Showing 297001 words to 300000 words out of 325075 words
a du?e tamkar munafuki. Harga ALLAH da yawan mutanen dake falonma sai yanzu sukasan da zamansa a falon. Hajjo ta sake gyara zamanta tana duban kowa.
"Nasan wasu zasuce miyasa duk nasan wannan amma na ?oye matsayina na mahaifiya ga wa?an nan yara su duka?. Amsarku itace duk da ni mahaifiyace a garesu fitowa da lamarin kai tsaye dasa sabuwar fitinace da zatafi wadda muke ciki girmama. Dan inhar da tun a wancan lokacin na fiddo komai zasu kare kansu akan ba haka bane, su jefa zuciyarmu a ru?ani mu duka kokuma su canja salo, ko komai ya ?aci duniya tasan halin da muke a ciki ma?iyanmu dake a waje su sami ?ofar yin kutse cikin wannan zuri'a su ?arasa ?arar da sauran abinda ya rage daga garemu. ?ya?y?yawar rayuwar da aka gina tsahon shekaru zata wargatse ta lalace kowa ya fita a hayyacinsa. Idan hakan ta kasance banci riba ba. Sannan wahalar da malam ya sha akan son gina zuri'arsa baici riba ba kenan shima. Dukansu ni na haifesu, tun a ?uruciya nasan halin kowannensu. Dama can Lurwanu hatsabibine tun yana ?an?aninsa, a cikin ?an uwan nan nasa babu wanda baisha wahalarsaba. Kaifin addu'a ne kawai ya ladabtar da shi, sai kuma kawaici da iya zama da su da ?an uwansu yayi. Na yarda inhar ka samu ?ya?y?yawar tushiya a cikin yabanyarka da izinin ALLAH zaka azurta da ?ya?y?yawar albarka. Kasancewar ?an malam ?a nagari, mai ha?uri da kawaici, mai juriya da ri?e girmansa matsayin babba ga ?an uwansa shine ya taimaki wannan zuri'a da kaiwa haka batare da mutanen waje sunyi tunanin samun ?arakar shigowa cikinmu su wargazamuba. ALLAH yayima ?an malam baiwa da ?yautar abubuwa da yawa. Ilimi, hankali, dattako, dukiya, sanin ya kamata, nasaba. Sai dai hakan ba yana nufin zai more rayuwarsa ?ari bisa ?ari ba tunda ya ha?a komai. Shiyyasa ALLAH ya jarabcesa da atsabibancin Lurwanu dana matar ?an uwansa Mustapha. Suka dinga wajiga rayuwarsa saboda UBANGIJI ya gwada ?arfin imaninsa. Koni da nake mahaifiya a garesa inajin sha'awar koyi da halayensa na ha?uri da juriya duk da zuciyarsa na ?onuwa shi da matarsa da ?a?ansu. Wannan kawaicin da uziri shine ya kaimu ga matakin nasarar da a yau gashi su da sukecin dunduniyar sane a gabanmu suna fa?in tsiyatakun da suka aikata da bakinsu, miyafi wannan nasarar da?i ga bawa kuwa?".
