Showing 279001 words to 282000 words out of 325075 words

Chapter 94 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29123

na atanfa da t-shirt mai ?arancin girma. Sai dai ta ?ara wa?anda take sawa a da kafin samuwar cikin da girmansa. plate ne a cinyar tata shima gab da cikinta ?auke da green apples a kai, sai ?aya dake a hannunta da ?aramar wu?a tana yanka tana ci a hankali.
Sassanyan numfashi ya sauke da lumshe idanu ya sake bu?ewa a kanta. sai kuma ya shiga takowa har inda take dan ganin ta?i daina kallonsa. Gefenta ya zauna daf da ?ora hannunsa akan fuskarta ya juyar mata da kanta ta koma kallon lap-top ?in.
Cike da sanyin murya yace, "K da kike ?aukar Lecture miye na zubamin ido kuma?".
Uffan batace masa ba, sai iska data furzar daga bakinta. Itama da sanyin muryar tace, "Lafiya naga ka dawo da wuri haka?".
Ajiyar zuciya ya sauke a karo na biyu, ya dora kansa a kafa?arta tare da kamo hannunta dake ri?e da yankan apple ?in ya kai bakinsa. Bata musaba ta saka masa itama. Sai da ya tauna ya ha?iye yana kallon lecturer ?in shima sannan yace, "thanks you Sweet girl" ya ?are maganar da kaima kuncinta sumbata, ya kuma tura hannunsa a rigarta yana shafa cikinta cike da ?warewar likitanci.
Kamar koda yaushe kuwa sai ga cikin na motsi. Dan duk sanda zai masa irin wannan shafar sai kaji ya motsa. Har mita Aymah ke masa akan ita miyasa cikin baya mata haka sai idan yaso motsinsa da kansa yakeyi. Kokuma idan tanajin matsanancin yunwa nanma yana motsawa.
A hankali yace, "Sheikh ?in Daddy ga daddy ya dawo gida. Ina fatan bakai fushi da canjawarsa ba?. kana kuma cikin ?oshin lafiya zinarin zuciyata".
Fuska Aymah ta?an ta?e tana ?auke kanta ta maida ga lecture ?in da sam yanzu ma ba fahinta takeba ita.
"Jealous ?in ya motsane madam?". Yoohan ya fa?a a cikin kunnenta cike da neman tsokana.
Hannu tasa ta ture nasa da zuba masa harara. "Tunda Jealous ?in nakeyi mizai hana a ciremin na huta". Gimtse murmushin dake neman kufce masa yayi yana ta?e baki da ?age gira ?aya sama. "Silly girl, ai idan kinga mun barki sai mun cika watanni tara da kwanaki tara ciff insha ALLAH. magajin Uncle na zuwa kuma wata ?wallon zata kuma fa?awa rag....."
Lap-top ?in da take shirin saukewa a jikinta yay azamar ri?ewa dan yasan sotake ta gudu. "Oh am sorry sweetheart wasa nake fa ni. Mu mun isa miki gadara bayan yanzu kece boss ?in gidanma, kammu bisa wuya Mie-mie. Nifa namazo miki da wani albishirne mai da?i".
Batare data tanka masa ba ta sake yun?urawa zata tashi. "ALLAH seriously Sweet girl".
Ajiyar zuciya ta?an sauke ka?an. Sai kuma ta kallesa, "To ka bari naje na kawo maka ruwa".
"Okay harda abinci. dan yunwa nakeji".
"Ai baka da kaso anan gidan malam".
Tai maganar tana shigewa kitchen. Murmushi yayi mai fa?i daya jima ba'a gani a fuskarsaba. Ya jingina da kujera yana furzar da zazzfar iska. Shi ka?ai yasan mi yakeji a ransa. Yana daurewa ne kawai saboda fahimtar halin da yake ciki na ?untata ta itama. Shikuma bayason haka kodan yanayin da take ciki........
"Uhyimmm! An tafi tunanin ko?".
