. Sai dai kuma zaka dawo kwanar ne ni na koma ciki..."
Ta ?are maganar da wani salo tana kashe masa ido ?aya.
Da gasken gaske sa?onta ya iso inda ta turosa. Dan gaba ?aya jijiyoyin Yoohan suka saki dama kwana biyun nan rakinta ya sakashi ?an bata ?afa. Lip ?insa ya cije da ?arfi yana wani jan ajiyar zuciya ya ?auke kansa. Batare da yace komaiba ya jawo wayarsa ya mi?a mata. Yana mata wani kallo ?asa-?asa. Amsar wayar tayi da tura baki gaba tana ?un?uni. Ta kalli hoton abincin da ?yau sannan ta ?an dubesa ta ?auke kanta tana murmushi.
Kujerar dake gaban tebir ?in tsakkiyar kitchen ?in yaja ya zauna. Ya wani mi?e ?afafu da bajewa da ?yau, irin fa shine boss ?in nan.
Nu'aymah bata sake bi ta kansa ba ta fara ?o?arin ?aura girkin tana addu'a a ranta da fatan yin komai yanda ya kamata.
Ko ?auraye cokali bai tayataba, tunda ta fara. Yama ?auke kansa gaba ?aya daga gareta sai danne-dannen waya yake yi hankalinsa kwance. Duk da kuwa a ba?ini duk wani motsinta nakan idonsa ne.
Kasancewar ta kwana biyu batai girkin ba yasa takeyin komai cike da ?oki. Kafin cikar awa ?aya kuwa sai ga ?amshi ya gama gauraye kitchen ?in gaba ?aya har falo. Shi kansa Yoohan sha?a yake cike da jin da?i da kwa?ayin son cin abincin. Tsaf ta kammala komai ta gyara kitchen ?in da ?auraye duk abinda ta ?ata duk yana zaune dai yana kallonta. Abincin ta zuba a plate tare da ?an ?ora kwalliyar data ?ara ?awatashi ta ?auki cokali tazo ta dire gabansa tana wani shan ?amshi.
Idanu ya tsirama abincin dake ta tashin ?amshi mai saka yunwa. Kafin ya ?ago ya kalleta. ?auke fuskarta tai gefe murmushi nason kufce mata. Sai kuma taje ta tsiyayo apple and orange juice ?in data ha?a a glass cup tazo ta ajiye shima a gabansa. dai-dai yana gyara zamansa. Bai fahimci minene ba, amma yaga sanda take marka?a abu dai. Cokalin ya ?auka ya ?iba abincin ka?an ya kai bakinsa tare da yin bismilla. Duk da da?in daya ratsa masa baki da kunne da ?wa?walwa sai ya wani yamutse fuska harya ha?iye. sake ?iba yay yaci nanma fuska a yatsine. Aymah dai na kallonsa baki a ?age dan tasan wlhy ?arya yake yace abincinta babu ?an?ano.
Cike da son danne dariyarsa na ganin yanda tai da fuska ya kai lauma ta uku. A hankali ya lumshe idanunsa da sauke wata sassanyar ajiyar zuciya. Sai kuma yay mata alamar jinjina da kashe ido ?aya ya ha?e yatsunsa biyu???? alamar komai zam.
Itama ajiyar zuciyar ta sauke a hankali da juya bayanta idanunta na cika da ?wallar farin ciki dajin ?aunar Umm ?inta mai tsanani. Dan itace ta maidata tauraruwa wajen tsayawa akanta tun tana ?ar mitsitsiyarta. ?an?antarta baisa Umm ta ta?a rangwanta mata ba akan aikin gida duk da sunada mai aiki. Kamo hannunta da Yoohan yayi ya ?ora bisa cinyarsa ne ya sakata sauke ajiyar zuciya a karo na biyu.
"K ta dabance Cutie". Ya fa?a a cikin kunnenta yana tura hannunsa cikin rigarta.
Idanunta ta lumshe itama da kai hannunta ta shafo kwantaccen sajensa mai laushi dake cin ku?a?e wajen gyaransa. Kiss ya bata a wuya tare da ?agowa ya kamo fuskarta ya manne bakinsu waje ?aya. Bata hanashi ba. Dan ya riga da ya koyar da ita wannan sirrin.
Sai da taga wasan na neman canja salone ta ?wace kanta da ?yar tana masa dariya. Sai ko ya ?wa?e fuska tamkar zaiyi kuka dan da gaske ya zurma da yawa.