Abban Adawiya ya share hawaye da fadin, "Babu inna, wlhy babu makamancin wannan nasara kuwa, dan hakan yana nuna mana duk mai ha?uri da tsayawa akan gaskiya, da adalci gana ?asa da shi, ma'abocin bautar UBANGIJI, ALLAH bazai ta?a ta?ar da shi ba, ALLAH bazai ta?a ?as?antar da shi ba. ALLAH bazai ta?a wula?anta rayuwarsa a hannun azzalumai ba. Ni shaidane akan hakan, dan Lurwan yaso jan ra'ayina sosai akan lamarin Yaya, kullum zancensa shine Yaya cutarmu yake a ?oye. wai tayayama za'ai ace a raba mana gado tare, amma yazo ya fimu komai. Yafi kowa kaso mai tsoka a duka kamfanonin mu. Ga wasu harkoki da yakeyi kuma a gefe masu bala'in bashi ku?i. Sannan kuma wai ai muduka munada ilimin addini amma tayaya za'ace kowa yafi sonsa da ?aunarsa dajin maganarsa. Hatta mahaifiyarmu sai abinda Yaya yace takeyi a gidannan. Acewarsa wai Yaya ya asirce kowane kawai amma yake fakewa da malanta. Da farko na fara bin ra'ayinsa. Sai dai ba'ai nisaba ALLAH ya soni da rahamarsa ya fargar dani, danni dai ban ta?a ganin wani abu sa?anin ?yautatawa ga yaya ba. Da ku?insa na gado ya tsaya mana mukai karatu duk da kuwa muma muna dasu. Da ku?insa na gado ya dinga mana hidimar rayuwa tamkar mahaifi. Idan mukai kuka shima sai kaga ?walla a idanunsa. Idan mukai ciwo shima sai kaga ra?a?in a fuskarsa. Idan mukai dariya sai kuga tashi fuskar fa?a?e da murmushi mai tsada. Shine ya nuna mana hanyar tashi mu nema na kanmu, dan shine ya fara shan wahalar kafa dukkan kasuwancin da ayanzu sune suke ri?e da duk wani motsinmu. Shine ya tsaya akanmu mukai karatu tu?uri bayan ya tattare martabar mahaifinmu ya ri?e mana bai bada ?ofar da zamuyi sakacin da zata kufce mana ba. To miyasa son zuciya zaisa zamuyi sakaci ya sargafe tunaninmu?. Hakan yasani janye jikina daga wannan mummunar a ?idar naita istigifari akan zargin da aka sakani nai masa babu gaira babu dalili. Ashe ya koma sun ?ulle da matata suna cutama yaya da zuri'arsa da basujiba basu ganiba. Minene laifin wa?an nan ?ananun yaran da basuma gama sanin rayuwarba balle da?inta. Basai nace komaiba, dan Fauza azabarma da kike ciki ta isheki. kai ko Lurwanu ka jira naka sakamakon kaima, dan duk wanda yaci zalin gwani rabbi zai saka masa da alkairi a duniya ko a lahira".
Abba Musbahu yace, "Tabbas haka zancenka yake Yaya Mustapha. Dan koni ma yaso jan ra'ayina. Sai dai fa ka sanni ni, a zuwan farko na shata masa layi duk da kasancewar sa yayana. Shine dalilin da yasa zama waje ?aya a Lagos ya nema gagararmu sai da yabi ya lalla?a yaya malam ta ?ar?ashin ?asa aka maidasa Abuja aka bu?e masa company wanda ALLAH ka?ai yasan irin ?arnar da yake a cikinsa shi da abokan aikin nasa. Domin a duk lissafin ?arshen shekara idan mukayi sai mun tsamo yawan cuwa-cuwa da akai da ku?a?en company. Shi Yaya cayake daga ma'aikatanne. Niko nasan Yaya Rudwan ne dama wlhy. Nayi shiarune kawai dan ina fatan Yaya Malam ya kamashi da hannunsa dumu-dumu. To ashe aikin nasama ba anan ya tsayaba duk bala'in da ake kunnama Yaya malam da ?an ?a?ansa biyu da suka rage yanada hannu aciki. Wlhy ko alhakin ?ananun yaran nan bazai barku ku zauna lafiya ba balle kuma ha??in yaya malam da Umm-Muhammad da a kullum burinsu su ?yautata rayuwar ?a?anmu a gidan nan. Ka?anma kuka fara gani yanzu kuma".
