Showing 186001 words to 189000 words out of 325075 words
irin salo na daban..._
_Labarin *BA AMO* ya faru akan wata yarinya da d'an sarkin garin su, yarinyar gidan su gidan yawa ne...Baban su yana auri saki ya tara 'ya'ya da mata da yawa. Tirqashi! To ita yarinya sunan ta KHAIRAT... Tun farko dangin mahaifin su sun tsani mahaifiyar tasu,Bayan ya auro ta, Ta haifi yara mata zallah suna kiran ta da uwar mata kuma kwata-kwata basa kaunar ita da 'ya'yan nata. To ita yarinya ta gama karatun ta.... wato KHAIRAT.. shekarun ta 22 matan gidan nasu suna mata gorin tayi kwantai tak'i aure. Kwatsam wata rana yarinyar ta samu labarin d'an sarkin garin su ya bude sabon company ya fara daukan sabbin ma'aikata, ?????¡á???cikin ikon Allah ta zuwa ta samu aiki. Ta fara zuwa aikin ta, a karshe su kansu da suka fahimci kwazan ta da nutsuwar ta samu karin matsayi. To a lokacin ne kuma Yarima da PA dinsa suka sami matsala aka kore ta a ma'aikata sai aka daura ita Khairat d'in a matsayin P.A dinsa. Tafiyar tasu batama yi nisa ba! Aka yi makiya suka yi masu sharrin wai karuwar sa ce, har labarin yaje gun mai martaba. Itama Khairat d'in labarin yaje ga mahaifin ta har ya nemi korar ta daga gidan sa, da kyar aka lallashe shi ya hakura.._
_Tab rungutsumi din fa kenan??Ya zata kaya ne ga YAREEMAH GA KHAIRAT..a roof d'aya? Ya rabbi?? labarin kauna yayi.. Amma fa Za'a sha rikici.. Karku manta khairat daga gidan yawa tafito??Ga basuda wani hali.. Shin sarki zai yadda da Khairat amatsayin personal assistant din yareemah ko kuwa.? Duk wannan ruguntsumi n REAL FEEDO ce kadai zata iya warware mana.._
_BA AMO::::: (Ba Labari...)_
_DOMIN MALLAKAR NAKI/'NAKA TUNTUBE MU TA:_ +227 81 73 10 21
________________
No. 50
............Ya jima tsaye a jikin ?ofar wutar kansa a ?auke. Kafin ya ja ?afa da ?yar zuwa saman gadonsa. Duk yanda yaso barci ya ?aukesa hakan ya gagara, har kusan 2, daga ?arshe dai ya mi?e zuwa toilet, ruwa ya sakarma kansa kafin ya ?auro alwala ya fito. Daga haka yay nafilfilin daya saba, ganin ya kai har asuba saiya bari sai da yay sallar asuba ?in sannan ya haye gadon ya kwanta ko azkar yau bai iya kammalawa ba saboda barcin dake cike da idanunsa.
A ?angarrn Aymah kuwa kanta ta dafe tare dayin jifa da hijjabin tana ballama ?ofar harara, sai kuma ta zabura ga ?ofar ta murza mata key wai karya dawo. Addu'a ta komayi akan ALLAH yasa bai ganta da ?yauba, idanko ya ganta to bata yafe ba (dan ?ari??). Da ?un?uni ta koma gaban mirror ?in inda ya ajiye tea ?in, babu kunya ta zauna ta sha dan dama ?ar yunwa na cinta ?asa-?asa, alwashin data ?auka na daina cin abincin gidanne kawai ya sata cewa ta ?oshi. Sai da ta shanye tsaf taci rabin biscuit ?in sannan taje ta sake yo brush tazo tai kwanciyarta.
