Showing 93001 words to 96000 words out of 325075 words

Chapter 32 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29140

murmushi, insha ALLAH indai su baba malam suka amince zuwan nasu ya koma sai bikin su Kubrah yanada ya?inin samun cikar burinsa. Dan babban fatansa shine shirinsa akan mallakar Nu'aymah ya tafi dai-dai, shima ranar ?aurin auren su Kubrah a ?aura nasa da masoyiyarsa, farin cikin rayuwarsa.
Wayarsa ya jawo dake a gefensa, ya shiga ma'adanar hotunansa yana kallon hotunan da yaytama Aymah a wannan zuwan nasu batare da ita kanta tasan yana ?aukarba. Ya jima yana kallon hotunan kafin barci yay awon gaba da shi a wajen
Barcin nasa bai kai mintuna ashirin da ?aukarsa ba Adawiya ta shigo gidan ita da maman Aaida. Ganin ?akinsa a bu?e ya sakata nufar can tana fa?ima maman Aaida, "Aminiya zauna ina zuwa, naga kamar Yah Ab yana gida ma".
?an murmushi maman Aaida tayi da bata amsa cike da zolaya. "To adaibi a hankali azumi ake hajjaju". Batare da Adawiya ta bata amsa ba ta shige tana dariya.

Hajjo da dariyarsu ta sakata farkawa da ga ?an barcin daya figeta itama ta fito dan taji ba muryar Adawiya bace kawai. "Ba?uwa mukayi a gidan?". Ta fa?a lokacin da take fitowa falon. Maman Aaida dake latsa waya ta ?ago idanunta ta sauke akan Hajjo. Sai kuma tace, "Barka da fitowa hajiya".
Hajjo dake mata kallon sani tace, "Barka dai ?ar nan, gashi kuma kamar na sanki".
Da sauri maman Aaida ta zaro idanu waje da mamaki, sai kuma ta tuna maganar hajiya datai mata garga?i tun farko akan zuwa gidan, amma yau tsabar taurin kai sai gashi ta biyo Adawiya data dinga mata da?in baki..........
"To ko dai kamanni ne?"
Hajjo ta katse mata tunani. Da sauri maman Aaida tace, "Eh gaskiya hajiya inaga hakane, dan ni ?ar nance". Cike da nazarinta Hajjo tace, "Oh to ALLAH sarki, kinsan idon tsufa ?ar nan. To barka da zuwa, halan ke ?awar Adawiya ce?".
"Eh hajiya". Maman Aaida ta bata amsa a ?arare, dan tasha jinin jikinta da kallon ?urulla da hajjon ke binta da shi...

?angaren Adawiya kam tana shiga ?akin Yah Ab sai ta iske yana barci, ga wayarsa ajiye saman ?irjinsa kamar wanda ya rungume mace. Harta juya zata fita, sai kuma zuciyarta ta ?wa?auta mata wani abu daban. Dawowa tayi da baya a hankali ta ?auka wayar, kasancewar ta jima da sanin password ?insa sai batasha wani wahalar bu?ewa ba. Gabanta yay bala'in fa?uwa saboda cin karo da hoton Nu'aymah da tayi, ta kafe hoton da idanunta da suka ciko da ?walla, sai kuma ta kalli Abdallah dake barcinsa hankali a kwance batare da yasan tanai ba. Harararsa tayi kamar idanunta zasu fa?o, mikuma ta tuna oho mata, saita ajiye wayar a inda ta ?auka ta fito a ?akin.
Karo da taci da hajjo ta fito suna ?an hira da maman Aaida yasata ha?iye damuwarta ta zauna tana gaisheta.

