Showing 87001 words to 90000 words out of 325075 words
da kallo tamkar idanunta zasu zubo ?asa, Abdallah yay ?aramin tsaki yana barin wajen ya nufi ?akinsa. Har Nu'aymah ta cira ?afa itama zata bar wajen Adawiya ta dakatar da ita ta hanyar ri?o mata hannu. Juyawa tai tana kallonta fuska a ha?e sosai, "Malama sakeni". Nu'aymah ta fa?a a hasale.
"An?i a sakekin, idan kin isa kiyi duk abinda zakiyi. miya ha?aki da mijina?". Kallon tsantsar mamaki Nu'aymah kema Adawiya, sai dai kuma a fili saita saki lallausan murmushi da har ya bayyana ha?oranta. Tace, "Tunda kinsan mijinkine mizai hana shi kije ki tambayesa miya ha?ashi dani? Inaga kamar hakan zaifi birgewa a gareki shashasha kawai". Ta ?are maganar da fisge hannunta tai gaba tabar Adawiya da huci.
Hajjo data hango tahowar Nu'aymah saita saki labulen cikin ?akin ta zauna a bakin gado. A haka Nu'aymah ta shigo ta sameta. "Hajjaju kin tashi ashe?". Nu'aymah ta fa?a tamkar babu wani abu daya faru. Murmushi Hajjo tayi tana kallonta, "Ba dole na tashiba tunda kin gaza zuwa ki tadani mu wuce massallaci".
Kusa da ita ta zauna tana dariya, "Ho hajjonmu, yanzu kuma dana tadakin cazaki ban barki kin rintsa ba, gara mu maidake da ?warinki karsu Abba suga kin sake rugurgujewa".
Duka Hajjo ta kaima Nu'aymah da filo. Hakanne ya sakata tashi ta shige bayi da gudu tana dariya. Cike da tausayinta Hajjo ta sauke ajiyar zuciya, a ranta kuma tana ?ulla abubuwa da dama game da rayuwar Nu'aymahr
A falo kam Nu'aymah na shigewa Adawiya ta nufi ?akin Abdallah a fusace, babu ko sallama ta tura ?ofar ta shiga. Sai dai ganinta yay kawai a kansa kamar an jehota. Kallo ?aya yay mata ya ?auke kansa. Hakan ne ya sake hasala mata zuciya, sai ta fashe masa da kuka. "Yanzu Yah Ab abinda kakemin kana ganin adalcine? Ni dake matarka baka da lokacina amma kanada lokacin dawowa gida da wuri dan ka kasance da Aymah? Badan ALLAH yasa yau na shigo gidan da wuri ba bama zansan hakan na faruwaba tsakaninku. Shin wai da mi Nu'aymah ta fini ne? Wlhy sai ALLAH ya sakamin duk cin amanata da akeyi, kuma ni na gaji zan kira baba malam na fa?a masa komai tunda naga ita hajjo goyon baya take baku ma, ?ilama wataran a gabanta zaku shiga ?aki ku rufo bazata tankaba saboda tana tsoronku......"
Wani wawan mari ya sauke mata a fuska da saida taga stars na mata kaikawo, balle dama ga azumi. A take ta zube ?asa da sakin wata ?arar kuka data kai har kunnen Hajjo.
"Kai Abdillahi lafiya kuwa? Mike faruwa hakane nakejin kukan Adawiya?". Ta ?are maganar tata dai-dai lokacin da take ?arasowa cikin ?akin. Ganin Adawiya kwance ?asa dafe da kunatu ya saka hajjo zaro idanu, "Mikai mata Abdullahi?".
Cikin ?acin rai yace, "Hajjo barni da ?ar iskar nan kawai, wlhy tai wasa wataran saina karya ?asusuwanta a gidan nan tunda ita kamar dabba take".
"Ya isa haka". Hajjo ta fa?a tana ?ago Adawiya dake ?asa tana cigaba da sakin gunjin kuka. Saida ta zaunar da ita saman kujera sannan ta sake tambayar Abdallah miya faru?. Fa?a mata komai yayi amma banda tsayuwarsu da Nu'aymah, baisanma ita taji komaiba.