¡ï¡ï¡ï¡ï
A ?angaren madam Chioma kam ta fitane da wani irin jin zafi da takaicin Aymah, dan ita duk a tunaninta da biyu tayi abinda tayi. Batasan ita Nu'aymah ko tarin farko da tayi, tayine kawai dan neman tsokana bawai danta kawo wani abu a ranta game da zaman nasu ba, tunda tasan sudai basu ?auki ta?a jikin juna komaiba musamman ma ita dake a matsayin mahaifiyarsa. Ko kallon Victoria da Abraham dake rigima akan camara batai ba ta shigewarta ?akinta ta banko ?ofa. Zama tai kan sofa zuciyarta tamkar zata tarwatse dan tsanar Aymah. Waya ta ?auka kamar zata kira ?awarta sai kuma ta fasa, a ganinta gara ta bari su ha?u a church jibi lahadi zasufi yin maganar yanda ya kamata ai.
Hular gashin dake a kanta ta tuge ta ajiye, cirku?a??en ainahin nata dake guntu ya bayyana. Fitowa ta sakeyi daga ?akin zuwa sashen Papa. Baya falo, dan haka ta nufi bedroom ?insa kai tsaye. Saurin tura hoton hannunsa da lighter da zai ?onashi yayi ?ar?ashin gado dan yazata cikin yaransa ne wani ya shigo masa. Amma ganin matarsa ne sai ya ?an sauke ajiyar zuciya. Sai dai hakan baisashi sake ?akko hotonba duk da itama tasan wani abu akan hoton.
Ita sam bama ta lura da abinda yayi ba, ta zauna a bakin gadon kusa da shi tana hawaye. Duk rikicewa yayi, ya shiga jera mata tambayaoyi da rungumota jikinsa. Bata iya bashi amsaba sai da tai kukanta ta more sannan ta labarta masa abinda ya faru. Murmushi yayi dan shi baiga wani abin fushi ba anan, a fili kam sai yace, "Uhm-uhm Darling cool down, ke mima ya kaiki sashensu yanzu? Kin sanfa yanzu yana da mata, duk kulawar da kike tunanin baya samu yanzu akwai mai masa". ?an turesa tai ta tashi zaune sosai. Ya ?yal?yale da dariya yana ri?o hannunta, "Ah son ?a?a yamiki yawa Madam, karfa kice zaki ringa irin halin su mama akan matar John Please, dan indai kina nuna mata ?i bazamuci nasara akan burinmu ba zaki rusa mana aiki".
"Honey yarinyar nan bata da kunya, ciwon da kaga Mira taji fa itace ta saka mata ?afa ta fa?i saboda ta mata tsaki". Idanu papa ya zaro waje sosai da fa?in, "Da gaske?". "Na rantse maka kuwa Honey, abinda yasa nai shiru banyi maganaba saboda itama Miracle ?in shegiyan kanta ne, danni tama isheni a gidan nan, ya kamata ta koma gidansu hakanan tunda ta kammala karatun ai".
Da sauri Papa yace, "No baza'ayi hakaba Darling, kawai dai zan mata garga?i karta sake shiga rayuwar matar John, inba hakaba kuwa shine da kansa zai koreta a gidan nan tunda tasan halinsa". Wani shegen kallo Madam Chioma kema Papa mai cike da tuhuma. Amma sai ya basar kamar bai ganta ba. "Humm" ta fa?a tana ha?iye abinda ke a ranta. a ganinta inma hakanne ai zata saka idanu ta tabbatar. "Naji, yanzu dai inason kaima John magana, dolene idan yana garin nan ya ringa fita church bawai dole sai Sunday ba. Idan bamuyi hakaba yarinyar nan zata iya sakashi ya fara salla. Gara mu saka masa ido sosai itama kanta duk Sunday ya sata tana binmu tunda akwai addu'oin da ake masa, tunda kuma yanada mata kaima kasan a ?a'ida dole saita ringa kasancewa a wajen".
"Eh maganarki gaskiyane kam, zan zauna da shi sai muyi magana".
Kanta ta jinjina masa alamar gamsuwa. Daga haka suka cigaba da hirarsu har ya manta da batun ?ona hoto ma.