Momyn Abdallah daketa kuka tun ?azun tace, "Lallaikam yanzu suka fara gani Musbahu. Wannan wace irin cin amanace haka? Wane kalar son zuciya ce?. Ba yaya ka?ai kuka cutarba ai, muma kammu iyalanku kun cutar damu, kun shiga ha??inmu. Wace irin ni'ima ce ALLAH bai baku ba a rayuwa amma ku gaza gode masa har sai kun ?aura ?ammarar shiga ha??in wani. Alhalin dukiyar da kukema zarin ma kunfi mai ita amfana da ita ku da iyalanku. Wai miyasa ?an adam ?in da ALLAH yayma ni'ima shike fin tsaurin idon rashin gode masa? ALLAH ya baku ilimi alhalin ga wasu can jahilai ko yanda zasu bauta masa basu saniba. Ya baku lafiya, ga wasu can a gadon asibiti kwance basu da ku?in neman lafiyar. Ya baku muhallin zama. Ga wasu can suna ra?e-ra?e basu da ko kangon da zasu ra?a. Ya muku sutura. Ga wasu can tufafin da zasusa su rufe tsiraicinsu bai wadacesu ba. Ya baku mutunci da daraja a idon duniya, bayan akwai dubunku da suka fiku shekaru a ?as?ance. Ya baku dukiyar da bama kuda iyalanku ba, wa?anda suka ra?u da ku zaku iya ciyar da mutum sama da ?ari a kowanne yini. Ga wasu can iyalansuma basa iya wadatawa. Ya azurtaku da ?a?a maza da mata, ga wasu can suna nema da miliyoyin ku?a?e basu samu ba. Ya azurtaku da iyaye na gari, bayan ga wasu can iyayen nasu a gidajen ba?ala. Duk wa?an nan ni'imon kuka gagara godema ALLAH a kansu, to mikuke jira UBANGIJI ya muku kafin ku gode masan? Mi kuke nema kukuwa a duniya bayan duk wa?an nan tarin ni'imomin da yay muku. Bafa kunfi wa?anda basu da shi bane, ba kuma tsoronku yasa aka baku ba. Ba kuma ?o?arin ibadar kuce tasa aka baku ba. Kai jama'a kaicon hannu mai butilcin amsa ga mai bashi. Kaicon zuciya mai ba?in cikin cigaban mai ?yautata mata, Kaiconku Rudwan, tabbas bazan yafe muku ?oramin yaro akan mummunar a?ida da kukayiba........"
Kuka ya sar?eta ta kasa cigaba da magana. Shi dai Abban Abdallah ya kasa koda ?wa?waran motsi, kansa du?e a ?asa ya gagara kallon kowa. hakan yasa babu wanda zai iya cewa ga a yanayin da yake.
Baba malam ma dai kansa a ?asa yake du?e. Babu mai shaida yanayinsa. Umm kam ganin al'amarin take tamkar a mafarki zuwa anjima zata farka. Zuciyarta ta kasa gaskata komai akan Abban Abdallah da Fauza. Mutanen da sukafi kowa kusanci da su a gidan. Kai jama'a duniya ina zaki kaimu?.....
Jin kowa bai ?ara cewa komai ba yasa Jay yin gyaran murya. Kusan duk kallonsa sukayi. Ya furzar da numfashi na takaici da fa?in, "To inaga idan kun gama da su zamu kaisu station mu ha?a bayanansu sai mu mi?asu kotu su amshi hukunci kamar yanda shari'a ta tanadar".
Tari Addah ta fara ka?an-ka?an, hakanne ya saka baba malam ?agowa ya kalleta ya maida dubansa ga Jay. "Muhammad Jawaad mubar zancen zuwa kotu kaji. Ita wannan kuma miya rage mata a duniyarma gaba ?aya. Ai wannan izayar da take ciki kawai ta isheta izina. Sai dai mu taimaketa mu mi?ata asibiti kawai...."
Murmushi Jay yayi yana jinjina kai. "Duk da haka malam ai ya kamata su fuskanci shari'a kodan hakan ya zama ilimi ga ?an baya masu sha'awar sake aikatawa. Duk da tana cikin halin ciwo bashi ke nuna zata mutu ba, mutuwa ta ALLAH ce, takanzo a sanda taso ga wanda taso. Dan haka zamuje asibitin taga likita amma bisa ?ar?ashin kulawar hukuma. Shi ko zamu wuce da shi station". Ya ?are maganar yana nuna inda Abban Abdallah yake zaune.
Baba malam zai sake magana Hajjo ta katsesa da cewar, "?an malam hakan shine dai-dai kuma ya kamata. Kaga idanma da mai sha'awar aikatawa a nan gaba sai ya bada himma".
Tarin Addah daya ?ara ?arfine ya sakasu duk maida hankalinsu gareta. Da wannan damar Abban Abdallah ya samu ya sulale a hankali yabar sashen. Sauran jami'an dake a waje basusan yaya aka ?areba shiyyasa basu hana Abban Abdallah bi ta gabansuba ya wuce sashensa yaje ya ha?a duk wasu abubuwa nasa masu muhimmanci ya zuba a ?aramar jikka ya fito. A gaban jami'an ya shiga motarsa maigadi ya bu?e masa gate ya fita batare da shima yasan mike faruwa ba.