Cikin ?acin rai Hajjo tace, "Adawiya dama baki da wayo haka? Ita ?ar uwar takice kuma tazama abar kishi a gareki? Har kike jifansu da wannan mummunan lafazin ita da mijinki? Adawiya yaushe kika bari ?awayen banza suka canja miki tarbiyya ne? Har haka. To wlhy ki shiga hankalinki, idan kuma ba hakaba ni bazan ?auki wannan banzan halayen a cikin zuri'ata ba, saina ?atama kowa rai a cikinku har iyayen naku ni babu ruwana. Bandama iya shege kowa na fama da ibadar ALLAH a baki ke kina biyema she?an yana ?oraki akan dokin zuciya. To idan na sakejin makamancin wannan zancen lallai sai kinyi nadama shashasha kawai. Banda ?addara da yanzu ita wadda kike cin zarafin ba itace matsayin matar tasa ba".
Haka Hajjo taima Adawiya tas sannan ta fito ta barsu. Duk abinda akeyi Nu'aymah najinsu, sai dai ko tari bataiba balle a fahimci ta sani ?in. Daga ?arshema sukai shiri suka wuce massallaci, suda gidan kuwa sai anyi sallar asuba kuma.
Tun daga wanan ranar Adawiya ta shiga fishi da kowa a gidan. Daga gaisuwa bata sake tankama wani. Ahmad yamata nasiha harya gaji ya watsar da ita shima. Bayan kwana biyu da yay dai-dai da cikarsu kwanaki biyar da zuwa, ashirin kuma ga watan azumi Nu'aymah ta tattara inata-inata ta koma massallaci zaman ittiqafin.
Abdallah yaso hanata, sai dai Hajjo tace ya barta tai ibadarta yamafi zaman nata a gidan aita fitina. Badan yasoba ya ha?ura, dan yaso a wannan zaman suyi magana ta fahimta da Nu'aymahr ya samu ya lalla?a hajjo dasun koma a ?aura musu aure.
Bayan barin Nu'aymah gidan sai ga Adawiya ta saki jikinta, ashe dama Nu'aymahr ce natsalar rayuwarta. Babu wanda yace mata komai. Saima hajjo ce taima Abdallah magana akan su shirya shi da Adawiyan dan tare zasu wuce Najeriya ayi bikin salla. Kai tsaye Abdallah ya nuna cewar bazaije ba, sai dai Adawiya, dan shi bai manta ALLAH ya isan da mahaifiyarsa tai masa akan zuwan nasaba.
Balbalesa da masifa sosai hajjo tai dan ita batasan dalilinsa na bijirewarba. da taga dai ya tirje ?in saita kira baba malam ta fa?a masa komai. Shine ya kira Abdallahn cikin bada umarni ya sanar masa ya shirya suzo salla gida tunda suna samun hutu a wannan lokacin.
Abdallah ya shiga tsaka mai wuya sosai akan hakan, dan yasan dai umarnin mahaifiyarsa dana baba malam babu wanda yake da damar tsallakewa a ciki, dan duk sunada daraja da kima a idanunsa da rayuwarsa.
_________________________
*_NIGERIA_*
A kwanaki biyun nan abubuwa sun sake tsamari akan Yoohan, gaba ?aya neman birkicewa yake saboda rashin samun barci, tun daga jiya zuwa yau ya?i magana da kowa a gidan, yama kulle kansa a ?aki ya hanama kowa ganinsa. Momy tayi kukan tayi ro?on amma ya?i bu?ewa. Hakama su Gebrail sunyi nasu ?o?arin ya sharesu.
Amma saboda ?arfin hali da burinsa nason cika al?awari sai gashi a safiyar yau talata yayi shirin tafiya kano. Tunda safe ya bama Solomon umarnin fa?ama guards ?insa su tafi kano. Su kuma ya nema musu ticket guda uku. Solomon nason tambaya akan hakan yanajin tsoro, dan haka yaja bakinsa yay shiru yaje dai ya cika umarninsa
Kusan ?arfe hu?u na yamma sai gashi ya sauka ?asa cikin shigarsa ta suit blue mai haske. sun masa bala'in ?yau duk da yana a yanayin da a kallo ?aya zaka fahimci akwai damuwa tattare da shi.