WASHE GARI

Washe gari ya kama ranar salla, a kuma ranar Nu'aymah ta fito daga ittiqafi bayan sakkowa sallar idi. Duk da tayi ?ar rama sai gata ta ?ara haske saboda yanayin zafinsu da kuma zama cikin ac a koda yaushe. Tayi mamakin ganin Abdallah yazo ?aukarta. Da farko taso ta?i binsa, amma ganin rana zatayi saboda yau zasu wuce sai ta ha?ura ta bisa.
Motar tayi shiru babu mai magana a cikinsu har suka isa ?ofar gidansa. Tana ?o?arin bu?e ?ofar yay saurin saka lock. Juyowa tai tana kallonsa fuska a ?aure, shima sai ya ?aure tasan, batare da ya kalleta ba yace, "Inason muyi magana da ke a yau".
Kamar bazata tanka masaba, sai kuma tace, "Yah Ab maganar mi? Dan ALLAH ka cire komai a ranka kamar yanda na cire nima, bana bu?atar wata sabuwar fitina dan girman ALLAH".
Cikin zafin rai yace, "Saboda kin samu wanda ya fini? Nu'aymah minai miki ne a rayuwa har kika za?i sakamin da wa?anan abubuwan? Mina rasa irin na sauran maza ne.....?"
"Baka rasa komaiba Yah Ab, sai dai ka sani mu wannan itace ?addarar mu, UBANGIJI kuma shine yasan hikimar dake cikin yin hakan. ALLAH shine shaidata ban gujeka ba, ban kuma daina sonka ba. Sai dai wata katanga mai tsauri tariga da tayi gicci a tsakanin ?addarar mu. A ganina kuma babu amfanin maida yanda akayi domin bakin al?alami ya riga da ya bushe........."
"Sai dai idan kece kika busar da shi Nu'aymah, idan har kin amince inason a wannan karon mu cika burinmu na mallakar juna, na yadda da kaifin wu?ar data datse zaren ?addarar mu a wancan karon, sai dai a yanzu na sake ?aura ?ammarar ?aure zaren domin mu zama abu guda kamar yanda mukai fata".
Murmushi mai ciwo Nu'aymah tayi, ta gyara zama tana fuskantar Yah Ab, cikin raunin murya tace, "Yah Ab, karka manta a yanzu kai ?in mijin Adawiya da Yusrah ne, tayaya kake tunanin zan yarda ka sake ?ulle wancan zaren ?addarar da kaifin wu?a ya datsa ta. A ganina muyi ha?uri kawai da yanda yau tazo garemu, domin kuwa jiyanmu ta wuce sai labari. Muyi ha?urin fuskantar gobenmu sai muzama masu cin riba. Wlhy Yah Ab bazan ta?a iya ha?a zaman kishi da Adawiya da Yusrah b........."
Da sauri ya saka hannu ya rufe mata baki, cikin matu?ar ?acin rai yace, "Hakan ya zamemiki dole kuwa Nu'aymah, idan kuma kikace zakimin taurin kai, wlhy a yanzu sai kunbar ?asarnan da Adawiya tare da takardar sakinta ?ai-?ai har uku kuwa". Yana gama fa?ar haka ya cire lock ?in motar tare da ficewa a fusace.
Nu'aymah da tun farkon fara maganarsa akan su Adawiya ta ?aura hannu a ?irji da fa?in, "Na shiga uku ni Zainab! Yah Ab mi kake fa?i haka?". Bai saurareta ba ya shige gida, da sauri itama ta bu?e motar ta fito ta bisa da ?an gudu tamkar zata fa?i.

Adawiya dake a ?wance bayan motar tai saurin cire hannunta data toshe baki, dan da?yar tai control ?in kanta lokacin da Abdallah ya furta zai sakesu inhar Nu'aymah bata amince da bu?atarsa ba. Motar ta bu?e ta fito itama da sauri tana fa?in, 'Tab?i jan, ashe lokacin yin ya?in duniya na uku ya gabato kenan, lallai yanzune za'a fara wasan na gaske wlhy'. Ta ?are maganar hawaye masu zafi na gangarowa a kumatunta.
Tun lokacin da taji Abdallah na sanarma Hajjo shine zaije ?aukar Nu'aymah bayan an idar da sallar idi ta ?udiri aniyar binsa a ?oye. Dan haka kawai taji a ranta akwai manufa a zuwa ?aukar, dan ta gama fahimtar take-taken Abdallah tun lokacin dasu Nu'aymah suka zo ?asar. Shinefa ta lalla?a taje ta shige motar ta ?oye sannan ya samama hajjo inda zatayi sallar idi a massalacin, shi kuma batare dayin wani tunani ba yana zuwa yaja motar ya wuce. Kuma harya ?akko Nu'aymah hankalinsa bai kai akan Adawiya dake lafe a ciki ba. wadda ko sallan idi ita batayi ba.