Daga ciki ma babu wanda ya farga da rashinsa sai bayan an fito da Addah daketa faman zuba aman jini aka saka a mota domin kaita asibiti. Suna wucewa su Jay suka koma kan Abban Abdallah sai yace ku ?aukeni inda kuka ajiye. A take suka hau cigiyarsa a lungu da sa?o na gidan, sai daga baya sukeji daga bakin maigadi cewar ya fita a mota tun kusan mintuna talatin da suka shu?e.
A razane Jay yace, "What?!!, shine kuka barsa saboda baku da hankali?!". Yay maganar wa yaransa. Duk rawa jikinsu ya kamayi suka hau rantse-rantse su basusan mai laifi bane. Ai kota kansu Jay baibiba ya shiga motarsa shi da Bily da Little. Suma duk suka shiga a wacce sukazo. sai da suka tambayi maigadi motar daya fita a ciki da lambarta sannan suka fice a guje.
Wayar Jabeer Jay ya kira, yana ?agawa ya ce, "Jabeer inason a baza zami'ai a kowacce hanyar fita garin kano domin tsaidamin mota mai Number..... Ruwan toka".
Jabeer na amsa masa ya yanke kiran, C.P ya kira shima dan ya taimakesu.
__________¡ï¡ï
A gidan su Nu'aymah kam musalta muku halin da suke ciki ?ata lokacine. Dan motocin su Jay na fita a gidan Umm ta yanke jiki ta fa?i. Hakama Malam ?arami shi?e musu yayi. Ga kukan da su Adawiya keyi ya taru ya ?ara ?aga musu hankali. Baba malam kansa dauriya kawai yakeyi dan gaba ?aya jinsa yake kamar kansa zai tarwatse dan ciwo. Gashi su Yoohan sun wuce da Addah asibiti. Hakan yasa dole aka kwashi su Umm ma zuwa asibitin.
?angaren Abban Abdallah kam tunda ya fito anguwarsu kai tsaye hanyar Katsina ya ?auka, shi kansa baisan mi yake shirin aikatawaba. Ceton kansa ko gudun kunya? Ko tsoro?. Gudu ya ke na hauka babu wasa a cikinsa. Musamman daya kasance ta gefe-gefen gari yake tafiyar, dan bai yarda yabi ta cikin gariba sam. Yana fara ?aukar hanyar Ktn bayan ya gota Dawanau ka?an ko mintuna goma baiyiba ya ga motar ?an sanda na binsa a baya. A take ya ?ara ?arfin gudun motar tamkar ya manta da kasancewarsa Dattijo. Abu kamar a film suka fara rere tsakaninsa da jami'ai.
ALLAH sarki rayuwa, duk iyawarka baka isa zarce ?addarar UBANGIJI ba. Dan kuwa dai wannan ?ar tsere na Abban Abdallah da ?an sanda sunansa gudu akan igiyar ?addara. Dan kuwa bisa tsautsayi sukau taho mu gama da wata mota dake nufo cikin kano. A take waccan tayi gefen titi, shiko ta Abban Abdallah sai ta kife ta fara wuntsil-wuntsil daga titi ya gangara cikin gona. Tun suna jin yanda yake neman ?aukin UBANGIJI har sukaji tsit, motar kuma ta bugi bishiyar dalbejiya ta tsaya cak.
Cikin sauri ?an sandan da dama tuni sun fito a mota suka nufi motar domin bashi taimako. Da ?yar kuwa akayi kama-kamar ?aga motar aka zarosa a ciki. Gaba ?aya jikinsa yayi face-face da jini har ba'a iya gane inane ya bugu koma yanada rai ko ya mutu. Kasancewar sun kira sun sanar sai ogansu ya basu umarnin maza su ?akkosa su dawo cikin kano asibiti. Bisa wannan umarnin ya sakasu ?akkosa suka juyo a guje.
Kai tsaye babban asibiti suka nufa, cikin amincin ALLAH kuma akai sa'a can aka kai Addah da su Umm suma. Su baba Malam na tsaka da tashin hankalin abinda ya faru sabon labari akan ha?arin Abban Abdallah yazo musu. A take na gida dana asibitin suka sake harmutsewa.
A yanda Yoohan yaga al'amarin ya kasance sai da yaji nadamar shigewa gaba wajen wannan banka?e-banka?e. Sai gashi da idanunsa ya ga baba malam na rusar kuka. Nu'aymah kam ai sai allurar barci ya danna mata saboda yanda ta birkice kamar dai ?wa?walwar ta bata gama dawowa dai-dai ba.