Saurin dubanta yayi yana ?o?arin canja yanayin fuskarsa, Aymah da idanunta suka cika da ?walla ta ajiye tiren data ?oro masa plate ?in abinci da ruwa sai kofin lemo ?aya. Saurin ri?ota yayi ganin zata gudu. Ya ?orata a cinyarsa duk da tanata ?o?arin ?wace kanta ga hawayen sun fara sauka a kumatu da gudu. Matseta yay da ?yau ya lumshe idanunsa, tun tanason ?watar jikinta harta ha?ura tayi luf a jikinsa tana shashshekar kuka da sauke ajiyar zuciya.
"Am sorry Zeeynab. I'm very sorry. Nasan tabbas ina ?untata rayuwarki da laifin da banakiba. Nima bada son raina bane, ina cikin tashin hankaline mai tsananin ru?ani Nu'aymah......."
"Shine ka za?i ka ?oye min saboda ni banda matsayin sanin sirrinka? Amma ni har sirrin daya kasance na family ?ina mun baka dama ka shiga tsundum saboda baka darajarka, sai ni da......."
"Shiii!!!. Wlhy bani da wani sirri a duniyar nan sai ke Nu'aymah. Da ana bu?e zuciya ma'abocin kallo yaga sirrin dake cikinta dana bu?e miki tawa kin gani Zeeynab. Da kinsan wacece ke a gareni da dukkanin tasirin da kikayi a rayuwata da bazaki ta?a yin tunani irin wannan ba. Amma kiyi ha?uri nasan da laifina. Laifina shine ?oye miki damuwata. Bana ?oye miki dan baki isa bane, na ?oye miki ne saboda al'amarine mai girma a gareni. Ki tayani da addu'a ke dai kinji. Ki kuma cire komai a ranki, ki yarda ke ta dabbance ga mijinki. Bakiga duk yanda kika rameba, hakan na tayarmin da hankali....."
"Yah Yoohan amma ai......"
"Oh my Cutie karkice komai Please. Yanzu dai mu ajiye wancan batun bashi da wani muhimmancin cigaba da hargitsa mana rayuwa da tunani ok?. Ina miki albishirin zuwa Nigeria gobe insha ALLAHU ".
Duk da kewar ahalinta da ?okin son zuwa garesu da takeyi sai taji kamar tafiyar bata lafiya bace, musamman da tasan yace itada 9ja ?in sai ta shiga watan haihuwa lokacin sun sami hutun ?arshen shekara da Christmas.......
"Tunani again baby?".
Numfashi ta kawo tana kallonsa. Kallo irin na tambayoyin da baki ya gaza furtawa.
"To ko a fasa nayi tafiyata kawai ni ka?ai".
Da sauri ta girgiza masa kanta alamar a'a. Ya ?an murmusa da sumbatar la??anta. "Karfa kisa komai a ranki surprise ne kawai".
Duk da bata yarda da shiba haka ta shanye abinta a rai. Sai dai ta masa maganar karatunta yace babu damuwa ko suna a can zata cigaba da ?aukar lectures ta online ?in. Daga haka suka fara shiri a ranar, duk da daima bawani sun ha?a kaya bane dan bama zasu tafi da kayanba tunda akwaisu acan babu bu?atar hakan.
A dai ranar duk wani abu da zai iya lalacewa sun fitar da shi. Suka ?an fita shopping na abinda zata iya bu?ata saboda lalurarta. Ranta cike yake da ?okin Isa ga ahalinta bayan rabuwa da su tsawon watanni tara. A gefe kuma cike take da fargabar sakamakon abinda zataje ta tarar.

*_WASHE GARI_*

Washe gari safiyar juma'a jirgin su Nu'aymah ya sauka a ?asar haihuwarsu batare da kowa yasan da zuwan nasuba. Sai da taimakon Yoohan ta sakko a jirgin saboda ?afafunta da sukai mata tsami da kumburi. Sai faman ta?e fuska take kamar zatai kuka. Shi kam dai ga tausayinta ga dariya na cinsa a rai. a zuciya ya ayyana, 'Abufa yazo ga ma'iya'.