Tana shigowa cikin gidan duk a falo ta iskesu har Nu' Abdallahn. Duk suka bita da kallon mamaki dan sunta nemanta bayan idar da salla basu gantaba, shine Ahmad yace suyi tahowarsu tunda ita ?in ?ar garice ai.
"Ke kuma dama ba gidan kika dawo ba?".
Abdallah ya fa?a cikin kaushin murya dan har yanzu ransa a ?ace yake. Kamar bazata tanka masa ba, dan ranta a bala'in cinkushe yake, ji take kamar ta burmama Nu'aymah wu?a ta mutu kowama ya huta. Amma komi ta tuna oho mata, sai tai kalar tausayi tana ha?iye ?ududun daya tokare mata ma?oshi. "Eh na biya nan ma?wafta wajen Umm-Farukh, dama wasu kayane mukai da ita zan amsarma su Aymah to kuma ma dai anyi rashin sa'a basu isoba, dama daga Mexico ake kawo matasu".
?auke kansa yay bai tanka ba, sai Ahmad ne da Hajjo sukai magana. Nu'aymah da tasha jinin jikinta akan yanda Adawiya ke magana ma bata tanka ba, sai dai a ?asan ranta bata yarda da itaba sam.

¡ï¡ï¡ï

Duk yanda Abdallah yaso sake ke?ewa da Nu'aymah dan su sake cimma matsaya akan zancensu ta?i basa dama har suka wuce Nigeria bayan awanni hu?u da sakkowa idi, dan kobi takan bikin sallar da ?an saudia ke gudanarwa basuyi ba, dama Adawiya ?in dafa komai tai saboda takaici. Abdallah zaiyi magana kuma Hajjo ta hanashi, acewarta su da zasu tafi yanzu mizasuyi da wani abincin salla bayan nasu nacan na jiransu a ?asarsu.

Sun sami ?ya?y?yawar tarba kuwa daga su baba malam, dan ana sakkowa daga sallar juma'a (da yake ranar sallar ta kama juma'a ne) suka nufi airport domin tarbar mahaifiyarsu tamkar yanda suka saba. Babu kunya Nu'aymah taje ta rungume Baba malam, dan harga ALLAH tayi kewarsa shi da Umm da Muhammad. Kai dama ?an gidan duka.
Fuskar baba malam ?auke da murmushi ya shafa kan ?ar tasa yana fa?in, "Ja'ira, duk ga iyayenku cike da wuri bakiga kowaba sai ni ko?". Fuskar Nu'aymah washeda murmushi tace, "Abba nayi kewarka ne sosai, kuma ALLAH kullum sai nayi mafarkinka kai da Ummuna".
Baice da ita komaiba sai murmushi kawai daya sakeyi, dan shi mutum ne mai tsananin kawaici ga yaransa, yanama ?an uwansa kara sosai. Dan haka suma a kullum suke ?o?arin koyi da ?abi'unsa akan nasu ?a?an.
Bayan Nu'aymah ta ?arasa ta gaida sauran iyayenta uku suma cike da girmamawa. Suma suka amsa mata da tsananin kulawa sai suka rungu?a gaban mahaifiyarsu suna jera mata sannu da zuwa. Cike da kulawa da kewa take dubansu, fuskarta fa?a?e da murmushi. Ta kama hannun Abba Musbahu tana fa?in, "Wayyo autana duk ka fa?a, ko azuminne?".
Dariya Nu'aymah da Ahmad sukayi, Malam ?arami da Omar na tayasu kuwa. Hakama su baba malam sunata murmushin akan diramar autan nasu da mahaifiyarsu.