Momy ce kawai zaune a falon sai Victoria da Abraham. Cikin girmamawa a garesa yaran suka shiga gaishesa. Hannu ya ?aga musu kawai tare da ?arasowa inda suke duk ya shafa kansu batare da yayi magana ba..
Ya maida dubansa ga Momy da idanunta suka kumbura saboda kuka, ?auke kanta tayi ita a dole fushi take da shi. Baice komaiba ya ?araso inda take ya tsaya a gabanta tare da ri?e kunnuwansa da hannayensa alamar ban ha?uri.
Bata iya dogon fushi da Yoohan ?inta. Dan haka tai murmushi tare da mi?ewa ta rungumesa. Yau dai ya daure bai tureta ba, sai da ta gaji dan kanta ta sakesa sannan, ta amshi tie ?in hannunsa ta ?aura masa tana fa?in, "My Boy nikam yaushe zaka fara saka necktie da kanka?".
Bai bata amsaba, sai dai ya sake ?ata fuska alamar shagwa?a. Da ?ar dariyarta ta shafa masa kwantaccen sajensa da yasha gyara yau, ya kama hannun nata ya sumbata ka?an.
"Ina zakaje ma wai?". Ta tambaya tana tsatstsaresa da idanunta manya. Da ?yar ya bu?e baki wajen bata amsa da "Kano". "Kano!! kuma Yoohan? Mizakayo a kano kaida kake cikin wannan halin? Badai aiki ba?". Kansa ya girgiza mata, batare daya bata wani ?arin bayani ba yace mata, "Bye" yana nufar ?ofa.
Saurin binsa tai tana kira, amma sai ya?i tsayawa, saida ta ha?a da?an gudu ta cimmasa, duk da kuwa tafiyarma ba wani sauri yakeba saboda rashin ?warin jikinsa. Yanda ta ri?osanne ya sakashi waigawa ya kalleta. Tace, "Ina tambayarka mizakayo acan amma ka taho baka kulaniba Yoohan".
Kansa dake faman masa ciwo ya dafe ka?an, kafin cike da ?osawa yace, "An gayyaceni ne" danshi baison yin ?arya a rayuwarsa, kamar yanda ya tsani kuma sa?a al?awari. Yana gama fa?a ya zare hannunsa zai juya ta kuma ri?ewa. Yanzunkam bai juyoba sai da yaja wasu sakanni. Muryarta da damuwa ta zagayo gabansa tana magana. Amma maimakon ya bata amsa sai ya saka yatsansa akan baki yace "Shiii!!!".
Shirun kuwa tayi tana kallonsa, ya ?aura yatsunsa saman baki yay mata alamar *_Smile_* kamar yanda ya saba mata aduk sanda ya ganta a damuwa tun yana yaro. Duk da batason yin hakan saita murmusa. Yay mata jinjina yana ?an lumshe idanunsa dake a kumbure sosai.
Tanaji tana gani ya shiga mota driver ya jasu shi da Solomon suka bar gidan, gashi Papa bayama ?asar jiya sukai tafiya shi da Uncle Zamani.
¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï
Airport driver ya kaisu. inda acan suka ha?u da Manager Hamza Ibrahim yana jiransu. Sun gaisa cikin mutunta juna Hamza na mamakin ganin Yoohan ?in a ?unci fiye da waccan ranar. Ga idanunsa da fatarsu tai jajur hakama farar fuskarsa. Haka kawai yaji a ransa akwai abinda ke damun Yoohan ?in. amma sai baiyi magana ba suka nufi ciki.
?arfe biyar da rabi jirginsu yabar Abuja zuwa birnin dabo kodami kazo mun fika????.