Bayan shigarsu texi taji yace a kaisu hotel. Ai babu shiri ta kallesa, "Hotel kuma Yah Yoohan? Gidan papa ?in fa?".
Cikin jin zafin dake taso masa a rai ya girgiza mata kansa. "Zamuje, amma yanzu muje ki huta ko?".
Hankalinta tashe akan tunawa da hoton nan da sauri tace, "A'a ni dai gaskiya inba gidan papa ba sai dai ka sani a motar kano na wuce. Yaya gamu da gidan iyaye mu kama ra?e-ra?en hotel kamar wasu marasa galihu. Kayi ha?uri gaskiya ni dai bazanje hotel ba".
Duk yanda yaso lallashinta akan suje hotel ?in dan shi bayason zuwa gidansu. Ko sha'awar kallon fuskar Momy bayayi sam. Amma Nu'aymah ta tubure duk da bawai dan tanason zama gidan bane itama. Tana son sujene saboda hoton nan. Gara suje tun a yau ta ?auka kafin papa ya farga suna ?asar tunda ya bada kwangilar kasheta. Daga lokacin da matsaloli suka fara kuma ai maganar hoto sai tasha ruwa.
Badan Yoohan yaso ba dole yasa mai taxi ?aukar hanyar anguwarsu dan kuka Aymah ta sanya masa rirus babuko kunya. Sam baya bu?atar damuwarta a irin wannan lokacin. Dan yama fahimci jininta yayi sama saboda wannan tafiyar mai nisa da sukayo. Daga haka kuwa bai ?ara maganaba, sai dai ya sakata a jikinsa kawai yana shafa bayanta alamar lallashi. Saiko faman cijar lip ?insa na ?asa yake da ?o?arin danne abinda ke taso masa a rai.
Har ciki mai taxi ?in ya shiga dasu, koda maigadi ya le?i yaga Yoohan sai ya koma da sauri ya bu?e gate ?in ransa fal murnar ganinsu. Da taimakonsa Aymah ta fito yanzunma. yayinda gaba ?aya Guards ?in gidan suka rufu musu a ka suna kwasar gaisuwa bakin kowa a washe na murnar ganinsu. Zuciya kam fal gulma ganin Nu'aymah da ciki. Musamman ma Solomon daketa faman zare ido.
Solomon ?inne ya amshi ?an kayansu dake a trolly ?aya sai lap-top bag ?in Yoohan. handbag ?in Aymah kuwa tana a hannun Yoohan ?in ?ayan hannunsa kuma ri?e da nata.
Da Gebrail suka fara cin karo zaune a dining yana lunch ?in daya makara baiyiba. Idonsa na sauka a kansu kuwa ya sar?e da abinci har sai da Blessing ta fito daga kitchen a guje dan jin mahaukacin tarin da yakeyi. Ko kallon inda yake kuwa Yoohan da Aymah basuyiba.
Wani bala'in waro idanu Blessing tayi tare da daka tsalle gefe hannayenta duka a saman kai tace, "Heeyyy!!! Ahhhhhh!! Emiiii!!!".
Dariya ta bama Aymah sosai. Hakan ya sakata darawar kuwa. Yoohan kuwa daya zaunar da ita a kujera ko kallon Blessing ?in baiyiba. Sai dur?usawa yay a gabanta ya kama ?afafunta ya zare takalman da take sanye da su masu taushi, amma saboda tsabar hawa da ?afar tayi sun manne mata har sunyi mata sayi. Matsa mata ?afar ya farayi a sannu-sannu ransa fal tausayinta duk da yasan bawai wata matsala bane. Yanayine kawai da wasu masu cikin kan shiga.
Ihun Blessing ne ya fito da Joy da Miracle daga ?aki suma a guje. Sai ga Victoria dasu Favour da har yanzu su suna abuja basu koma ?auye ba. Makaranta ma Yoohan yace zai duba musu anan, sai kuma aka samu akasi wancan matsalar ta faru Yoohan yabar ?asar babu shiri.
Da gudun bala'i su Destiny sukayo kan Nu'aymah da itama take kallonsu fuskanta washe da dariyar Blessing data gama kwasa...