Lokacin da suka iso gidan nasu sun iskeshi da dangi da yaransu na ma'auri duk anzo tarbar hajjo da kuma yawon salla. Inda gidan ke wadace da tarin abinci kala-kala da kowanne sashe ya tanada. An gyarama hajjo sashenta tsaf an kuma kai mata abinci daga kowanne sashe an ajiye mata. (Dama haka suke mata).
Motocin na gama tsayawa Nu'aymah bata tsaya sauraren masu tarar tasu ba ta shige sashensu da gudu tana ?walama Umm kira. Da sauri Umm dake ?o?arin fitowa taja baya dan ka?an ya rage suci karo da Nu'aymah.
Fa?awa jikinta tai ta ?an?ameta tana fa?in, "Wayyo Ummuna, nayi kewarki wlhy". Umm dake murmushi ta amshi ?iyar tata da hannu biyu ta rungumeta itama, sai da ta tabbatar sunji ?umin juna kowa na sauke ajiyar zuciya kafin ta ?agota da ga jikin nata. "Nu'aymah! Yaushe ne zakiyi hankali kisan kin girma ne? Bakisan yanzu ba da bane, shekararki goma sha bakwai fa kina shirin shiga sha ta?was".
Cike da shagwa?a ta saka kanta a kafa?ar Umm tana fa?in, "Umm ni indai ina gabanki wlhy jaririyace sabuwar haihuwa, nayi kewarki ne sanyin idaniyata. Ina Muhammad yake?".
"Nayi cinikinsa" Umm ta bata amsa tana janyeta daga jikinta ta fice domin shiga tawagar masu tarbar surukar tasu.
Baki Nu'aymah ta tura gaba, ta ?aga ?afa zata biyo Umm tajiyo muryar Muhammad a bayanta yana fa?in, "Marhaban biki Aunty na". Saurin juyowa tai garesa, sai kuma ta nufe da sauri kamar yanda yake nufota suka rungume juna cike da kewa da ?oki.

Haka gidan ya kasance a hargitse ranar saboda shagalin bikin salla, Nu'aymah bataje ko inaba, dan bayan tayi salla ta?anci abinci sai ta shiga ta gaida kowa na gidan, kafin ta koma ?akin Umm tai kwanciyarta, duk wanda yazo musu yawo a ranar bai samu ganinta ba, dan ta ?oye kanta a cewarta saita huce gajiyarta da ?yau tunda dai tasan zasu zaga gari yawon sallar gobe idan ALLAH ya kaimu ai.