Kamar yanda Yoohan ya iske Guards ?insa na jiransa haka suka iske motoci biyu na tarbarsu kuma. Hakan ya sai ya sake birge Yoohan matu?a, dan haka bai shiga tasa motarba ya shiga wadda aka aiko musu, Guards ?insa kuma suka bisu a baya.............?
[4/7, 3:03 PM] +234 901 860 0202: No. 24
...............Baba malam daketa kaikawo na ?o?arin ganin komai ya kammala yanda yake bu?ata ya nufi sashen nasa a karo na babu adadi. Yanda ya hana kansa sakat akan tarbar ba?onsa haka ya hana Umm sakat itama, dan baiwar ALLAH nan tun ?arfe biyun ran take a kan ?afafunta tana hidima. Sau?inta ma Addah ta shigo tana taimaka mata, ga kuma mai aikinta.
Omar ne biye da shi, dama yafi sha?uwa da shi a samarin yaran gidan fiye da kowa, duk da dai ada kam sunfi sha?uwa da Abdallah, amma daga baya da Omar ?in yafi Abdallah zaman kano sai sha?uwarsu ta zarce ta tsakaninsa da Abdallah ma. Dan shi Omar yarone mai tsananin ?wazo da biyya ga iyayen nasa, sannan baba malam shine babban malaminsa na addini fiye da kowa, shiyyasa koda yaushe yana kano bai cika son zaman Abuja ba shi.
Kai tsaye kitchen suka nufa, inda suka iske Umm da Addah suma dai kamar su tsinke nasu ran, dan tare suke aikin daya rage ?in. Bayan Baba malam yay sallama baima bari an amsa masaba yace, "Umm Muhammad yaya kun kammala?".
?agowa Umm tai ta?an kalli mijin nata, sai kuma ta maida akan aikin gabanta tana cewa, "Abban Nu'aymah wlhy nikam dai zakama sake rikitamu gaba ?aya, insha ALLAH muna gab da kammalawar, dama zuwa kai kayi wanka dan magrib ta gabato".
Murmushi shimfi?e a fuskarsa ya ?araso yana amsar abinda take tace lemon mangwaron daya rage su ha?a. "Ke dai kawo na taimaka miki ki kammala kawai, dan yanzu haka an wuce ?akkosu fa".
Dariya Umm da Addah da Omar sukai, ya ?araso wajen baba malam ?in yana fa?in, "Abba kawo ni nayi basai kayi da kanka ba. Dan nikam yau namafi kowa zumi?in son ganin wannan ba?o mai daraja a wajenku Abba, dan naga gaba ?aya hankalinku na kan son ganin an ?yautata masa, yau kota abincin bu?a bakinmu bakwayi sai na ba?o".
"Kace ido ka saka mana? Hakama malam ?arami (baban yaron Addah) sai da ya gama ?orafi kafin ya wuce airport ?akkosu". Ita dai Umm da Addah dariya sukayi musu kawai, ta matso suka ?arasa ha?a komai ita da baba malam ?in. yayinda Omar da Addah kuma suke ?orawa tray. Omar ne ya ?arasa kwashewa ya kai komai can sashen kakansu inda za'a sauke ba?on. Hakan kawai ya isa kasan an daratta ba?on sosai, dan duk ba?on da su Baba malam zasu kai da shigo dashi cikin gidansu to lallai ya isa kuwa.
Sai da yaga an fita da komai sannan ya sauke ajiyar zuciya, tare da ficewa domin aiki da shawarar Umm ta farko. Cike da gulma irin ta aminai Umm da Addah suka kalli juna, sai sukai murmushi kawai dan Baba malam ?inne ya basu dariya.
Ficewa sukai a tare suma zuwa sashen da aka shirya abincin, suka ?ara gyara komai tare da saka turaren wuta da kuma Air Fresheners masu ?amshi. Kamar Umm ta sani har zasu fito saita yanke shawarar fita da kaskon turaren, acewarta kar ko a ba?in asamu mai Asthma ya cutu. Ta ?an ?aga labulen Windows ?in ka?an haya?in turaren ya ragu sosai. Cikin sa'a ma sai gashi Omar yaje ya tada Genretor. Ac suka kunna tare da sake duba komai suka tabbatar yayi dai-dai sannan kowa ya nufi part ?insa Umm nama Addah godiya.