Plate ?in abincin ta ?auka ta ?aro musu tare da ?akko juice ?in gaba ?aya shima. Sai lokacin Yoohan ma ya ?auki wanda ta fara kawo masa yasha yana sauke ajiyar zuciya. Cike da ?age gira yace, "Kin ha?u a abubuwa da dama Hausa girl".
Murmushin jin da?i tayi, dan har ranta tanajin nisha?i idan ya kirata Hausa girl. Tana son yarenta tana alfahari da shi fiye da zaton mai karatu. Tanaji a ranta komi ta zama dolene duniya tasan ita?in ?ar ?abilar HAUSA ce gaba da baya.
Sunci abinci cike da farin ciki, yana bata tana bashi har suka kammala. Da taimakonsa yanzu kam suka tattare wajen suka fice a kitchen yana fa?in ta za?i ?yautarta.
Ita dai dariya take masa kawai. Sai da suka fito falo ya zauna da ita a jikinsa sannan ta dubesa tana murmushi. "Soyayyarka da kulawarka a gareni ka?ai ta isheni tukuyci my sweet boo". Tai maganar cike da salon da take ?ara ?warewa wajen koya a hannun Aunty Hajarahn mai sonta da ?aunarta.
Rungumeta yay a jikinsa ?aunarta na sake ratsasa. A ?asan ransa kuwa godiya yakema ALLAH da samunta tare da jin girma da darajar iyayenta a cikin ransa. Fatansa ALLAH ya basu ?a?a masu albarka suma su basu irin wannan tarbiyyar tata abin son kowanne ?a nagari.
__________¡ï¡ï
Haka kwanaki suka cigaba da shu?awa ga Nu'aymah da Yoohan cike da farin ciki da tattalin juna kasancewar har yanzu a amarci da ?okin juna suke. (Kunsan shi farkon aure dama haka yake. Za'aita nunama juna soyayya cike da zalama. Ku kanku jin kanku kuke tamkar babu ya ku a duniya. Sai rayuwa ta fara nisane abubuwa ke fara tsauri. Sai dai da yake UBANGIJI mai rahama ne da jin?ai sai kaga hakan baya hana a nunama juna soyayya da kulawa koda sa?ani na shiga. Duk da jarabawa kan ratsa a zamantakewar ma'aurata kaga matsalolin nata yawaita fiye da hasashe. ALLAH ya cigaba da zaunar damu a gidajenmu lafiya tare da mazajenmu da ?a?anmu da abokan zamanmu baki ?aya mata sarakunan gaskiya a fadar gaskiya??????).
Kwansu goma sha uku a U.S Yoohan yay shirin zuwa Oman yin wani aiki na kwana biyu. Daga can kuma zai wuce Nigeria insha ALLAH.
Yasha ta?ara kuwa a wajen Aymahn sa. Dan kuka sosai ta dinga yimasa akan saita bisa. Da ?yar ya lalla?ata da tabbatar mata Juliet matar Omar (Rich) tana zuwa daga 9ja a daren yau. Idan ma batason zaman anan gidan ita ka?ai sai ya kaita gidan Juliet ?in ta zauna a can harya dawo.
Da ?yar ta amince kuwa. Shima sai da aka ha?a da hajjo wajen lallashi. A ranar kuwa Juliet ?in ta iso. Sun tarbi juna da mutuntawa. Kuma har cikin zuciya Nu'aymah taji zata iya zama tare da Juliet ?in. Musamman yanda taga itama Juliet ?in na nuna mata ?auna da yaba komai nata tana sake taya Yoohan murna. Shi dai murmushi kawai yakeyi yana bin mutuniyar tasa da kallo ?asa-?asa.
Washe garin da zai wuce sai da ya rakata gidan Juliet sannan ya wuce ya barta da kewarsa kamar yanda shima ya tafi cike da tata kewar.
¡ï¡ï¡ï¡ï
Tamkar jira jikin Aymah keyi Yoohan ya wuce ta fara ?ananun ciwuka. Kullum da zazza?i take wayar gari, zuwa ?arfe ?aya na rana kuma sai ya gudu. Tun Juliet bata fahimtaba harta fahimta saboda sha?uwar dake ?ara shiga tsakaninsu da Nu'aymah. Dan Juliet tanada sau?in kai sosai. Bata ta?a kuma nuna ?yamar addinin Nu'aymah ba koda kuwa akan fuskartane. Wani lokacinma idan Aymah na salla ko karatun Al-qur'ani har zama take taita kallonta. Dan itama zuwa yanzun tasan mijinta Omar (Richard) ya musulinta............?
*_Gaba ?aya na manta yau monday fa??????????_*
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????
Mamu gee??
MIN ?ALB!!????
Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????
Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????
Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????
Duka akan