*******
A ranar gaba ?aya Nu'aymah wasan ?uya ta dingayi da Yoohan, gaba ?aya ta?i yarda su ha?u har yamma duk da dai ya da?e bai tashi a barci bane, sai gab da azhur ya tashi, yana yin wanka kuma yay shirin massallaci ya fita. A lokacinne ya isketa a falo tana kallo. Amma tanajin motsinsa ta tashi da gudu ta shige ?akinta harda mirza key. Shi dariya ma ta bashi a lokacin, amma sai ya gimtse baiyiba yay ficewarsa dan ya kusa makara.
Sai bayan sallar la'asar ya dawo massallaci ne ya ritsata ta fito zataje garden. Karo sukayi a bakin ?ofa, tai baya da sauri tana tura baki gaba da dafe goshinta. Uffan baice mata ba, sai idanu daya kafeta da shi. Dan doguwar rigar atamfar jikinta ta mata ?as, daka ganta kaga cikkakkiyar bahaushiya ?ar arewaci.
Jin ya?i cemata sannu ta sake tura bakin tana tara hawayen ?arya, ita a lallai dole taji zafin bigewar da tayi. Ra?ashi tayi zata wuce yay azamar ri?o hannunta ya dawo da ita gabansa. "Kin gama gudun?". Ya fa?a a hankali kamar bayaso. Yanda yay maganar muryarsa a sanyaye ne yasa kallonsa da sauri, kallon ido cikin ido sukaima juna, ya ?an lumshe nasa dake da ja a ciki, gashi sun ?an kumbure ya sake bu?ewa a kanta.
Samun kanta tai da fa?in, "Baka da lafiya?". Kansa ya ?an jinjina mata da yamutse fuska, kafin yace, "Kaina ke min ciwo". Ya bata amsa yana sakin hannunta dake cikin nashi.
A bazata yaji tace, "Dama likitoci na rashin lafiya?". Tai maganar da waro idanunta manya waje sosai. A karan farko ya saki murmushi yana ?o?arin ra?ata zai wuce, sai da ya shige falon sosai sannan yace, "Shi likita ba mutum bane?".
Harta bu?e baki zatayi magana sai ta fasa saboda hango Papa na sakkowa daga sama waya a kunnensa. Sai dai kuma idanunsa na kansu da ga ita har Yoohan ?in. Juyawa tai ta fice abinta.
_______¡ï¡ï¡ï¡ï________
*_KANO TA DABO_*
Kamar yanda baba malam yayma Umm bayani akan ?ar aiki da Aymah ta bu?ata daga nan, itama Hajjo ya sameta da zancen, ?ari bisa ?ari hajjo ta bada goyon baya, sai dai tace ya kamata a tuntun?i Yoohan idan ya amince, idan bai aminceba a ha?ura kawai, a hankali zata saba da wa?anda ?adadara ta kaita zama da su. Harma suna mata fatan cin riba akan hakan.
Duk da baba malam ya riga da yayi magana da Yoohan akan maganar tun kwana biyu daya wuce sai ya amsama hajjo da cewar insha ALLAH a yau zai tuntu?i Yoohan ?in, yanda sukayi kuma zataji. A ransa kuwa da biyu ya?i fa?a mata gaskiyar yanda al'amarin zai kasance. Ba komai ya jawo hakaba sai la?e daya fahimci anai musu shi da Umm kwana biyun nan, inuwarnan daya gani a ranar da za'a kai Aymah Abuja. Sai kuma ya sake ganinta randa yakema Umm bayani akan wayar da sukayi da Nu'aymah. Sai dai yayi shiru da bakinsa ko Umm ?in bai sanarmawa ba. Sai Yoohan da shima yay masa zancen ganin mutum a randa akai maganar cikin nan na Aymah, dan randa Nu'aymah tai masa maganar mai aiki daga nan kano ya kira baba malam sunyi doguwar waya.
A yanzu haka fatansa ALLAH yasa maganar da sukayi da hajjo an la?e musu ?in. Dan duk mai aikata musu SARAN ?OYEN zaiso ace koma wace ?ar aiki za'a turama Nu'aymah ya samu dangantakar da zai ringa samin bayanai akan Aymah.