Lallai wannan ranace da wa?a?an nan ahali bazasu ta?a mantawa da itaba a jerin tarihinsu. Sau?insu ma har yanzu ainahin labarin bai fita kunnuwan jama'ar gariba. Sai dai kawai ana maganar Sheikh Rudwan Hashim jibiya yayi Accident a hanyarsa ta zuwa Ktn yanzu babu jimawa. A take mutane suka shiga jera masa addu'ar ALLAH ya tashi kafa?a, musamman ma mabiyansa.
Zan iya ce muku yanda wannan ahali sukaga yinin wannan rana haka sukaga dare. Duk da kuwa Alhmdllh zuwa dare an tabbatar da Abban Abdallah bai rasuba. Ya dai samu karaya a kafa?unsa duka biyu da kafafu. Sai manyan raunika da sukai masa kaca-kaca da jiki. Itako Addah barci suka sakata yi. Umm ma Alhmdllh ta farfa?o ita da malam ?arami. Hakama Nu'aymah ta farka.
Sai kusan tara na dare suka bar asibitin, ba kuma a barsu sunga Abban Abdallah ba dai. Yoohan da kansa ya fiddo Nu'aymah da ga ?akin office ?insa daya sakata barci. Ananah ta taimaka mata suka ?arasa shiga mota. Baba malam yaso su Yoohan su bisu can gidan su kwana amma suka bashi ha?uri akan zasu zauna anan asibitin ne. Badan yaso ba ya barsu.
Yoohan na ganin motocinsu sun gama wucewa ya sauke ajiyar zuciya mai kauri, A ?aya daga kujerun dake a waje ya zauna hannayensa duka dafe da kansa. Sai yanzu komai ke dawo masa a ?wa?walwa tamkar almara. Dan ?azun su Addah na bayani ne little na fassara musu shi da Umar, duk da shi yana ?an jin hausarma ka?an-ka?an yanzun.
Kusa da shi Umar yazo ya zauna shima yana sauke nasa ajiyar zuciyar. Yoohan bai motsaba balle ya kallesa. Shima sai bai damuba ya fara magana a hankali. "Haka mafi yawancin mutanen da suka samu ?aukaka suke. Sai kaga na nesa da su na matu?ar sonsu da begen kasancewa da su. Amma wa?anda ke tare da su mafi yawancinsu ba son gaskiya suke musu ba. ?aso ?aya bisa uku a ciki zaka samu suna musu ?auna ta tsakani da ALLAH. Kaso biyun kuwa sai kaga suna ra?e da sune bisa wannan ?aukakar da ALLAH yay musu. A zahiri kuwa su zugasu da nunama duniya babu kamarsu, a ba?ini sune masu musu SARAN ?OYE. lallai wa?anan mutanen masu zagon ?asa suna ?aya daga cikin jarabawar masu mafi yawan ?aukaka".
Ajiyar zuciya Yoohan ya sake saukewa. Ya ?ago ya dubi Umar a karon farko, idanunsa sunyi jajur. Ga barci ga yunwa ga gajiya. Shi kansa Umar ?in a galabaice ya ke. "Zancenka haka yake Umar, bazan ?oye makaba al'amarin mutanen nan ya sake saka tsoro a zuciyata gaba ?aya, nasake jin tsoron halin mutum da ayyukansa. Wannan wane irin bushewar zuciya ne haka? Su da ya kamata su zauna suyita godema ALLAH bisa ni'imar da yay musu ta rayuwa, su dinga ibada sai suka zama masu butulcewa ta hanyar cutar da wanda shi ya kusan ?are tasa rayuwarne a ?yautata tasu da ta ?a?ansu. Umar wai miyasa ?an adam keda manta alkairi da yawan butulci ne?. Miyasa ?an adam yafi yarda da biyayya wa hu?ubar shai?an akan dokar ALLAH ne?. Miyasa ?an adam yafi yarda ya zama mai samu bamai sadaukarwa ba? Miyasa mafi yawan mutane sunfi sha'awar cutar da wanda suka ?yautata musu amma sunajin tsoron mai munanasu?. Ko addu'a mutum zaiyi, sai kaji yace ALLAH ka tsareni daga sharrin masu sharri. To miyasa bama addu'ar ALLAH ya karemu da aikata sharri ga masu ?yautata mana ne?".