A wani zabure Yoohan ya mi?e yana dakatar dasu, amma ina sukam idonsu ya rufe yau saboda farin cikin ganin auntynsu da kullum suke nacin son dawowarta. Gata kuma da ciki zata haifa musu baby a gida.
Goshi kawai Yoohan ya dafe yana fa?in, "Oh GOD!".
Itako Aymah da dama ba hankalinne ya gama isartaba oho. Tuni ta tarbi ?an yaranta da suka nuna mata ?auna zalla a gidan babu algus. Sai da Yoohan yaga lamarin nasu bana ?are bane yasa hannu ya fara ?agasu ?ai-?ai daga kan Nu'aymahr.

Ihun su Destiny ne ya farkar da mama debora a barcin da takeyi. Ta fito jikinta na rawa dan ta ?auka wani abunne ya faru da yaran. Ka?an ya rage bata bangaje su Joy da Miracle tai suman gigitaba ta tarota. Kota kansu batabiba ta fara sauka a benen da gudu zane a hannu.
Wani bala'in waro ido tayi akan Nu'aymah tana fa?in, "Jesus John matarka ne da ciki? Cikin jikana ?anka. Kaima zaka haifi yaronka John ?". Sai kuma ta nufeta cike da Sassarfa. A take annurin fuskar Aymah ya ?ace ?at, hakama Yoohan kallon kakar tasa yake yaga mizatayi. A mamakin kowa sai mama debora ta fashe da kuka tana rungume Nu'aymah. Sai kuma ta dur?usa ?asa ta ?aura hannunta akan cikin Aymah tana sambatun zance da yare wanda sam Aymah ba ji takeba. Sai dai yanda taga Yoohan ya langa?e kai yana kallon kakar tasu fuskarsa da murmushi ya sata fahimtar ba mummunan abu mama debora ke fa?i akan gudan jinin nasu ba. Tabbas duk wanda ya kalli mama debora a wannan lokacin yasan farin cikine na gaske tattare da ita. Ba komai yay silarsaba kuma sai cikin jikin Nu'aymah ?in. Dan kanta batasan yaya akai ?aunar cikin ta saukar mata ba lokaci ?aya tare da Nu'aymahn kanta. (Nace ?arfin addu'a ce mama debora).
Tana faman sharar ?walla ta kamo hannun Yoohan ta zaunar a kusa da Nu'aymah. Ta ha?a hannayensu cikin na juna sannan tai Kneeling a gabansu tare da rufe idanunta duka ta ?aga hannaye sama ta fara raira wa?ar addu'a da yare tana hawaye, ganin hakan yasa su Victoria ma dur?usawa tare da Blessing suka fara tayata suma duk idanu a rufe.
Cike da zaro idanu Nu'aymah ta kalli Yoohan kamar zatai kuka. Dariya taso kufce masa. Amma sai ya gimtse yay murmushi kawai. A cikin kunnenta yace, "Karki damu addu'ar kariya sukema baby dakema ALLAH ya saukeki lafiya cikin ?oshin lafiya".
Duk da tasan su ba musulmai bane ta ?anji sanyi a ranta tunda ba wani tsafi baneba dai. sai kawai ta ?ora kanta a gefen hannunsa tana mai addu'a a ranta itama ALLAH yasa sunada rabon musulinci. Dan tabbas yau taji gaba ?aya haushin mama debora da takeji ya kwaranye. Dama ance mai ?a wawa.
Bayan sun gama addu'arsu sun zauna, mama debora nata wani ji da Nu'aymah. Ita dai abin har dariya yake bata. Hakam Yoohan dariya kakar tasa ke basa da gaske. Ta dungure masa kai tana fa?in, "Mara mutunci. kasan matarka nada ciki baka ta?a fa?ama kowaba. Yarinyata watansa nawa?". Ta maida maganar kan Nu'aymah bayan ta zubama Yoohan dake kumbura mata fuska saboda mangarar masa ?eya da tayi harara.