___________

Kiran sallar la'asar ne ya tada Nu'aymah dake kwasar barcin gajiya. Ta mi?e da ?yar dan jikinta ko ina ciwo yake faman mata. Wanka ta farayi, ta saka ?aya daga cikin kayan sallarta. Tayi ?yau sosai cikin shaddarta ruwan hoda, taji aikin stones da yay ?yau sosai. Kayan sun mata ?as ajiki, tare da sake fiddo haskenta saboda ?ar ramar da tayi.
Lokacin data fito Umm kanta sai da tace, "Masha ALLAH". Hakama ?a?an yayun Umm ?in su uku da sukazo mata yawon salla duk sai da suka yaba ?yawun da Nu'aymahr tayi. Ta zauna fuskarta da murmushi tana gaidasu cike da girmamawa. Dan dukansu matan aurene, kuma duk suna da yaransu. Cike da kulawa suke amsa mata, kowanne na mata ?orafin rashin zuminci, musamman babbarsu.
Nu'aymah tace, "Lah Aunty Zulfah wlhy ba rashin son zuminci bane, ni abinda yasa banason zuwa gidanki wannan ?anin mijin naki takuramin yake wlhy. ya cika shegen kallo kamar ?an daudu".
Dariya suka sanya gaba ?ayansu, aunty Zulfah tace, "To kwantar da hankalinki, indai Fa'iz nema aurensa zaiyi, tunda ke kin?i. Kinga nima dakin yarda ai dana samu ?ar uwata kusa dani ko......."
Da sauri Nu'aymah ta katseta da fa?in, "Taf, aunty daina fa?a dan ALLAH, wlhy ya cika iyayi, banason namiji yayta gwalli kamar wani mace, shiba ?an daudu ba shiba mata maza ba".
"Amma Nu'aymah baki da kirki wlhy, kin gama ?ebema ?anin mijin aunty Zulfah albarka gaba ?aya". Aunty Rafi'a ta ta fa?a tana dariya. Ita kanta Nu'aymah dariyar takeyi, Umm dai batace musu komaiba. duk da kuwa tana zaune tana jinsu.
Sai da suka tsagaita da dariyarne Nu'aymah ta mi?e tana fa?in, "Umm yunwa nakeji, ALLAH yasa akwai waina dai?".
"Kin kuwa makaro, dan su Basira na ?eboma ita gaba ?aya, kinsan zakici wainar kika?i ?iba ki ajiye?". Kamar Nu'aymah zatai kuka tace, "Kai Umm! ALLAH yanzu kin daina sona, amma yanzu duk wainar dana gani ace ta ?are? Su su aunty Basiran miyasa basu zauna sunci a sashen Addah b......."
Harar da Umm take jefo matane ya sakata yin shiru, dan su Basiran ?annen Adda ne. "ALLAH ya shiryeki to, to ance miki sune ka?ai suka cinye. Ga yayunki nan suma duk ita sukaci, sannan Abbanku da yay ba?o duk da baya a gidan shima ita yace akai musu kafin ya iso gidan".
Komawa tai ta zauna kamar zatai kuka, su Aunty Zulfah nata tsokanarta wai ta amshema Muhammad guri tana shagwa?a bayan shine auta.
Umm tasan yanda Nu'aymah keda jarabar son waina, dan haka ta dubeta sau ?aya ta ?auke kanta tana fa?in, "ki wuce sashen hajjo idan bata ?areba". Aiko zumbur ta mi?e, a ranta tana fatan ALLAH yasa ta samo.
Duk da takalman data gani na maza a ?ofar falon na hajjo kusan ?afa biyar bata damu ba, sallama tayi kawai, kafimma su gama amsa mata ta shige dan duk zatonta yayunsune a ciki, tunda tasan duk suna gidan. A shagwa?e ta bu?e baki zatai magana. sai dai cin karo da fuskar da batai zato ko tsammanin gani ba ta sata waro manyan fararen idanunta waje cike da al'ajabi.
Yoohan dake zaune shima cikin Suit ruwan babypink kallon nata yake cike da mamaki, a ransa fa?i yake, 'Dama yarinyarnan ba'a cikin Orphanage ?incan take ba? No wander ?azun baiga komai kama da itaba a cikin yaran'. A fili kuwa sai ya ?auke kansa cike da shan ?amshi kamarma irin bai ganta ba ?in nan shi.......
"Lafiya wai kika tsayama mutane ?erere a kai Zainabu?". Maganar Hajjo ta katse mata tunaninta. Juyawa tai inda hajjon take, har yanzu mamakin ganin Yoohan ?in bai barta ba, "Hajjo wannan mutumin kuma ina kika sanshi?".
"Wa ?in?". Cewar Hajjo tana kallon inda Hamza Manager, Yoohan dasu baba ?arami ke zaune.
Maimakon Nu'aymah tai magana sai ta je ta zauna kusa da hajjon, matsar da bakinta tai dai-dai kunnen Hajjo tace, "Hajjo arne ne fa wlhy". "Aina sani" Hajjo ta bata amsa cikin nuna halin ko in kula.
Sosai mamaki ya kume Nu'aymah, tai tsai tana kallon Hajjon, kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta sake maida dubanta ga Yoohan daya maida dukan hankalinsa kan wayarsa.
"Wai lafiyarki kuwa? Kina ganin mutane baki iya gaisuwa bane? Sai shegen kallo malama". Yah Ahmad ya fa?a idonsa akan Nu'aymah. Sai da ta?an tura baki kafin ta duba Hamza manager data wuce da dukanin imaninsa tace, "Ina yini". Cikin narkakkiyar murya da shi kansa baisan ta fitaba ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login