Baba malam ya jima a wajen Hajjo da tunanin ko zai sake ganin inuwar mai la?en nan. sai dai harya ?araci zamansa da kallon windows babu ko ?yallin mutum balle wata inuwa. Hakan ya bashi mamaki amma sai ya share dan baya bu?atar hajjo ta fahimci komai tun yanzun, sai sun kammala ?ana tarkunansu tsaf sannan.
Washe gari baba Malam ya sake samun Hajjo da maganar cewar Yoohan ya amince da maganar mai aikin. Fuskar Hajjo fa?a?e da murmushi tace, "To to Alhmdllhi, madalla da ?an albarka Yahya. Kaga bara na shiga nan gidan Iyami da kaina sai na mata bayanin a samo mai hankali ba yarinya irin Zainabu ba. Dan bazai yuwu a irin wannan zaman a ha?a ?uruciya da ?uruciya ba. Sai dai wadda ta?an tasa idan taga ba dai-dai ba ta nusar da ita".
"Eh gaskiya ne inna, hakan yayi kam. Dan mamana halinta kam sai ita, inba mai ?orata a hanyar aka samoba sai aita samun matsala dan har yanzun hankali bawai ya gama isarta bane".
"Ai karka damu ?an malam, wlhy duk abinda kaga Zainabu nayi nima nayisa, babu abinda ta bari na ?uruciyata. Malam yasha fama dani bana wasa ba. Amma kaga ina fara haihuwa duk saina rage nawa. Garama Zainabu ai a shekarun da akai mata aure ta tasa fiye dani. Tunda ni ina sha uku aka aurama babanku ni, itako sha bakwai fa harda wasu watanni".
Baba malam dai kansa a ?asa yanata ?o?arin ha?iye dariyarsa. Dan shima kafin mahaifinsu ya rasu ya ta?a bashi labarin ?iriniyar da Hajjon tayi a gidansa. Da yake shi haka yake, duk randa ?an labarin nasa ya motsa sai ya zaunar dasu yayta basu tarihin gwagwarmayar da yayi ta rayuwa harma da ?uruciyarsu. Wannan ?abi'ar ta mahaifinsu tana ?aya daga cikin abinda basa iya mantawa a rayuwarsu su duka.
Kamar yanda Hajjo tai al?awari da yamma kuwa sai ta shiga gidan su Hamisu wajen mahaifiyarsa Iyami. Sosai Iyami ta dinga haba-haba da hajjo duk da kuwa kasancewar su ma?wafta. Amma da yake ba ?abi'ar shige-shigence da suba inba da ?wa?waran dalili ba, sai yazam duk randa akaga juna kamar ba?i.
Bayan sun gaisa hajjo tasha ruwan da Iyami ta kawo mata duk da ba ?ishin take jiba, sai dai a cewarta ruwan zuminci yafi zuma gar?i. "Yauwa Iyami nasan kinata mamakin ganina da maraicen nan. To dama ba wani abune ya sani fitarnan ba ta gabannin magriba sai takwarata ?ar jikalleta Zainabu da aka kai Abuja".
Iyami dake murmushi tace, "Oh ALLAH sarki Nu'aymah amarya zaki cemin, inadai fatan suna nan lafiya ko?".
"Ah lafiya lau suke sai alkairi kam. Mijin ne dama ya kira wai a nema mata mai aiki daga nan, shine nace to bara nazo da kaina wajenki ?ila ta hanyarki a samo wata mai hankali. Danni ?an aikin gidan nan namu yanzu tsoro al'amarinsu ke bani wlhy Iyami. Kuma kinsan duk deluwa ce dama take kawo manasu gashi ALLAH yay mata rasuwa".
"To hajjo babu damuwa. Tunda har kika za?eni nikuwa insha ALLAH zan samoma Nu'aymah mai aiki ?ar gaske wadda baza'ayi kuka da ita ba. Duk da dai yanzu kinsa al'amarin mutanen namune sai dai addu'a. Baka fiya ganin abinda ke cikin zuciyar mutum ba a fuskarsa. Sai dai muce ALLAH ya datar damu".