Haka kawai sai Aymah taji nauyin fa?a. Sai Yoohan ?inne ya bata amsa. Sai kawai ta tashi ta kama rawa tana wa?ar yarensu irinta tsoffi.
A wannan yanayin papa da Madam Chioma da basa gidan suka shigo suka samesu. Gaban Nu'aymah yay mummunan fa?uwa. Da sauri ta shiga karanto addu'a a cikin ranta. Sannan ta yun?ura ta mi?e kamar yanda taga Yoohan ya mi?e fuskarsa a tsuke saboda ganin Momy.
Da wani irin kallo papa kebin Nu'aymah da cikinta. madam Chioma kam Yoohan take kallo kamar wata tsohuwar mayya. Dan sam hankalinta bai kai kan Aymah ba tukkunna.
Cike da farin ciki Mama debora ta nufi papa tana rera wa?arta da ke nuna tana a tsantsar farin ciki na ha?i?a, hannunsa ta kamo ta nufi inda Nu'aymah take. Da sauri Madam Chioma takai dubanta inda mama debora ta nufa da Papa. Aiki idanunta sukai mata mummunan gani. Da tsanin gigita ta furta, "What??! Impossible!. Na rantse da ALLAH impossible!!!".
A kusan tare kowa dake a falon ya kalleta, sai kawai ganinta sukai a ?asa ta sulale sumammiya.
A guje su Destiny sukayi kanta da papa. Yoohan kam fuska ya kauda gefe cike da ?unar zuciya. Nu'aymah da tasan ba sonta madam Chioma keyiba dama can sai bata ?auki hakan komaiba face ?iyayyar da take nuna mata dama can.
Mama debora kam wani irin ta?e baki tayi da fa?in, "Aiko Chioma zaki mutune a haifamin jikana duniya. Kujimin yarinya da ba?in halin ba?in ciki. Ke sanda kika haifi John nayi miki hassada ne? Bandama inada zuciya me ?yau ai saina saka ayar tambaya a kanki dan Yoohana baya kama dake, nayi shirune kawai dan yana kama da yarona, amma kekam ai kamarma ba ?anki ba. Sai shi yanzu zaki ba?in ciki matarsa zata haifa masa ?a. Kema sai kinji abinda naji na rabani da ?ana da kikayi......"
A guje Blessing ta kawo ruwa aka yayyafama Madam Chioma. Tako fasa wata razananniyar ?ara da mi?ewa zaune tana nuna Nu'aymah. "Wannan ba cikin yarona bane, kufitarmin da ashawo ?innan a gida, na rantse da ALLAH john wannan ba cikinka baneba. Dan hakan bazata ta?a kaswncewaba. Idan baku fitarmin da ita a gidaba zan kasheta. Ku kaita can ta nemo uban cikinta dan bana John bane. Darling narsantse damfararmu yarinyar nan zatayi cikin nan bana John bane. Sun tsafemin yaro sun rabani da shi. Yanzu zasu manna masa cikin kuma da ba nasab......."
Yanda take surutan zaka ?auka bata da hankalima sam. Yoohan da takaici ya kume yaja hannun Nu'aymah suka haye sama abinsu batare da yayi ko tariba. Mama debora ma wani dariya da ihu ta sanya tana tafa hannaye. "Chioma kishi da matar ?anki yasa kin haukace gaskiya. Tunda ni kakar John na yarda cikinsa ne koke da goshpower kuka?i yarda nasan kishi ne. Yanda nasha ba?in cikin rabani da ?ana da kikayi kema sai kinsha fiye da wannan ba?in cikin na rabuwa da John. Wuuuuuuu!!! She she Shem!!! Wuuuuuu!!!! Hhhhhhhh!!!! Anji kunya uwa mai kishi da matar yaronta!!!!".

Hankalin papa ya sake tashi da abinda mahaifiyarsa keyi. Dan har cikin zuciya shima a ki?imen yake game dayin tozali da wannan cikin da ko a labari bai ta?a sanin akwaishi ba. Lallai wannan shine lokacin daya kamata a fara ya?in na gaske. Dan tura takai bango anzo dai-dai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login