Dan tasan badan itaba da aikin baiyi sauriba sam. Mama amaryar Abba Musbahu kuwa dama ita sai a hankali ce, San jikinta bai bari tama kula da sashenta ba balle taimakon wani kuma, komai ?an aikine keyi, kodan taga mijin ba mazauni bane oho.
Motocin na shigowa anguwar ana fara kiraye-kirayen sallar magriba. Yoohan na kwance shiru a jikin kujera idanunsa a lumshe. Baisan inda ake shiga da fita ba har saida motocin suka tsaya a ?ofar katafaren gate ?in. Hakan sai yayi dai-dai da fitowar baba malam da Abban su Adawiya, sai Malam ?arami da Omar da sauran samarin gidan da yara amma iya mazan kawai.
Duk da yanda guards ?in Yoohan suka firfito suka zagaye motar da yake a ciki hakan bai saka fuskokin su baba malam sauyawa daga fara'ar dake tattare da suba. Akan idonsu Hamza Ibrahim ya fita. Kafin Yoohan da Solomon ya bu?emawa shima.
Shima a gaban idanun nasu ya fito, bayan ?afarsa kuma da sar?ar Cross ?insa suka fara cin karo kafin cinkusashshiyar fuskarsa. Abinda zai baka mamaki a tare su baba malam sukayo caa a kansu. Cikin ?ya?y?yawan tsari na masu ilimi da baiwar hikima suka tarbesu. Wani iri Yoohan yaji a ransa shima duk da kuwa dama ya fahimci masu gayyatar tasa musulmai ne, amma sai ya dake ya basar.
Duk yanda yaketa faman musu shan ?amshi da cika da batsewa babu wanda ya canja yanayin nasa, saima sannu da zuwa da suka shiga jera musu tare da basu hannaye suna musabaha har guards ?in. Kafin baba malam ya bama Malam ?arami da Omar damar shiga da Yoohan ?in ciki. Danshi Hamza Ibrahim ya bu?aci a inda zaiyi alwalane kai tsaye.
Yoohan dai baiyi musu ba yabi bayan su Omar, sai dai idonsa da zuciyarsa nakan hasaso masa a inda ya ta?a sanin fuskar baba malam a rayuwarsa. Guards ?inma bin bayansu sukai. Omar zaiyi magana baba malam ya girgiza masa kai alamar ya barsu.
Tun a farkon shigowa gidan Yoohan yasan masu gidan sun wuce raini, dan babu abinda nasu gidan zai nuna masa sai dai kayan ?awa da ?yale-?yale, nasu baba malam ma yafi nadu girma sosai. A haka su Omar suka kaisa har falon, guards ?insa biye da dasu kamar wasu jela ko suna ganin za'a cutama Yoohan ?inne oho musu. Sai da sukaga ya zauna suka ajiye masa ruwa da lemo kozai bu?ata sannan sukai masa sallama suka fito, duk da basuji ya amsa musu da ?yau ba. Dan Solomon ma tunda ya fahimci inda suka kawo kansu sai takaicin ogan nasa da bu?a??en ra'ayinsa ya shiga masa zafi a rai. Dolene yay saurin sanarma Madam Chioma kafin a bama Boss ?in nasu wani abin yaci a tsafesa.
Yana cikin shawara da zuciyarsa ta yanda zai silalo daga cikin falon ya kira madam ?insu sai ga sallamar su Baba malam, da alama ana idar da sallar magrib basu zaunaba suka shigo gidan. Aiko takaici kamar ya kar Solomon, amma duk da haka saida yayi dabarar turama Momy text message ko za'a dace wayar na a hannunta ta gani.
Koda suka shigo Yoohan na'a zaune yanda yake baiko motsaba, sai dai yana binsu da kallo ne ta ?asa ido. Abban Adawiya da suka ta?a