"To amin dai Iyami. Lamarin bani adama kam na wannan rikitaccen zamani sai godiyar ALLAH kawai. Yanzu dai sai a bincika mana ?in daga nan zuwa kwana biyu. Amma sai a samo mana ?ar babba ko tunda kinga ba'a ha?a Zainabu da sha katafi irinta ba. Wadda dai idan tayi ba daidaiba za'a tsawatama yaro a kuma ?orasa akan hanyar data dace".
"Eh gaskiya kam hajjo, aiko indaima hakane bari zuwa anjima idan cikin su Hamisu wani ya ya shigo sai na saka su kira min Uwaliya idan zatayi, ?ar wajen yafendona ce acan wudil, mijinne ya tafi da ita can kudu da yake ?ansanda ne ya gama wajigo rayuwarta shine fa ya turota da takardar saki har uku. Shekara biyu kenan wani auren ya gagara abu kamar na magani".
Hajjo daba cika son irin wa?annan ?ananun maganar tayiba ta mi?e tana fa?in, "Ai ?an adam sai ki barsa kawai Iyami, ALLAH dai ya ?yauta ya shiryrmu mu da halinmu".
"Amin dai to".
Iyami ta fa?a badan taso firar ta tsaya iya haka ba. Daga haka hajjo tai mata sallama ta dawo gidan dan anata haramar fara kiraye-kirayen sallar magriba ma.
_________¡ï¡ï¡ï¡ï_________
*_SUNDAY MORNING_*
Washe gari ta kama Sunday. Gaba ?aya ahalin gidan sun tashi ne da shirin tafiya church kamar yanda suka saba. Papa ya riga kowa fita shida bodyguard ?insa. Aymah da batasan hidimar da sukeyi ba tana tsaka da mopping a falo akai knocking ?ofa. Batare da ta damu da sanin wanene ba ta nufi ?ofar zata bu?e. Dan akwai hijjab ?arami a saman kayan barcin jikinta.
Momy ce cikin shiga ta alfarma, anci uban kwalliya kamar zataje gasar ?yau. Abraham biye da ita shima cikin gayunsa. Kamar zata shareta karta gaisheta sai kuma tace, "Good Morning". Bata saurari amsarta ba tai gaba abinta. Haka kawai itadai Madam Chioma batai mataba, badan mahaifiyar Yoohan bace ba da lallai zamansu a waje ?aya zai iya haifar da matsaloli, dan a rayuwarta ta tsani wula?anci koda a wajen babba ne.
Da harara Momy ta raka bayan Aymah data koma kan aikinta batare da ta sake bi takansu ba. ?akin Yoohan kai tsaye ta nufa Abraham biye da ita. Sai dai koda ta tura ?ofar suka shiga sai taga wayam. Jikin ?ofar toilet taje nanma babu wani motsi, ta tura ?ofar ta le?a babu kowa a ciki, amma dai da alama anyi amfani da shi babu jimawa. Tunanin ko yana ?akin motsa jikinsa ne ya sata fitowa ta nufi can. Lokacin Aymah tana dining tana aikinta ko kallonsu batayi ba. Canma babu Yoohan, babuma alamar yau ya shigo wajen dan komai tsaf yake.
"K ina my son?".
Nu'aymah taji muryar Momy a bazata. ?ago dara-daran idanunta dake saka tsigar jikin Momy tayi tana kallonta. A yanayin halin ko-inkula tace, "Nima ban gansa ba tunda na tashi". Daga haka ta ?auki botikin ruwan mopping ?inta ta nufi ?akin Yoohan ?in danta gyara tunda taji baya a ciki.
Cike da takaici Madam Chioma ta bita da harara, kafin taja hannun Abraham su fice. Fita tai harabar gidan, dan sauranma duk sun fita harma sun shishshiga motoci.
Guards ?in Yoohan ?in ta shiga tambaya ko sunga fitarsa?. Solomon ya bata amsa da cewar ya fita tun ?azun ma, sunce zasu bisa yace baya bu?ata. Ranta a ?ace tace, "Baku da hankali, sau nawa nake jaddada muku kubar barinsa yana fita shi ka?ai?. Da wace motama ya fita tunda naga duk ga motocinsa?".
Kan Solomon a ?asa yace, "Sorry